Showing 117001 words to 120000 words out of 121675 words
su kasheni suka kaima babanta motar shi ya shiga ya mutu a lokacin. Daga baya bayan sunsha alhinin mutuwar babanta labari yazo mata nima na mutu, sai dai tana shirin samun dukiyar Alhaji Zakari itama ciki ya bayyana a jikinta, shine ta hakura saita haihu. To bayan haihuwar tatane kuma abubuwa sukaita faruwa ta gagara kashe auren ta gagara mallakar dukiyar tasa har wanan abun ya faru na ?watar ku?a?en Alhaji Zakari aka bama Alhaji Garba da ?arsa, ta tura ?aninta yaymusu fashi ya amshi ku?in dan itama ta samu rabonta karta tashi a tutar babu, shine suka jibgi Alhaji Zakari saboda gardamar dayay musu, dama tace ko kasheshine ya kama ayi itadai ku?in take bu?ata, shikuma ?aninta dama yajene da nufin amsar ku?in ya hanata, nikuma na saka aka bishi aka amshe ku?in shima aka kasheshi, dan nayi al?awarin bazataci ku?inba itama. Wanan bayanin danake muku duk ina samunsa ne ga direban gidansu, wanda ni yakema aiki tsawon shekaru ba tareda hindu ta saniba, na za?i zuwa na fa?i wanan sirrine domin Alhaji Zakari yasan ?a?an daya ?wallafa rai a matsayin nasa to ?ayane nasa, ita kuma na nuna mata ramin mugunta ?urarrene, ta gina kuma ta afka, sanan tasan ina nan a raye ban mutuba kamar yanda tayi fata".
Kotufa takuma ru?ewa da ihu, daga masu ALLAH ya ?ara sai masu fa?in maganin Abba kenan, sai masu tsinema hindu da shazali, Su Jiddah kam kuka suke sosai, dan ita kasama daurewa tayi tafito daga cikin kotun itada Umma.
Da ?yar Al?ali ya samu kotu ta nutsu, aka tambayi hindu abinda shazali ya fa?a gaskiya?.
Batayi jayayyaba ta amsa da eh hakane tana sharar ?wala.
Al?ali ya yankema hajia Hindu hukuncin shekaru Ashirin a gidan yari, shikuma Shazali saboda kisa da yayi ?aurin rai da rai.
Ihu Hajia hindu take tana kururuwa, amma ba'a sauraretaba aka fiddata, shazali ya roki alfarmar abashi ?a?ansa, dan suka?ai ke gareshi a duniya sai mahaifiyarsa. Atake kotu tace ta bashi, mahaifiyarsa tazo ta amsa.
Har aka wuce da hajia hindu da takoma tamkar mahaukaciya tanata sambatu su Uncle yahya basu iya motsawaba, saida kowa ya watse suka fahimci Abba a sume yake ma.
Da gaggawa aka ?aukeshi zuwa asibiti mafi kusa........???
*_Abba kagani ba aima ALLAH wayo, kuma ba ai masa tilas_*.?????¡â
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*?AURIN ?OYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ?ADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ?AYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RA?UMI..!* (Bilyn Abdull)
????karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*????????????
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[1/2, 1:04 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[67?68]_*
............Kuka sosai su Jiddah keyi, tunda suke basu ta?a gamo da makamancin wannan rikitacciyar rayuwarba, bakuma su ta?a kawo faruwarta a zahiriba sai yau, ashe abinda ke faruwa a films da hikayoyin marubuta yana faruwa a zahiri?.
Dafe kai Jiddah tayi saboda wani jiri dake neman kwasarta ?asa, da sauri ta dur?ushe a ?asa tana toshe baki da hanci saboda wani warin magani daya doki hancinta.
Da hanzari Zarah da Walida sukai kanta suna tambayar lafiya? Hakama Uncle yahya, Umma nadaga tsaye tana kallonsu amma ta kasa koda motsa ?afarta balle tazo garesu.
Da hannu tai musu nuni da Amai.
Zarah data fahimta tai saurin fa?in, "Yaya Jiddah Amai?".
Kai ta ?aga mata tana kuma danne bakinta dan gab yake da zubowa.
Kamata sukai da hanzari sukayo waje, bama su ?arasa inda ya daceba tafarashi babi ?a??autawa, sau?inma sunbar idanun mutane, sosai Jiddah ta galabaita, idonta sai lumshewa sukeyi, ga wani azababben ciwon ?irji daya taso mata lokaci ?aya, kafin kace mi tuni tagama fita hayyacinta, daganan bata sake sanin abinda ke faruwaba kuma.
¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï
A hankali ta bu?e idanunta da sukai mata jingim saboda nauyi, ?amshin turarensa ne yabata amsar shaidar yana kusa da ita, takuma ?aga idonta da ?yar takai dubanta gareshi, dishi-dishi take ganinsa.
Sheikh Aliyu da shima idonsa ke a kanta ya sauke ajiyar zuciya tareda kai bakinsa saman goshinta ya sumbata, hannunta dake cikin nashi ya matsa a hankali, kafin cikin sanyinsa ya ce, "Sannu Jiddatulkhair kinji, ALLAH yabaki lafiya".
Bata iya cemasa komaiba, sai idanunta data maida ta lumshe hawaye na zirarowa ta gefen idonta.
"Ya isa kukan haka Hauwa'u, ki kwantar da hankalinki Abbanma ya farfa?o, likitoci na Complain jininki ya hau, gashi kuma bake ka?ai baceba".
Babu shiri takuma bu?e idonta tana kallonsa, kamarya ba ita ka?ai baceba? Kardai maganar dayaketa ambata mata kwanannan ace tazama gaskiya?. bayan tafiyar Maimuna wanka da kwana biyu saitaita fama da ciwon kai da jiki, ko tausar yay mata batajin ya daina, saiya fara cemata anya kuwa wanan ciwon nata bana ?anin Muhammad ko ?anwarsa bane? Ko ka?an bata ?auki batun da muhimmanci ba, dan itadai bayan ciwon kai babu abinda takeji sai ciwon jiki wanda take dangantawa da wanan hidimar haihuwar dasuka sha. Kwana biyu dayi mata wanan zance ya kasance da ita, tun a daren yaketa maimaita mata lallai tanada ciki, dan takuma canja masa gaba ?aya. Ita maganarma kunya taita bata, ta?ima yarda su ha?a ido balle ta yarda da maganarsa, yau kuma sai gashi yakuma maimaitawa, hakan kuma na nuni da cewar doctor ne ya fa?a musu.........
Hawayen dayake share matane yasata dawowa hayyacinta, ta kama hannunsa ta ri?e tana kallonsa, "Abbu Muhammad ina Umma yanzun?".
"Sun wuce gida, sabod Abba ya matsa akaishi gida".
"Dan ALLAH mu bisu to, inason ganin halinda Abbana yake ciki ko zuciyata zata samu nutsuwa".
"Kinga kiyi ha?uri, dare yayi yanzun kalli agogo ?aya saura na dare, insha ALLAHU da safe zan kaiki idan kinji ?warin jikinki".
"Ni wlhy na warke".
"To naji ya isa haka bar kukan Umm Muhammad".
Murmushi tayi badan ta shiryaba, a duk sanda ya danganta sunanta matsayin Uwa ga ?ansa tanajin wani sanyi a ransa, hakama Maimuna yanzu gaba ?aya takoma kiranta Umm Muhammad, tana yaba karamcin wa?annan bayin ALLAH a ranta a kullu yaumin, tamusu kutse a zamansu amma sai suka jawo hannayenta suka ri?eta da zuciya ?aya, itako mizatayi ta biyasu dashi?. Ajiyar zuciya ta sauke saboda abinda taji Aliyu na mata, ta ri?e hannunsa tana tura baki ka?an.
Murmushi yayi ya janye hannunsa yana tashi zaune, itama ya taimaka mata ta tashi, da mamaki tabi ?akin da kallo sanan ta kallesa. "Yaushe ma na dawo gida to?".
"Ai tun bayan farkowarki a asibiti sai likita ya fahimci warin magani da Asibitin yakeyine ba?yaso, dan yun?urin amai kika fara farkawa dashi, shine yakuma miki allura, a lokacin kuma Zarah ta kirani da wayarki a ?oye, dan Uncle yahya ya hana a kirani a tadamin hankali".
Jiddah tayi murmushi tanajin ?aunar kawun nasu wanda takeji ?aunarsa tamkar mahaifi.
Da taimakon Aliyu tayi wanka sanan ta rama sallolin dake kanta, da ?yar yasamu tasha tea ?in daya ha?a mata, tana gama sha ma ta amayar dashi.
Kallo ?aya zakai masa ka hango tsantsar tausayinta a gareshi, ya gyara mata jikinta sannan ya kamota suka dawo ?aki suka kwanta yana saka mata albarka da jera mata sannu.
*WASHE GARI*.
Da ?yar Aliyu ya yarda ya kaita gwammaja kusan ?arfe ?aya na rana, dan kallo ?aya zakai mata ka fahimci batajin da?in jikinta, gashi takasa cin abinci, tace, "sai taje gida zataci awara".
Kana doso hanyar shigowa cikin gidan zaka fara jiyo kukan Abba da sambatun da yakeyi, cikeda sassarfa Jiddah ta ida shigowa, dan Aliyu yana mota saiya jira tamasa iso, mamaki ya kama Jiddah ganin duk ?an uwanta zagaye da Abba dake ri?e da hannun Umma dana Uncle yahya yana kuka. Yana ganinta ya saki hannayen su Umma ya mi?a mata alamar tazo gareshi, ganin lamarin take tamkar a mafarki, dan haka tai tsaye takasa koda motsi, aunty Zulai da suma suketa sharce hawaye tazo ta kama hannunta ta kaita gaban Abba.
Dur?ushewa Jiddah tayi takuma fashewa da kuka mai ban tausayi tana fa?in, "Abbanmu kayi ha?uri, ka ?auki hakan matsayin ?addar da bata goguwa a rayuwar ?an adam, dama rayuwa tana tafiyane da jarabawa kullu yaumin......."
Abba ya katseta shima cikin kukan, "Jiddah wannan ba ?addara bace kawai, akwai son zuciya irin nawa, na bitilcema ni'ima da rahamar da Ubangiji yay mini ta ?yautarku, na wula?anta mata masu ?yawawan zuciya akan abinda basuke badawaba, nakasa sauke nauyin da ALLAH ya ?oramin na tarbiyarku da ha??okinku a matsayina na mahaifi, na yofantar da matata da ?an uwana, na wofantar da karatunku inata bautama ?a?an wasu. Kaicona da dukkan masu irin halayyata a duniya, wlhy ?a?ana inajin matu?ar kunyarku a rayuwata da tsanar kaina........"
"Abba ka daina fa?ar haka dan ALLAH, insha ALLAHU mu masu yafe makane, dan duk duniya bamuda kamarka, kuma bamu ta?a takaicin samunka a matsayin uba ba, sai dai abinda nakeson tuna maka Abba nau'in abinda ake samarwa a mahaifa na daga ?iya mace ko Namiji ?wan namijine ke badashi, sanan ALLAH ta'ala dai yace shine ya haliccemu baki ?aya kuma ya sanyamu maza da mata domin musamu natsuwa da juna. Amma kuma seyace mafifici acikinmu shine wanda yafi tsoron ALLAH sannan kuma yace Maza sunada fifikon daraja akan mata saboda sadakin auren da suke biya dakuma ?awainiyar ciyarda matan dasu mazan sukeyi, wannan kawai shine abunda yasa maza suka samu fifikon daraja akan mata. Amma kuma wannan baya nuna cewa su matan ?as?antattune kokuma basuda daraja. A'a akwaima matan da sunfi mazan daraja nesa ba kusaba kai akwai mace guda ?aya wadda matsayintama yafi na mazanda suke rayuwa a duniya ayanzu dukkansu. Kukaranta ?issar Maryam mamar Annabi Isa (AS) sadda aka haifeta se mamarta take cewa ai namiji ba kamar mace ba, tanuna bataji da?iba dan ta haifi mace se nan take ALLAH yace shi yafita sanin abunda ta haifa, sekuwa gashi ya bayyana cewa wannan macen da ta haifa tafi duk mazajenda take tunani. Kaga kenan kasancewa mace ba aibu bane bakuma nakasu bane. Sannan Kaduba Nana Khadija uwar Muminai kuma kaduba Asiya matar Fir'auna kaduba irinsu Sayyidatuna Fatima ga irinsu Aisha dasu Ummu Shuraikh wadda saboda karfin walittakarta daga Aljanna kai tsaye aka miko mata ruwa tasha ta koshi, shin kanada wani namiji a yanzu wanda zakace yafi wa?ancan matan daraja? Dan haka babu shakka maza da yawa masu wanan a?idar suna kan kuskure, amma su sani kasancewa mace ba aibu bane bakuma gajiyawa bane, illa iyaka aduba tsoron ALLAH kawai da takawa, sannan idan kaduba sharhinda malamai sukaiwa hadisinnan na ANNABI (s.a.w) dayace ayiwa mata wasiyya da kyautatawa dakuma hadisin wanda ya raini mata biyu zuwa sama zasu kasance masa garkuwa tsakaninsa da shiga wuta, to wa?annan hadisan sun kore abunda mutanenmu suke fa?a, kuma su tabbatar da cewa mata sunada daraja, kuma suna daga cikin waliyyan ALLAH, sannan kuma ba kaskanci bane kasancewar mace, sannan kuma idan mace taji tsoron ALLAH to zata iya fin maza daraja. Malamai irinsu Zahabi idan kaduba Siyaru A'alamin Nubala yakawo tarjamar manyan malaman hadisi mata kuma shima daga cikin malamanshi akwai mata sunfi hamsin, sannan acikin Mizanul I'itidal yana cewa ba,a samu wata mace ba wadda tayiwa ANNABI (s.a.w) ?arya, dan haka inkaga mace malamar hadisi to amintacciyace, ba'a tuhumarta da yiwa ANNABI ?arya. Kai malamai dayawa sun ambaci falalar mata a wajaje daban daban saboda haka zamantowa mace babbar darajace matukar akwai imani da ta?awa, kuma acikin magabata akwai wa?anda har raba dare suke suna ro?on ALLAH akan yabasu ?a?a mata yabasu ikon musu tarbiyyah, wani kuma zuwa yake cikin danginshi yaro?i su bashi ?a?ansu mata domin ya rainesu, dan yasani cewa macece zaka raineta dandanan kasamu gidan aljanna, dan haka mata sunada falala sosai kuma duk mutuminda har yagama haihuwa be haifi maceba to yakamata ayi masa jaje. Amma koda ace mutum aduniya ?a mace guda ?aya tal ya haifa to wannan aimasa barka matu?ar ya iya jure tarbiyyarta. Mata babu shakka a musulinci sunada daraja sosai inhar sukaji tsoron ALLAH, sannan kuma duk wani malaminda kasani ya shahara a duniya to inka bincika zaka samu cewa mata sunyi ?o?ari sosai a wajen tarbiyyarshi, hatta mamalan da suke karama juna sani daku anan idan da ace andaka ta iyayenmu mazane banda matan to da bamuzo kan wannan matsayinba. Kuje kuji tarihin Shafi'i mana ko Malik ko Abu Hanifa da Ahmad binu Hambal cikinsu wanene mace batai masa tasiba akan iliminsa? Imamul Bukhari albarkacin mace yazama abunda yazama a babin hadisi, hakaman Sibawaihi a fannin nahwu ya gagarane albarkan Mace. Ibnu Taimiya kuwa ai Taimiyar ma macece ba namijiba dan haka mata sunada tasiri sosai da amfani a rayuwa kuma duk wani wanda kaganshi a duniyarnan yana ?afafa da tun?aho to arzi?in macece, dan haka mata suma mutanene kuma banda sadaki da ciyarwa babu abunda maza suka daramu dashi. Amma kuma saurin kai mutum aljanna da saurin kaishi wuta to babu kamar mata, abu ka?an zakaiwa mace ka samu aljanna kuma abu ka?an zakayiwa mace katafi wuta. Kuma ana iya gane nagartan namijine tayadda akaga yana kulawa da matarsa da ?a?ansa Abba".
"Wlhy duk gaskiya kika fa?a Hauwa'u, nima son zuciyane ya lullu?e ganina da jina, Yagana dolene na gode muku matu?a keda yahya, ALLAH ne gatana kune gatana, kune kuka tsaya tsayin daki wajen ganin tarbiyyar ?a?ana da ha?uwar kawunansu a waje ?aya, ku kun kasance mutanen kirki ababen alfahari da kwaikwayo ga kowanne mutum, duk wanda ALLAH ya bama ?ya?y?yawar zuciya irin taku yagama cin ribar duniya da lahira, dan girman ALLAH ku gafarceni akan kurakuraina kuda ?a?ana, wlhy nayi nadama nayi nadama matu?a......"
Daga Umma har Uncle yahya dasu Jiddah kuka suke suna fa?in sun yafe masa, suma ya yafe musu.
"Ba kuyimin laifin komaiba wlhy, koma kunyi mini na yafe muku tuni".
Wannan rugun tsumi ya mantar da Jiddah Aliyu dake ?ofar gida, wanda shi tunima ya gaji da jiranta yashigo soron da nufin yin sallama, sai yaji kukan jiddah tanama Abba nasiha, hakane yasashi fahimtar akwai matsala kenan, saiya juya dan wannan ba huruminsa baneba ai.
Haka Jiddah ta yini a gida cikin ?an uwanta batajin da?i, awararma datasaka Walida ta sayo mata tanaci sai Amai, sosai tabasu tausayi sukaita jera mata sannu, data motsa Abba zaice "Sannu Jiddah kinji, ALLAH ya rabaku lafiya".
A yau kam duk wanda ka kalla a ?an gidan su jiddah zaka fahimci suna cikin tsantsar farin ciki, komai suna yinsa cike da walwala, gasu ga Abbansu a inuwa ?aya suna hira da dariya, abinda bai ta?a faruwaba a tarihin gidan.
Sai dare Aliyu yazo yaga Abba ya ?auki Jiddah suka tafi, saida ya kaita gidan malam ganin Muhammad da Maimuna sannan suka wuce gida.
???????????
Haka rayuwa taci gaba da tsabagen gudu da sauri, Jiddah nata rainon cikinta, ga soyayya da take samu ga mijinta mai tsayawa arai da ruhi, dolene ka gansu suyi matu?ar birgeka sosai. Watan Maimuna biyu a gida tadawo, yaronta yayi ?ul-?ul dashi tamkar ta bani??.
Tunda suka dawo ?awainiyar Muhammad ta koma ga Jiddah, idan ka gansa hannun Maimuna nono zaisha kokuma barcin dare, hakanne yabama Aliyu da Maimoon ?insa damar cin soyayyarsu da kewar juna da sukayi.
Abba ma dai jikinsa Alhmdllh, dan zamu iya cewa ya warke sarai, sai dai kuma baya koda iya mi?ewa, ko yaushe yana cikin wheelchair zaune, itace ?afafunsa a yanzu, idan kaje gidansu Jiddah saikaga dukya canja saboda kwanciyar hankali takuma samuwa, sai dai matsalolin yau da kullum da baza'a rasaba. Muneer yana wajen Umma, ta kama ta ri?e tamkar nata, yayinda duk gidan suka ?auki son duniya suka ?ora masa. A wanan yanayinne kuma aka shiga hidimar bikin zarah da mijinta Nazeer.
Su Jiddah kirjin biki, ga shagali ga ciki daya fito sosai kowa na gani, sai dai tanata kumshe abinta a hijjab kar a gani, dangi abokan wasa kam suka tasata gaba da tsiya, itadai nata murmushi, saisu Aunty Nafisa ne ke rama mata.
Wannan karonma Uncle yahya shine yayma Zarah komai, dan Abba yace basuda uban daya wuce Uncle yahya, shi hotone a garesu, bai isa zuwa rana tsaka ba yace zai wata fiffika akansu.
Ansha biki aka kai amarsu Zarah gidanta tana ti?ar