Showing 33001 words to 36000 words out of 121675 words
ya matseta tun d'azun shita samu ta tsugunna yi cikin kwamin wankan dake bayin. Wata muguwar fad'uwa gabanta yayi lokaci d'aya, ta waro idanu waje tanabin jan abun da ke gudu cikin kwamin Wanda da alama jinine.
A fili ta furta "Jini! Kuma?, ni Jiddah mike faruwa dani haka?". Ido takuma sakawa sosai dan sake tabbatarwa, lallai da gaske jinine wannan, to amma ai yau kwananta uku kacal dagama period, ina kuma tasamo jini.........."
Bata ankaraba kawai taji maganar mutum a kanta. Alhaji garba daya gaji da jiran fitowarta ya biyota, harya shigo bata saniba, shima bin jinin yay da kallo kafin ya furta "K minene hakan?".
A rikice ta juyo tana kallonsa, in banda iskanci mizaisa ya biyota band'aki, saurin mik'ewa tayi tana sakin zaninta, dukda jinin dake bin k'afafunta bata damuba. Shiko ya k'urama jinin data zubar ido, sosai ransa yakai matuk'ar 6aci, dan wannan jinin ko kad'an bai masa adalciba, batareda ya tanka mataba yafita fuuuu. Da kallo tabisa harya 6acema ganinta sannan ta lumshe idanu tana sauke ajiyar zuciya. Bata kawo komai a rantaba tahau gyaran jikinta, dan ita duk zatonta ko jinintane kemata wasa, sai dai yanda yake zuba da yawa yabata mamaki. Tsaf ta gyara jikinta da wajen sannan ta fito, dan komai da mace zata iya buk'ata akwaishi a bayin, ganinma an ajiye always da fants abin har mamaki ya bata, saikace ansan da zuwan jinin Nata.
Koda ta fito babu Alhaji babu dalilinsa, bata wani damuba tayi kwanciyarta bayan ta canja zaninta kawai, amma rigar da d'an Kwali duk da abinta ta kwanta. Taja bargo ta lullu6e saboda sanyin ac ya addabeta, itakuma batasan yanda ake kashewaba, har kanta ta saka a bargo. Sai dai yanzu takasa barci sa6anin d'azun, tunanin y'an uwarta da kewarsu tadawoma zugiyarta sabuwa, tuni tafara zirar da hawaye. Ta dad'e tana kuka, dan harkusan karfe uku kafin barci 6arawo ya saceta bayan tasamu tayi addu'a da k'yar.
¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï
Alhaii Garba dai daga k'arshe sai wajen Hajia deluwa Yakoma ya sauke kayan wahalarsa, inda Sam tak'i saurarensa daga farko, dak'yar ya iya shawo kanta bayan sunyi cinikin zai bata dubu d'ari biyar. Atake kuwa yaymata transper d'insu dan hakan shine k'a'idarta Dama, saitaji dumus a hannu ko a asusun banki ( wannan bawai sabon Abu baneba).
Aiko ranar tagane kuranta, dan saida takoma yimasa kuka rurus sannan ya hak'ura ya barta badan yasamu yanda yakeso ba, a zuciyarsa kam sai kuma tsinema jinin Jiddah yakeyi, dayanzu yanacan yana morewarsa, sai sanda yaso barinta, amma ita wannan ta ishesa da shegen raki badan yagama nutsuwaba. (??????¡â)
*Wanene Alhaji garba?*
Alhaji Garba Mai tabarba kowa ya sanshi dashi, haifaffen cikin birnin kano kuma girman nan, sana'ar tabarma dayakeyi tun yana matashi shine sunan ya bishi, Wanda sanadin tabarmar ALLAH yay masa arzik'in da harya bud'e kamfanin da akeyinta, ahankali arzik'insa yacigaba da bunk'asa.
Matarsa ta farko (ladan noma) itace Yahanasu, wadda tun tana k'arama ake kiranta da suna Deluwa, tuni sunan yagama binta harma an manta da yahanasu gaba d'aya.
Yaransu bakwai da ita, maza hud'u Mata uku. Y'ay'ansa Mata biyu sunyi aure shekara d'aya kenan, mazan kam babban ne yahuza kawai yayi, amma sauran ukun duk sunanan suna ruwan ido, iyayansu kuma babu maicewa basu k'yautaba, duk d'insu sunyi katunema a k'asashen k'etare, yanzu haka autarsu Zaliha wadda zasuyi sa'anni da Jiddah tana Niger karatu.
Tun zamanin kuruciya akaima hajia deluwa shaidar batason zama da kishiya, Dan Alhaji Garba yayi aure-aure bayan ita amma babu mai rufa shekara biyu take barin gidan saboda masifar hajia uwargidansa. Sannan koda ciki kika samu to dawuya ki haifeshi, kodai kiyi 6arinsa kokuwa ma ki haifeshi babu rai, mace d'ayace tahaihu dashi bayan hajia deluwa, yaran yana shekara d'aya da haihuwa ya rasu Alhaji Garba kuma ya saketa.
Dangin Alhaji Garba basu isa su ra6eshiba, wannan yasaka duk sanda zai sake aure cikin d'oki suke, saidai auren baya wani Kai labari.
Hajara itace mace ta k'arshe daya sake aure, wadda a k'alla takai shekara uku a gidan, kowa yafara murna da fad'in Hajarah ta gagari Hajia deluwa sai kwatsam ranar ya dank'ara mata Saki. Tundaga nan kuma bai sake zancen aureba kusan shekara hud'u kenan, yay hak'urin cigaban zama da matarsa wadda tun zamanin kuruciya bata yarda yay kwanciyar aure da ita saiya biya, (wanna daliline yake sakashi yawan aure-aure, harga abin Na binsa har tsufa) ahaka ALLAH ya albarkacesu da haihuwar y'ay'anan bakwai.
Kwatsam ranar sai yaga Jiddah kusan shekara biyu data wuce, to amma kuma yarasa ta inda zai tunkari Alhaji Zakari yaro da zancen, dan shima yasan ba kanwar lasa bane, sannan yasan mafi yawa daga sirrkan gidansa, abokinsane shekaru masu yawa wadda sanadin kasuwanci suka kulle, saidai Alhaji Garba yafi Alhaji Zakari kud'i nesa ba kusaba, dan ko a kwatancema bazasu had'uba. To rana tsaka kuma saiga Alhaji Zakari yazoma Alhaji Garba da buk'ata, wadda itace sanadin daya samu damar sako zancen Jiddah a tsakkiyar hark'allarsu. Shiko Abba domin biyan buk'atarsa saiya amince, yakuma dage saboda Neman biyan buk'atarsa.
Sosai Hajia Hindu ke k'awance da Hajia Deluwa tuni.
¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï
Sai k'arfe kusan takwas ALLAH yabama Jiddah ikon tashi, dan barcin dabata samu tayiba shiya janyo mata doguwar makara, da addu'a d'auke a bakinta ta farka, idanunta duk sunmata nauyi luhu-luhu saboda kuka, hakama kanta jingim take jinsa, dak'yar ta iya sakkowa a gadon tanufi bayi tana hawayen kewar ahalinta da bak'incikin wannan auren.
Wani mugun mamakine ya kamata sosai dankuwa k'amas babu ko d'igon jini a jikin always d'in data saka, hakama jikinta normal yake, to kodai jiya ta iske jinin a wajen ne itakuma ta tsugunna? To amma kuma ai tagansa har a jikinta ajiyan kuma? Kai wannan lamari da mamaki, itadai dukma takasa fassara lamarin, dan haka tahad'a ruwa Mai d'umi tayi wanka, irin wad'annan ta6e-ta6en kayan y'an gayun dukta iyasu gidan aunty Nafisa, shiyyasa anan basu zame mata sabon abuba, itadai wankan tsarki tayi saboda kore kokwanton ko jinintane yaymata wasa, koda ta fito saita rama sallarta kamar yanda shai'a tabamu damaryi.
Koda ta idar saman gadon ta koma ta sake kwanciya tana cigaba da kukanta, har kusan k'arfe d'aya bataji motsin kowaba a gidan, ga yunwa tafara addabarta dan batasan iya lokacin data d'aukaba rabonda taci abinci mai nauyi. Da k'yar yanzuma tatashi tayi salla, bayan ta idar ne tasamu zarafin bud'e ledar da Alhaji yashigo da ita jiya, dan itadai har jiri-jiri take gani.
"Alhmdllh" tafad'a saboda ganin kaji dasu ice-creem da sauran kayan kwad'ayi irinsu chocolate mai dad'i dawasu kalolin biscuits dadai tarkacen kayan kwad'ayi. Kazar kawai ta d'auka taci kusan rabi, saida taji tafara zufar k'oshi sannan ta mik'e taje ta wanko hannunta da bakinta.
Handbag d'in datazo da ita gidan ta bud'e tazaro Qur'ani madaidaici a girma tazauna tafara karatu cikin suratul Bak'ara da muryarnan tata mai saka zukata nutsuwa. Har aka kira sallar la'asar tana karatunta, saida taji za'a shiga salla sannan tayi addu'ar ta mik'e ta gabatar da salla.
Yanzu dai ta daure ta gyara bedroom d'in musamman ma gadon. Amma koda wasa batayi tunanin lek'a koda falonba, tana gamawa takoma ta zauna tana tunanin su Ummanta ko misukeyi yanzu oho. Hawaye taji suna kwararo Mata, jin kanta zai Fara ciwo saita maida akalar tunaninta zuwa yin Azkar Na yamma.
¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï
Ango Alhaji Garba kam fitace ta gaggawa ta sameshi tunda sassafe, dan haka yafita batareda ya lek'o Jiddah ba, har dare kuma bai dawoba.
Hajia deluwa kam dak'yar yau ta iya tashi tana tsinema Alhaji garba a zuciyarta, tareda zubama likitocin da sukawo maganin dayakesha ALLAH ya isa fiyeda cikin buhu, tasamu nasarar aikinta amma wuyar tadawo kanta....
Tana cikin wanna tunanin Kira ya shigo wayarta, kallon wayar tayi a yatsine, amma ganin Mai kiran saita d'auka har jikinta Na 6ari.
"Malam lafiya dai kuwa?".
Daga can malam na barewa yace, "Dadai sauk'i, amma hajia haka mukayi dake? banace idan an daceba ki kirani tun a daren nasan abunyi? Kinsanfa wannan yarinyar nafad'a miki tanada tsari sosai a jikinta, dan bata wasa da addu'a ko kad'an, wannanma munsami damartane saboda taimakon batada lafiya".
"Malam kayi hak'uri dan ALLAH, wlhy anyi nasara, nima wahalar daya maido kaina wadda yayma amaryar shiri shine yahanani sukuni, yanzudai zance maka an dace, dan jiya a sashina yadawo ya kwana yana masifa, Dana tambayesa kuma ya sanarmin komai akan jini takeyi wai".
"Ni dama nasan za'a dace, ammafa aikin tun a daren jiyama ya warware, dan tanayin addu'ar barci aljanin yakasa matsarta, hasalima kasa zaman gidan yayi gaba d'aya saida ya dawomin, ayanzu danake miki magana lafiyarta lau, hasalima babu sallar dabatayiba a yau".
Sosai hankalin Hajiya Deluwa ya tashi, jikinta Na rawa tace, "Malam yanzu minene mafita?".
"Mafita kam a yanzu dai babu ita daga gareni, dan saina sake sabon shiri akanta da Neman lagonta, ammafa gaskiya komai zai iya faruwa tsakaninta da mijinki, dan naga hakan a istaharar danayi".
Rud'ewa sosai hajia deluwa tayi, bata kuma sauraren malam ba ta yanke wayar tana zagaye-zagayen Neman mafita. ta nufi k'ofa yafi sau biyar da nufin tafiya sashen Jiddah saikuma zuciyarta ta gargad'eta ta dawo baya, daga k'arshe dai Kira ta kwalawa bilki Mai aikinta.
Bilki tazo da sauri tana fad'in "hajia gani".
Kallonta Hajia deluwa tayi tana d'an Huci, "Balki kunbama amarya abincine?".
"A'a Hajia ai baki bada Umarnin hakanba".
"Jeki sashenta yanzunan ki kiramin ita".
Da to bilki ta amsa tana mik'ewa zuwa sashen Jiddah.
A zaune ta isketa tazuba tagumi, sai dai ba tunani takeba Azkar takeyi.
Sallamar Bilki ta sakata d'agowa ta kalleta. Bilki tad'an risina ta gaidata, amsawa Jiddah tayi cikin Y'ar fara'ar yak'e. Bilki tace, "Amarya kizo hajia Na kiranki".
Ba k'aramin fad'uwa gaban Jiddah yayiba, ta had'iye wasu yawu masu kauri kafin ta d'agama bilki Kai da k'yar.
Fita Bilki tayi domin ta jirata a falo.
Gaba d'aya Jiddah ta rikice a tsorace take, jikinta sai rawa yake ta d'auki hijjab d'inta ta tasaka ta fito, a falo ta iske bilki, dan haka taimata jagora zuwa 6angaren hajiya deluwa.....
???????????
Malam kam ganin burinsa Na farko bai cikaba saiya yanke shawarar aurama malam Aliyu Maimunatu, dan haka babu 6ata lokaci yadsamu Iya habi da maganar.
Shiru tad'anyi tana nazarinsa, kafin zuwa can ta sauke nannauyan numfashi "Malam bank'i wannan had'inba, amma kana ganin Aliyu ya warke daga lalurarsa?".
Murmushi kawai malam yay yad'an girgiza kansa da mamakin furucinta, "Habiba kenan, wannan shine matsalarki kenan? to gaskiya bamuda tabbas akan hakan, sai dai munada yak'ini da addu'ar samun nasara, duba da yanda yay amfani da magunguna da dama akan lalurar domain Neman waraka".
"To ALLAH ya datar damu, aishi lamari na aure ba'ai masa shishshigi, Zan Kira Sani muyi magana (kaninta Baban mamuna)".
Malam yace, "To shiken sainaji daga gareku, dan inason ayi auren kusa, daya dawo da sati biyu, tunda yanzu saura sati biyu ya dawo, kinga nanda wata d'aya kenan".
"Hakane, insha ALLAH zakaji".
Bayan kwanaki uku dayin wannan magana iya Habi taima malam maganar sukai kud'i ga mahaifin maimunatun, danshi yayi farinciki kwarai da gaske da wannan had'in.
Sosai malam yayi murna, dan haka babu 6ata lokaci akayi komai aka gama. Koda malam ya sanarma Aliyu cayay ALLAH yasa haka shiyafi alkairi kawai. Dama malam baya hangen matsala daga gareshi, saboda yasan biyayyar Aliyu akan mahaifa.
Kwana goma dayin wannan magana Aliyu ya dawo, d'alibansa da malam sunyi matuk'ar farinciki da dawowarsa dakuma nasarar daya samo.
Kwana biyu da dawowarsa y'an uwansa sukazo yimasa sannu da zuwa, aunty Ruk'ayya da Siyama.
Yana k'aunar y'an uwansa haka suma suna k'aunarsa, hira sosai ta 6arke a tsakaninsu har akazo kan maganar aurensa da Maimunatu, a yanda ya lura duk basuso had'inba, dan haka yashiga kwantar da hankalinsu cikin nasiha da nuna musu muhimmancin yin k'ysk'yk'yawan zato ga musulmi. Hakan ne yad'an saka kwanciyar hankali agaresu, har suka fara jefa kalmar fatan alkairi ga auren nasa, dan koba komai suma sungaji da zamansa haka, kowa yana girmamashi matsayin babban mutum amma kuma bashida cikon rigar kamala Na aure, idan har yay auren koyaya mutuncinsa da k'imarsa zasu kuma bayyana ga jama'a.
Duk abinda yadace su tsara Na al'ada Wanda baishiga hurumin addiniba sun tsarashi aranar, tareda had'a k'arfi da k'arfe wajen burin fita kunya, dukda auren gidane bazai hana ai kananun maganaba idan sun gaza.
A 6angaren malam ma sunata k'ok'arin gyara gidan Aliyu, Wanda tunbayan rabuwar aurensa da Asma'u ya saida wancan gidan ya cika yasai fili, yana Saudia yayta aiko da kud'i a hankali aka gine filin da madaidaicin gida Wanda akai masallaci Mai d'an girma a jikinsa da islamiyya Mai ajujuwa da bazasu gaza shida ba. Iya gwargwado gidan yayi k'yau, sannan duk Wanda yagani yasan ba tsarin zaman mace d'aya baneba, kusan komai angama sai abinda ba'a rasaba, dan haka a yanzu malam ya tsaida malam mustafa akan k'ok'arin kammala komai.
Ahaka aka shiga hidimar biki, ango kuwa kosau d'aya bai ta6a ke6ewa da amarya ba da sunan zance, yace ai gidansa zata, minene abin 6ata lokaci a waje.
Shagali biki yafara gudana tamkar yanda Shari'a ta tanadar, babuwani hayaniyar shed'anci Mara amfani, ranar juma'a bayan sakkowa masallaci aka d'aura auren Aliyu da Maimunatu acan gidansu dake anguwar d'orayi. Taron d'aurin aurene daya samu halattar mutane daban-daban a sassan Nageria, burin kowa ya nuna halacci ga Sheikh Aliyu Abdul-ra'uff Maina, Alhmdllh anyi cikin nasara an k'are lafiya, bayan d'aurin aure aka gudanar da gagarumar walima wadda malamai suka zazzaga wa'azi akan aure da rayuwar ma'aurata, tareda jan doguwar Addu'a ga wad'annan ma'aurata.
Amarya Maimunatu tana cikin farin cikin mallakar cikar burinta, yayinda ango baka gane nasa yanayin.
Bayan kammala walima aka mik'a amarya d'akinta tareda fatan alkairin ALLAH yasa bad'i adawo suna...............???
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
_Zaku iya samun RAINA KAMA a audio ta wanann link d'in Na sama, Abban Dausayi YouTube channel tv??????_
*_Bazan 6oye mukuba jiya bak'aramar dariya naci akan Comments nakuba gaskiya, lallai nalura kund'auki aurennan da zafi, Abba zakari da Alhaji garba sun zagu babu k'arya????, ALLAH ya taimakeni ba a had'a daniba nima????¡â._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????
[11/30/2019, 1:17 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[14?15]_*
..............Sosai Jiddah ke yaba k'yawun tsarin sashen hajia deluwa, dan bak'aramin kud'i aka narkaba gaskiya, gabanta ya fad'i saboda hango Hajia deluwa dake hamshak'e cikin kujera, taci kwalliya cikin wani ubansun leshi ruwan ganye, ga wani kamshi Mai kwantar da hankali datake zabgawa.
Tunda Jiddah ta shigo itama Hajia deluwa kemata kallon k'asan ido daga k'asa har sama, sosai Jiddah taimata k'yau fiye da yanda hajia Hindu ta nuna Mata ita a hoto, dukda a yanzu cikin hijjab take kuwa.
Gabanta Jiddah taje ta zauna a k'asa, cike da girmamawa muryarta a matuk'ar sanyaye tace, "Hajia ina yini".
Cike da yatsina hajia deluwa ta amsa da "lafiya amarya ya kwanan amarci?".
Shiru Jiddah tayi takasa amsawa, yayinda hajia deluwa keta wani ta6e baki tana gyara zamanta, cikin dakewar murya tace, "To amarya inason muyi magana ta fahimta dake, dan banason biyo miki ta hanyar da zaki gaza 6illewa, da farko dai kisani ina matuk'ar son mijina da dukiyarsa, babukuma wata danake k'aunar tazo ta haihu dashi bayan nawa y'ay'an, kullum burina dagani sai y'ay'ana mu mallaki komansa, a girme Na girmi Mamanki ma balle ke nasani, Alhaji kam inda su Yahuza auren wuri sukayi sun Isa Haifa masa kamarki matsayin jika, inason nabaki shawarar kibar gidannan tunda arzik'inki, Zan baki ko nawa kikeso domin kibarmin mijina, dan tabbas nasan dukiyarsa tasaki aurensa, dan Ku y'an matan yanzu duk inda naira take kuna a nanik'e, abinda yasa duk nake miki wannan jawabin cikin lalama saboda nakula kamar zakiyi hankali, sannan kece mafi k'ank'anta a matan da Alhaji yata6a aura adukkan aure-aurensa. Kifita kisamu saurayi dai-daike ki aure, inma baida