Showing 63001 words to 66000 words out of 121675 words

Chapter 22 - MUTUM-DA-DUNIYARSA COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Sep 2024

17154

lemo yana kumfar baki, ba a wani ja dogon lokaciba ya kife a tebirin ya hau barci.
A wajen babu Wanda bai sauke ajiyar zuciyaba, kafin su Uncle yahya sushiga yima d.p.o godiya.
"Ai babu godiya a tsakaninmu, domin wannan yima Kaine, Na fahimci Alhaji baya tare da hankalinsa yanzu, wane ubane mai mutunci ALLAH zai masa wannan ni'imar ya bijire?. Shekaranjiya muka gama makamancin irin Case d'innan naku, shima Uban bayason yara mata, ya watsar dasu uwarsu Nata wahala dasu, sai yanzu cikin y'ay'an wata ta auri mai arzik'i shine yadawo zaima uwar fin k'arfi, itako tace Sam bai isaba, rikici dai ya kawosu har nan. Wato shawarar dazan Baku shine kusami likitan dazaita dank'ara masa allurar barci daganan harta tare gidan mijinta, dan baima kamata kubari gidan malam suji wannan shirmen nasaba wlhy, kodan Ku nemama y'arku mutunci, lokacin dazai dawo hayyacinsa rikicinsa da wancan Alhajinma ya isa ya d'auke hankalinsa".
'Dari bisa d'ari sun gamsu da shawarar d.p.o, dan haka sukaita zubamasa godiya da fatan gamawa da duniya lafiya, kafin y'an sanda suyi kama-kamar Abba sukaishi mota.

Har gida su Uncle yahya suka kai Abba, Hajia Hindu zatai musu hauka suka taka Mata birki akan baida lafiyane, likita zaizo ya ringa dubashi.??


¡ï¡ï¡ï¡ï..

Su Uncle yahya basu fad'ama kowa halin da ake cikiba har Umma, dan basason 6ata musu farimcikinsu.
Washe garima su Kawu Surajo suka juya bayan sunma Jiddah Nasiha mai ratsa jiki, akan ta Zauna lafiya da mijinta da abokiyar zamanta, dan a wannan auren sunA k'yautata Mata zaton alkairi da samun kwanciyar hankali mai d'orewa har abadan insha ALLAH. Tadai sha kuka sosai.
Su Yaruwaiya dai nan aka barsu, dansufa da shirin gyaran y'arsu Jiddah sukazo, dan haka tun a washe garin d'aurin aure suka fara gyara Jiddodon Uncle lungu da sak'o, dansu duk zatonsu jiddar tarasa budircinta a aurenta Na farko, itakuma dayake ba yawan surutune da itaba takasa fad'ima kowa babu abinda yashiga tsakaninta da Alhaji Garba, sai dai a gefe kuma Umma datasan halayen yaranta kaf tuni ta fahimci Jiddarta har hanzu budurwace.
Umma na mamakin rashin zuwan Abba gidan, harma takasa hak'uri ta tambayi Uncle yahya, shine yace Mata bashida lafiya. Tsakanin Mata da miji sai ALLAH, duk sai ta damu kanta kuwa, harma ta matsa akan zata dubashi Amma Uncle yahya ya bata shawarar tayi zamanta, daga baya kuma saiyaga yadace suje d'in kodan kauda hankalin mutane..
Gaba d'ayansu gidan da iyalin Uncle yahya suka rankaya duba Abba, dukda ma sun iske yana barci, hajia Hindu sai cika take tana batsewa. Babu Wanda yabi takanta a cikinsu in banda Balu da taita yanka Mata habaici ita da Gajiram, sai da Umma ta tsawatar musu da harshen kanuri, duk dariyar dakecin Zarah da walida basuyiba, dan wannan ba tarbiyarsu bace saka Kansu a hurumin manya, tun suna k'anana Umma bata ta6a basu damar cin zarafin hajia Hindu ba ko Mata rashin kunya, koda kuskure kayi hakan kuwa ranar zakaci uwaka wajen Umma.
Tsakanin su Umma dasu kalifa kuwa babu ko gaisuwa, hasalima d'auke Kansu sukai suna cigaba da kallon ball d'insu da hayaniya da uhu kamar basu ga su Umma ba. (Sun manta Ubansu Na kwance??????).
Suma su Jiddah babu Wanda yashiga harkar yaran.
Garama Umma tamusu magana suka wani basar da ita, kuma sarai sunsan matsayinta a gunsu, Itama daganan saitayi shiru. Kuma hajia Hindu naji da kallonsu amma bata tsawatar musu ba.
Basu wani dad'eba suka taho, kuma ko a Hanya Umma Hana kowa maganarsu tayi balle asamu Na saka zuciya 6acin rai.

???????????

Maimunatu dai ta kuma kwantar da hankalinta a gaban jama'a da mijinta, amma inhar tana ita kad'ai takansha kukanta ta k'oshi, kullum kuma addu'arta shine ALLAH ya k'ara Mata dangana da juriya, yakuma basu zaman lafiya da amarya.
Ko'a ranar d'aurin auren da kanta ta shirya Aliyu, shikam yanata saka Mata albarka da kuma nuna Mata tsantsar k'aunar da yake mata. Amma yana fita saboda kiranda Malam mustafa kemasa a waya saita rushe da kuka, shikenan yau mijinta yazama nasu su biyu, komansa yanzu saita raba da wata.
A wannan halin Aunty Ruk'ayya da Aunty Siyama sukazo suka isketa, zama sukai suna lallashinta da Mata nasiha mai ratsa jiki, hakanne yasaka Mata jin sanyi a ranta, koba komai y'an uwan mijinta suna k'aunarta.
Su Hassana da sukazo sai sukai turus ganinsu Aunty Ruk'ayya a gidan, hakanne yasaka suka Kama Kansu.
Suna a gidan harsu Aliyu suka koma daga d'aurin aure, nanfa suka shiga masa addu'ar ALLAH ya sanya alkairi da fatan zaman lafiya.
Dukkan wani zumud'i ya danne a binsa a zuciya yanda ran matarsa bazai sosuba, daga k'arshema yaja abarsa suka shige d'akinsa ya hau lallashi, dan yakula tasha kuka, idonta kawai sun Isa shaida. Hakan dayay Mata saiya sake bata nutsuwa harta d'an Saki jikinta ma.
Har dare su aunty Siyama Na gidan, harma da sauran y'an uwansu da Matan yayyensu da sukaita zuwa daga baya. Wasa-wasa dai sai sukasha wani d'an k'aramin shagali a cikin gidan, Wanda kowa yake bama Maimunatu kulawa da nasiha tareda fatan zaman lafiya, bakuma su munana amarya ko k'intaba ko sau d'aya a gabanta, kowa dai Na fad'a Mata ta rik'e girmanta shine mutuncinta ga miji ga abokiyar zamanta harma dasu danginsa.
Aliyu kam tuni yabar musu gidan dayaga sunfara cika, bai dawoba sai dare.
Akuma lokacinne yakejin yakamata koda a wayane yaji muryar Jiddah, dan yanzu dai hak'k'inta yarigada ya rataya a wuyansa dukda bata tareba.
Amma kokad'an baibari wannan tunani yayi tasiri a ransaba dahar zai hanashi bama matarsa kulawa, koma a fuska bai nuna Mata yana tunanin Jiddah bane, saima ita dataketa yawan sakko sunan Jiddah a hirarta, harma ta tambayi number ta.
Kwanciyarsa ya gyara yana kallonta, "Maimoon k'anwar nan takifa banyi zaton tana rik'ema wayaba gaskiya".
"Haba dai Yaya miyasa?".
"Ban saniba nima, sai dai inaga daga gidansune suka hanata, kinsan wayoyinne yanzu sunada tasu illar suma, shiyyasa wasu iyayen kan Hana yaransu rik'ewa har sai sunyi aure".
"Hakane kuma, nikam banga laifinsu ba, dukda hakan ba shine zai tsare maka yaroba, amma to yanzu dai yakamata a barta ta rik'e".
"Insha ALLAHU zanyi k'ok'ari a saya Mata koda k'aramace kafin abubuwa su warware, dan a tsakaninan banida wani isashshen kud'i Maimoon, inaga aikinnan da aka bani nak'i Zan koma Na kar6a, dama ganinai nauyin zaimin yawa, kuma dai-dai gwargwado dai sana'ar magungunan nan tana rik'emu, ga wadda Adeel ke mana a saudia, to amma yanzu nauyi ya k'aru, inaga sai nahad'a da aikinnan kodan nasamu damar sauke nauyinku".
"Yaya bazance maka a'a ba, amma Zan saka lamarin cikin addu'a ALLAH ya za6a mana abinda yafi alkairi".
"To Amin matata". Aliyu yay maganar yana jawota jikinsa ya rungume.


???????????

Alhaji garba baya gari, dan haka baisan wainar da ake toyawa ba akan auren Jiddah, matarsa kuwa koda wasa bata sanar masaba ko a waya, dukda ita kuwa tanajin komai a wajen hajia Hindu, harma rashin lafiyar Abba da hajia Hindu batasan sirrinba saida hajia deluwa taji.

**********

Washe gari da yamma lik'is Abba ya farka, sai dai jikinsa duk babu wani k'arfi.
Ganin ya farka hajia Hindu ta Kira Uncle yahya kamar yanda ya buk'ata.
Uncle yahya najin haka yakira doctor Abbas doguwa akan yaje Abban ya farka.
Doctor Abbas kwararren likita a asibiti. Aminu kano, Wanda d.p.o ya had'asu Uncle yahya dashi. Yanajin shirin da sukai akan Abba saiya canja musu shawara akan baza'a masa Alluraba barciba, dan zata iya cutar dashi, zai dai bi wata hanyar ya tsarashi.
Wannan daliline yasa koda Dr Abbas yaje duba Abba saiya sanar masa jininsa yakai k'arshen hawa, a zahiri kuma jinin Abban yahau k'ololuwa, Dr Abbas ya k'ara da fad'in "Alhaji inhar kayi wani hayaniya zuciyarka zata iya bugawa, kuma komai zai iya faruwa, mutuwa ko mummunan ciwon dayafi Wanda kake ciki yanzu, dan haka kahuta a gida tsawon kwana goma mugani, koda wanene yazo nemanka ace bakanan, idankuma ka amince inada inda Zan kaika ka huta".
Da hanzari Abba yace, "Dr kakaini koma inane, hakanne kawai zaisa Na tsira daga Alhaji garba, danshi kad'ai ya Isa yasani bak'untar kabari yau-yau d'innan".
"To shikenan Alhaji babu damuwa, ALLAH ya k'ara lafiya".
Wannan dabara ta likita itace tasaka aka samu damar killace Abba waje guda domin asamu Jiddah ta tare gidan mijinta lafiya.??


???????????

A washe garin d'aurin auren Aliyu bai samu shigowa wajen Jiddah ba, saboda zazza6i da amai da Maimuna taita fama dashi, saida aka maidata asibiti aka k'ara Mata ruwa sannan tad'an samu k'arfi-k'arfi.
Kwana biyu da d'aurin auren ya Kira Uncle yahya ya sanar masa zaizo.
Dan haka Uncle yahya shima yaje ya sanarma Jiddah dakeshan gyara itama.
A gida kuma ya saka Maman Sadiq ta shiryama malam Aliyu abin tarba dukda yace zuwan dare zaiyi.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï

Da taimakon Maimuna dake fama da kanta ya shirya, dan yanzu tarigada ta shagwa6ashi da komai sai an masa.
Yayi matuk'ar yin k'yau cikin boyal blue mai duhu sosai, hakama hularsa blue sai takalmi bak'i, sosai Maimunatu ta zazzage masa turarurruka har saida ya kwace yana fad'in "Malama ya isheki haka, sokike ki karyamin tattalin arzik'in turare ne?".
Cikin dariya Maimuna tace, "Haba dai Yaya, yada saurin karaya haka? Indai turarene zamu saka maka a lefe nida k'anwata Jiddah, kasanfa mu maza Na had'a lefe to mu mune zamu had'a maka wannan karon tsabar kaid'in d'an gatanmu ne".
"A haba dai tawajena da gaske? To kinga k'ara zazzagamin kawai". 'Yay maganar yana mik'a Mata kwalaben turarurrukansa'.
Dariya sosai Maimuna ta sanya masa, "Oh ni Yaya, ashe dama malamai sun iya son bati suma?".
Murmushi yayi har hak'oransa Na bayyana, ya damk'i hannunta yana matsawa yanda zataji zafi "Sake fad'e naji".
"Wayyo Yaya ALLAH da zafi, idan ka tsinke hannun maga Wanda zaima girki a gidannan, dan k'anwatama bazata makaba".
"Ahaf yarinya, basai naje Na auro Nana Hafsat (miss Xoxo) ba, dama kullum saitamin massage Na soyayya safe da yamma, dukda nace Mata matana biyu tace ko uku ne zatazo ata hud'u dan tsabar k'aunar da takemin".
Cikin had'e fuska Maimuna tace bazazzage zaka zama kenan? To ALLAH kama fad'amata ta kiyayeka, kai d'in mijin mace biyune kacal insha ALLAH, dan naji su Yaburra har suna yad'awa a gidan Alhaji khaleel mai mota dakaje duba y'arsa Islam cewa zaka auri Hafsat d'in, damadai shiru namaka naga gaskene?".
(Zazzagawa bayinmufa akwai son Mata da gaske uwargidan malam????¡â)
Hannu yakai zaikuma damk'ota ta gudu bayi tana fad'in "Wlhy katafi k'anwata Na jiranka, inba hakaba nakirata nace karta baka ruwa mai sanyi".
Dariyar dabai shiryaba yad'anyi, kafin ya juya ya fita yana d'aura agogonsa da fad'in "Habawa yarinya Zan kamakine, saikinmin bayani dalla-dalla idan Na dawo ai". Zuciyarsa cike take da farin ciki dakumajin k'arin k'aunar Maimunatu a ransa, gefe d'aya Na zuciyarsa Na ayyano masa yanda zai iske amaryar tasa mai idon kuka.............???


https://youtu.be/eOU-ju4f6KY

*_Sisters mai buk'atar Raina Kama a audio zai iya bin wannan link d'in Na sama, Abban Dausayi YouTube channel tv??????_*

*_Saura naji wani yace Abba Zakari ya zare kuma???????????????????¡â??_*







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????
[12/13/2019, 2:33 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*



*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce????_*

*_[33?34]_*


..............Cikin masifa Gajiram ta mangare Jiddah da akema kwalliya tana kauce-kauce, "K wlhy kishiga taitayinki, angaya miki mud'in sakarkarune irinki da zamu Bari kitafi harbutsai-harbutsai gunsa? Nakula saina miki sabon sabis akan zaman gidan aure Jiddah".
Dariya Zarah da Walida suketa k'umshewa, dan sudai yau iyayen nasu dariya da kunya suketa basu, sai 6aro manyan magana suke irinta manya. Umma da Yaruwaiya ma nadaga d'aki suna jiyosu, girgiza Kai kawai sukeyi suna dariyarsu daga can.
Tsaf suka kimtsa Jiddah, tareda bajeta da wasu sirrikan k'amshi na ainahin jinin barbarawa, bawata kwalliyar hauka sukai mataba, faudace kawai sai kwalli da lips gloss mai dad'in k'amshi, harda abin saka k'amshin baki aka zazzagama Jiddah a baki, waiko ya sheikh zai rage zafi inji Balu.
Kuka kawai Jidddah ta sanya musu, saboda maganganinsu sunmata girma, gawani tsoro da suke sake cusa mata, Gajiram harda cewa k'ilama su samo babie yau??.

Su Zarah sukai Mata rakkiya gidan Uncle yahya, lokacin harma Aliyun ya iso, dan haka Maman Sadiq batabar Jiddah tama zaunaba tace tacire hijab ga gyale ta sanya. Idanu Jiddah ta gwalalo kamar zata fasa ihu, cikin sanyinta daya had'u da rawar muryar son Fara kuka tace, "Mama dan ALLAH ki barni naje a haka, ALLAH bazan iya........".
Uncle yahya daya shigo ya katse Jiddah da tuni kwalla sun cika idonta, "Wai mikuke jirane kuma? Tun d'azu yana jiranta haka babu k'yau ai".
"Yi hak'uri Abban Sadiq yanzu zata tafi". 'Maman Sadiq tayi maganar tana cirema Jiddag hijjab da kanta. Gyalen ta yafo Mata tana d'an harararta, murya k'asa-k'asa yanda Uncle yahya dasu Walida bazasujiba tace, "Saura kije kimasa dososo wlhy, ki Saki jikinki komi ya nuna yanaso kibarsa, dan wlhy wata yabaro a gida kema kin sani".
Kai kawai Jiddah ta d'aga Mata tafita tana gyara gyalen zuwa saman kanta, abinda bai dametaba a rayuwarta kenan, wato saka gyale, zama ta iya rantsewa tunda ta mallaki hankalinta bata ta6a saka gyale tafita anguwaba.
Da wannan tunanin ta k'arasa k'ofar seat room d'in, saida taja gyalen sosai takuma rufe jikinta da fuskarta sannan tayi sallama a hankali.
Malam Aliyu dake tsaye akusan tsakkiyar falon ya amsa Mata cikin sanyinsa da zumud'in ganinta, gaba d'aya fitinannen turarenta ya dabaibaye hancinsa tunkan ta shigo, saida taja wasu seconds kafin ta d'aga labulen ta shigo kanta a k'asa, dama gashi gyalen ya rufe Mata fuska, amma tana ganinsa saboda gyalen babu kauri.
Shima yana hango fuskarta kad'an dukda tayi k'asa da ita, dan falon kwanyar yake da wutar Gen... Da Uncle yahya ya tayar.
Sassanyar ajiyar Zuciya Aliyu ya sauke, kafin ya bud'e dukkan hannayensa alamar tazo gareshi.
Ina Sam Jiddah bazata iyaba, dan haka takoma jikin bango ta mak'ure tana kumayin k'asa da kanta, yayinda bugun zuciyarta ke k'aruwa.
Murmushi yay mai sauti yana takowa a hankali gareta, duk wani takunsa kuma tsulmata a tsoro yake, dan ta gama lura da gaske kanta yayo.
Daf da ita yazo ya tsaya, k'amshinsu yagama gaurayewa waje d'aya yana fidda wani sirri na musamman saboda iskar fanka dake kad'awa tana kuma gaurayeshi.
Kallonta ya tsayayi daga sama har k'asa, dukda tana sanye da gyale hakan bai hanashi yaba halittar Ubangiji ba, shikam yadace da mata masu k'yak'k'yawar sura, dan Maimunatu ma masha ALLAH.
Sosai Jiddah takejin idanunsa na yawo a jikinta, dan haka takuma k'ank'ame jikinta waje d'aya. Murmushi yakuma saki yana d'an rankwafowa kanta yanda hartakejin fitar numfashinsa, cikin sassanyar muryarsa yace, "Lallai wannan amaryar mai tsadace, indai sayen fuskane nasiya da farashi mafi daraja Hauwa'u-Jiddah". Ya k'are maganar yana saka hannayensa duk biyu ya d'age gyalen data yane fuskarta ya saukeshi kan kafad'arta.
Da hanzari ta d'ago idonta daya gama tara kwalla ta kallesa, tuni idonsu ya shige cikin na juna, Jiddah tayi azamar janyewa da k'ok'arin duk'ewa k'asa saboda mazarin da jikinta yakeyi sosai, dan tunda take bata ta6a samun irin wannan kusancin dawani d'a namijiba, ko alhaji garba da aka d'aura musu aure bai ta6a koda rik'e mata hannuba, dan haka a yau takejin lamarin da girman gaske......
Kafin takai k'asa itada tunaninta tuni Aliyu yayi azamar ruk'o kafad'unta ya maidata tsaye, kafin tasamu damar yin maganar da take k'ok'arin yi tuni ya sakata a jikinsa ya rungume.
Rikicewa sosai Jiddah tayi, ga jikinta Na wani irin tsuma da rawar mazari, abin ya had'e Mata uku, sabon al'amari, lalurarta, gargad'insu Maman Sadiq dasu Balu.
Sheikh Aliyu kam lumshe manyan idanunsa yayi yana karanto addu'ar godiya ga Ubangiji ayayinda kasamu wata ni'ima daga garesa,

????????? ???? ??????? ???????????? ??????? ????????????? .
*_"Alhamdu lillahil-lazee bini'imatihi tatimmus-salihat"._*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login