Showing 27001 words to 30000 words out of 121675 words

Chapter 10 - MUTUM-DA-DUNIYARSA COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Sep 2024

17147

batareda ta cire Nikab d'inba.
Umma Na bayi, su Walida kam sun duk'ufa wanki shiyyasa basu Lura da halin da jiddah ke cikiba.
Sosai tasha kukanta, saida taji Umma Na kwala Mata Kira sannan ta share hawayen tafito.
Kallo d'aya Umma tayi Mata tafahimci tana cikin damuwa.
"Omon dake hannunta da jiddah ta sayo yanxun dan suyi tsaraba ta ajiye tana fad'in "Lafiyarki kuwa?".
Murmushin yak'e Jiddah tayi, "Umma babu komai, k'asace ta shigarmin Ido saboda iskar da akeyi, alamu zubar ruwa Nata kuma bayyana".
Badan Umma ta yardaba tabarta, saima ta d'akko wani zancen.
"Walida ku gama wankinnan kije gidan zainabar bashari ki amsomin dakan kuka da ku6ewarnan da Sauda (babbar yar su jiddah) tace aimata, Gurasar Hannatu (yayarsu ta biyu, y'ay'an matarsa Na farko Amina) dai sai a bari gobe idan ALLAH ya kaimu da yamma sai'a a amso gidan y'an gurasa dan karta bushe".
"To Umma bara mugama sainaje d'in".

Zarah ta mik'e tsaye tana rik'e kugu da sauke numfashin gajiyar wanki, "Umma waikuwa aunty Zulaiha (yayarsu, y'ar matar abba ta biyu) zataje d'in?".
"Wlhy Zarah ban saniba, tadai cemin yau zata Kira da daddare akan yanda sukai da Mijin Nata, idan ya amince gobe zata baro huntuwa tazo nan kano ta kwana saimu wuce jibin".
"To ALLAH dai yasa ya barta, wannan Mijin Na aunty Zulai bayason yaga tamatsa ko nan da can". 'Cewar Jiddah dake kulle omo a leda'.
Dariya su walida sukayi suna fad'in wayaga Yaya Adam cigam d'in aunty zulai.
"Kunci gidanku". 'cewar Umma tana musu dak'k'uwa'.
Dariya sukayi har Jiddah..............???



https://youtu.be/eOU-ju4f6KY

_Zaku iyabin wannan link d'in na sama domin sauraren littafin RAINA KAMA a audio, Abban dausayi YouTube channel??????_



*_Abba zakari Na gaisheku??, jiya gidansa Na yini tunda duk kunki zuwa gaisheshi ku????????¡â_*






*_ALLAH ka gafaiyayenmu??????_*

[11/27/2019, 8:11 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*



*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce????_*

*_[11...]_*


..............Yau su Jiddah da murna biyu suka tashi, Na tafiyarsu barno gobe da zuwan yayarsu Zulaihat dake aure a huntuwa Katsina state kenan.
Tsaf kowa yagama had'a kayansa, Zarah da walida suka fito cikin shirin zuwa kunshi Wanda Jiddah tace bazatajeba, ko kitso tak'iyi tace saitaje barno za'ai mata irin nasu.
"Umma dan ALLAH kibamu aron dubu d'aya inji aunty Nafisa, tace idan tazo zata baki".
"Wa? Kunga idan zaku kubar tsayani, idan kuma kunje kubar tunoni, sisi ban badawa, yanzunan zamu Shiga kasuwa nida Maman Sadiq da Jiddah ".
"Haba Umman mu ta mutunci, ALLAH ya k'ara miki Nisan kwana". 'Walida tafad'a tana salute d'in Umma'.
Cikin dariya Jiddah dake janyo ruwa a rijiya tace, "Kumace ta tsiyace mana".
"Kai Yaya Jiddah dan ALLAH karki 6ata mana tsari mana.........".
"kujimin yarinya, yoni minace? Umma nace karki basune?".
"Ai koma bakiceba ba bayarwa zanba, kuje taimuku bashi, idan Nafisar tazo Ku k'arata, ai Rashidar zata muku lamuni".
cikin shagwa6a Zarah tace, "ALLAH Umma sokike kawai girmanmu ya fad'i a wajenta, ga sabon d'inkinmu ki rik'e matsayin jingina, idan munbaki saiki bamu".
Jiddah ta kwashe da dariya tana mik'ewa, "Umma Na rantse ki kar6a, idan ba a biyakiba kibar gayu susa tsoffin kaya a wajen biki".
"Gaskiya Jiddah kin kawo shawara Mai k'yau, y'ammata aje a d'akko ga dubu bugun Abuja". 'Umma tak'are maganar tana dariya da ciro dubu a jaka'.
Walida data kwaso sabbin kayansu itada Zarah ta mik'ama Umma tana tura baki irin munji haushinan.
Kar6a Umma tayi tabada dubu, suka fuce suna musu sallama ciki-ciki. Dariya sosai Umma da Jiddah keyi harsu Zarah suka fice.
Cikin dariya Jiddah tace, "Umma y'ay'ankifa sun shak'a".
"Ai gara da suka shak'a, nima Na rama kiramin innata dasukaitayi d'azun da farar safiya".
Jiddah ta had'iye dariyarta tana zaro ido waje, "Tofa Umma ashe nima ba tsira zanyiba".
"Oh kinzata kema kinsha banzane? Inanan zuwa kanyi ai".
"Haba Ummanmu yi hak'uri, kingafa har kud'in saya mata goro na tanada ALLAH kuwa".
"Ban yarda dakeba Jiddah.........."
Kafin Jiddah tabama Umma amsa Maman Sadiq ta shigo da sallama. Amsawa sukai Umma namata lale. Yayinda Jiddah ke fad'in "Mama ina Rudwan d'in?".
"Nayi cinikinsa a hanya yanzunan".
"Haba dai mama, aiko dabaki k'arasoba".
Mama tai dariya, "Mizai hanani k'arasowa kuwa? Na gamu dasu Zarah ne suka amsheshi".
"Yanzu naji batu mama, yama huta dashan wanan ranar da turnitsin kasuwa".

Babu 6ata lokaci suka shirya suka fito domin tafiya kasuwa, sai da Jiddah ta lek'a gidan Rashida tabama su Walida key d'in gidan sannan ta fito suka tari napep zuwa kasuwa.




???????????

Tsaf malam mustafa yagama binciken da malam ya sakashi akan Jiddah, dan haka yau bayan idar da sallar zuhur yasameshi da bayanin komai daya danganci Jiddah da ahalinta.
Malam yayi farin ciki sosai da tarbiyyar yarinyar, saima yaji takuma Shiga ransa fiye da lokacin daya ganta, dukda ya jinjina mamakinsa akan lamarin mahaifinsu na jahilci, inba jahilciba babu wani bawa dazai guji Ni'imar ALLAH saboda tsarinsa na banza, indai kana numfashi kaji Abu iri-iri a duniya, na ban haushi dana ban al'ajabi..



???????????

"Da gaske kana sonta Alhaji Garba?". 'Abba yay maganar yana kallon abokinsa Alhaji Garba mai tabarma'.
"Wlhy da gaske nake maka wannan zancen Alhaji Zakari, inason Jiddah y'arka, danni dai bak'aramin birgrni tayiba wajen taronnan da akayi".
Abba yay murmushi kafin ya muskuta zamansa ya jingina da bango, "Alhaji Garba daga yau nabaka Jiddah, ko gobe kake buk'atar ganinta a gidanka kazo a d'aura muku aure"..
"Kai amma naji dad'i sosai abokina, ALLAH ya k'ara girma, tabbas inason auren ya kasance kusa, saboda matsalar hajia deluwa ta isheni ainun, ina buk'atar Matar da zata kwantar da hankalina nima, sai dai ba wai gobeba, idan babu damuwa yakai k'arshen watanan".
"Hakan mai sauk'ine, dama zasuje Barno biki gobe, nima jibi zanje a d'auro auren Dani, saboda k'anin mahaifiyar tasune zai aurar da yarinya, insha ALLAH zan sanar da danginta kai".
"Ai to indai hakane kawai bara Na shirya muje tare, kaga saisu ganni dak'yau nayi gaisuwar surukai ma".
Dariya sukad'anyi suna tafawa.
Abba yace, "Lallai kakawo shawara mutumina".


Turk'ashi????, yau munga idi abba zai 6aro mana ai??.



???????????

Sai kusan k'arfe 5 su jiddah suka dawo gidan, sun iske ko ina ya kacame da hayaniya, dan kuwa aunty Zulai ta iso da y'ay'anta biyu, tabar manyan guda uku acan gida wajen kakarsu, nanfa aka kuma kacamewa murnar ganin juna, dan kusan shekara kenan batazo kano ba, sukuma inba haihuwa tayiba Abba ba barinsu zuwa yakeba, garama Jiddah wani lokacin Umma kan aiketa tayi kwana biyu ta dawo.
Ana cikin Murnar ganin Aunty Zulai saiga Aunty Nafisa itama takasa hak'uri tataho nan ta kwana tunda da sassafe zasu wuce. Gidafa ya kacame tamkar ana biki, babu maijin maganar wani, ga y'ay'ansu Aunty Nafisa dama bajin magana sukeba, Umma dai tasamu ta rufe rijiya 6am saboda tsaro. Ganin k'unshin su Zarah yayi k'yau Jiddah tace dama itama tasani taje.
Dariya sosai suke Mata hardasu Aunty Nafisa.
Yaukam sunsha hira, dan kusan raba dare sukayi ana hirar zuminci.
Washe gari tunda asubar farko suka tashi, ALLAH ya sosu aka kawo wuta, dan haka sukasa ruwan zafi Mai yawa a hita, har suka samu ya tafasa akwai wuta.
Kaf yaran Zarah ce tai musu wanka, yayinda Walida ke shiryasu. Jiddah da aunty Nafisa kuwa sunata k'ok'arin had'a abin Karin kumallo.
Sunsami gudanar da komai akan lokaci har sallah, karfe 6 saura motar bos da Uncle yahaya ya tanadar musu ta iso, dan haka akaita fidda kayansu ana lodawa amotar, bayan angama tsaf, saikuma ga Maman Sadiq da tata gayyar y'ay'an itama. Tuni suka shishshiga mota aka rufe gidan suka shilla Barno.


Saina karaso nima??, dan bazan had'a mota da kowaba??.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï

Sun isa barno lafiya, yayinda dangi suka kacame da murnar isowarsu, bazaka ta6a cewa aunty Zulai da aunty Nafisa ba tsatsonsu bane, dan yanda akema su Zarah suma haka ake musu babu wani banbanci. Dan danan aka shiga hidima dasu, bayan sunci abinci sunyi nak kowa yanemi Mai fisheshi, tuni Zarah da Walida sunbar gidan bayan sungama tsokanar Inna hajia (kakarsu mahaifiyar Umma), ta tsufa kam, saidai bazamuce irin tukuf d'inan ba, daka ganta kaga cikakkiyar kanuri, dan harda 6ular hancinta ras, Hausa kam kad'an-kad'an takejinta ma.
Fitar su walida babu dad'ewa saigasu Fannah amare, tuni suma suka janye Jiddah bayan sun gaisa dasu Umma.

Washe gari da Hantsi saiga Aunty Sauda babbar yar su Jiddah tazo itama daga Yola, dan can take aure. Zokaga murna wajen Umma dasu Aunty Nafisa anga y'ar uwa, su Zarah kam basusan tazoba saida sukazo d'aukar kayansu, nanfa suma suka kadandaneta suna nuna murnar ganinta, tare damata tsogumin batazo da yaraba sai wadda take goyo kawai Hanan.
Wajen karfe 3 itama Hannatu ta iso tare da Mamansu (Amina Matar Abba ta farko) dakuma wasu daga dangin Abba da sukazo yima Umma Baici, y'ay'an Ummafa sun had'u, Amina da Umma kam idan kagansu abin sha'awa, tamkar wasu Yaya da k'anwa, dukda basu zauna gidan Abba a tareba hakan bai hana kulluwar zuminci mai k'arfi a tsakaninsu ba, dan sunajin dad'in yanda Umman ta had'a y'ay'an dukta rik'e, (itako aunty Zulai mahaifiyarta ALLAH yamata rasuwa dama) dan haka batada Uwa irin Umma, Abbanma daya haifesu ba damuwa sukai dashiba, dukda suna bashi girmansa kamar yanda koyaushe Umma ke nuna musu muhummancin hakan.
Biki yacigaba da gudana yanda yakamata, yayinda aketa zuba al'adun biki irinna kanuri, Su Jiddah dai anshige ko ganinsu ba'ayi, kuma duk wannan shagali bai hanata saka hijjab d'intaba duk inda zataje, nik'ab ne dai data d'akko zatasaka sai a kwace a hanata, babu yanda zatayi dole ta hak'ura, amma duk saitake jinta a takure, shiyyasa ko yaushe kanta a k'asa batason kallon kowa.
Washe garin d'aurin aure saiga Abba da abokinsa Alhaji Garba, kasancewar tafiyar wuri sukayi wajen k'arfe d'aya suka iso.
Basu sami ganin Umma ba saida aka d'aura aure, amma sun sami tarba ta mutunci daga y'an uwan Umma maza.
Bayan gama d'aurin Aure Umma tasamu da k'yar tafito cikin mutane ta samesu a gidan makwafta da aka saukesu a d'akin soro, ganin dukkan tarbar da zata iya musu an musu sai suka gaisa takoma kiran su Aunty Sauda.
Amina kan duk yanda Umma ta rok'eta tazo su gaisa k'i tayi.
Daga Sauda, hannatu, Zulaihat, har Nafisa haka suka shigo fuskoki babu walwala, kowacce kuma cikin kamalarta, dan duk ALLAH ya kaisu gidan hutawa, babu maishan wahala a gidan aure.
Abba yayi mamakin ganinsu amma saiya 6oye ya amsa musu gaisuwarsu babu yabo babu fallasa, ko tambayar ya yaransu baiyiba, amma su da suka tambayi yasu kalifa saiya hau washe baki da fad'in duk sun a lafiya.
Takaici ya cika zuciyarsu aunty Sauda da Umma, basubi takansaba sukai masa sallama suka fito.
Umma ma sama-sama taimasa sallama ta fito tabarsu, dan anan zasu kwana sai gobe zasu wuce. Aiko bata sake bi takansuba saida daddare data kawo musu abinci, anan ta iskesu da y'an Uwanta maza, haka kawai tasha jinin jikinta da zaman hirar tasu, saidai batace dasu komaiba ta juya tana fatan ALLAH yasa alkairine.

Washe gari Abba yasamu gaisawa da Inna hajia, itama yaymata dukkan bayanin da yama y'an uwan Umma, ta jinjina wannan lamari sosai, saidai batada hurumin hanashi yin yanda yaso da y'ay'ansa, dan haka tabishi da addu'ar ALLAH ya za6a abinda yafi alkairi.
A ransa yace, "ai yama za6a, dan auren Jiddah da Alhaji Garba babu fashi".
A ranar suka koma shida Alhaji garban bayan angama nunasa cikin dangin Umma da sunan Mijin da Jiddah zata aura.
Kowa dai wannan za6i bai masaba, amma basuda hurumin hanawa saboda dai shikeda iko da y'arsa. Umma da Jiddah da su Aunty Sauda dai basusan abinda ke faruwaba, duk da sunji anad'an maganar sama-sama, saidai basu fahimci wacce Jiddarba.

Kammala biki da kwana biyu suma sukayi azamar tafiya, dama tun jiya aunty Sauda da mama Amina da aunty Hannatu sun koma da sauran dangin Abba.

Abba dai daga Barno Ashe Adamawa ya wuce da Alhaji garba, inda yasanar dasu shine zai auri Jiddah, babu mai hurumin hanashi iko da d'iyarsa, amma wasu sun nuna masa illar hakan, dan Alhaji garba yayma Jiddah Tsufa sosai. Amma ganin ya dage sai suka bishi da fatan alkairi kawai, dan kowa yasan halinsa na kafiyar tsiya.

Da daddare Inna hajia ta kira Umma gefe, cikin tausasa harshe taimata dukkan bayani akan auren Jiddah da Alhaji Garba da Abba ya sanar musu. Take hankalin Umma ya tashe, tace wlhy Sam bazata aminceba, sai dai a wannan karonkam su rabu dashi.
Murmishi Inna Hajia tayi tana jinjina kai, kafin ta nisa cikin dattako tace, "Uhm-uhm Yagana karmu soma haka dake, wannan baikai abinda za'a tashi hankaliba, ALLAH dai shine maiyi, sannan komai da kowa a hannunsa yake, karnaji karna gani ance daga 6angarenki matsala take, kibarshi yayi yanda yaso da d'iyarsa, ALLAH dai maijine kuma Mai ganine, sannan yana tare da masu hak'uri".
"Hakane Inna, amma ita yarinyar lamarinta za'a duba, wlhy koshi kansa Alhaji ya girmesa, manyanfa y'ay'ane dashi zagada-zagada, dan ko autansa saidai suyi sa'anni da Jiddar, amma dan zalunci irina zakari shine zai had'ata aure dashi? Lallai yanzu nakuma aminta da baya k'aunar yarannan da gaske........"
"Koma dai Miye yagana nidai nace kiyi hak'uri ki saka masa ido, itako mucigaba da Mata addu'a, kokun koma karnaji wani tashin hankali tsakaninki dashi".
"Shikenan Inna". 'Umma tafad'a wasu hawaye masu rad'ad'i Na kwararo mata'.
Washe Gari haka suka baro barno ranta a 6ace, su Jiddah duksun damu da halin da sukaga ta shiga daga daren jiya zuwa yau, amma sunyi tambayar duniya tace babu komai.
Haka dai suka iso kano.
Tamkar Jira Abba yake dama da dawowar tasu saigashi a gidan bayan magriba, aunty Zulai da aunty Nafisa duk suna gidan, Maman Sadiq ce kawai suka wuce gida itada yaranta.
Babu wani 6oye-6oye ko lallashi cikin gadara ya sanarma Umma zancen Auren Alhaji Garba da Jiddah, harma da jadada mata zancen kawo kud'i da zaiyi gobe idan ALLAH ya kaimu.
Uffan batace dashiba harya k'araci hargowarsa ya fice.
Yayida tuni tashin hankali ya dabaibaye su Aunty Nafisa wad'anda Jiddah ta sume musu saboda abinda sukaji daga bakin Abba.
Wannan dare dai yazo musu cikeda k'unci da damuwa.
Washe gari Aunty Nafisa takoma gidanta cikin damuwa da tausayin Y'ar uwar tasu.
Itama aunty zulai kwanata hud'u tak'ara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login