Showing 6001 words to 9000 words out of 121675 words

Chapter 3 - MUTUM-DA-DUNIYARSA COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Sep 2024

17148

yaransa kuma ba kowa keda makamancin halayya ta Aliyu ba, hasalima yafisu indai a fannin ilimine.
Bisa ga bin Umarnin mahaifinsa ya tattaro ya dawo, kusan shekararsa d'aya kenan, tunda ya dawo malam ke zuba ido yaji kozaiyi batun aure, amma shiru kukeji babu wani motsi, sai harkokinsa Na k'ok'arin yad'a ilimin addinin islama yakeyi ta hanyoyi da dama. Dan ALLAH ya d'aga darajar *_Sheirk Aliyu Abdul-ra'uff Maina_* fiye da zaton mai hasashe a ciki da bai Na Najeria da k'asashe masu mak'waftaka, harma sunansa nason fin Na mahaifinsa dan masu iya magana kance kowa da zamaninsa.


Wannan kenan?????????¡â.



???????????

K'arfe d'aya dai-dai su Jiddah suka tashi daga islamiyya, kamar yanda ta saba saida tai salla a masallacin makarantar gudun kafin taje gida lokacin salla ya shige, gashi a k'asa zata tafi.
Bayan sun idar da sallar da d'alibai irinta masu tsayawa ta tako a nutse zuwa wajen makarantar, da d'an sauri-sauri take tafiya akan k'ok'arinta na isa gida da wuri ta taimaki Umma da aiki, tasan tana can tana fama da gawayi danyin girkin rana. A hankali ta furta "Anya Abba kana tsoron gamuwarka da mahaliccinka kuwa? Kana gudun tashi cikin masu shanyayyen jiki a jerin raunana wajen gina adalci akan iyalai? Ya rabbi ka shiryi Abbanmu, ka ganar dashi gaskiya kafin ka kar6i ruhinsa". hawaye masu d'umi suka gangaro a kumatunta, bata damu da son sharewa ba dan tasan babu mai ganinta, da wannan ta k'arasa gida.
Kamar yanda ta saba tai addu'ar shiga gida sannan ta shiga da sallama bayan ta tsaya a soro ta goge hawayenta.
A k'ofar kicin ta iske Umma nata faman fifita wutar gawayin.
Umma ta amsa Mata tana fad'in "Lale da malama Jiddah, har an dawo?".
Jiddah ta yaye nik'ab d'inta tana murmushi saboda jin tsokanar Umman tasu, "kai Umma inafa malama, kodai d'aliba, sannu da gida".
Umma dake dariyar amsar Jiddan tace, "yauwa, ai kuke da sannu".
Bokitin fenti Jiddah ta jawo ta zauna tareda k'ok'arin kar6ar maficin hannun Umman. Umma ta hanata tana fad'in "A'a baiwar ALLAH daga dawowa, kid'an huta mana ko Uniform ki samu ki cire, nasan dai kinyi salla a can?".
"Umma karki damu, wlhy banajin wata gajiya, dama saurin danaketa yi kenan, dan jiya gawayinnan Na fahinci jik'ak'k'ene, yau da safema da k'yar ya kama".
"Aifa naga alama wlhy, sauk'inma nagama miya, dan nasamu sund'an kawo wuta shine nayi akan abincan da Nafisa ta sayo mana, ina k'ok'arin d'ora shinkafar suka d'auke wutar".
"Ai y'an wutarnan basuda alk'awari, sannu da k'ok'ari Umma, amma ina kika samu kud'in kayan miya harda gatantamu?".
Murmushi Umma tayi, sannan ta mik'e zuwa cikin kicin d'in tana bama Jiddah Amsa,
"Kud'in adashin nanne hajia Lantana ta kawo, ni harma Na fidda ran samunsu, to naga ga kajin da Nafisa ta bamu sai kawai naba Dauda ya yomin cefane".
"ALLAH sarki Ummanmu abin alfaharinmu, mai share kukanmu, ALLAH ya saka da alkairi, kingani kuma darajar hak'urin da mukai ga kud'in wajen hajia lantanar sun fito, bayan kowa ya fidda ransa ga samunsu, Umma sai ki koma sana'arki karmu cinye kud'in a ciki mu koma tsugunne-tsugunne".
"Nayi wannan tunanin wlhy nima Jiddah, shiyyasa tun d'azun Na Kira Nafisa muka kuma shawartawa kafin kuma ku dawo kuji yanda mukai".
"To shikenan Umma, aimu duk abinda kuka yanke dai-daine a garemu, ALLAH yayi mana jagora".
"Amin" Umma ta amsa.

Bayan gawayin ya Kama sosai Jiddah ta d'ora ruwan shinkafa, cikin amincin ALLAH dandanan ta gama, tana cikin kwashewa a kula su Zarah suka shigo da sallama, kowa a galabaice yake saboda rana. Sannu Jiddah tai musu, hakama Umma. Walida ta wuce gaban randarsu da suke zuba ruwan sha saboda k'arancin rashin wutar lantarki ta k'asar tamu Tasha.
"Ke kuwa walida ki taimaki kanki da wannan ruwan hakanan kafin ya k'ulle miki ciki",
Kofin ta ajiye tana had'iye Na bakinta cikin hura hanci, "Umma wlhy k'ishirwa Na kwaso, yau Na manta banje da ruwaba saboda saurin karmu makara, nikuma bana iya shan Na bohol d'innan Na makaranta wlhy".
"to miye matsalarsa?". Cewar Jiddah dake shiga falo da kular abinci..
Caraf Zarah tace, "Yo iyayi irin nata dai Yaya Jiddah......."
"Kai Yaya Zarah kiji tsoron ALLAH, kemafa kinsan baida dad'i wlhy". 'ta k'are maganar da turo baki gaba'.
Umma dai tana jinsu bata sake tankawaba, saida tagama kashe wutar da Jiddah ta sauke abinci sannan tace, "Da wannan gardamar mara amfani dama tashi kukai kuka cire Uniform kuka watsa ruwa, dan sai k'aurin rana kuke".
Duk sai suka kumbura baki, wai danmu Umma zatace suna k'aurin Rana.
Fahimtar hakan ya saka Jiddah da Umma kwashewa da dariya, Umma ta toshe hanci tana ra6awa ta gefensu ta shige d'akinta. Jiddah ma saita shige d'aki tana dariya.
Zarah da Walida suka kalli juna suna jinjina kai irin zamu rama d'innan. Walida tace, "y'ar uwa barsu sunci bashi indai munai, daga Umma har yaya Jiddah kowa munsan lagonsa. Dariya suka kwashe da ita suna tafawa, sannan duk suka mik'e zuwa d'akinsu inda Jiddah ta shiga.

Duk d'insu saida kowa ya samu ya watsa ruwa, Walida tayi salla sanna suka hallara a falo domin cin abinci. A babban faranti Jiddah ta zuba musu suka saka miya da namansu a sama, suduka har Umma suka saka hannu bayan walida ta d'ebo musu ruwan tulu mai sanyi. Dama can haka suke cin abinci su Biyar, bayan auren Aunty Nafisa ne suka koma su hud'u, tunda suka taso a wannan tarbiyar suka tsinci Kansu, harma sun Saba, kowa baya iya sakin jiki yaci abinci shi kad'ai saida y'an uwansa. (Iyaye mu kula wlhy, cin abincin yaranmu a waje d'aya yana k'ara musu k'aunar juna a zukata, dan kowa nacin yawun d'an uwansa, shak'uwa da soyayya na sake shiga tsakaninsu, wannan k'yak'yk'yawar d'abi'ar da muka bari tana taka rawar gani wajen raba kayin y'ay'anmu tundaga tushe. ALLAH yasa mugane????).

Babu mai magana har suka gama tsaf, suka koma kan nama, kowa yanaci a nutse babu had'ama balle nuna zalama. Bayan sunyi nak walida ta kwashe kwanikan ta gyara wajen, daganan suka baje a falon suna cigaba da hirarsu mai cike da k'arama juna sani ba surutai marasa amfaniba............???



Wannan kenan?????????¡â.




*_Assalamu alaikum, dan ALLAH Zan d'anyi wani tsokaci a fahimceni. Gameda masu turamin massages ta PC wasu suna ganin tamkar wulak'ancine idan sun tura ban amsasuba a lokacin, Ku gane wani Abu, inada aurefa, sannan inada uzirirrika tamkar kowacce mace, sannan duk lokacin da ka gama typing ko sha'awar ta6a waya bakayi wlhy, ji kake kanka ya d'auki zafi, sannan fa bake kad'ai bace, mutum yakan samu sak'onni sama da 200 a rana d'aya, banda Na groups, tayaya kuke ganin Zan iya amsasu a lokaci d'aya???, shiyyasa nake barin kamar sak'o Na yau Na amsashi da safe kafin Na Fara typing, dana gama nai posting saisu wuce gaba d'aya, to dan ALLAH kuringa mana uziri????. Kuma masu Comments a groups wlhy ina kula da kowa, kuma inajin dad'i matuk'a, amma kunyi yawan da bazan iya binku d'aya bayan d'aya Na amsaba wlhy, dan groups ne sama da 30, dan ALLAH kuma kuyi mini afuwa, amma kuna raina kuma ina kula da motsin kowa wlhy, ngd ALLAH yabar zuminci, inajin dad'in addu'oinku gareni da mahaifina????????????????_*


_Naga an bud'e groups d'in MUTUM DA DUNIYARSA kusan 8 kuyi hak'uri sunyi yawa wlhy, dan haka Zan fita a wasu, kafin Ku had'ama wayata zafi??, inba hakaba nakoma la6e a WhatsApp aradu??????¡â??¡â._









*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????
[11/17/2019, 10:09 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*



*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce????_*

*_[4......]_*


..............Kamar yanda suka saba a kowanne dare bayan sallar isha'i akwai karatun manya magidanta a masallacin k'ofar gidan malam. A da shikeyi, amma dawowar Aliyu sai abun ya rabu biyu, malam Na koyar da dattijai, shikuma Aliyu matasa. Kowacce rana akwai littafin da suke karantawa, yauma kamar kullum Qur'an ne a gabansu, yayinda Sheirk Aliyu Maina ke karanto ayoyi daga suratul An-nisa cikin zak'in muryarsa da sanyin irinna masu nutsuwa. da alama ma yau suka shiga Surar, dan fako yake karantowa cikin kwarewar larabci da taka tsantsan.
Masallacin yayi tsit kowa yana saurarensa, sai da ya maimaita ayoyin daya karanta sau uku kafin ya d'ago idanunsa yana kallon d'aliban nasa da zasu iya kaiwa 40+, fuskarsa d'auke da murmushi mai sanyi.
Cikin nutsuwa suka shiga maimaitawa suma, yayinda yake musu gyara a inda yaji kuskure.
Har k'arfe 9 suna karatu.
Sheirk Aliyu ya kalli agogon fatar dake d'aure a tsintsiyar hannunsa, ganin har tara da kusan kwata yay d'an gyaran murya alamar su dakata. duk kallonsa sukayi, yad'an murmusa yana fad'in "Masha ALLAH, Inaga yakamata mu dakata haka, domin kowa yaje ya k'arasa Uzirinsa".
Duk sun amsa masa da to.
Addu'a yay musu kafin kowa yatashi ya fito bayan sunbashi hannu duk sunyi musabaha da bankwanar tashi lafiya.
Bayan fitar kowa ya tattare littatafansa yana zare farin glesses d'in fuskarsa sannan ya mik'e shima ya fito. Cikin gidan ya nufa, inda a zauren farko ya iske mahaifinsu malam Abdul-ra'uff da dattijan d'alibansa. Rissinawa yay ya gaidasu, dan yaga da alama suma sun gama karatun nasu na yau, har zai mik'e Malam yace, "Ali inason ganinka kuwa".
Kansa a k'asa ya amsa da "To Babah gani".
"A'a ba ciki zaka shigaba? Shiga ka fito zuwa sannan Na kammala nima".
"To". Ya amsa yana mik'ewa.

Da sallama ya shiga gidan nasu da a yanzu babu yawan hayaniya, saboda mafi yawan yaran gidan sunyi aure, wad'anda suka rage kuma duk sun mallaki hankalinsu, sai dai jikoki da wasu ke rik'o a matan gidan. Babu kowa a tsakar gida, sai wutar lantarki data haske ko ina kasancewar ba'a kashe gen... Ba saboda masu karatun dare. Kai tsaye k'ofar hajia bah-bah ya nufa uwargidan malam. Saida yay sallama a k'ofar d'akin aka bashi izinin Shiga sanna ya shiga da sallama.
Hajia Bah-bah da wata matashiyar budurwa da yara biyu suka amsa. Yaran suka taso suna masa oyoyo. Hannayensu ya rik'e cikin murmushi yana fad'in "A'a malam k'arami yau anan za'a kwana kaida Ai'shatu?".
A tare suka amsa da e Kawu! Zamu kwana wajen hajia bah-bah ne, Ammin mu taje Kaduna.
"Masha ALLAH, ALLAH ya dawo da ita lafiya". 'ya k'are maganar yana zama a kujerar kusa da k'ofa'
Budurwar tace, "Yaya ina yini? Wad'annan iyayen maganar sun tsareka da surutu".
Murmushi yayi sannan ya amsa da "lafiya lau Ni'ima, ya makaranta?".
"Alhmdllh yaya".
Murmushi yayi yana maida hankalinsa kan hajia bah-bah dake kishingid'e tana murmushi tun shigowarsa.
Cike da girmamawa yace, "Hajia ina yini?".
"Lafiya lau Aliyu, har an tashi daga makarantar?".
"Muntashi hajia, saikuma ALLAH yasa muna cikin masu kaiwa gobe".
"To ALLAH ya datar damu". Hajia bah-bah tafad'a tana tashi zaune sosai. Yayinda Aliyu ya yunk'ura zai tashi, amma sai hajia Bah-bah ta dakatar dashi ta hanyar fad'in "Aliyu abinci fa?".
"Alhmdllh hajia, dan yau nagaji barci zanyi da wuri, idan naci abinci yanzu zai takura min".
"To shikenan, bandama dai kanason zama babban kwabo ai kawuce cin abincin gidanku saina matarka, yakamata dai a motsa hakanan Aliyu".
Murmushi yayi yana mik'ewa da fad'in "Za a duba insha ALLAH hajia".
Bayan fitarsa Ni'ima tace, "Wlhy kuwa hajia yakamata Yaya Aliyu yay aure, yanzufa kaf gidanan shikad'ai ya rage baiyi aureba a maza, gasu yaya Mahmud da Yaya Usman harsun cika wata hud'u da aurensu, shiko ko maganar ma bayayi, yakamata ya cire Asma'u a ransa, tana gidan mijinta hankali kwance harda yara biyu da cikin Na uku shiko ya zauna".
Hajia bah-bah batace komaiba, amma fuskarta ya nuna alamun damuwa da tausayin Aliyun.
Shikam d'akin iya habi ya shiga itama bayan yayi sallama an bashi izinin shiga, ita kad'aice kawai a d'akin, dan dukta aurar da yaranta, sai yarinyar k'anwarta da take rik'o mai suna Maimunatu, itama budurwace, dan zatakai sa'ar Ni'ima.
Iya Habi ta tareshi da fara'a kamar yanda ta saba, dan ita mace ce mai yawan barkwanci, cikin tsokana tace, "Tuzurun gidanmu har an tashi daga karatun?".
Fuskarsa d'auke da murmushi ya zauna, cikeda sanyinsa ya gaidata, shi mutumne da bashida yawan magana, shiyyasa ko Ana tsokanarsa bai iya ramawa.
Maimuna data fito a d'aki tawani washe baki, a rayuwarta tana k'aunar Aliyu, amma shi yanda ta lura matanma basa gabansa kokuwa duk malantarce oho.
"Yaya Aliyu barka da dare".
Idanunsa yad'an d'ago ya kalleta kad'an ya janye sanann ya amsa da fad'in "Yauwa Maimunatu, ya makaranta".
"Alhamdllh yaya, d'azun a islamiyya nazo dubaka a office amma saina tarar ka fita ma".
"ALLAH sarki". Abinda kawai yafad'a kenan yay shiru da bakinsa, saima ya mik'e yayinda Maimuna ke shirin zama kusa da kujerar da yake zaune.
"Iya bara naje sai ALLAH ya kaimu".
"ALLAH ya tashemu Aliyu kaji".
"Amin iya".
Maimuna da takaici ya isheta kam batama amsaba, tarasa yanda zata shawo kan Aliyu kanta.
Iya Habi Na kula da ita, murmushi kawai tayi ta d'auke kanta, tuni ta fahimci Maimuna nason Aliyun.
Aliyu kam yana d'akin gwaggo itama suna gaisawa, itama mace ce mai yawan sakin jiki da mutane, nanma ya gaisa da k'annensa biyu dasuka rage a d'akinta basuyi aureba, Asiya da Fatima, sanan ya fito zuwa kiran malam.



???????????


Jiddah dake fitowa daga d'aki cikin shirin fita ta kalli Umma dake zaune a tsakar gida tanajin redio, su kad'aine a gidan, su walida sun wuce islamiyya.
"Umma bara naje Na duba Maman Sadiq daga nan zanje na duba sa'adatu sulaiman ta islamiyyarmu ance batada lafiya yau ko islamiyya batajeba".
"To jiddah saikin dawo, amma a dawo dai da wuri".
"To Umma insha ALLAH".
A k'afa ta taka har zuwa gidan Uncle yahaya, dan basuda wani nisa mai yawa, ta iske gidan shiru, su Sadiq duk sun wuce makaranta, Maman sadiq dake wance a tsakar gida ta d'ago Kai tana murmushi da amsa sallamar Jiddah.
"Yau malama ce a gidan namu?".
Jiddah ta zauna gefen tabarmar tana yaye nik'ab d'inta, fuskarta d'auke da murmushi ta fara gaisheta. Maman sadiq ta mik'e zaune itama tana amsawa.
"Maman sadiq yanaji gidan shiru?".
"k'annen naki duk suna islamiyya Jiddah, yasu Zarah?".
"Suna lafiya, suma idan sun dawo islamiyya zasu biyo dubaki".
"ALLAH ya dawo dasu lafiya",
"Amin mama". Jiddah tafad'a tana mik'ewa tsaye, hijjab d'inta ta cire ta d'auki tsintsiya ta share tsakar gidan. Duk wani aiki daya dace tayisa, ta dafa musu taliya bisa Umarnin Maman sadiq d'in. Bayan ta kammala komai taima Maman sadiq daketa kwarara Mata addu'a sallama ta tafi.
Daga nan napep ta hau zuwa gidansu Sa'adatu sulaiman d'in.
Bata wani dad'e a canba takuma hawo napep zuwa gida kasancewar yamma tayi lik'is, gab ma ake da kiran magriba.

Tunda ta fito a napep d'in gabanta ya fad'i domin ganin motar Abbansu a k'ofar gida, jiki a sanyaye ta mik'ama mai a daidaita hamsin d'insa tanufi k'ofar gidansu, kamar kullum saida tayi addu'ar shiga gida sannan ta shiga da sallama.
Tunkan ta k'asara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login