Showing 90001 words to 93000 words out of 121675 words
Cikin gamsuwa da dogon bayanin Jiddah Aliyu ya dakatar da ita ta hanyar rik'e hannunta a nasa yana fad'in Masha ALLAH, ALLAHU Akbar, ALLAH yayi miki albarka, ya k'ara ilimi mai amfani".
"Amin" Jiddah ta amsa a saman la66anta.
Hannunta ya saki ya mik'e tareda mik'ar da ita, batareda yayi magana ba yafita, hakanne yasaka Jiddah saurin hayewa gadon ta kwanta batareda ta cire hijjabinba, mintuna kusan goma saigashi ya dawo hannunsa rik'e da Kofi. Idonsa akanta ya zauna bakin gadon, "Nasan dai bakiyi barciba, Taso ki gani".
Tamkar Jiddah zata fasa ihu haka ta mik'e zaune, sai dai takasa kallonsa, matsawa yay sosai yahau gadon, yanda ta zauna k'afarta a tankwashe shima sai yayi haka yana mik'a Mata kofin.
"ALLAH banajin yunwa fa".
Cikin kuma sanyaya muryarsa yace, "Wannan badan yunwa ake shansaba, ana shane domin koyi da sunnar MANZON ALLAH (S.A.W), tun a daren jiya yadace nashigo dashi, amma kasancewar ban samu kainaba shiyyasa ban kawoba, ina fatan za'amin afuwa".
Dole Jiddah ta amsa ta kafa Kai tasha kad'an ta mik'a masa, kansa ya girgiza Mata damata nunin ta k'ara. Babu yanda ta iya tak'ara sha sannan ta bashi. Yanzunkam amsa yayi shikuma ya shanye sauran sannan ya ajiye kofin.
"Mu kwanta mu huta dare yayi fa" Cikin mintuna kad'an duhu ya mamaye d'akin saboda kashe fitilar da yayi, itadai Jiddah ta kwanta, jira take taji yace mata sai da safe, amma taji tsit.......
Kwanciyarsa kusa da itace yasaka tunaninta katsewa, tad'an muskuta zata matsa ya ruk'ota jikinsa, wani irin tsuma taji jikinta Na Mata ga tsoron dake k'ara girma a ranta.........
A cikin kunnenta yake fad'in "waya fad'a miki Matar aure na kwanciya da hijjab?".
Muryar Jiddah na rawa tace, "Sanyi nakeji ai".
"Karki damu ga bargonki yazo".
Abubuwan da suka cigaba da biyo baya sun kasance babban al'amari ga Jiddah, tun tana 6oye kukanta harya fahimci tanayi, sai dai ko kad'an babu gaddama ko jayayya daga gareta. Lokacin da ya sheikh yanufi k'ofar da yake tunanin samu abud'e saiya isketa 6am da kwad'o, dukda yadad'e yana zargin hakan baigaza shiga al'ajabiba, hakanne ya sakashi dakatawa daga yunk'urinsa, har Jiddah tafara murnar yabartane saitaji ya sake sabon salo, dan fahimtar sabuwace ya sakashi Binta a salon da bazata cutuba, zuwa wani lokaci kuma UBANGIJI yay ikonsa wajen bama ya sheikh dama wajen mallakarta a matsayin matarsa halalinsa.....
¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï
Shine ya Fara farkawa sabodajin kiran sallah, ya lalubo wayarsa a durowar gefen gadon, mamaki ya kamashi ganin sun makara, dan sallar shigama ake Kira, "Ya Salaam" yafad'a yana dafe kansa, yasan dolene su makara, dan basu kwanta da wuriba, fitilar wayar ya haska yana janye Jiddah a a jikinsa ya tashi zaune, itama d'in ta farka tunda ya motsa, amma saita kasa yunk'urin tashi tayi luf. Fuskarta yad'an haska tai saurin jan bargo ta rufe. Murmushi yayi yana fad'in "Rowa za'amin amarya?".
Itadai k'in bud'ewa tayi, saida taji yashiga bayi sannan. Bata saukaba harya fito yakuma dawowa gaban gadon, laimar hannunsa yad'an shafa mata, "Idan zaki iya tashi kiyi alwala, naje masallaci kinga Na makara".
Kanta kawai ta iya d'aga masa.
Fita yay, a gaggauce ya lek'a Maimuna ya iske itama ta tashi, baiyi maganaba ya juya ya fita da hanzari.
Tashi Jiddah ta daure tayi dukda yanda takejin jikinta, danma ya taimaka Mata sosai tunda daddare ya gasata da ruwa mai d'umi sosai tareda bata dukkan taimakon dazataji sassauci. Kallo d'aya zakai Mata ka fahimci tafiyarta ba dai-dai takeba, hakadai ta daure ta d'ingisa tasake d'anyin tsarki da ruwan zafin daya rage a cikin filas d'in, sosai takumajin dad'i, alwala ta d'auro ta fito.
Yaukam tana idar da sallah takoma saman gado ta kwanta, azkar ma azuciyarta tayi Wanda ta rik'e harma barci yakuma kwasheta.
Koda Aliyu ya dawo sashen Maimunatu yakona, dukda zazza6in ya sauka hakan bai hanashi tarairayarta ba da nuna Mata kulawa, yace ta shirya suje asibiti, amma saitace a'a yabarshi tunda zazza6in ya sauka, dole ya barta amma ya hanata shiga kicin yace ta kwanta ta huta.
Murmushi kawai taimasa, yana fita tatashi tashiga kicin, dan aganinta bai dace su zauna da yunwaba ai, itakuma Alhmdllh tanajin jikin nata da sauk'i.
Zama yay a bakin gadon kawai ya tsurama Jiddah idanu, bacci take, yakai hannu ya shafa fuskarta zuwa saman idanunta da suka kuma kumburowa saboda kukan datasha.
Hakanne ya saka Jiddah farkawa ta bud'e idanunta tamasa kallo d'aya ta maida idonta ta lumshe, fuskarsa d'auke da murmushi ya furta, "Dama ba barci kikeba".
Tamkar zata nutse dan kunya, dukda Idonta a rufe suke ba kallonsa takeba, da k'yar tace, "Barci nakeyi" tayi maganar Idonta na cika da kwalla, dan duk a takure take da zamansa wajen.
Bai ankaraba yaga hawaye Na gangarowa a fuskarta.
Yace, "Ya salaam khairunnisaa! Kukannan dai bazai k'areba, ayi hak'uri Aliy yayi laifi yau mai girma ko?". 'Yay maganar yana kwantowa jikinta da d'ora goshinsa akan nata, cikin kuma k'asa da murya sosai yake fad'in,
*1 ???? ????? ????.2???? ???? ???? ???? .3???? ????? ????? ?????? ???? ??*
_"ALLAH yakareki hasketa 2.allah ya haskaka zuciyarki .3allah yakiyayeki da Sauran matan duniya gaba daya"_.
"Wannan shine mafi alkairin kowacce mace, shine mutuncinta da kimarta a wajen miji, duk wadda taje gidan aure babushi tagama asarar daraja da kimarta, sai dai wadda ta kasance a k'addarar zalincin fyad'e, ALLAH yabaku ikon bama y'ay'ana tarbiyyar da suma zasu kasance kamilallu kamar yanda kuka kasance Mata kamilallllu salihai".
Haka yayta fad'i Mata dad'ad'an kalamai da suka sanyaya ranta har barci yakuma kwasheta, ya d'an sauke ajiyar zuciya yana sumbatar la66anta da saman idonta zuwa goshi, shikam babu abinda zai cema Ubangiji sai godiya, shine buwaya gagara misali daya azurtashi da wad'annan mataye nagartatttu, samun Maimunatu matsayin cikakkiyar budurwane yasaka ginuwar k'aunarta a ransa, wadda har gobe take k'ara yad'o, a daren jiya kuma yakuma gamo da abin mamakin dabaiyi zatoba, shida ya auri bazawara saiyaci Karo da budurwa fil a Kwali, juyawa yay yasake kallon Jiddah dake barci yay murmushi.............???
*_kwace anya kuwa wannan matar zata cika mana alk'awari??._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????
[12/24/2019, 10:03 AM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[49?50]_*
..........Kasancewar yau mafi yawan bak'in suka wuce sai Umma tasamu damar zaman k'irga y'an kud'ad'en data samu a wajen dangi na gudunmawa ita dasu Aunty Hannatu, bayan sun kammala sukayi d'an lissafin abinda Jiddah bata dashi za'a Kai Mata, walida dake rubutawa ta kalli su Aunty Nafisa cikin kwantar da murya tace, "Auntys dan ALLAH baza'a sayama Yaya Jiddah freight ba wai?".
Duka Umma takai mata tana fad'in, "Walida ki kiyayeni wlhy, Ubanki yabani kud'in? Yanzu kina gani dai a gabanki aka lissafa kud'in duka nawane ya rage a ciki".
"Kiyi hak'uri Umma badan ranki ya 6aci na fad'aba, ni dama dan nagafa kishiyarta nadashine, sainaga itama da da hali sai a saya mata ko k'aramine".
"Humm Walida kenan, bakisan mutuwar mageba sai kinga tana shure-shure, dan kawai abokiyar zamanta nadashi sai akace itama dole sai an saya mata? Tomu bagasa zamuyi da waniba, abinda ALLAH ya hore mana dashi zamuyi amfani".
Dariya duk sukayi, Aunty Saudah tace, "ALLAH Umma maganar Walida abar dubawace, badan gasa za'a saya mataba, kinga kodai Sana'a tayi da kayanta ai, amu talakawa ajiye firij ai badan gayu muke ajiyewa ba, ina ganin mizai hana acire a sadakin Jiddah sai a saya ko Wanda bai wuce dubu arba'in baneba zuwa hamsin haka".
A take kowa ya aminta da maganarta, Yaruwaiya tace, "Kumafa gaskiyane wlhy, inaga hakanma shi kawai za'ayi, amma afara sanarma kawunku yahya sanan, saimuji shi mizaice, mace babu sana'a ai akwai matsala, randa miji yatashi baidashi sai kowa yay zuru-zuru, irin wannan ke kawo yawan husuma kuma wlhy, shi yana wuya saboda talauci kaima kana mak'ogwaro, abu kad'an zai hasala kowa ya fusata saikiga anyi sama".
Umma ce ta d'auki waya ta Kira Uncle yahya, cayay mata gashinan a hanyar gidan ma. Tana ajiye wayar babu jimawa saigashi yazo. Bayan an gaggaisa Yaruwaiya tamasa bayani, 100% ya yarda da shawarar, danshima aljihun nasane yayi k'asa, amma harga ALLAH yayi niyyar siyama Jiddah duk abinda yadace mace ta bud'e ido tagani a d'akinta, musamman abinda za's iya Mora har a sana'a.
Bayan sun gama tattaunawane yasamo musu motar dazata kwashi sauran kayan Jiddah da akwatinanta da kayan gara dadai sauran tarkace.
Umma kawai aka bari a gidan sai wasu tsoffi uku danginsu Jiddah 6angaren su Abba, su Balu, aunty Zulai, aunty hannatu, Walida, suka wuce gidan Jiddah. Maman Sadiq, Yaruwaiya, aunty Saudah, Aunty Nafisa, sai Zarah suka wuce kasuwa k'arasa sayo abinda ya rage Na Jiddah.
???????????
Ikon ALLAH ne kawai yakawo Abba kano, ammafa wujiga-wujiga ya Iso saboda 6acin ran da yake a ciki.
Su Hajia Hindu na zaune a Dani itada yara suna dinner ya shigo ko sallama babu, Maneer yatashi da gudu yaje yana masa oyoyo. Rik'e hanunsa yayi kawai amma yakasa magana, saima wata uwar harara daya zubama su hajia Hindu itada yaran, "yanacan yana wahala su sunanan hankalinsu kwance", dan duk sunwani zubo masa idanune amma babu Wanda yace masa koda sannu.
Tsaki yaja yana sakin hannun Muneer yashige abinsa. Hajia Hindu ta ta6e baki tana d'auke kanta. Shima Hussain bakin yad'an ta6e kafin yace, "Wai Mom mi akaima Dady ne daga dawowarsa?".
"Ina Zan sani Hussain, ai tare muke daku anan ya shigo".
Dariya Kalifa yayi yana fad'in, "ku nifa kwana biyunan gani nake kamar Dady a rikice yake, kokuma rud'un tsufane oho".
Dariya suka sanya gaba d'aya, Hajia Hindu ta mik'e tana, "Kai yaranan ALLAH ya shiryeku, kodai tsohonne ma ai ubankune dai, bara naje naji mike faruwa".
Kwance ta iske Abba hannunsa dafe da kansa, zama tayi gefen gadon kusa dashi, "Abban kalifa lafiya kuwa?".
Banza yay mata tamkar baimajiba, saida ta maimaita sau uku kafin ya janye hannunsa ya kalleta da idanunsa dake jajur, sai dai yagaza cemata uffan.
Hakanne yad'an tada hankalinta, takuma maimaita masa tambayar.
Mik'ewa yay zaune yanajan guntun tsaki, "Yanzu nan Hindu na d'auki tsawon kwana shiddah bana gidannan, amma nadawo kuna kallona tamkar wani kashi, wane iron rainine wannan?".
cikin kwantar da murya ta kallesa, dan zatonta koya samo kud'inne, shiyyasa ta aro sabon ladabi, "Ohni Hindu, yanzunan Abban kalifa wace irin maganace wannan dan ALLAH? To kayi hak'uri, wlhy mamakin yanda kashigone yasanyamu yin hakan, yaya Abuja? Ina fatan dai andace da samun kud'ad'en?".
Jin yanda ta kwantar da murya sai Abba ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta "Bansan yanda zanyiba Hindu, ina cikin tsaka mai wuya, kud'in danaje nema ban samoba, dolene a darenan naje na turke Y'ar iskar yarinyarcan yaronan ya saketa, nasan inhar Alhaji garba yaga zata dawo gareshi zai hak'ura ya barni".
"Hummm Alhaji kenan, to ai daga baya kenan wannan, komafa miye ya faru laifinkane, Kaine ka 6ata komai a randa Alhaji garba ya kiraka, sannan nabaka shawarar musanya masa da Zarah, amma sai kak'i saurarena, to ai yanzu bakada hurumin rabama Jiddah aure kuwa balle bashi ita, dan ta tare tunma shekaran jiy....."
A zabure ya mik'e, "k ban fahimcekiba? Ni da raina za'akai y'ata gidan miji ban saniba?".
Baki hajia Hindu ta ta6e tana masa wani kallon rainin wayo, balle taji babu kud'in, "Oh kajimin Abban kalifa fa, yo yaune karan farko da aka Fara Kai y'ay'an naka gidan aure bada saninka ba? Naga ko hannatu sai dama tayi wajen wata biyu da aure ka sani, Zulai kuwama saida takusan haihuwa".
Hannu yakai tamkar zai maketa saikuma ya fasa, ya bangajeta ya wuce zuwa bayi. Bayansa ta raka da harara tana k'ya6e baki, saima ta fice abinta kawai tabar masa d'akin.
???????????
Kamar da wasa k'aramar magana saita zama babba, dan tsawon kwana uku Alhaji garba ya gagari hajia deluwa sakawa a ido, tunda ya shige sashen amarya a randa aka kawota bai sake ko lek'o wajeba, sallama agida yakeyi, abinci kuwa bashida Matsala, dan amarya ke musu daddad'en girki, cikin k'awayenta takira tabada umarnin ayo musu cefane mai yawa, wannan yasa suka kuma yima hajia deluwa nisa, sai dai tajiyo sautin kid'a Na tashi, knocking kuwa tayi har hannunta ya gajiya, tayi wujiga-wijiga da ita, nutsuwa ta gagareta, takira malam Na marwa yafi sau dubu amma wayar yak'i shiga, komai saiya kuma harmutse Mata. Su Kansu su Ashir sunma kasa gane kanta kwata-kwata, gefe kuma su hajia Hindu k'awayenta na kuma tunzurata a waya.
Aiki ya samu mata??
???????????
Sai wajen sha d'aya Jiddah ta farka, ta tashi kuma bata samu Sheikh Aliy a d'akinba, hakanne ya sata d'anjin dad'i, yunk'urawa tayi zaune da k'yar, dan jikinta duk ciwo yake Mata, ji kawai tayi hawaye suna zirara Mata, yanzu nan wannan abunne har kesa mace yin zina?, miye abin dad'i anan banda bak'ar wahala? Wai a hakanma shi bawani gama shigarta yay gaba d'aya ba kamar yanda yafad'a, tayi kusan zaman minti talatin tana hawayenta, Wanda dalilinsu yafi k'arfi a kewarsu Ummanta, sakkowa tayi a gadon zuwa bayi, tasamu takumayin tsarki da ruwan zafi tayi wanka, lokacin walha ya wuce, hakan Yakuma sakata takaici.
Saida ta shirya sannan ta gyara d'akin tasaka turaren wuta, takardar data gani saman mirror ta d'auka ta karanta.
_Ina fatan tashinki cikin aminci da farinciki Aglan Nisaa (Mafi tsadar mace) amin afuwa na fita saboda wani uziri, ga abinci nan a falo auntynki ta kawo miki, Ku yini cikin aminci da kariyar ubangiji matana._
Guntun murmushi tayi tana had'iye hawayen da suka cika idonta, ta linke takardar ta ajiye sannan tafito. A falo ta iske abincin karin kumallonta daya ce, bata cutama kantaba ta zauna taci dai-dai iyawa tasha maganin daya ajiye Mata. Tanason zuwa ta duba Maimuna amma tanajin kunyar tafiyarta, haka ta zauna shiru harma takai da kwanciya cikin kujera ta fad'a duniyar tunani.
A wannan yanayin su Walida suka iso suka sameta, wani farin ciki Na musamman ya kamata, ta tashi cikin hanzari domin tararsu, sai dai taku biyu tayi tatsaya cak saboda kallon dataga sun tsaya sunama k'afafunta.
Aunty Hannatu dayake tanada hankali saita basar dasu ta hanyar zuwa ta rungume Jiddah.
Jiddah tad'an sauke ajiyar zuciya dan a ganinta k'ila basu fahimci abinda take zarginba.
Kayan hannunsu suka ajiye suma sauran sukazo suka rungumeta, kafin su saketa su kuma fita kwaso sauran kayan.
Maimuna dataji hayaniya ta fito, dan dama tun d'azun take d'an zagayo Jiddah taga kota tashi, Aliyu yace Mata kanta ke ciwo, dukda zuciyarta ta sosu da tunanin wani Abu daban hakan bai hanata lek'owa taga kota tashiba.
Da fara'arta takemusu sannu dazuwa. Suma suna amsawa fuskarsu d'auke da Fara'a, koda tace zata tayasu d'aukar kayan sai Balu ta hanata, dukda haka saida ta amshi agogon dake wajen Aunty Zulai suka k'arasa falon Jiddah.
Jiddah Na ganinta tai k'asa da kanta tana wasa da yatsun hannunta, dan ita gani take kamar Maimunatun tasan abinda sukayi a daren jiya.
"Ashe kin tashi K'anwata, tun d'azun nake zagayenki amma saina iske kina barci".
Batare da Jiddah ta kalletaba tace, "eh wlhy aunty, maganin murar Dana Shane yasani barci".
"Dama yace kanki ke ciwo, yanzu dai ya daina ko?".
"Eh ya daina Alhmdllh".
"To ALLAH ya k'ara afuwa, sannu".
"Yauwa aunty, kema yanaki jikin?".
"Alhmdllh".
Su Balu ma duk sukaima Maimuna ya jiki bayan ta zauna sun kuma gaisawa cikin mutunta juna, mik'ewa tayi ta