Showing 66001 words to 69000 words out of 121675 words
_Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika._
?????????? ????? ????? ????? ?????.
*_"Alhamdu lillahi ala kulli halin"._*
_Godiya ta tabbata ga Allah a cikin kowane hali._
Jin d'umin hawayen Jiddah a k'irjinsa ya sakashi d'agota da hanzari, raba idanu ya shigayi akan fuskarta wadda sai a yaune yasamu yimata kallon tsaf, masha ALLAH tanada k'yawunta dai-dai gwargwado, baiyi magaba sai hannunta kawai daya kama zuwaga kujera, yana k'ok'arin sakata ta zauna a kujerar tai saurin zamewa k'asan carpet ta zauna.
Fuskarsa d'auke da murmushi shima ya zauna a k'asan kusa da ita daf, k'afarsa d'aya a tankwashe d'aya kuma a zaune ya d'ora hannunsa Na haggu akai, yayinda yarik'o hannun Jiddah Na haggu Dana damarsa.
"Sannu da zuwa, ina yini". 'Tafad'a hawaye na sauka a kumatunta". Jikinta kuma har yanzu rawa yakeyi.
"Ya salam *_Khairunnisaa_*, minene ya sakaki kuka haka? A zatona yau farincikinki bazai musaltuba kamar yanda nakasa kwatanta nawa nima, kisaka a ranki insha ALLAHU babu wani shaid'ani dazaiyi cigaba da tasiri a kanki a halin yanzun, indai kina k'arfafa ranki zakibarma jin wannan tsoron kwata-kwata kinji". 'Yay maganar yana d'ago da ha6arta da hannunsa na Haggu, Na damarma kuma yana rik'e da hannunta har yanzun yana murza yatsun a hankali.
Lumshe idanunta tayi, dan bazata iya had'a ido dashiba, sosai takejin kunyarsa irin wadda bata ta6ajinta gawaniba tunda take, dan abinda yake Mata babu wani mahaluki daya kwatanta yimata bayan alhaji garba da d'ansa, sukuma nasu ya banbanta da nashin. Kanta ta d'aga amasa alamar amsawa.
Shi Aliyu duk zatonsa lalurartace takawo hakan, danshi kallon bazawara yake mata, shiyyasa bai kawo a ransa wannan shine Karon farko data samu kusanci da wani d'a namiji irin haka ba, da bazai zo Mata kaitsayeba, zai bita mataki-matakin dazata fara sakin jiki dashine. Goshinta ya sumbata kafin yadawo ya sumbaci la66anta ma da tun d'azun hankalinsa ke wajen. Wani irin zirrr Jiddah taji a jikinta, Wanda harya sakata saurin ja da baya.
"O, ALLAH. A kulani mana, ai najawu sosai hakanan Amarya".
Yanda yay maganar sai Jiddah duk taji babu dad'i a ranta, dan haka tace, "Kayimin afuwa dan ALLAH, ni....ni...wlhy...".
Saikuma tayi shiru takasa k'arasawa.
Rank'wafowa yay saitin kunnenta cikin rad'a sosai yace, "K...k...mi? madam! Ke a bari saikinje can gidan ko?".
Batare data shiryaba ta d'ago idonta ta kalleshi jin ya canja mata magana. Ganin yanda ta waro ido saiya bashi dariya, amma baiyiba yasaki lallausan murmushi yana fad'in "Maida idon karki sakan Na kasa gane hanyar gidana hajiya".
Gyalenta taja ta rufe fuskarta, Kafin tabashi amsa Walida da Zarah sukayi sallama a k'ofar d'akin.
Shine ya amsa yana mik'ewa ya koma saman kujera ya zauna, tareda nasu Izinin shigowa.
Kallo d'aya sukai musu kowacce tai k'asa da kanta, yayinda tuni kunyar duniya ta taru akan Jiddah da itama tai azamar matsawa baya tunda su Walida sukai sallama, amma Aliyu ya zauna jikin kujerar data matsa, harma k'afarsa Na gogar jikinta .
Kayan hannunsu suka ajiye, suka durk'usa suna gaisheshi. Cike da kulawa da fara'a ya amsa, yagane Walida, Zarah ce bai saniba, dan haka ya tambayi sunanta itama ta fad'a masa, daganan yacigaba da musu tambayoyi suduka akan karatu suna amsa masa. Sosai suma suka birgeshi, dan ya yaba da tarbiyyarsu d'ari bisa d'ari.
Sallama sukai musu suka fita.
Suna fita yay shirin dawowa k'asa kusa da ita, amma sai tayi azamar fad'in "Dan ALLAH kayi hak'uri karka zauna a k'asa kuma".
Kansa yad'an langa6e gefe yana narke Mata murya "Sai dai idan kema zaki dawo nan". Yay Mata nuni da cinyarsa.
K'irji Jiddah ta dafe irinna tsorata d'innan.
Sheikh Aliyu da dariyar abinda tayi ke cinsa yace, "Oh bazaki iyaba ko? Aiko saina fad'ima matata".
"matarka?!" tayi maganar tana kuma waro idanu akansa sosai da bud'e baki tana fad'in, "Rufamin asiri".
Kasa hak'uri yayi yanzunkam saida ya dara kad'an musamman dayaga idonta harya kawo ruwan hawaye. "To shikenan nafasa tunda kin karaya, ammafa ki d'auka 1-0, nine nayi winning kenan".
Gefen gyalen tasaka ta share hawayen da suka cika idonta tana fad'in "naji ba komai".
"Lallai wannan amaryar tawa shagwa6a66ace, Ashe aiki ya samemu nida Maimoon".
Baki tad'an turo masa batareda ta saniba.
Lumshe idanunsa yayi yana sauke ajiyar zuciya, datasan turo bakinnan abinda ke sakashi data daina, amma zaiyi maganintane inhar bata bariba kafin yabar gidannan.
Itakam batasan yanayibama, tuni tamik'e takoma gaban tiren dasu Walida suka kawo tafara zuba masa kunun aya mai sanyi daketa tashin k'amshi.
"Bismillah". Tafad'a cikin sanyinta.
Bud'e idonsa yayi yana d'ago kansa daya jingina jikin kujera, hannunta da kofin ya had'a ya rik'e yana kallon abinda ke ciki, "Madam minene wannan?".
Batareda Jiddah ta kalleshiba tace, "Kunun ayane".
"Toke hajjaju dakika bani kunun aya matata Na fama da kanta yakikeson Na k'are?".
Jiddah bata fahimcesaba, dan haka tad'an kallesa tana fad'in "Baka sonshine?".
Kallonta yay sosai, danta fara d'aure masa Kai, gaba d'aya yanda take masa sai yake ganin tamkar bata ta6a mu'amula dawani d'a namijiba da sunan miji, had'iye tunaninsa yayi saboda hannunta data motsa, saurin janye idanunta tayi dan satar kallonsa takeyi da.
Shima saiya kar6i kofin yana gyara zamansa, "Badan inada kishi mai tsananiba dana miki wata tambaya, amma bazanyiba, saboda ko'a tunani banason tuna kin ta6a auren wanina kafinni d'in. bara Zansha kawai, ALLAH ya fidda A'i daga rogo dai".
Jiddah batace komaiba itadai, dukda maganarsa ta d'aure Mata kai, dan batasan miyay niyyar tambayartaba. Kulolin tafara bud'ewa, tuwon shinkafane miyar ganye sai tashin k'amshi take. Tana k'ok'arin zubawa Aliyu dake shan kunun aya yace, "Afuwan Juddatulkhair, danasan zakiyi abinci danace karkiyi, banacin abinci da daddare, wannan kununma ya wadatar dani, amma insha ALLAH zanzo darana kodan naci abincinki kafin kikoma kusa Dani gaba d'ayanki".
Kanta ta gyad'a a kunyace, kafin ta maida kulolin ta rufe, gefe takoma ta zauna sosai yanzuma kanta a k'asa, tace, "Yaya auntyna?".
"tana gaisheki sosai itama, dan lafiya tamata k'aranci, shiyyasama kikaga tun ranar da aka d'aura aure ban zoba, alhalin hakan kuma ya cancanta, dan ALLAH amin afuwa".
"ALLAH Sarki ALLAH yabata lafiya, yasa kaffarane, mike damunta haka?".
"Babienkune". Yafad'a a wani yanayi daya kuma dulmiya Jiddah a kunya, harma tayi dana sanin tambayartasa.
Murmushi kawai yayi ya canja firar. "Kinga sarkin kunya da kuka, k'aramin kununnan tunda kin zurmani gara nasha dama hujja, amma Zan fad'ama auntynki duk ranarda zaki tare tayi kununnan aya itama danta rama".
"Ni Hauwa'u, yin kunun ayar yazama laifi malam?".
"Niba malaminki baneba yarinya, amsarki kuma sai a nan gaba zaki samu, nidai k'aramin".
Tashi Jiddah tai ta k'ara masa, ita dai yau gaba d'aya bata fahimtar maganganunsa, sannan yana k'ara bata mamaki, batai zaton yana magana hakaba itakam.
Haka yayta d'ora kunun aya yana Mata hirar da rabinta duk sakata kunya yakeyi, iyakarta murmushi ko e ko a'a.
Goma da rabi nayi ya mik'e, "To Juddatulkhair bara Na matsa ga Uwargida itama, zuwa talata insha ALLAH zankuma zagayowa gaisheki, a gaidamin Umminmu da k'yau".
Itama Jiddah tashi tayi tsaye, "Zataji insha ALLAH, ka gaida aunty, ALLAH yabata lafiya".
Harya d'an Fara tafiya yadawo da baya kusa da ita sosai yana fuskantarta, "Yanzu nan ba'amin oyoyoba, Na gaida gidanma bazan samuba kenan?".
Yunk'urin ja tayi da baya yay azamar d'ora hannunsa a k'ugunta ya matsota jikinsa ya rungume, duk tsumar da jikinta yake da rawa bai saketaba, saima bakinsa daya d'ora saman goshinta ya sumbata kafin yace, "wannan lalurar taki batamin adalciba, dolene kafin ki tare da izinin ALLAH na nemo mafita". Yana gama fad'a ya sumbaci la66anta sannan ya saketa.
Dukda halin datake ciki Na gushewar nutsuwar wucin gadi hakan bai hanata yomasa rakkiyaba kamar yanda Gajiram ta gargad'eta.
Tun a bakin k'ofa ya Danna key d'insa motarsa takawo haske day'ar tsuwwa, bud'ewa yay yashiga yana d'ebo ledojin gefensa ya mik'o Mata.
K'in kar6a tayi tana shirin juyawa. Da hanzari ya damk'o hannunta yana fad'in "Hajiyata tunadai miji nake ba saurayiba".
Dariya maganarsa ta bata, ledojin ya zura mata a hannu yana sumbatar hannun, "Kiyi mafarkina daga farkon dare har k'arshe".
Kanta a duk'e tace, "Nagode ALLAH ya k'ara bud'i na alkairi, yakaika gida lafiya".
"Amin *Qurratul ain*, maza shiga gidan dan bak'aramin k'ok'ari naiba barinki fitowa nan da wannan gyalen, danma kawai Darene kuma mota ta kare".
Murmushi tayi tana d'an risinawa da fad'in "saida safe".
Harta shige idonsa k'yam akan bayanta, ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauke tareda jingina da kujera yana lumshe idanunsa, yakai hannu yana shafa gemunsa Na sunnah kafin ya maida hannun ga cikinsa, a hankali ya furta "Kunun aya yafara aiki kenan".
Bud'e idonsa yayi yatada motar a kasalance yabar anguwar tamkar bayason tuk'in.
??????.
Duk a falo Jiddah ta iskesu har Uncle yahya dasu Sadiq da basuyi barciba, gaba d'aya suka zubo Mata idanu, hakanne yasakata yin kasa da kanta tana sakin ledojin hannunta a k'asa, gani take kamar duk sunsan miya faru tsakaninta da Sheikh Aliyu.
"A'a Jiddodo yada sakin ledoji haka?".
Uncle yahya yafad'a fuskarsa a washe da murmushi.
"Babu komai Uncle".
"To Alhamsullhi, ya tafi ne?".
"Eh".
"To ALLAH ya tsare, basaikin zaunaba kumuje Na rakaku gida dare yayi".
Ledojin Jiddah ta d'iba takaima Maman Sadiq.
"A'a Walida d'aukar Mata, wannan nakine ai".
"A'a mama bafa nawa baneba".
Uncle yahya ya katse zancen da fad'in "Kinga walida d'auka Mata kumuje".
Babu Wanda yay masa musu sukabi Umarninsa.
Jiddah ta d'auki hijjabinta ta saka suka fita sunama Maman Sadiq dasu Mageed saida safe.
Har k'ofar gida ya rakasu, saida yaga sun Shiga sannan ya juya batareda yashigaba shi.
Su Umma duk suna zaune basuyi barciba suna jiransu.
Balu ce ke fad'in "A lallai wannan d'an nawa ya iya zuwa, amarya mikika samo mana?".
Fita Jiddah tayi takoma d'akinsu takasa bata amsa, nanfa suka shiga yimata dariya da tsokanarta, tana jinsu amma tak'iyin ko tari, sai abinda ya faru tsakaninta da Aliyu keta dawo Mata kamar wata almara ko shirin film.
A can kuwa Gajiram ta bud'e ledojin dasukazo dasu. Kayan marmarine sai ice-cream da kaji guda biyu, sai kuma kwalin waya harda Sim card.
Nanfa suka shiga godiya ga Aliyu da fatan alkairi dana zaman lafiya garesu.
Gajiram tace walida ta d'auka takaima Jiddah, amma sai Umma ta dakatar da ita. "Ba haka ya kamata ba, ki raba kowama ya samu, wannan shine dai-dai".
Gajiram tasan halin Y'ar uwarsu da k'yak'yk'yawan tsari akan yaranta, dan haka tabi umarninta, kaza d'a aka ajiyema gidansu Uncle yahya, kayan marmarinma aka d'iba musu, ice-cream aka ajiye roba d'aya, ta raba komai nasu tabama su Jiddah rabi suma su uku suka d'auki rabi.
'Dauka su Zarah sukai da wayar Jiddah suka nufo d'akinsu zuciyarsu wasai dakumajin lallai yanzune Y'ar uwarsu tayi aure.
A tsanake sukaci komai sukai gidiya ga ubangiji, kafin su dasa fira da k'ok'arin had'a wayar Jiddah dukda babuma wuta.
Suma su Umma dai hirar tasu duk akan tariyar jiddahrne, sunayi sunacin abin arzik'in da ya sheikh Aliy ya kawo.
???????????.
A haka ya lalla6a hanyar gida bayan ya tsaya yasayama Maimunatu abin motsa baki itama.
Dukda dare yafarayi hakan bai hana ya iske tsirarun mutane a bakin masallacin k'ofar gidansaba, dayake akwai wuta a anguwar tasu su, dukda yabaro anguwarsu Jiddah babu kuwa.
Wani saurayine dasuke a bakin masallacin ya tashi ya bud'e masa gate, bayan yashiga ya rufe, saida ya tsaya Aliyu yafito a mota ya gaidashi sannan yafito yana masa saida safe.
Aliyu kuma ya kulle gidan danya shigo kuma kenan, tsarabar Maimunatu ya d'iba yanufi cikin gidan duk a matuk'ar kasalance, Wanda kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da bashida kuzari ko kad'an, dukda shi mutumne mai sanyi dama amma saiya kuma narkewa yanzu.
A yanda Maimunatu dake zaune a falo taji sallamarsa kawai saida ta d'ago da sauri ta kallesa da k'yau.............???
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[12/15/2019, 3:10 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[35?36]_*
..............Kallo d'aya taimasa ta d'auke kanta tana murmushin k'arfin hali, jikinta duk sai ya kuma sanyi, itadai tasan Aliyu ba mutum bane mai yawan fitina, hasalima sunkan jera kwana hud'u batareda ya nemeta ba, sannan baya d'aukar dogon lokaci tare da ita, wannan dalilin yasakashi dagewa wajen gyara kansa, dan a ganinsa ba mace kawai yakamata taima miji gyaraba, suma mazan yadace suna gyarawa........
"Ko ba'ayi murna da dawowataba Na koma Gimbiya". Maganarsa ta katsema Maimunatu tunaninta, mik'ewa tayi ta nufosa, sai da ta rungumesa da sumbatar kumatunsa kafin ta sakesa ta amshi kayan hannunsa tana danne kwallar data cika idonta, dan sosai taji k'amshin turaren daba nashiba a jikinsa, tasan kuma bai wuce Na amarya ba, a yandama yadawo mata kad'ai ya isheta amsa.
Bin bayanta yay ya zauna yana sauke numfashi, kallonsa tad'anyi batareda tace komaiba tawuce kicin, babu dad'ewa tadawo d'auke da tire.
Gabansa ta dire, ya d'ago kansa daya jingina a kujera yana kallonta, itama shi take kallo, cikin danne zuciyarta tasaki murmushi tana fad'in "Wai miya sakaka laushi haka Annur?".
Zamansa ya gyara sosai tareda kamo hannunta ta zauna a gefensa. Muryarsa a matuk'ar sanyaye yace, "Babu komaifa madam, naga kin damu".
"To ba doleba Yaya, kafita muna farin ciki kadawomin a sanyaye, kaga sainaga ko wani abune yafaru da jiddan ko wani a gidansu ai?".
"To kwantar da hankalinki, babu abinda yafaru tanama gaisheki. Bani ruwa nasha kedai".
"ALLAH Sarki, ina amsawa nima, kuma Alhmdllh tunda babu wata damuwa". Jug dake kan tire ta d'auka tafara tsiyaya abin ciki a k'aramin kofi.
"Minene wannan zaki bani?".
Da mamaki ta kallesa sannan ta kalli jug d'in, "Yaya had'in kwakwar dakace namakane d'azun ai, to wlhy nama manta, sai bayan fitarnan taka dasuka kawo wuta Na tuna shiyyasa nayi, kajiko harma yayi sanyi".
Amsar jug d'in da kofin yayi ya ajiye k'asa, "Barshi dan ALLAH Maimoon inba kasheni zakuyiba".
Cikin waro ido Maimuna tace, "Yaya kashewa kuma?".
"Eh mana, ba dole nace kashewa ba, ita tabani kunun aya, kekuma zaki bani had'in kwakwa?".
Babu shiri Maimuna ta kwashe da dariya, haba no wonder tagansa a sanyaye.
Harara ya zuba Mata yana wani shagwa6e fuska da fad'in "Abindama zakimin kenan ko? Maimakon kiji tausayina".
Baki Maimuna ta toshe da hannu tana had'iye dariyarta da k'yar, "ALLAH Yaya kaid'inne kaban dariya, ni duk kasakani a tsorone da farko".
"Humm bazaki ganeba wlhy, tsautsayi kawai ya sakani shan kunun ayarnan da yawafa, gashi kuma yasha had'i kamar yanda kikemin, Nidai Ahmad ai yagama dani daya bani wannan sirrin".
"Haba dai Yaya godiya yakamata Kai masa ai".
Hannu yasa ya jawota jikinsa, murya k'asa-k'asa yace, "Wayace ban gode masaba, badan iyakancewar Mahaliccina da taimakon Ahmad ba da yanzu ban mallaki koda mace d'aya ba balle Mata