Showing 42001 words to 45000 words out of 121675 words
kuka jikinta Na kuma tsananta rawa, "Uncle kayi hak'uri, wlhy banason ganin maza ko muryarsu banason jiiiiii!!!!!!!". 'Ta k'are magar cikin razananniyar tsawar data gigitasu'.
Dole sai fita Uncle yahya yayi, yana fita kuma tafara dai-daita, a hankali saita dawo normal, jikin Zarah dake kusa da ita tafad'a tana kuka, suma su Zarah kukan sukeyi.
A waje Uncle yahya da Umma suna magana ne akan ya Kira Abba ya sanar masa halinda Jiddah take ciki amma yace wai k'arya takeyi, dan haka shikuma ya faffad'a masa magana akan wlhy koda zasuyi yak'i Jiddah bazata koma gidan Alhaji garba ba, dolene ya saketa koyanaso ko bayaso.
"Kamin dai-dai Uncle d'insu, wlhy a shirye nake da igiyar aurena ta tsinke akan komawar Jiddah gidancan, acikin sati uku kacal an maidata haka inaga nan gaba kuma?".
"Ki kwantar da hankalinki Maman Nafisa, nima ina dai-dai dashi ai, dan yace gobe zai dawo daga legas d'in".
"ALLAH ya kawoshi lafiya". Cewar Umma a zafafe.
*_HARGITSI_*.
Dolene mukira wannan tsakani da suna hargitsi, dan kuwa komai ya rikice, ga jikin Jiddah da yak'i dad'i, dan koda maganar Abba daya dawo washe garin dawowarta gidan Alhaji Garba taji to zata fara fisge-fisge da k'ara.
Tsakanin Umma da Abba da Uncle yahya kuwa anyi barank'an-barank'an, dan Abba yaje ya duba Alhaji Garba a asibiti ya shirys masa k'arya da gaskiya akan Jiddah, yayinda hajia deluwa ke tunzurashi a gefe.
Umma da Uncle yahya sun dage sai Alhaji Garba ya saki Jiddah. Alhaji garba ya kafe akan wlhy bazai ta6a sakintaba. Abba ma yadage sai Jiddah ta koma, dan shima akwai nasa dalilin Mai tada hankaki.
Lamari yayi tsamari sosai, yau kusan kwanaki takwas da Fara badak'alar amma babu wani sassauci, hakanne ya saka Uncle yahya shigar da Alhaji Garba kotu domin raba auren Jiddah.
Alhaji Garba yasamu sauk'i harya koma gida, dan haka gidansa akakai masa sammaci.
Sosai hajia dealuwa ke zubar masa tijara akan ya Saki Jiddah mana, aiba girmansa bane ace yashiga kotu akan wannan banzan maganar.
A zafafe yace, "ke Yahanasu, nifa ba auren wannan yarinyar bane matsalata, kud'ina da Ubanta yaci sune matsalata, kinsan nawa ya amsa a wajena kuwa? To naira miliyan Hamsin, ya amsa yabiya banki bashin da yaci, bisaga wannan ne yabani aurenta akan zai biyani rabi nanda shekara biyu, nikuma nace Na hafe masa rabi, dan haka saiya biyani kud'ina Zan saketa".
"Humm wlhy Alhaji ban ta6a sanin Kai mayen Mata baneba sai yau, akan mace ka d'auki wannan uwar dukiyar ka bashi? To bara Na fad'a maka, rashin sakin y'arsa ba shine mafitaba, dan dama can bason Y'ar yakeba, kobakaga damuwarsama ta dawoba a kullu? To ka saketa, nikuma Zan baka dabarar da zakayi kud'inka su fito cikin sauk'i a hannun Alhaji zakari yaro".
Jimmm Alhaji Garba yay yana kallonta, saikuma ya gyara xamansa yana fad'in "kamar kuma Na yarda da shawararki, ke nama yarda, samomin takarda da alk'alami".
Da hanzari hajia deluwa taje ta d'akko masa, dandanan ya zana Saki a takarda yabata yace tabama driver yakaima Alhaji Zakari.
*_SANADI_*
Wannan shine sanadin rabuwar Alhaji Garba da Jiddah.
Su Umma Na tsakar gida zazzaune, Zarah da Walida na wanke-wanke, Umma Na girki yayinda Jiddah ke kwance akan tabarma tayi shiru tana tunanin rayuwa da yanda al'amura suka sauya cikin wata biyu kacal. Sallamar Abba ce ta sanyata mik'ewa zumbur, da gudu ta afka d'aki tajecan karshen gini ta 6uya. Yanzu haka take, ko Uncle yahya ne ya shigo saita gudu ta 6uya, addu'oin da malam alfah ke bata tanasha yasa aka samu rangwame tabar yawan k'ara, amma idan Namiji yacika kusantota tana wannan fisge-fisgen harma ta suma.
Cikin hargowa Abba ya jefama Umma takardar sakin Jiddah yana fad'in "Hankalinki ya kwanta yagana, kin kashema Jiddah aure, saiki zuba ruwa a k'asa kisha kinji ko, itakuma daga yau dan Ubanta saita dainama mutane haukan k'arya, kuma wlhy kinji Na rantse Na zare hannuna daga duk wani lamarin Jiddah, ta nemi wani uban baniba d........"
Cikin katseshi Umma ta d'aga masa hannu "Ya Isa haka Alhaji, dama baka a lamarinsu, dankuma ka fita yanzu bazanji komaiba, amma ina Mai tabbatar maka, ko watan watarana katina wannan maganar taka, sannan ka fad'ama Alhaji Garba, ina godiya matuk'a ni yagana akan sakarmin yarinya da yayi, kaikuma ka gane TUBALIN TOKA baya k'arko, duk abinda ba'a ginashi domin ALLAH ba to baya k'arko, abinda kuma akaima yarinyata nabar wannan ga ALLAH, shine zai Mata hisabi da koma wanene".
Umma nagama fad'a tai shigewarta tabi Jiddah, sukam su Walida dama tuni sun shige ai, daga d'aki suke jiyo abinda ke faruwa.
Kwafa kawai Abba yay batareda ya iya cewa k'alaba, sai yanaji a ransa badan ALLAH ya Isar da mamansa taimasa akan yagana ba da wlhy yau itama Saki Uku zai Mata, to amma anriga an saka masa Kara da hakan.
Duk wani masoyin Jiddah ya tayata farin ciki da wannan Saki, washe Gari da aunty Nafisa tazo itakam harda rawarta tasha su Zarah na tayata, Jiddah da Umma sai dariya suke musu.
Tuni maganar sakin Jiddah ya karad'e dangi, kowa yaji dalili saiya tayata murna da hakan, tareda nemawa abba shiriya wajen ubangiji.
A yanzu matsalar Jiddah ta tsoron mazace kawai matsalarsu, dan har yanzu bata shan inuwa da koda sautin muryar mazane, iya kokari kuma ana maganin akan warware sihirin jikinta, amma lamarin ba'a cewa komai sai sambarka.
Abba dai ko sisinsa babu balle tambayar Yaya Jiddah hasalima yabar zuwa gidan gaba d'aya, shi a dole fushi yake, sannan ciwon Jiddah yace k'aryane. Kokad'an hakan baya damun Umma, dan a cewarta wannan matsalarsace.
Alhamdllh jikin jiddah yad'an murmure daga ramar da tayi, saidai kulum tana gida bata fita ko ina, zuciyarta nason komawa makaranta, amma tanajin tsoron yanda zata fiti taci Karo da abokan gabarta maza.
Ahankali kuma farin cikin gidansu ya dawo, sunkoma tamkar da, saima ka d'auka wani tashin hankali bai ta6a ziyartarsuba a kwanakin baya, yanzu fatansu kawai ALLAH yabama Jiddah lafiya ta koma normal.
*_A KWANA A TASHI_*
babu wahala wajen Ubangiji, yau ga Jiddah tagama iddah, har wani d'an walima su Zarah da aunty Nafisa suka shirya Na murnar Jiddah tarabu da alak'ak'ai.
Umma dai dariya kawai suke bata, Uncle yahya harda taya 6era 6ari kuwa shida maman Sadiq.
???????????
"Mustafa yanzu ya kake ganin zamuyi akan maganar wadda zataje musabak'arnan ta Saudia tunda yanzu babu yarinyarnan? Kagafa wasu kwanakine kawai ya rage Wanda bazasu gaza ashirin da biyu ba, a ko yaushe kuma za'a iya buk'atar ganinta ma".
"Wlhy malam nima abun Na damuna, shiyyasa nake kuma takaicin rashin Jiddah, amma yanzu inaga zamu samu wata d'alibar mukuma horata kawai".
"Eh to shawararka tayi sosai, ALLAH yasa mu dace".
Ameen Malam mustafa da Sheikh Aliyu dake zaune yana saurarensu suka fad'a.
Daga nan wani zancen suka d'akko, mafi yawa akan gudunmawar da Jiddah tabama makarantarne Na ciwo musabuk'ok'i kashi-kashi da tayi. Shidai Aliyu na zaune yana nazarin wani littafi yana saurarensu, amma k'ala bai tofa ba, dan ba huruminsa baneba. Sai dai k'ok'arin yarinyar ya burgeshi kamar yanda su malam suke fad'a dukda bai santaba.
???????????
Yau Su Zarah duk suna makaranta, gashi Umma nason yin aike shago, Dauda kuma baikai ga zuwaba, rasa yanda zatayi tai, ta lek'a kozata samu yaro amma layin fetal yara duk suna makaranta. Dawowa tayi ta kalli Jiddah daketa hidimar d'aura abincin rana.
"Jiddah koda kanki zaki fita dai siyen yis d'innan, kinga nariga nafara kwa6a fulawar alkubus d'inan, ki lek'a konan shagon sama'ilane, idan kuma kingamu da wani yaron saiki bashi ya sayo".
"To Umma kawo naje d'in". 'Jiddah tafad'a tana d'auraye hannunta data ta6a gawayi'. Tana gamawa ta kar6a naira d'arin hannun Umma taja hijjab a igiya ta fita bayan ta d'aura Nik'ab tamkar yanda ta Saba.
Dukda tsoron dake addabarta da tsumar da jikinta yafara haka ta k'arasa shagon sama'ila, da k'yar ta iya mik'a masa kud'in tana fad'a masa abinda takeso, lokacin daya mik'o mata hannunsa yad'an ta6a Nata kad'an sai kawai tai baya jiki Na rawa, bai ankaraba kawai yaga ta zuba da gudu tabarsa rik'e da yis.
Mamaki da al'ajab suka kamashi, dan haka yabiyota yana kwala Mata Kira, amma ina gudu take iya karfinta.
Umma Na gyara mata wutar sai kawai gani tai ta shigo a guje, tana tambayarta lafiya amma bata sauraretaba ta afka d'aki. Umma na shirin binta Sama'ila mai shago ya rabga sallama daga soro.
Wata razananninayar k'ara jiddah ta fasa tana toshe kunnenta. Tuni hankalin Umma ya tashi, dan ita tashagala Jiddah ta samu sauk'i sosai, dan tadad'e batai irin wannan firgitar mai karfi hakaba.
Jikin Umma na rawa ta lek'a dantaga wake sallama, ganin sama'ila saitake tambayarsa komi yafaru da jiddah?, iya abinda ya sani ya sanar mata, sannan yabata yis d'in ya juya.
Dole Umma ta kira Uncle yahya a waya, babu shiri yabaro kasuwa, tsayawa yay suka taho da malam alfah.
Tunda suka shigo gidan malam Alfah yaga halin da Jiddah take ya girgiza Kai kawai.
"yahaya inaga yakamata mukai Jiddah wani waje, bak'in aljanin da suka had'ata dashi yanada matuk'ar naci, tunda munyi namu ba'asamu warakaba yakamata mu gwada wani wajen kuma nakega".
"Malam duk yanda kace haka za'ayi, mu mun aminta dakai d'ari bisa d'ari, Kai Ubane a garemu, ko bama kusa zaka iya zartar da komai akan jiddah".
"Nagode da wannan karamci, yanzu ita mahaifiyar tata saitai k'ok'arin fidda mana ita zuwa mota".
Da k'yar Umma ta iya fidda Jiddah, daga k'arshema saida taimakon Uncle yahya, aiko Jiddah sank'ame musuma tayi amota.
Tafiya sukayi sukabar Umma a gida............???
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[12/4/2019, 4:49 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[20]_*
..............Tunda suka tafi Uncle yahya keta tofama Jiddah addu'a saboda fisge-fisgen da takeyi da wata Y'ar siririyar k'ara maikama da muryarta ta dishe. a cikin wannan halin malam Alfah ya faka motarsa k'ofar wata cibiyar magungunan musulunci. Shikad'ai ya fita yana fad'ama Uncle yahya yana zuwa.
Kai kawai Uncle yahya ya iya d'aga masa, idonsa yay jajir yana rik'e da Jiddah daketa fiffisgewa har yanzun.
Bud'e motar da a kai ya saka Uncle yahya d'ago kansa ya kalli malam Alfah dake k'ok'arin zama a mazauninsa.
"Baba Malam miya faru?".
"An samu matsalane yahaya, malam tajudden baya nan, amma anmana kwatancen wani wajen a Gadon k'aya, dukda shi bawai yana bada magunguna bane, yana taimakawa dai idan yaga abun ya tsananta ne, sai dai na rok'i alfarmar d'aya daga cikin almajiran malam tajudden wani ya rakamu, ga shinan zuwa".
"To baba malam muje cand'in, ALLAH ya saka da alkairi".
Gosulon da suka fuskanta a hanya yahanasu damar isowa da wuri, Ana sallar la'asar suka iso dai-dai masallacin bisa jagorancin kwatancen Zubairu Almajirin malam tajudden.
Malam Alfan ne kawai da zubairu suka fito, massalacine babba dake jingine da wani babban gida shima, anguwar tayi tsitt sai sautin karatun salla dake tashi cikin wata sassanyar murya. Alwala su malam Alfah sukayi suma suka shiga sallar, amma Uncle yahaya yana wajen Jiddah dan ba'a barta ita kaid'aiba..
Bayan an idar mutane suka fara fitowa d'ai-d'ai, sai da kowa ya fito, aka bar malam kawai da wasu tsirarun mutane a masallacin, su malam alfah suka k'arasa ga malam dake shirin fita shima.
Cikin mutunta juna malam da malam alfah suka gaisa, sosai malam zai iya girmar malam alfah a shekaru, shima zubairu ya gaisheshi kafin ya masa bayanin abinda ya kawosu.
Cikin jinjina kai malan ya amsa sannan suka fito.
Ana k'ok'arin fiddo Jiddah amota za'a shiga da ita ciki malam mustafa ya iso wajen, da mamaki yake kallon Uncle yahaya dake share zufa daya had'a saboda rik'e Jiddah.
"Uh uhm malam yahaya kaine yau a anguwarmu? Injidai lafiya?".
Juyowa Uncle yahaya yayi damson ganin Mai maganar, shima cikin mamaki yace, "A malam Mustafa dama nan anguwar kake? Amma Alhamdllh nayi farin cikin ganinka, wlhy Jiddah ce babu lafiya muka kawota".
"ALLAH Sarki, jiddah dai dana sani? Wadda akai biki watannin baya?".
"Wlhy kuwa malam Mustafa itace".
"Subahanallahi, ina mijin nata? mike faruwa haka?".
Murmushin takaici Uncle yahaya yayi, yana gyara tsaiwarsa, "Malam Mustafa labarin maid'an tsawone, amma bara mushiga da ita dan malam Na jiranmu".
"To ba laifi, amma inaga ad'an matsar da motar gaba saboda idanun jama'a".
Shawarar malam mustafa sukabi, aka matsar da motar kusada k'ofa sosai ta yanda ko an fito da Jiddah babu mai ganinta.
Tunda Aka shigo da Jiddah cikin falon malam Abdul-ra'uff maina take wata k'ara da jijjiga da fisge-fisgen guduwa.
Tausayin Jiddah da tunanin yaushe tagamu da wannan lalurar ya ishi malam mustafa. Sai dai bashida zarafin neman k'arin bayani a halin da ake yanzu......
Maganar Malam Abdul-ra'uff ta katse masa tunani ya maida hankalinsa gareshi.
Kallon Uncle yahaya dake rik'e da Jiddah malam Abdul-ra'uff yayi yana fad'in "kaga inkaso sakarta kawai".
"Malam da an saketa guduwa zatayi". 'Uncle yahaya yafad'a tamkar zai saka ihu'.
Murmushi malam Abdul'ra'uff yayi yana gyara zamansa, "Karka damu sakarta, babu inda zataje insha ALLAH",
Sakinta Uncle yahaya yayi ya matsa gefe, yayinda Jiddah keta bige-bige tana wani irin gunji, ga uwar zufa da takeyi tamkar fanka bata aiki a falon.
"mustafa jonamin abin turarennan na gefenka".
"To Malam". Malam mustafa ya amsa cike da girmamawa..
Tunda Malam Abdul-ra'uff yafara zuba garin magani Na turare hayak'i ya fara tashi sai bige-bigen Jiddah ya k'aru, hakama gunjin da takeyi, sai dai kuma tak'i magana, kamar yanda malam yake buk'ata. Kusan mintuna goma sha biyar ana Abu d'aya lamari Na Neman cin tura, gadai alamun shaid'anin dake tare da ita yana jigatuwa, amma taurinkai ya hana yayi magana.
Malam ya tsaya daga tofama Jiddah Addu'a mik'ewa yay ya fito yana fad'in su Uncle yahaya su biyosa.
A zaurensa bisa rukunin kujerun ya zauna yana kallon su Uncle yahaya cikin yarce gumi.
"Wato maganar gaskiya yarinyarnan akwai sihiri mai k'arfi a jikinta, bisa alamu kuma anyi ne cikeda makirci mai wahalar fassara, dan shaid'anin dake jikinta ma kunga yak'i nuna kansa, alhalin kuma alamu sun nuna yana jigata da addu'oin dake ratsashi, shin kozaku bani wani haske akan al'amarin?".
Kafin Uncle yahaya yay magana malam mustafa ya sanarma malama wacece Jiddah. Sosai malam Abdul-ra'uff yay mamaki, danshi ko kad'an bai ganetaba, dandanan hankalinsa Yakuma tashi, ya shiga tambayar Uncle yahaya Yaya akai haka? Miya faru da Jiddah bayan gaba d'aya dayin aurenta bata wuce watanni biyarba.
Kan Uncle yahaya a duk'e yana tsiyayar da hawaye yayma su Malam bayani dalla-dalla akan auren Jiddah da sanadinsa harma k'arewarsa sanadin matsalar da ayanzu Jiddah ke ciki.
Ran Malam Abdul-ra'uff ya6aci sosai, ga tsananin tausayin Jiddah da k'aunarta ke k'ara ratsashi, nawa yarinyar take da mahaifinta zai za6i sakata a gararin rayuwa irin wannan saboda cikar burinsa? Lallai alokacin dayasan irin auren da za'ama Jiddah kenan koda nuna k'arfine dasai ya aurama Aliyu ita. Amma babu komai, ya d'auki hakan a matsarin *RUBUTACCIYAR K'ADDARA* a gareta, babu wani mahaluki daya isa gogeta kuma...........
Malam nacikin tattaunawa da zuciyarsa sukaji