Showing 39001 words to 42000 words out of 121675 words

Chapter 14 - MUTUM-DA-DUNIYARSA COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Sep 2024

17160

an d'orashi aka nad'e hannun da bandeji aka bashi magunguna da sallama.
Tunda suka shigo gidan yake Harar sashen Jiddah yana kunkuni, kai tsaye sashen hajia deluwa driver ya rakashi.
Sai wani sannu da tarairayarsa takeyi, "Sannu kaji Ashir, amma dai yarinyarnan muguwace wlhy, muna ganinta salaf-salaf kamar bazata iyaba".
"Wlhy mami bazan hak'uraba saina rama, haka kawai kinsakani aikata Abu naje a banza an nakasani, to ayanzu naratse miki saina aikata Na gaske a kanta, naje da nufin Mata barazana tamin haka, to ta shirya Na gaskiyar kuwa w........"
"Kai wai bakada hankali Ashir! Ba Matar Ubanka baceba, banason halin dabbancifa".
"To amma mami ai duk kece kikaja ko, dabaki turani mata barazanarba tayaya hakan zata faru? Ni koma kallo da zata ishenine? ALLAH kinji Na rantse saina fatattaka yatinyarnan kuma a cikin gidannan saidai dad ya koreni bayan nayi".
Dafe kai hajia deluwa tayi, dama tasan Ashir akwai bak'ar zuciyar tsiya, duk maganar da take masa bai sauraretaba yafice fuuuu zuwa sashensu.

Jiddah kam bayan taci kukanta ta more tashitai ta koma d'aki abinta.
Bata sakejin motsin kowaba Na gidan har ta kwanta, sai a cikin barcine tad'anji motsi a d'akin, idonta ta bud'e kad'an saitaga Alhaji zaune yana latsa lap-top.
A tsorace ta tashi zaune, yad'an kalleta yana wani had'e fuska.
"Dama kin kwantar da hankalinki kin kwanta abinki, ni idanma mace Na jini a tsarina ko ta6ata banayi balle tunanin ra6arta".
Badan Jiddah ta yardaba tazame ta kwanta, saidai dukta takura takasa barci, har kusan karfe d'aya taga yazo gefenta ya kwanta tareda juya mata baya, tun tana fargaba harta farajin saukar numfashinsa cikin gurnani.
A hankali ta sakko k'asa ta kwanta itama barci 6arawo yayta fusgarta har yay galaba a kanta.


*_Bayan kwanaki hud'u_*

Jiddah dukta kuma figewa saboda tunanin su Umma da fargabar halin datake ciki, bata sake had'uwa da Ashir ba balle hajia deluwa, Alhaji Garba kam yakan shigo mata da safe, da daddare kuma anan yake kwana, amma zai raba dare yana latse-latse a laptop, tarasa ubanda yakeyi, zamansa a d'akin yake sakata barci rabi da rabi saboda tsoro, shiyyasa dasafe saitaita zabga barci, ALLAH dai ya taimaketa yau yagama kwana bakwai ya koma wajen uwargidansa itama tasami sukuni.
Da wannan barcin hajia deluwa tasamu damar shigowa sashenta ta saka wani Abu a k'ark'ashin gadon Jiddah tun a randa tacika kwana uku a gidan.
Jiddah dai batasan mike faruwaba, yau bayan tayi sallar azahar tad'an fito falonta ta zauna, gaba d'aya batajin kwarin jikinta, saboda tunda tazo gidan bataci abinciba, kullum sai kayan kwad'ayin da Alhaji garba ya kawo Mata na sayen baki, a kullum kuma Alhaji garba Na tambayarta Ana kawo mata abinci? Itakuma saitace eh kawai. Bai ta6a sanin ba'a kawowaba shidai, dan itama hajia deluwa daya tambayeta haka takecewa ankai Mata. da wannan ya d'auke hankalinsa bai saka idoba. Yau kuma gashi a lissafi sashenta zai kwana, duk fargaba ta isheta
Sallamar Alhaji garba tajiyo cikin nishad'i, dan muryarsa a matuk'ar sake, tasan farin cikin nasa baya rasa nasaba da rutsata tana sallar walha d'azun, dan sai kusan 9 ya fita daga gida yau, yashigo mata sallama ne ya isketa tana sallah, tun sannan yaringa farinciki da tambayarta Ashe tasamu tsarki? Itadai kasama bashi amsa tayi a d'azun......
Tunanintane ya katse jin yace, "hummmmmm!" Yana toshe hanci. Da mamaki ta kallesa, ganin zai juya da sauri tace, "Alhaji sannu da dawowa".
Hannu kawai ya d'aga Mata ya fice da sassarfa. Yana fita ya sauke numfashi da fad'in "Kai wannan wane irin warine a sashen yarinyarnan?". Babu Mai bashi amsa dan haka yay gaba zuwa sashen hajia deluwa.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï

Wasa-wasa dai sashen Jiddah ya gagari Alhaji garba harma da Ashir dake fakon Jiddah yay ramuwar gayya.
Ita kuma Jiddah haka kawai takejin wani masifar tsoron maza, ko maganar namiji taji a TV saita rikice, cikin kwana uku kuma saiya koma ma tana tsorata da ganinsu koda a TV ne, dan dama ananne kawai take ganin nasu, tunda ba fita take konan da canba.
Tashin hankali Na biyu abinda take samu taci komai ya k'are, yauma duk a jigace ta wuni saboda yunwa, sallama ta magrib sai a zaune tayita saboda rashin karfin jiki, babu abinda take d'urama kanta sai ruwa.
Zuwa washe gari ko ruwa tasha sai amai, saboda babu komai a cikinta, ga wani Uban jiri dake d'ibarta.
Cikin ikon ALLAH saiga bilki mai aikin hajia tazo kawo Mata waya inji Alhaji, dan yakai kararta wajen Abba shine abban yace ya had'asu, shikuma bazai iya zuwa sashenba shiyyasa ya aiko bilki.
Ganin halin da jiddah take ciki sai hankalinta ya tashi, dan jiddah da k'yar ta iya fad'a mata yunwa takeji, da hanzari ta ajiye wayar takoma sashen hajia deluwa a sace ta had'o tea da abinci takawo sashen Jiddah. Itace ta taimaka Mata tad'ansha tea d'in cikinta ya warware, sannan tabata abincin shima kad'an taci saboda cikinta ya cinkushe, tanama gamaci sai amai.
Sosai bilki taji tausayinta, itace ta taimaka Mata ta gyara jikinta sannan ta gyara wajen, koda Abba ya Kira sai bilki ta d'aga a matsayin Jiddah, yagama bambaminsa harya yanke wayar bilki dake mamaki da al'ajabi bata tankaba, aiko ko fad'a ma Jiddah yanda akayi batayiba. Tadai koma sashen Alhaji tace masa Jiddah batada lafiya.
"ALLAH yabata lafiya". Yafad'a a k'ufule yana amsar wayarsa.

Tundaga ranar sai bilki takoma kaiwa jiddah abinci a sace, dukda Jiddah nasamun abinci sai ciwo ya zame Mata jinya, kullum tana a kwance babu lafiya, ciwon baya da k'irji ga wani tsoron maza dake kuma shigarta babu gaira babu sabar.
A haka tacika sati uku a gidan, ranardai Alhaji garba yakasa hak'uri, dan haka ya aika bilki da yamma dayake yadawo da wuri saboda juma'ace ta kirawo masa Jiddah.
Tunda Jiddah taji Mai kiranta saita birkice tahau kuka da rokon bilki taje tace tayi barci.
Bilki tace, "Hajia karama dan ALLAH kizo muje Karna rasa aikina".
Jin wannan furici Na bilki ya saka jiddah Binta, dan bata fatan bilki ta rasa aikinta ta sanadinta. Sai dai kumafa suna yin ido biyu da Alhaji garba jikinta ya Kama rawa tafara kuka da Neman kofar fita, da sauri yazo ya rufe kofar yana matsota cikin toshe hanci, yayi alkawarin yau ba wariba kominene saiya more dubu d'ari biyunsa Na sadaki.
Yana kai hannu zai ta6a jiddah ta kwala Kara da lalumar filawa dake kusa dashi ta kwala masa akai.
Take anan ya zube a sume, jiddah kuma tayi waje da gudu tana kuka.
A k'ofa sukaci Karo da hajia deluwa zata shigo, ram ta rike jiddah tana tambayarta miya faru? Ina jiddah takasa magana, jikinta sai kuma 6ari yakeyi saboda hango Ashir da Bala dake nufosu saboda jin kururuwar jiddah.
Da k'arfi ta hankad'a hajiya ta nufi fita da gudu, Ashir da bala sukai tara-tarana kamata, Bala Na rik'e hannunta shima ta hankad'eshi da karfin tsiya yafad'i kasa da fasashshen kai ta fice a guje saboda Mai gadi da Ashir da direba da suma ke tara-taran kamata.
Haka jiddah taita gudu, mahaukaciya zam a titi, babu inda take dosa sai hanyar gida kuma, saikace wadda ake control da remote. Mutane da yawa sunyi yinkurin kamata abu ya gagara saboda mazane.

A gidan Alhaji garba kam tashin hankali biyu, Alhaji da bala duk sun sume, hakanne yasa Ashir kiran y'an sanda ya sanar musu su Kama jiddah, yayinda mai gadi da driver ke kokarin saka su Alhaji mota za'a kaisu asibiti.
Hajia deluwa kuwa sai shar6ar majina take tana kuka da tsinema jiddah, ita bazata yardaba inhar mijinta da d'anta suka rasa ransu wlhy saita kashe jiddah itama, shi bala daga dawowarsa kwana biyu kenan Jiddah ta kashe matashi. Haka taita sambatu har sukaje asibiti dasu.


???????????.

Su Zarah na zaune a tsakar gida kowa nad'an wiki cikin rashin kuzari, dan tunda Jiddah tabar gidan dukkan farin cikin gidan ya gushe, Ga Umma kuma ta hanasu zuwa gidan Jiddah su ganta kwata-kwata, sai Maman Sadiq ce da aunty Nafisa suka shirya zuwa gobe su dubota, shiyyasa Umma tace Subari idan sunje sunga hankalinta kwance suma saisuje.
Da gudu Jiddah ta shigo musu, dan haka suma duk sai suka kwasa da gudu zuwa cikin d'aki, amma k'arar da jiddah ta kwala tana zubewa a k'asa yasakasu lekowa a rikice, ganin jiddarsu ce duksai suka yo waje hankali a tashe, gaba d'aya kanta sukai suna kiran sunanta, amma ina fisge-fisge kawai take tana kwalla gigitattar k'ara......
A haka Uncle yahya yashigo a rikice shima, dan tuni sama'ila Mai shago dasukaga shigowar jiddah anguwar Ana shirin sallar magriba sukaje suka kirashi.
Yana kai hannu zai ta6a Jiddah takuma sakin wata k'arar datafi ta farko.
Kowa saiya kuma birkicewa, ga kofar gida yacika da y'an anguwa, kowa yana tambayar miya sami Jiddah?. Isowar motar y'an sandane yasa kallo komawa Kansu, kutsawa sukai zuwa cikin gida babu ko tsayawa Neman iso.
Babbar magana, y'an sanda dai sunga abinfa yawuce tunaninsu, dan shigowarsma saita kuma kid'ima Jiddah tacigaba da sakin wani ihu Mai fita da gurnani maiban tsoro, sai wata irin fisga takeyi nason guduwa daga rikon da sukai Mata........



Tashin hankali ba'a saka maka rana??, wayyo jiddah.??

???????????


A 6angaren Aliyu kam Maimunatu na samun tsarki a ranar yay shirin gwajin lafiyarsa cike da fargaba.
Da farkoma shareta yay kusan kwana goma da samun tsakinta, saida yau yaji yakasa jurewa saboda sha'awar kasancewa da mace yakeji ainun. Dan haka yaymata shiri Na musamman irinna masu ililin da sukasan sirrin yanda ya kamata a tunkari mace, musamman ma budurwa.
Cike da tsoro yayta driving Nata akan abinda yakamata tayi kafin akai ga kwanciya, sunyi salla da tambayoyi dayay Mata akan addini Wanda baisamu Matsala da itaba sai kad'an-kad'an.
Daganan kuma sukai shirin barci.
A farkon Fari da fargaba yake sarrafata, da lamura sukai nisa kuma sai komai ya tafi dai-dai fiyema da yanda yay zato.
A ranar yasamu nasarar Fara bin hanyar cikar burinsa, dan baiyarda yazo Mata kaitsayeba.
Haka yayta Binta a hankali har tsawon kwanaki hud'u kafin yayi Mai gaba d'aya.
Maimuna dai kam tazama Aliyu, Aliyu kuma yazama maimuna. Saidai muce ALLAH yabada zaman lafiya Na har Abadan.
A kwanakin da suka biyo baya sosai yake Nuna Mata kulawa Mai cike da martaba ta, dukda tasan baya sonta b¨¤i ta6a Nuna mataba koda a fukane kuwa.
Saima mamaki da yake bata yanda ya iya sarrafa mace a zaman takewa Na yau da kullum da shinfid'arsu. Abin ba'a cewa komai sai sambarka.
Tuni kaunarsa takuma mamaye jini da ruhinta, suk hanyar dazata k'yautata masa ita takebi.
A haka sheikh Aliyu yafara gudanar da al'amuran addini a anguwar, masallacinsa da makarantarsa suka Fara aiki, da dare maza magidanta ke d'aukar karatu, wataran kuma ya gudanar da tafseer.
Da safe kuma matan aure, da yamma yara da y'ammata.
Kafin kacemi makaranta tafara cikewa, dan kowa yaji babban malami sheikh Aliyu maina ne, to baya sanya saiya kawo iyalansa dashi kansa.
Angwanci yayi matuk'ar kar6ar Aliyu, danya murje yayi wani 6ul-6ul dashi, sai wani k'yalli da cikar kamala yake k'arawa.
Kullum yaje gaida malam kuwa saiya tsokanesa akan mirjewar da yayi, hakama malam mustafa.
A yanzukam bashida wata Matsala, komai yana tafiya masa dai-dai saidai abinda ba'a rasaba Na kalubalen rayuwa Wanda ba'a taba raba Bawa dashi musamman ma irinsu dake d'auke da nauyin al'umma.............???


https://youtu.be/eOU-ju4f6KY

*_Zaku iya sauraren RAINA KAMA a audio ta wannan link d'in Na sama, Abban dausayi YouTube channel tv??????_*



*_Humm yau dai nasan ba sauk'i a wajen fans????¡â??¡â??¡â??¡â??¡â????????_*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu??????_*
[12/1/2019, 11:17 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*



*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce????_*

*_[18?19]_*


..............Duk yanda akaso nutsuwar Jiddah abin ya gagara, sai da y'an sanda suka kira Uncle yahaya waje dansuyi magana sai akaga Jiddah ta lafa daga fisge-fisge da k'arar da takeyi. Hakanne yasaka Umma dake kuka son fahimtar wani Abu, amma batace komaiba tajigaba da tofama Jiddah Addu'a.
Bayan kamar mintuna goma Uncle yahaya ya dawo, yana shigowa Jiddah ta tashi aguje zata bar wajen, rik'eta Zarah da walida sukayi da k'yar da taimakon Uncle yahaya suka kaita k'asa.
Cikin kuka Umma tace, "Uncle d'insu ka fahimci abinda Na fahimta kuwa akan yarinyarnan?".
Kansa ya jinjina alamar eh, idonsa jajur shima saboda damuwa yace, "Maman Nafisa Jiddah batason maza su ra6i inda take, lallai akwai abinda ke faruwa dabamu saniba, dan dak'afa fa tazo gidannan tundaga can gidan. Kuma yanzu y'an sandarnan waifa anturosune su kamata saboda Alhaji garba da d'ansa suna asibiti sanadin kwala musu abu datayi. Amma halin da sukaganta a ciki yasakasu komawa".
Daga Umma harsu walida kuka suka kuma fashewa dashi, Uncle yahya yace, "Ba kuka zamuyiba Maman Nafisa, bara naje nayi sallah nazo da malam Alfah".
Da to suka amsa.
Uncle yahya yafice zuciyarsa cikeda tausayin Jiddah. Tunda ya fita sai Jiddah takuma samun nutsuwa, dan haka su Umma suka kamata zuwa d'aki saboda mutane makwafta dasuke shigowa jajanta abin, wasuko gulmace ta kawosu.


???????????

A asibiti kam da k'yar aka samu jinin dake zuba a kan Alhaji Garba ya tsaya, shiko bala sunama zuwa ya farfad'o, dan baiwani buguba sosai, allurar barci sukai masa danya samu Hutu.
Ran Hajia Deluwa da Ashir kam yakai k'ololuwar 6aci, musamman ma da y'an sandan sukazo suna Kora musu bayanin wai ai Jiddah ta haukace, suko tayaya zasu Kama Mara hankali. Tamkar Ashir ya makesu haka yaji, hajia deluwa kuwa datasan abinda ya faru komawa tai gefe takira malaminta tace ya warware asirin dayay ma Jiddah, amma yayi wani Abu akan Alhaji garba danya Saki Jiddah, tanason akama Jiddah aimata hukunci.
Da to kawai ya amsa mata, danshifa akwai abin tsoroma dayake hangowa gameda wannan abin da suka aikata, shiyyasama tunkan ta kirashi ya warware Na warin ja6a da jiddah keyi, saurama d'ayan.
Shima Alhaji garba wajen karfe tara aka samu ya farfad'o, alurar barci suka sake masa danya samu nutsuwa.



???????????

Bayan an idar da sallar magriba Uncle yahya sukazo shida malam alfah, kallo d'aya yayma Jiddah yafahimci akwai sihiri a jikinta, dan indai daga ita saisu Umma ne zakajita luf, da namiji yashigo gidan zata hau ihu da fisge-fisge. Addu'oi yabada kafin safiya asan abinyi.

Tunda aka bata ruwan addu'ar sai barci ya kwasheta, bata kuma sanin inda kanta yakeba har asubahi. Yayinda su Umma suka kusan kwana a tsaye suna Kai kukansu ga ALLAH.
Washe gari Alhamdllh jikin nata, dan dakanta tai alwala tagabatar da salla.
Bayan ta idar ne Umma tabata Qur'an, babu musu ta amsa tana karatu, har wajen awa d'aya kafin ta ajiye tahau yin azkar. Duk wannan abun dake faruwa y'an uwanta na zagaye da ita, saida ta kammala sannan ta gaida Umma, su Zarah suka gaidata suma suna rungumeta danjin dad'in ganinta normal.
Babu Wanda yay Mata magana akan matsalarta, saima itace ke cewa "wai Umma ya akai nadawo gidane?".
Murmushi Umma tayi tana Kama hannunta, murya a tausashe tace, "Uncle d'inkine ya d'akkoki Jiddah".
Murmushi ta d'anyi amma batace komaiba. Ana cikin haka sukaji sallamar Uncle yahya, atake jikin Jiddah yafara rawa tashiga matsawa baya.
Uncle yahya yad'an murmushi kawai, cikin k'arfin hali yace, "Haba jiddodona ninefa, ko baki ganeniba?".
"Na ganeka Uncle". 'tai maganar murya a raunane tana cigaba da matsawa'.
"Kinga yi hak'uri karkiyi kuka, amma fad'amin tsorona kikeji?".
Fashewa tai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login