Showing 30001 words to 33000 words out of 121675 words
ta koma gidan mijinta.
Gaba d'aya gidan Umma ya canja daga yanda kuka sanshi, babu wani farin ciki ko walwala tartare da ahalin gidan a yanzu, komai ya canja musu, kwata-kwata Jiddah tabar zuwa makaranta saboda damuwa.
Tuni Alhaji garba yakawo kud'i, Wanda Uncle yahaya yayta zabga masifa akan hakan. amma sai Abba ya yayyanka masa magana wadda tai masifar 6ata ransa ya janye hannunsa daga maganar Auren Jiddah.
Kwata-kwata sati hud'u aka saka bikin, koma tunanin Yaya batun karatunta baiyiba.
Su Zarah Kansu duksun fita hayyacinsu tamkar sune Jiddahn.
Ahaka aka cinye sati biyu, ana saura kwanaki 10 cif lefe ya iso, saboda Abba yabama Umma haushi saiyasa y'an kawo lefe suka Kai gidansa da Hindu ke ciki, Aunty Nafisa da Maman Sadiq ne kawai sukaje, sauran kam duk k'awayen hajia Hindu ne. Sai shak'iyanci sukeyi wai tsoho ya iya had'o kayan lefe.
Sosai lefen kam aka kashe kud'i dan komai yaji d'am, kaikace na saurayi d'an shekara 26 ne??.............???
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
*_Zaku iya samun RAINA KAMA a audio ta wancan link d'in Na sama, Abban dausayi YouTube channel tv??????._*
Yau babu magana????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu??????_*
[11/28/2019, 5:14 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[12.....]_*
..............Malam Mustafa yadamu kwarai da rashin ganin Jiddah a makaranta, dan da wahala kaga tayi fashi, inhar kuwa tayi washe gari sai kaga k'annenta sunzo sun fad'i dalili, kokuma idan itace tazo tafad'i abinda ya hanata zuwa.
Madina ma ta damu da rashin zuwan Jiddah, gashi ko gidansu bata saniba, dan duk iyakar shakuwarsu k'awancen iya makaranta ya tsaya, sai a yaumane takejin takaicin hakan.
Da aka tashi Malam mustafa yaso zuwa gidansu Jiddah, amma sai wani uziri ya rik'eshi, dole ya hak'ura akan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.
Saikuma da yamma malam yay kiranshi a waya akan yazo yana nemansa.
Bai samu ganin malam ba sai bayan sallar isha'i, dan ya iskeshi yana da bak'i. Bayan tafiyarsu yasamu gaisawa da malam.
"Mustafa dama akan yarinyarnanne, inaso asamo mana inda mahaifinta yake, dan inason ganawa dashi kafin musan abinyi".
"To malam, insha ALLAH zuwa gobe zanzo na sanar maka".
"To ALLAH ya kaimu da rai".
Washe garima malam mustafa bai samu zuwa wajen Jiddah ba, sai dai binciko Alhaji Zakari dayayi, gidansa da wajen kasuwancinsa.
Duk yanda akai malam mustafa yazo ya sanarma malam.
???????????
Jiddah dukta fige a tsaye, da kaganta kasan tana tare da damuwa, Umma takan danne tata damuwar tayita lallashinta da nuna Mata muhimmancin yadda da k'addara Mai k'yau ko sa6anin hakan, tareda tunatar da ita amfanin biyayya ga iyaye.
Da wannan shawawar warin ne Na Umma take d'an rage nauyin damuwarta, har yau take d'an ta6a aikin gyaran gidan saboda su Zarah suna makaranta.
Gaba d'aya bikin saura kwana shidda ne ya rage, amma bazaka ta6a cewa za'ayi wani biki bane agidan, dama Abba yace Umma karta sai komai, dan Alhaji Garba yace amarya kawai yake buk'ata, komai ya tanadar mata.
Wannan dalilinne yakuma saka Umma banzatar da zancen auren, tacigaba da yima d'iyarta addu'ar nema za6in ALLAH.
¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï
Biki ya rage saura kwana hud'u dangin Umma suka fara isowa, hakama su Aunty Sauda da aunty Zulai, kowa dai kagani babu wani d'okin auren a tattare dashi. Kowa dandai babu yanda zaiyine da lamarin Abba kawai.
??????.
Yayinda shirin biki keta kankama a gidan su Jiddah ga malam Abdul-ra'uff kam shirin zuwa Neman auren Jiddah suke ga Alhaji Zakari. Alhmdllhi sun sami isowa yana gida bisa jagorancin malam Mustafa.
Dukda Alhaji Zakari baisan mike tafe dasuba yaymusu tarba ta mutuntawa saboda ganin manyan malamai a gabansa, dukda gefen zuciyarsa Na zargin Jiddah ce takai k'ararsa garesu, shiko ya k'udiri aniyar mutuwar Jiddah ce kawai zata Hana ya aura mata Alhaji Garba. Amma duk saiya danne wannan zancen zucin nasa ya fuskanci su malam.
A nutse malam Salis yayma Abba bayanin abinda ke tafe dasu.
Abba dake masifa a zuciyarsa hace, "Ahaf zargina yazama gaskiya, to lallai dagaku har ita zanyi maganinku ne".
Kwantar da murya yayi a fili tamkar mutumin kwarai yafara magana, "ALLAH sarki malam gaskiya banji dad'in zuwan wannan magana Mai dad'i a k'uarraren lokaciba, dan abin farin cikine ga kowanne Uba yahad'a jini da malam, danasan da wannan kudiri naku daban amshi za6in Jiddah ba, yanzu haka maganar danake muku ranar asabar d'innance d'aurin aurenta wlhy".
Gaba d'aya jikinsu malam yayi sanyi, amma babu yanda suka iya, dan Neman aure akan nema bashida kyau, balle wannanma da aski yazo Gaban goshi.
Sallama sukaima Abba suka tafi, saidai gefen zuciyar malam mustafa bata aminta da maganar Abba ba. Shima Abban kuma ya tsargu da kallon da malam mustafa ke masa.
Dan haka suna tafiya yanufi gidan Umma, kiran Jiddah yay ya Kora Mata gargad'i akan wlhy idan wani malami a makarantarsu ya aiko koda kiranta taje saiya matuk'ar 6ata ranta sosai.
Da to ta amsa, takoma cikin gida tana hawaye. Umma kallo d'aya taimata ta d'auke kanta, bakuma ta tambayeta miya faruba.
Ana saura kwana biyu hajia Hindu ta maido lefen Jiddah gidan Umma, duk da ta kwashi abinda take so aciki babu Wanda ya gane sai aunty Nafisa da maman Sadiq da sukaga lefen. Amma koda sukai magana sai Umma tace subar zancen, ita ta sani, inma dai dai tayi inma sa6anin hakan kanta taimawa.
Aranar y'an Adamawa suka Iso, hakama y'an Barno, tuni gidan ya kacame da yaren Fulatanci da Hausa da kanuri, dolema sai kusan rabuwa akayi, dan gidan yamusu kad'an, wasu suna gidan Uncle yahaya wasu gidan Umma.
Gaba d'aya Uncle yahya ya kauda idonsa akan bikin dukda takaicin auren da tausayin Jiddah Na damunsa ainun.
Wannan biki dai ana yinsane kawai, amarya ma da k'yar tayarda akai mata k'unshi da kitso, gyaran jiki kam komai akace xa'ayi saita saka musu kuka tace bataso.
Tausayinta ke sakasu barinta. Duk wani shagali irinsu kamu babu Wanda akayi, dama ita bawasu k'awayene da itaba, y'an uwanta sune k'awayrnta da Ummanta.
Ranar d'aurin aure gida yagama d'inkewa tab, Amarya kam nacan karshen d'aki kudundune babu lafiya itadasu walida, kowanne zazza6i yamasa rijib, ko wanka basuyiba balle ai batun kwalliya.
Karfe 12 aka d'aura auren Alhaji Garba da Hauwa'u Jiddah akan sadaki naira dubu d'ari biyu.
Abin mamaki saiga Malam Abdul-ra'uff dasu malam mustafa sunzo d'aurin auren suma, saboda koba komai dai d'alibarsu ce, wadda sukeji da ita da alfahari da ita.
Tunda zancen d'aurin auren ya shigo cikin gida jikin Jiddah yakuma rikicewa, dole aka fita da ita zuwa asibiti.
Amma Kiri da muzu Abba yace wlhy ko suma take yau saita kwana gidan mijinta, shi yagaji da wannan iskancin.
Umma duk tana jinsa amma uffan bata ceba, dan itama tunda aka fara hidimar bikinnan cikin ciwon k'irji take, dannewa kawai take tana daurewa.
A asibiti sai da Jiddah tasha ledar ruwa uku, barcin data samune yasaka sauran y'an uwanta zabga tagumi sukai jigum-jigum, kowa shikad'ai yasan minene damuwarsa.
Anayin Sallar magriba Abba yazo asibitin yace a sallami Jiddah, dukda bayani da likita kemasa nason abarta tasami hutu yace Sam yanzunan yakeso, dan gidan miji za'a kaita.
Badan likita yasoba aka basu sallama suka dawo gida akahauma Jiddah shiri.
Koda akazo batun yimata fad'a Umma ficewartama tayi daga d'akin tana hawaye, amma bata bari kowa ya gantaba.
Dangi dai sun tofa albarkacin bakinsu nayima Jiddah nasiha akan abokiyar xamanta da mijinta harma da y'ay'ansa da danginsa.
Tuni Jiddah tabar kuka masu hawaye sai dai kukan zuci, a haka aka fiddota wajen motocin d'aukar amarya da akalla sunkai 25, dan haka kowa yasamu waje aka shilla da amarya.
Y'an anguwa wasu Na sambarka wasu Na tausayin Jiddah.
???????????
*Gidan Alhaji Garba mai tabarma* babban gidane sosai Wanda kallo d'aya zakai masa ka tabbatar da maishi ya tara.
Bayan an wangale musu k'aton gate d'in gidan kusan motoci goma suka sami wajen shigewa ciki harda ta amarya.
Tarba suka samu mai k'yau daga dangin Alhaji Garba, wad'anda suketa fatan ALLAH yasa wannan karon an dace Jiddah tazo kenan.
6angaren Jiddah aka kaita, Wanda ya k'awatu da kayan alatu tamkar suyi magana, komai yaji zam, duk had'uwar gidan Alhaji Garba da dukiyar cikinta hakan baisa dangin Jiddah jin zasu tayata murnaba.
Basu wani jimaba suka juya, akabar Jiddah ita kad'ai kudundune cikin hijjabi daboda zazza6i Mai tsanani daya sake rufeta.
Kusan mintuna ashirin da tafiyar y'an kawo amarya Jiddah tafara jin hayaniya sama-sama, abinda ya dameta shine matsalarta, dan haka bata damu kanta dasonjin mike faruwaba. Zuwa wani lokacima sai taji gidan tsitt tamkar babu kowa a cikinsa.
Tun tana sauraren k'arar AC har barci 6arawo ya saceta a haka, dama Allurar bata gama sakintaba.
*Ango*
Kusan k'arfe sha biyu da rabi ango yashigo gidan, lokacin gidan yay tsit kowa yakama gabansa, Daga y'ay'ansa sai matarsa hajiya deluwa.
Fakin motar yay yafito hannunsa d'auke da k'atuwar leda, Kai tsaye sashen Uwargida ya nufa Wanda yafi kowanne sashe girma a gidan.
Tsit babu motsin kowa sai AC da TV daketa faman aiki, ko ina tsaf tamkar ba taron biki akayiba, koda yake yasan babu wani Wanda ya Isa taka mata sashe da sunan zuwa biki. Ledar hannunsa ya ajiye yanufi corridor d'in dazai sadashi da d'akunan barcinta.
Na farko yafara lek'awa babu kowa, Na biyu ma haka, sai a Na uku ya hangota zaune a saman gado, hamshak'iyar macece wadda ta amsa sunanta Hajia, daka ganta kasan tagama jik'uwa cikin nera, ta girma sosai sanan tanada k'iba dai-dai gwargwado, dan bawata k'atuwa baceba can, Ammafa babu k'arya Y'ar gayuce, dan ko shirin barcin Nata kad'ai ya Isa tabbaatar maka hakan, gata Fara tas masha ALLAH.
Manyan idanunta ta sauke akansa, kafin tasaki wani murmushi cikin kissa tafara fad'in "Kaga ango Mijin Amarya Hauwa'u".
'Dan Murmushin yak'e Alhaji garba yayi, ya zauna kusa da ita k'asan zuciyarsa Na mamakin canjawarta akan wannan auren nasa, Ada inhar zaiyi aure zata d'aga hankalinta, randama aka kawo amarya bata Barin kowa yayi barci Mai dad'i a gidan, amma tunda yafara maganar auren Jiddah ko kad'an bata ta6a nuna damuwartaba, hasalima lefen Jiddah itace ta had'oshi matsayin gudun mawarta.
Fuskarsa d'auke da murmushi yad'an shafa kumatunta.
"Uwargida ran gida!".
Fari tayi masa da fararen idanunta, kafin ta furta "Fad'I kanka tsaye alhajina".
Yad'an dara, "Kinyi k'yau gimbiya ta, sai nakejima tamkar ked'in aka kawomin a yau".
Wani shegen murmushi ta Saki, "Alhajina rufamin asiri, kaga tashi katafi wajen matarka, kar zumud'in son ganinta yasaka juyemin kalaman daka tanada dominta anan wajen".
"Haba gimbiyata, aike kin wuce aimiki jirwaye da zancen wani, duk abinda yafito zuciyar Abubakar a kanki to lallai nakine, babu Mai kamanceceniya dake balle kamoki".
Murmushi takuma Saki tana kamo hannunsa ta sumbaci tsakkiya, kafin yagama dai-daita da shiga sak'on Nata ta haye saman gadon sosai taja bargo da fad'in "Ango mukwana lafiya, kadai bimusu yarinya a hankali karkai mata irinna hajarah, nasanka yanzu haka kaje ka d'irko magunguna".
Wata Y'ar dariyar mugunta yasaki yana mik'ewa, "Hajjaju akwaiki da tsokana wlhy, ni sharri kikemin babu wani magani danake sha, Na barki lafiya".
Cikin watsama bayansa harara da murmushin mugunta tace "A gaida amarya".
Fita yay yana fad'in "zataji".
Daga nan sashensa ya nufa Wanda shima ya had'u, sai dai baikai girman Na hajiya deluwa ba ko kad'an, had'uwa kawai zai iya nuna masa.
Sai faman zabga murmushi yake yana cire kaya. Wanka ya shiga kusan mintuna talatin sannan ya fito, ya saka jallabiya bayan ya goge jikinsa, yakawo turare ya fesa. Ledar daya shigo da ita ya bud'e yaciro wata karamar leda aciki, saida ya bud'e firij ya Ciro gorar ruwa sanan yakoma bakin gado ya zauna yana zazzage abinda ke ledar saman gadon, magungunane masu d'an yawa, ya 6alli kusan kala shida ya shanye yana zabga murmushi, sai shafar gemunsa dayasha aski yakeyi, tashi ya kumayi ya d'auki wata gorar da aka had'a tsumin magungunan gargajiya a ciki nanma yasha sosai sanan ya d'auki babbar ledar ya fito zuwa sashen amarya Jiddah.
Lokacin daya shigo sashen Jiddah tsit nanma, dan ita koma TV babu a kashe komai yake, sai k'amshi irin wanda akasan d'akin amarya dashi.
Bakinsa har k'arshen kunne ya Isa bedroom d'in Jiddah, sai wani lasar la66a yake tamkar tsohon maye????............???
Kuyi manage please, yau banajin typing??
Yau dai nasan Naga idi??????¡â
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[11/29/2019, 3:24 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[13....]_*
..............Tunda ya shigo idonsa nakan Jiddah k'yam, duk da a kudundune take da hijjab hakan bai hanashi jin wani farin cikiba, haryay tuntu6e da gado kad'an yarage ya fad'i, yadai samu ya dafa gadon.????
Ledar hannunsa ya ajiye saman dirowan gefen gadon kafin ya zauna a bakin gadon shima yana fad'in "Amarsu ta ango mai dad'in tuwo! Nidai abud'e fuska indai bakine nasayi abuna dubu d'ari kash".
Jin Jiddah tayi shiru bata amsaba yakai hannu ya janye hijjabin, wani hucin zafine ya bigesa, yayinda sanyin AC kuma ya shigi Jiddah tahau kankame jikinta. 'Dan canjawa fuskarsa tayi, yace, "K Jiddah tashi"..
Jiddah dake jinsa sama-sama tad'an bud'e idonta kad'an ta kalleshi, saikuma ta maida ta lumshe tare da k'ok'arin jan hijjabinta daya janye......
Tsawa ya daka mata, wadda tasata mik'e babu shiri, dama Jiddah akwai d'an banzan tsoro, dan haka jikinta keta k'yarma tana hawaye da karanto duk addu'ar datazo bakinta.
'Dan sassauta fushinsa yayi ganin ta rud'e, ya kwantar da murya yana fad'in "Bakida lafiyane?".
Kai ta d'aga masa alamar eh.
Shiru yay yana kallonta, danshifa gaskiya bazai iya hak'uri ba, yanda yay savise d'innan ace yatashi a banza ai akwai babbar matsala. Gyaran murya yad'anyi yakai hannu zai Kama nata, amma sai tayi saurin janyewa, yad'an murmusa da ta6e baki, "Kinga da safe likita idan yazo dubaki zai had'a yabaki magani, dan nikamdai yau babu fashi saina more sadakina. Maza tashi kicire kaya, koda yake kefa malamace yo alwala mufara salla".
Kan Jiddah a k'asa ga hawaye na zirara da Uban tsoro fal ranta tamkar zuciyarta zata faso k'irji ta fito.
Harara ya zabga Mata, kafin yay Mata magana ad'an tsawace. Ai babu shiri ta rikito daga gadon, dukta rikice tarasa ina zata dosa, wannan yasaka dukkan illahirin jikinta motsawa saboda babu hijjab, sanye take da riga da zani nawani yadi ruwan goro, kayan sunmata d'as a jiki, dan dai-dai gwargwado ALLAH yayma Jiddah cikakken jiki da sura, danma damuwa da ta sakata ramewane yanzu.
Gaba d'aya sai jikin Alhaji Garba Yakama rawar jaraba, sai faman lasar la66a yake saboda yakai makurar buk'atarta, maganin daya loda sha yanzu magani yanzu ne, sune karfinsa ga mace, inbabusu babu uwar dazai iya daboda shekaru sunja garesa sosai, dak'yar ya iya Mata nuni da hanyar band'aki dake cikin d'akin, ta shiga.
Bata damuba da kallon band'akin, fitsarin da dama