Showing 108001 words to 111000 words out of 121675 words
duk bai afka masaba, amma ya daure yace, "Wannan kukan ya isa haka ko?".
Kasa tsayar da kukan Jiddah tayi, Maimunatu tazo gabansa itama ta durkusa ta gaidashi, da masa ya jiki?.
Amsawa yay cikin alamun yanajin jiki matu?a, itama Jiddah ta gaidashi, ana cikin haka Uncle yahya daya fita suka shigo da Aliyu, dama su Umma duk sun kimtsa, gashi a kwai wutar nepa.
Tabarmar dake shinfi?e a farkon shigowa wadda Jiddah taje ta zauna kusa da Abba Uncle yahya ya nunama Aliyu, kansa a ?asa bai kalli kowaba ya zauna, Jiddah da gaba ?aya hankalinta baya wajen saijinsa tayi kusa da ita, mi?ewa tai tabar wajen, takoma inda Umma take tana sharar hawayenta.
Aliyu ya gaida Abba yana fa?in,
"??? ?????? ??????? ???? ????? ????? .
La ba'asa tahoorun in sha'al-lah. (Ba komai, tsarkaka ce in ALLAH ya yarda).
???????? ????? ??????????? ????? ????????? ?????????? ???? ????????? .(??? ????)
Asalul-lahal-'azeem rabbal-'arshil-'azeem an yashfeek (7). (ina rokon ALLAH mai girma, Ubangijin Al'arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa).
*_(MANZON ALLAH, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; "Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya fadi wannan (addu'a) sau bakwai face ya sami lafiya")_*.
_Falalar Da Ke cikin Ziyarar Mara Lafiya._
*_(ANNABI, tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, yace; "Idan mutum ya ziyarci dan uwansa Musulmi (da ba shi da lafiya) to yana tafiya ne cikin lambunan aljanna yana tsinkar 'ya'yan itaciyarsu, idan ya zauna sai rahama ta lullube shi. Idan da safe ne Mala'iku dubu saba'in za su yi ta yi masa salati har ya shiga maraice. Idan kuma da maraice ne mala'iku dubu saba'in za su yi ta yi masa salati har ya wayi gari)_*.
Aliyu yaja doguwar addu'a ga Abba yana share kwallar da shima suka cika mada ido na tusayin Abban
Su Aunty Sauda na amsawa da amin.
Duk sun gaidashi da masa godiya, itama Umma ya gaidata tareda jajanta lamarin, Jiddah na jikinta tana hawaye, yayinda Umma keta shafa kan Jiddah alamar lallashi.
Aliyu ya janye idonsa daga jiddah ya maida akalar gaisuwar ga Hajia Hindu data cika tai fam da haushi, itama yay mata addu'ar samun afuwa.
Ta amsane kawai dan yayi mata mugun kwarjini, yanda takema mazajen su Aunty Nafisa yatsine-yatsine shi saita gaza masa, harshenta har sar?ewa yake wajen saurin amsa gaisuwarsa.
Basu baro gidanba sai goma da rabi, shima saida Uncle yahya yace yakamata su tafi dare yayi, ?an dubiya daketa shigowa ma sin?an rage saboda dare ya farayi.
?iri-?iri Jiddah ta sanya kuka ita anan zata kwana, tun kowa na ?aukar abin wasa har suka lura da gaske take, shikuma Aliyu baice uffanba yay musu sallama ya fice abinsa bayan ya ajiye ku?in da malam yace aba Abba da wanda shima ya bashin, sai kayan marmari dasuka tsaya a hanya suka saya.
Uncle yahya ne yayma Jiddah jan ido sanan ta mi?e su Zarah suka rakota inda Maimuna da Aliyu ke jiranta.
Babu wanda ta kalla ta bu?e bayan motar tashiga tana cigaba da kukanta, Uncle yahya yabama Aliyu hannu sukayi musabaha da godiya shikuma Aliyu nama Abba addu'ar samun lafiya.
Saida suka bar ?ofar gidan su Zarah da Uncle yahya suka koma cikin gida.
A hanyama Jiddah kukanta takeyi, sai dai bamai sautiba, amma su Aliyu na jinta, Maimunatu ce kawai keta lallashinta da bata baki, amma sam Aliyu ya?i tankawa, ita kuma shirunsa saiya kuma tunzurata takasa yin shiru kodan lallashin da Maimuna ke mata.
Suna isa gida itace farkon fita tabarsu a mota, da kallo kawai Aliyu ya bita, Maimuna zatabi bayanta Aliyu ya dakatar da ita, "Kinga Maimoon barta kinji".
Cikin langa?e kai tace, "Haba yaya yazakace a barta, kukafa takeyi?".
Fitowa yay daga motar shima, "Tunda nace kibarta kawai ki barta, kukan nata harda na hanata kwanane, indai banda rashin son gaskiya taya za'a ?ara musu nauyi bayan wanda suke ciki, idan tayi ha?uri da safe zata koma insha ALLAH".
Shiru kawai Maimuna tayi, amma ita harga ALLAH bataga laifin Jiddah ba, ko itace sai taso kwana ?in, to amma ita kanta shaidace akan wannan halin nasa, zata iya rantsewa tunda akai aurensu bai ta?a barinta taje gida ta kwana ba, yini ma yata ?ata rai kenan. Dan haka sai bataja maganarba ta wuce sashenta.
Shima nasa ya nufa batare da yabi ko wannensu ba.
Tunda Jiddah ta shigo ko hijjab bata cireba ta kwanta a gado tana cigaba da kukanta, tausayin Abbansu da ba?incikin an hanata kwana cikin ?an uwanta yake kuma tunzura kukan nata, ga haushin Aliyu, dan da ace yaso ta kwana ai zaice ta zauna, kuma babu wanda zai hana, rashin amincewar tasane ya saka Uncle yahya korota.
Tana nan kwance harya shigo, dukda taji ?amshinsa ko motsi batayiba.
Kansa kawai ya ?an girgiza, ya ajiye kofin shayinsa da Maimuna ta ha?o masa sannan ya zauna kusa da ita.
"Hauwa'u!". 'Ya kirayi cikakken sunanta abinda bai cika yiba, saboda sunan mahaifiyarsa kenan'.
Tsoro ya kama Jiddah, saboda jin yanda ya kirata a dake, tamkar ba shiba, hawayenta ta goge sanan ta amsa cikin rawar murya.
"Tashi zaune ki cire wanan hijjabin".
Bata musa masaba ta tashin, takuma cire hijjabinta amma ta?i kallonsa.
Shima bai kalletan ba yace, "Tashi kiyi shirin barci".
Tamkar munafuka haka ta tashi sum-sum zuwa bayi. Shikuma ya ?au shayinsa yafara sha yanamai jin tausayinta da ahalinta, sosai lalurar Abba ta tsaya masa a zuciya, ita kuma tana neman ?ara masa zafi da ?uruciyarta.
Yana shan shayin ta fito, kayan barcinta ta ?iba ta dawo ta bayansa ta saka, nanma baice mata ?ala ba, amma da lafiya-lafiya ne cazai shi zai saka mata.
Tana gama shiryawa ta ?aura zani tazo ta kabbara shafa'i da wutiri. Shidai Aliyu na zaune yana kallonta harta idar.
Sai kumbura fuska takeyi tana cigaba da share hawayen dake zubo mata, hannu ya mi?a mata alamar tazo, da tayi nufin no?ewa, amma sai taga rashin dacewar hakan, tadai turo baki sanan ta matsa kusa da gadon.
Hannunta ya kamo ya jawota zuwa jikinsa a hankali. Tana jinta kwance a ?irjinsa saita kuma fashewa da sabon kuka.
"Oh ALLAH, ya isa haka mana Jiddah, ko sokike nima namiki kukan ne?".
Kanta ta girgiza masa alamar A'a.
"To kiyi ha?uri kinji, insha ALLAH zai samu lafiya, Addu'a ya kamata muyi masa ai ko".
"Amma shine ka?i yin magana danace zan kwana?".
Murmushi yayi yana shafa kanta, cikin kuma sanyaya murya yace, "To nayi laifi amin afuwa, amma kema kinsan hakan bai ?yautuba, kwananki ai ?arin wani nauyine, idan ALLAH ya kaimu saikije ki yini kinji".
Da sauri ta kallesa, "Da gaske dan ALLAH?".
Yanda tai maganar saita so bashi dariya, amma sai ya gimtse ya sumbaci goshinta yana fa?in "Insha ALLAH Qurratul ain, ALLAH dai ya basu lafiya, yakuma tsare gaba".
"Amin ya rabbi, ammafa ni babu wanda ya fa?amin abinda ya faru".
"Ni dai Uncle yace min ?an fashine suka shiga, amma nasan za'a fa?a miki insha ALLAH, sai kinje gobe idan ALLAH ya kaimu".
Shiru kawai Jiddah tayi, tausayin Abba nakuma ratsata.
???????????
Washe gari da wuri ta tashi ta ha?a breakfast, kunun gya?a sai soyayyan dankalin hausa data yankashi dogaye, saita soya miyar attarugu zalla da albasa, harta gama Aliyu bai shigoba daga massalaci dayaje. Tana gyaran bedroom ya le?o.
Durkusawa tayi ta gaidashi, bai shigoba ya amsa daga inda yake tsaye a ?ofa, "Mizan tayaki dashine?".
Kanta ta girgiza masa tana fa?in "A'a ka barshi, shara kawai zanyi".
Kansa ya jinjina mata ya juya ya fita, ta bishi da kallo saida ya fice sannan ta mi?e taci gaba da aikinta. Ko morping yau ?inyi tayi, tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta atanfa, kayan karin kumallon ta ?iba zuwa sashensa. Shima har yayi wankan yana shiryawa ta shigo.
Idanu ta zaro tana ?an dafe ?irji, sanan ta marairaice fuska tana fa?in, "Dan ALLAH kayi ha?uri, banzo na ha?a maka ruwan wankaba".
"Tab ai bazan ha?uraba yarinya"..
Dur?usawa tayi agabansa, "Dan ALLAH fa nace".
"To saikin fa?i sunana".
Babu shiri ta ?ago ta kallesa, yako yi kicin-kicin da fuska tamkar gaske, "Idan har baki fa?aba gwammajan ma bazaki jeba ko".
Tuni ta fara hawaye, "ALLAH ni bazan iya fa?ar sunanka ba".
"To saikin fa?i abinda zaki ringa kirana dashi, danni nagaji da maidani surukinki da kikeyi".
Wai shi dama haka wanan mutumin yake?
Jiddah ta ambata a zuciyarta dan takaici, harga ALLAH da burin zuwa gidansu ta kwana, hardasu mafarki, dan haka gara tafa?a tasamu taje, kuma kasa tayi da kanta sanan tace, *_"Zauji ghaliy"_*.
Kafa?unta ya kamo ya ?agota zuwa jikinsa yana fa?in "Masha ALLAH Aglannissa, daga yau karna sakejin an ?oyemin suna ana kwana-kwana".
Kanta ta ?aga amasa alamar amsawa.
Sakinta yayi ta taimaka masa ya ?arasa shiryawa, sanan taje kiran Maimuna dansuyi kari..........???
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*?AURIN ?OYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ?ADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ?AYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RA?UMI..!* (Bilyn Abdull)
????karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*????????????
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[12/31/2019, 3:25 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[61?62]_*
............Koda su Ashir suka amso ku?i a kotu ?iri da muzu suka hana Alhaji Garba, hasalima shi baisan wainar da suke toyawa ba, dan yakoma sashen amaryarsa ya tare, kwata-kwata baya barin rana ta gansa, musamman ma da yanzu yasan yanada laifi a wajen ?a?ansa akan abinda yayma mahaifiyarsu, toshi babban ma abinda yakeji a ransa gameda ita shine tsananin tsanarta, ko ka?an baya sha'awar koda tunata ma.
A yau yay nufin kiran Abba ya tuna masa zancen ku?insa, amma sai wayar ta?i shiga, hakanne yasakashi maida akalar kiran ga yaransa na kasuwa akan su bincika masa Alhaji Zakari a shagonsa.
Mamaki ya kama Labaran, yace, "Alhaji wane kuma Alhaji Zakari za'a gani a kasuwa bayan shagon nasama yadawo naka?".
Zaune sosai Alhaji garba ya tashi, dama kwance yake amarya namasa tausa, "Labaran ban fahimci zancen nakaba ai nima, bani a warware".
Labaran dai baiyi jayayya ba ya ?akko labari tundaga tushe ya zayyanema Alhaji Garba, babu shiri kuwa ya rikito a gado, amarya na tambayarsa mike faruwa bai kulataba.
Sashen Hajia Deluwa ya nufa, wadda zuwa yanzu ka ganta dole tabaka matu?ar tausayi, dukta kuma ficewa hayyacinta, ?an ku?in da su Ashir suka amso miliyan goma suka bata, sukuma suka rabe sauran harda ?anwarsu dake karatu. Shagon kuma yazama na yayansu saboda shine ya saya. Amma sai sam ku?in basu gusar mata da damuwarta ba, itadai tafi bu?atar mijinta a gareta, babban tashin hankalinta na gaba kuma warin da takeyi, wanda hatta ?a?anta saisun toshe hanci suke iya zuwa inda take, jiya wata ?ar uwarta tazo gidan, amma sam kasa zama tayi tanata faman toshe hanci, ita kuma ko ka?an batajin warin saima ?amshinta na gayu datake zubawa a kullum........
Banko ?ofar da Alhaji garba yayine da ?arfi yay matu?ar firgitata ta mi?e zumbur tana kallonsa,
"Alhaji lafiya kuwa?".
Hannunsa toshe da hanci yace, "Ban ku?ina".
Cikin sanyaya murya tace, "wane ku?i Alhaji?".
"O bama ki saniba ko? To wanda ?a?anki sukaje suka amsa a kotu".
Baki ta ta?e cikin ?arfin hali, "Yanzu dan ?a?anka sunci wa?annan ?an ku?in daga cikin abinda yake ha?insu shine zakazo kanamin haya?i, idan ka mutu sukeda gadon su ai".
Galala yay yana kallonta tamkar wani soko, yace, "Aiyyyy dama maganar danakeji a gari gaskiyane? Bakida buri saina mutu kuci gado keda ?a?anki, to aiko yau ?innan basai gobeba zaki kama gabanki, saidai kisa a biyo dare yau a kasheni, kosu su Ashirun suzo su karni gobe a raba muku gado, bankuma yadda ke?in jahila baceba sai yau wlhy, dama da ALLAH yayma namiji arzi?i to kullum burin mace ya mutu suci gado itada ?a?anta, shiyyasa kikaita korar min mata kina musu asiri ko?, to ai dama tuni bokan naki yazo ya sanarminin kafin ya mutu, dan har kasuwa yazo ya sameni ya fa?an duk tsiyatakun da kuka aikata, harda haukata yarinyar Alhaji zakari, wanan ne yasani burin barmasa ku?in, dama ina masa barazana ya banine domin hakan yazama izinina a garesa ya kiyayi halayyar cin bashi, shine ku ?wararru kukaje kuka amshi ku?in, kisani wanan karon bazakuci a banzaba kamar yanda kuka sabaci, insha ALLAHU kuma saikin rigani mutuwa, kije na sakeki saki Uku, kuma a yau nakeson ki barmin gidana".
Wani gigitaccen ihu hajia deluwa ta kwala ta yanke jiki ta fa?i a wajen babu rai.
Alhaji garba baibi takantaba yay fitowarsa.
A wanan mummunan yanayin autarta data dawo daga makaranta yau cikin ?okin ganinta ta isketa, bata sanarma kowa zatazoba saboda ta basu mamaki, sai ita ta tarar da abin mamakin.
Itace takira baban yayansu a waya.
Ankai hajia deluwa asibiti a san?ame, bakuma a samu farfa?owarta ba sai washe gari, wanda har zuwa lokacin babu alhaji garba babu dalilinsa, ama ranar suka cane dubai yawon amarci shida amaryarsa.
Hajia deluwa dai sai yamma lis ta farfa?o, saidai kuma tasamu mummunan ciwon ?arin jiki, ?arinta na dama baya aiki gaba ?aya har ido ?aya, saida ?aya take gani shima bishi-bishi, baki kuwa ya karkace yana zirar da yawu.
?a?anta sun shiga tashin hankali matu?a, sunyi kuka sosai dan suna ?aunar uwar tasu, sai dai basuda yanda zasuyi.
Haka suka cigaba da jiyyarta, tun sunayin abun da marmari har suka koma biyan likitoci su kula da ita, suko suka koma kan harkokinsu, sai dai suzo su dubata. A kwana a tashi kuma sai dubiyarma ta fara gagararsu zuwa, dan saisu ha?a kwanaki biyu basu le?ata a asibitiba.
Likitoci suma suka fara ?osawa da ?azantarta, aiko suka kira su Ashir suzo su kwashi abarsu.
Wannan ne silar dawowarta gidan jiyya, har kuma sanan Alhaji garba bai dawoba, dan sunacan suna hutawarsu da amarya dake fama da ?aton ciki, haihuwa yau ko gobe.
Tunda aka maido hajia deluwa gida fa babu mai mata kallon arzi?i, dan bilki mai aikima tuni ta gudu abinta, haka hajia deluwa zatayi kashinta da fitdari babu mai gyarawa, ga tsoro da ake bata kullum, taita ganin halittu masu ban tsoro, haka zataita kuka babu damar ihu, wanima lokacin dariya za'aita ?a??akawa, amma tarasa a inane, kokuma aita kuka, ko kukan dabbobi kala-kala, gaba ?aya ta susuce, itaba mahaukaciyaba ita ba gawaba. Mai kula da itanma saita gadama take bata abinci tana toshe hanci, data zirara mata take baro sashen.
autarta kuwa ?iri-?iri tabar zaman sashen, takoma sashen babanta, saitayi satima bata kalli sashen hajia deluwaba.
Ruwa a jallo hajia deluwa ke fatan ganin koda ?aya daga cikinsu Jiddah ne ta nemi gafara, tasan dai bama kowane zai yafe mataba, dan ita kanta batasan iya adadin matan data salwantar ba akan kar'a zauna mata da miji, wasu jini ta sakar musu, wasu warin ja?a, wasu hauka, wasu kuwa taita ?arar da cikin da suka samu dan karsu haihu a gidan, watama muguntar data saka bokanta yayi ta manta kalarta, gashi a yau tana girban abinda ta shuka.
ALLAH ka shiryemu, ka tsaremu daga son zuciyoyinmu??????
???????????