Showing 3001 words to 6000 words out of 121675 words
islamiyya kawai.
Zuwan Hindatu saiya kuma harmutsa komai Na gidan, domain kuwa shekararta d'aya ta haihu d'a Namiji, murna da shagalin da Alhaji Zakari yayi 6ata lokacine, bayan shekara biyu takuma tagwaye duk maza. Nanfa likafa taci gaba, dan gidan da Alhaji Zakari ya gina dukda girmansa sai yace Hindatu ce kawai zata koma ciki. Dukda abin ya6ata ran Yagana saita danne, tai masa ALLAH ya sanya alkairi.
Acanma akayi sunan tagwayen hindatu. Bayan suna babu dad'ewa Nafisa tasamu miji, babu bincike babu komai Alhaji Zakari yace yabashi, takaici Yakama mahaifiyar Nafisa da Yagana (dayake mahaifiyar Nafisan suna mutunci da yagana sosai saboda ruk'on gaskiya da taima y'arta, itama tayi aure tuni ta hayayyafa ma).
Haka dai akasha biki, Alhaji Zakari baima Nafisa wani abun arzik'iba, a cewarsa baya zuba jari inda bazai kwashi ribaba. Komai sai mahaifiyarta da yagana sukayi iya k'ok'arinsu, saikuma dangi.
Sosai Alhaji Zakari ke nuna banbanci tsakanin y'ay'ansa maza Na wajen Hindu (wadda suke kira Aunty Amarya) dasu Jiddah.
Hindu takuma saka haihuwar d'a Namiji, yanzu yaranta hud'u duk maza, kalifa, Hassan, hussen, Najib.
Alhaji ya sakasu makaranta mai tsada, komai suke buk'ata an tanadar musu, sun taso y'ay'an Hutu, Ana shagwa6asu ainun.
Yayinda gasu Jiddah ba haka bane, ko Alhaji zakari zai musu Abu saiyayi musu tozarci, bakuma zaiyi yanda ya kamata ba, saiya had'a wata baizo wajen Ummansu Jiddah da sunan sauk'e mata hak'k'i Na aureba, kayan abinci ma saiya gadama, saidai yahaya yakawo, wataran kuma ya hanashi ma.
Jiddah iyakarta firamare itada Nafisa, yanzu haka shekararta 20 dai-dai, tana makarantar islamiyya, hafizace ta alkur'ani mai girma, tayi zurfi matuk'a a fannin ilimin addini, ta halarci musabak'an alkur'ani kashi-kashi, kuma tayo nasara, amma a boko saidai abinda ba'a rasaba da Wanda k'annenta su Zarah ke koya Mata.
Da taimakon Uncle yahaya dana Umma, Zarah da walida ke karatu, dukda makarantar gwamnati sukeyi saida ji6in goshi ake iya kare musu buk'atun yau da kullum, dukda ALLAH yayima mahaifinsu arzik'i gwargwadon hali babu ruwansa da su.
Zarah Na shekara 18, tana aji biyar a makaranta, tasamu Matsala ne a wata shekara aka maidata baya, amma da yanzu tagama secondary, itama babu laifi tana ta6a karatun addini. Walida kuwa tana 16 itako ajinta uku a makaranta, sune zasuyi jsce yanzu. To ankoma Hutu amma gashi uncle yahaya bayanan, yayi tafiya, shine Umma tace Jiddah taje wajen Abbansu kozai taimaka ya bada, amma saita dawo da 6acin ran cin mutuncinsa dana matarsa hindu (aunty amarya).
???????????
*_MUN DAWO LABARI_*
Sai yamma lik'is Zarah da Walida suka dawo nik'i-nik'i da ledoji, Jiddah dake tsakar gida tana tuk'in tuwo akan gawayi tai sagade tana kallaonsu, dukda tasan hakan daga aunty Nafisa ne, kullum cikin k'ok'arin k'yautata musu takeyi da abinda ALLAH ya hore Mata.........
Maganar Zarah ce ta katse ta.
"Kai Yaya Jiddah, irin wannan sakin baki haka? ALLAH sai sauro ya antaya ciki".
Walida dake dariya tace, "gashinan kuwa yana yawo k'umu-k'umu wlhy, aimu gidannan ALLAH yay mana arzik'in sauro kam tamkar d'angwate da kud'i".
Dariya sukayi su duka har Jiddah, ta rufe tukunyar tuwon data gama tuk'awa tana d'an yarfama rutsin wutar ruwa danya rage zafi kar tuwon ya k'one. "Y'ammatan Umma ya kuka baro Aunty tamu dasu Affan?".
"Lafiya lumi wlhy Yaya Jiddah, tamace ace miki ta gode da cika alk'awari".
Murmushi kawai Jiddah tayi, dan tasan laifinta.
"Wai ina Umma?". 'Cewar Zarah dake k'ok'arin shiga bayi'.
Jiddah tace, "Taje gidan Uncle yahaya, Maman Sadiq ce k'irjinta ke ciwo, shine taje dubata".
Walida da Zarah suka had'a baki wajen fad'in "Ayya ALLAH ya k'ara lafiya to".
"Amin", Jiddah ta amsa.
Ledojin walida ta d'auka takai cikin d'aki tana fad'in "Yaya Jiddah mi zamu tayaki dashine? Naga yau aikin yamuku dare".
"Wlhy kuwa auta, amma nama gama, dan miya na farayi sannan, sai dai idan tsakar gidannan zaki share a kunna maganin sauro musami wajen zaman hira".
Walida ta amsa da to tana nufar inda tsintsiyarsu take.
Zarah ma koda tafito sai tace bara ta kwashe tuwon ita kuma. Haka suka k'arasa dukkan ayyukan suna hirarsu a nutse, dolene su burgeka, dankuwa akwai shak'uwa da k'aunar juna mai yawa tattare dasu, hirar tasuma duk akan Auntynsu ce Nafisa.
Ana kiraye-kirayen Sallar magriba Umma ta shigo, a lokacin su Jiddah sun gama komai, sai k'ok'arin d'aura alwala da sukeyi, amma banda Zarah dake fashin salla.
Atare suka amsa sallamar Ummansu, yayinda suke mata sannu da zuwa da tambayarta mai jiki.
"Da sauk'i Alhmdllh, y'an yini sai yanzu muke ganinku?".
"Wlhy kuwa Umma, aunty dasu Affan Na gaisheki, yanata kukama saiya biyomu gashi gobe akwai makaranta".
Y'ar dariya Umma tayi tana cewa, "Ja'iri yau kuma? Amma ranar dayake yaga babansa ai babu yanda banyi ya zaunaba yak'i. Yaya kuka baromin yarinya ta?".
"Lafiya lau take Umma, ammafa ni sai naga aunty Nafisa kamar laulayin ciki take?".
Harara Jiddah ta zubama Zarah mai maganar,
"O ke Zarah, wlhy bakida kunya, yaushe kikai girman gane mai ciki?".
"Tab lallai, kaji Yaya Jiddah da wani batu dan ALLAH, cikin saikace wani abu........"
Hijjab Umma ta cillam¨¤ Zarah tana fad'in "Zarah k'aniyanki kinji, Anya kuwa ba aure zansa ayi mikiba?".
"Wlhy dama yafi Umma, dan Idonta kullum k'ara fetsarewa yakeyi yarinyar nan".
Waleeda dake alwala ta kwashe da dariya, yayinda Zarah ta kwad'a Mata harara.
"A'a nikam Yaya Zarah karki huce kaina, bani nakar zomanba".
Haka kullum suke cikin tsokanar juna da wasa da dariya, hakan kuma baisa raini yashiga tsakaninsu ba, Ummansu ta maidasu tamk'ar k'awayenta, sune abokan hirarta sune shawararta, shiyyasa suma basuda wasu aminai a waje sai ita, saikuma a tsakaninsu su biyar.
Sune abokan juna, sune aminan juna, sune y'an uwan juna.
*_Dare_*
Da daddare suna zaune a tsakar gida sunacin tuwo, yayinda Zarah kema Umma bayani akan kayan da sukazo dasu.
"Umma tsarabar Dadyn Affan ce Aunty tace mu kawo, takuma bamu kud'in makaranta tace gobe muje mu biya mukoma makaranta".
Umma tace, "ALLAH sarki Nafisa baiwar ALLAH, ALLAH ya saka Mata da alkairi, yamata albarka itada zuri'ar ta daku baki d'aya, ALLAH ya cigaba da had'amin kanku kunji".
"Amin Umman mu".suka had'a baki wajen amsawa. Kayan aka shiga bud'ewa, sabulan wanka da wanki, sai man shafawa da omo, kayan shayi da maltina rabin katon, da biredi manya guda uku da kud'in makarantar su Zarah sai kaji biyu gasassu.
Addu'a sukaita zubama yayar tasu, Umma ta kirata tai mata godiya da addu'a, tace aima dadyn Affan godiya shima.
Sund'an ta6a hira zuwa tara na dare suka mik'e domin kwanciya, saboda sauro daya damesu gashi kuma su Zarah zasu makaranta gobe.
????????
Da wuri su Walida sukai shirin makaranta, sannan sukai Karin kumallo da d'umamen tuwon jiya da Jiddah ta tashi da wuri ta d'umama musu.
Bayan wucewarsu makaranta tagyara gidan duka da taimakon Umma, dukdama gidan bawani babba baneba. Saida tagama komai itama zuwa tara da rabi tai shirin tafiya Islamiyya.
Tsaf tai shirinta cikin Uniform d'inta kalar ruwan toka, (ash color) yad'au guga sai d'aukar ido yake, turarenta da Aunty Nafisa ke k'ok'arin saya musu ta fesa kad'an, sannan ta d'aura Nikab, saidai bata sakeshiba tafito rataye da jakarta mai d'an tsawo kamar suwaga. 'Dakin Umma tashiga da sallama, tana zaune da alama sallar walha ta idar.
"Umma naga bakiyi Addu'a ba, gashi nakusa makara, nawuce saina dawo".
Kai Umma ta d'aga Mata batare da tayi magana ba, dan batason katse addu'arta.
Jiddah Na fitowa soro ta Saki nik'ab d'inta tare da gyara hijjab d'inta tai addu'ar fita daga gida sannan tafito. Tafiya take a nutse kuma a sanyaye, kanta a k'asa dukda ta sakaye fuskar tata da nik'af. Kullum haka take cikin suturta jikinta, dayawan y'an anguwar a haka suka Santa, saika Tara mutum goma basu iya siffanta maka kamannin fuskartaba, saidai a tafiya kokuma kwatancen ta da suna mai saka hijjab har k'asa da nik'ab, amma mafi yawancinsu sun manta da kamanninta, dan tunda tafara mallakar hankalinta takoma suturta fuskarta..............???
*_Yanda kuka kar6i labarin yasakani farinciki matuk'a, ina godiya??????, dan haka kumuje Zuwa my guys??¡â ??¡â_*
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[11/16/2019, 6:33 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[3......]_*
..............Malam Abdul-ra'uff Maina babban malami ne da akeji dashi cikin Najeriya da wasu k'asashen k'etare makwaftan k'asar, ALLAH ya azurtashi da tarin ilimi, ga tsage gaskiya komai d'acinta a wa'azinsa, yanada manyan makarantun addini sosai a cikin Najeriya da k'etare, dukda bashine kad'ai ya ginasuba, akwai taimakon attajirai da jama'ar gari masu buk'atar d'aukaka kalmar ALLAH.
Matan malam Abdul-ra'uff hud'u cif, duk da dai a yanzu uku suka rage, ALLAH yayma matarsa ta biyu rasuwa shekaru kusan 15, ALLAH ya azurtashi da y'ay'an da adadinsu zai iya kaiwa 17 a duniya kuma maza da Mata.
Huwaila itace uwargidansa, yaran gidan suna kiranta da suna Hajia bah-bah, yaranta shidda, maza uku mata uku, Muhammad, Zainab, Abubakar, Adawiyya, Ni'ima, Mahmud.
sai ta biyu da ALLAH yay mata rasuwa, Sunanta Hauwa'u, suna kiranta da Annau, yaranta uku, Ruk'ayya, Aliyu, Siyama.
Ta Uku Habiba, suna kiranta iya habi, yaranta hud'u, Umar, Bilal, Aminatu, Abdul-aziz.
Sai Amarya Mariya, suna kiranta gwaggo, yaranta hud'u itama, Binta, Usman, Asiya, Na'imah.
Agidan malam bazamu ce ba'a kishiba, anayinsa kam sosai, saida ba kishi Na haukaba, kishi akeyi Na matan da sukeda ilimi.
Mafi yawa daga cikin y'ay'an malam ALLAH yabasu ilimi sosai, amma Wanda zai iya bugar k'irji yakira magajinsa Kai tsaye shine *ALIYU*.
*Aliyu* mutumne nutsatstse, ma'abocin zirfafa ilimin addini da yad'ashi, yanada sauk'in Kai sosai, bashida fad'a ko yawan hayaniya, komai nasa zaka gansa a sanyaye akuma nutse, badan bashida k'arfi baneba, a'a sanyi tamkar halittarsace, dan ko maganarsa haka take cikin sanyi da nutsuwa. Tunda ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa sai suka koma kamar an waresu, bakomai Na gidan zakaga an sakosuba sai dai idan mahaifinsu Na kusa, hakan yasaka Aliyu bai damu da sabgogin gidanba inhar bana y'an uwansa biyu ba Mata, gashi yanzu duk sunyi aure sun barshi.
Zurfin iliminsa da yawan maida hankali wajen bama addini gudunmawa yasaka mahaifinsu malam Abdul-ra'uff yawan jawosa a jiki, ga tausayin maraicin da suke ciki. Aliyu ya ziyarci wurare daban-daban domin Neman ilimin addini, kullum cikin ziyartar zaurukan malamai yake, ba a Neman ilimin addini ya tsayaba, yana ta6a kasuwanci dai-dai k'arfinsa, dan yanada shago Na saida kowane irin nau'in littafi na Addini da magungunan musulinci, ko kad'an bai yarda yajira daga waniba, koda kuwa mahaifinsane.
Wannan k'ok'arin nasa da ho66asa yasaka wasu daga cikin y'an uwansa jin haushinsa, dan aganinsu kullum Malam yafison Aliyu fiye da kowa a gidan. Bawai su kad'aiba, hatta da iyayensu suna a kan wannan tunanin.
Saidai kuma bahaka bane ga malam, dukda dama ko cikin y'ay'anka akwai Wanda zakaji yafi soyuwa a gareka shi duk yanason yaransa, dan mutumne Maison y'ay'a sosai, kawai abinda basu ganeba (zuciya na k'aunar mai k'yautata Mata a koda yaushe) wannan shine kawai sirrin da Aliyu yabi wajen samun matsayi ga mahaifinsu dama wasu jama'ar dake zagaye da mahaifin nasu.
Yanada shekaru 27 a duniya ALLAH ya had'a jininsa da wata yarinya y'ar makwaftansu, sannan kuma d'aliba a makarantar mahaifinsu inda shima yake koyarwa idan yana gida.
Tunda malam ya fahimci k'aunar dake tsakanin Aliyu da Asma'u saiya nema masa aurenta, dayawan jama'ar gidansu hakan ya 6ata ransu, dan akwai yayunsa da basuyi aure ba kusan su uku. Dayake babu mai damar magana sai basuce komaiba akasha biki cikin tsari Na addinin islama.
Bayan aure da kamar wata uku matsaloli sukai yawa a gidan Aliyu, dan kuwa tunda akakai Asma'u gidansa yakasa kusantarta, badan bashida sha'awar hakanba, a'a lamarinne kawai ya gagara bisa alamun bashida cikakkiyar lafiya.
A matsayinsa na mai ilimi zaunar da Asma'u ya farayi ya fahimtar da ita akan tayi hak'uri ya fahimci baida lafiya, baikuma ta6a fahimtar hakanba saida yay aure, dan kafinma yay aure yakanji sha'awa, sai dai a jarabawa ta Ubangiji yakasa biya Mata buk'ata, yana neman alfarmar fara neman magani.
A wannan zama tayi masa uziri da fahimtarsa, amma yayinda tafiya tafara nisa sai hak'urinta ya nemi gazawa, dukda k'ok'arin neman magani da Aliyu yakeyi ba'a daceba har kusan watanninsu bakwai da aure.
Yakanyi wasanni da Asma'u, amma idan anzo batun biyan buk'ata sai Abu ya gagara, ita kuma hakan yana tada hankalinta daga k'arshe kuma babu biyan buk'ata.
Tabi ta saka kanta a matsananciyar damuwa, dukda k'ok'arin kwantar mata da hankali da Aliyu keyi. Ahankali sai y'an gidansu suka fara fahimtar akwai Marsala, mahaifiyarta ta turketa da tambaya itada yayarta, amarya dake murjewa danjin dad'i ita sai bushewa take a tsaye.
Bata wani tsaya Jan maganaba ta sanar dasu komai.
Tun daga lokacin komai ya harmutse, sukace sai Aliyu ya sakar musu yarinya. Yanason matarsa, dan haka yayta basu hak'uri da k'arin neman alfarma akan magani dayake nema, amma Sam sai sukak'i saurarensa.
Ganin abun zai tasarma tozarci dan harsun fara yawo da magana a anguwa sai malam yayma Aliyu nasiha da nuna masa muhimmancin hak'k'in Asma'u, tunda ta nuna bazata jureba ya sawwak'e mata kawai, kar nan gaba wata 6arnar ta biyo baya.
Cike da damuwa da tashin hankali yabama Asma'u saki d'aya, har hawaye saida yayi, dan yana masifar son Asma'un.
A ranar dai kam sai a asibiti ya kwana, kwanansa uku ya murmure yadawo gida, lokacin dayaje gidansa saiya iske sun kwashe komai, sai iya kayansa kawai aka bar masa, shima abinda keda muhimmanci ya d'iba ya kulle gidan ya fito zuwa gidansu.
Ganin yana tare da damuwa malam ya shawarcesa kozai koma karatune?.
Babu musu ya amsa. Dandanan aka shiga cuku-cukun nema masa gurbin karatu a k'asar Saudia. Cikin sati biyu komai ya kammala, ya cane cikeda kewar ahalinsa da y'an uwansa Mata biyu, Ruk'ayya da Siyama.
Tafiyar Aliyu Saudia saita zame masa alkairi abin alfahari, dan ya ture komai gefe ya maida hankalinsa ga karatu da addu'oin ALLAH ya bashi lafiya, tunda yakuma jin dad'in zak'in karatu saiya manta da wani batun aure. Ya maida hankalinsa tuk'uru. akan Neman ilimi da zurfafa bincike wajen malamai. Cikar kamala da girman mazantaka irinna nutsatstsun samari ta bayyana a gareshi, yazama cikakken mutum ma'abocin yawan ilimi, dukda shekarunsa kad'an suka haura talatin hakan bai hana masana duniyar ilimi girmamashiba, idan yana zuba maka tafsir da yaren Nasara (English) zaka d'auka baisan komai a yaren Africa ba, hakama idan ya juye Larabci abin ba'a magana, saika d'auka wani cikakken balarabene d'an asalin k'asar Saudia, hakama 6angaren yarensa Na Hausa yana nan daram a harshensa bai manta komaiba, dukda baya cikin Nageriya tafsiransa suncika ko'ina Na k'asar cikin harshe daban-daban, wa'azinsa yana saka zukatan bayin ALLAH nutsuwa ta musamman da k'arajin tsoron ALLAH, idan kaji tafsir nasa dolene ka nutsu wajen saurare da k'arajin tsoron UBANGIJI matuk'ar k'urewa, tsage gaskiya yake komai d'acinta.
Tunda yabar Najeria bai sake waiwayenta ba, saidai idan mahaifinsa yaje Umara ko wani Abu ya kaishi ya ziyarcesa, amma koda yaushe suna tare a Video call da mahaifinsa da y'an uwansa su Siyama dama sauran jama'ar gidansu.
Ganin shekaru sunja malam ya shawarcesa akan ya dawo k'asarsa hakanan, kodan ya cigaba da kula dawasu al'amura nasa, saboda shi girma yafara kamashi, sauran