Showing 99001 words to 102000 words out of 121675 words
Ha?iye sauran kukan tayi da ?yar, cikin sinne kanta tace, "A'a na daina, bara naje kar aunty tace zatayi aiki da kanta, kaga jiya ta yini batajin da?i ma".
Murmushi yay idonsa akan la??anta dake motsawa a hankali, ya ?ora goshinta saman nasa yana kallonta, "Ai kema bakida lafiyar, kiyi kwanciyarki zanje na tayata ni, dan yau a gida zan yini".
Ba ya da ta iya dole tabi Umarninsa ta kwanta ?in, shikuma ya fice sashen Maimuna.
A kicin ya sameta tana ?o?arin kwa?a filawar da zatai fankasu, ya sumbaci gefen kuncinta yana fa?in, "Jazakillahu bil jannah Ummudduniyah".
Murmushi tayi dukda kishinsa da takeji na taso mata, ta?an juyo itama ta sumbaci kuncinsa tana amsawa da, "Tare da kai Kalby".
"Ya babyna?". Yay maganar yana zagayo da hannunsa a cikinta daya fito sosai.
"Yana cikin ?oshin lafiya Nurry, sai dai kewar Abbunsa da yakeyi sosai".
Numfashi ya sauke a cikin kunnenta, cikin ra?a yace, "Shima Abbu yana kewarsa matu?a, ko zamuje yanzu mu gaisa".
Dariya Maimunatu ta sanya, "Yaya nikam rufamin asiri, ina ?anwata?".
Murmusawa yay yana sakinta kafin ya shafa kansa, cikeda jin kunyarta yace, "nabarota tana azkar, mizan tayaki dashine?".
Maimuna tai murmushi kawai, dan tasan badai azkarba, da azkarne ai dabaizo tayata aikiba, a filikam sai tace, "A'a na hutashsheka".
"Nikuma ban hutar da kainaba madam".
Babu yanda ta iya dole ta barsa sukayi aikin tare, bayan sun kammala yakoma ?akinsa.
Wayam ya tarar babu kowa jiddah ta gudu, amma an gyara ?akin tsaf yanata ?amshi.
Wanka yayi yashirya cikin ?ananun kaya, sosai yay ?yau tamkar ba shiba.
Jiddah data gudo tuni koda tadawo sashen natama ba kwanciyar tayiba, gyara ?akinta zuwa falo ta?an kumayi, ta ?aura ruwa ta dafa takuma gasa jikinta sosai sannan tai wanka, tagama shirinta tsaf tana ?o?arin kunna wayarta Aliyu ya shigo.
Kallo ?aya tamasa ta ?auke kanta tana amsa masa sallamar, sai dai yamata ?yau sosai, yaune ranar farko data ta?a ganinsa da ?ananun kaya, ashe dama yana sakawa....?
Har ya iso gabanta bata saniba, saida ya ri?o hannuntane tadawo hayyacinta. "Malama jiddah tunanin mi akeyine haka? Ko nawa?".
Murmushi tamasa kawai.
Shima saiya murmusa yana fa?in "Kinyi ?yau sosai tawan, irin wannan gayu haka mai hana ango fita?".
Sosai ta dara yanzukam tana rufe baki, shima dariyar yakeyi zuciyarsa namasa da?i da sakin jikinta da takeyi dashi sosai yanzun.
Saida ta saka gyale sanan suka nufi sashen Maimunatu, yauma dai kosau ?aya Jiddah bata yarda sun ha?a ido da maimuna ba, sanan bata saka baki yau a hirarsu sosai kamar sauran ranakun, shi Aliyu yasan kunya da sauyin da jikinta ya matane ya kawo hakan, itakuma Maimuna sai takejin tsoro a ranta kar jiddah ta fara sauyawa saboda da?in miji data fara ji.
???????????
Da safe koda su Kalifa suka wuce makaranta sai hajia hindu tai shirin zuwa gidan Umma da nufin mata barka da tashin ba?i wai, amma kuma abinda ke a ranta shine son ganin idon Abba.
Ta iso Umma ce ka?ai a gidan, Walida da Zarah duk sun wuce makaranta, zarah wata islamiyya ta shiga anan anguwarsu ta matan aure, ana zuwa tara a taso sha ?aya, gani tagama ssce exam ?inta da zaman banza sai Umma tace tashiga islamiyyar kafin ALLAH ya kawo mafita, idan auren ne kokuma sa?anin hakan.
Umma na jan ruwa a rijiya Hajia hindu tayi sallama ta shigo.
?agowa Umma tayi tana amsa mata sallamar da mata sannu da zuwa, sai dai ?asan ranta tayi mamakin ganinta, dan ranar tariyar jiddah ma sai yamma li?is tazo gidan, kuma bata da?eba ta tafi.
Amma sai Umma ta tareta da ?ya?y?yawar fuska, bayan tace mata tashiga falo itakuma ta ?iba ruwa ta bita.
Kafin Umma ta shigo hajia Hindu tai saurin le?a bedroom ?inta wai ko Abba yana ciki, wayam ta gani, hakanne ya sakata saurin komawa ta zauna saboda jin motsin tahowar Umma.
Ruwan Umma ta ajiye mata sanan ta zauna suka gaisa suna tambayar juna yara. Kafin cikin kissa hajia hindu tace, "Ai zuwa nai dama Zarah ta rakani nagano gidan ?ata Jiddah".
Umma tace, "ALLAH sarki, gashi kuma kunyi sa?ani tanama islamiyya".
"Kai amma banso hakanba wlhy, shiyyasa naita ro?on Abbansu ya jirani mufito tare tunda yace nan zaizo".
Murmushi Umma tayi batace komaiba, hakanne yasakasu yin ?an shiru na wasu mintuna......
Sallamar Uncle yahya ne yasaka Umma mi?ewa tafito tana amsawa, yanda ta gansa kamar a rikicene ya sata tambayar "lafiya kuwa Uncle ?insu?".
"Wlhu Maman Nafisa babu lafiyarnan, dan yaya aka kama tun jiya, sai da safenan naje kasuwa nakeji, naje station ?in da aka kaisan kuma sun?i bani belinsa, yanzu dai haka zancen danake mikima sunce kotu za'a shiga gobe idan ALLAH ya kaimu".
Cikin dafe ?irji Umma tace, "Akanmi ni Yagana?".
Cikin tsantsar damuwa Uncle yahya yace, "maganar ku?in Alhaji Garbane".
Hajia hindu tafito itama a rikice tana sallallami, mamaki sosai Uncle yahya yayi da ganinta, amma dayake a ru?e yake sai baibi takantaba suka shiga maganar mafita kawai.............???
*_Masoya ina mi?o ?unbin gaisuwa a gareku tareda fatan alkairi, alkairin ALLAH ya kai a gareku aduk inda kuke, Comments naku na sakani nisha?i ?warai da gaske, shikuma ke ?aramin ?warin gwiwar muku typing koban niyyaba, ina godiya da addu'oinku gareni ga mahaifina???????????????????_*
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*?AURIN ?OYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ?ADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ?AYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RA?UMI..!* (Bilyn Abdull)
????karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*????????????
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[12/28/2019, 12:33 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[55?56]_*
..............Belin Abba dai ya gagara gasu Uncle yahya gaba ?aya, dagashi har Umma kallo ?aya zakai musu ka fahimci suna tare da damuwa, hakama su Zarah harda kukansu, sai Ummace taita lallashinsu.
?angaren Hajia Hindu ma tashiga damuwa, hakama yaran data sanar musu duk sai suka shiga rashin walwala, itama saita kwantar da kai suka ha?u dasu Uncle yahya akai cuku-cukun lauya aranar.
*WASHE GARI*
Washe gari ?arfe shabiyu aka shiga shari'ar su Abba, tun a bayanin ?arar jikinsu Uncle yahya yay sanyi, anama Abba tambaya, amma sai ya?i amsa laifinsa, saida aka kai ruwa rana shida Lauyan Alhaji Garba, saida shedun dake tsakani lokacin da aka amshi ku?in suka bayyana kafin Abba ya nutsu. ya amsa kar?a ku?in Alhaji garba da yayi, amma yay bayanin yanda sukayi dashi daya bashi auren Jiddah, daga baya kuma saiyace ya janye.
Sosai ran Al?ali ya ?aci jin sunyi amfani da yarinya cikim har?allarsu, take anan ya yanke hukunci dan ?
Shari'ar bata bu?atar zama na gaba kuma
"Bisa ga sauraren wannan shari'a da mukayi, dakuma amsa laifin da wanda ake ?ara yayi, tareda shaidu ?warara, wananan kotu ta yanke hukuncin dolene Alhaji Zakari yaro ya biya Alhaji garba ku?insa naira miliyan ashirin da biyar kamar yanda suka tsara lokacin auren ?arsa, sanan miliyan Ashirin da biyar dayace ya barmasa dolene yacika al?awari ya bar masa ?in, tunda anyi auren, kuma yarinyar harma ta tare a gidansa, wani abune daban ya rabasu bayan auren, shikuma Alhaji zakari yaro bazaici miliyan ashirin da biyar ?innan shi ka?ai ba, zai ?auke miliyan goma ne a ciki, sauran miliyan sha biyar kacokan zai ?aukesu yabama ?arsa da yay auren jari da ita. anmasa sassauci yafara biyan Alhaji garba ?u?insa kafin ?arsa, yanzunan za'aje da dillalai gidansa da inda yake sana'a a ?iyasta da ku?in da ake binsa, idan sunkai abashi canjinsa, idan basukaiba yanema ya cika nanda sati ?aya kacal. Kotu". Al?ali ya buga guduma an tashi kenan.
Sosai hankalin Abba yagama tashi, banda zufa babu abinda yakeyi, kotu kam tuni ta ?auki ?ananun maganganu, kowa yana tofa albarkacin bakinsa akan wannan lamari
Ita Umma ma tarasa abin cewa, jinwai Jiddah taci miliyan goma sha biyar. Shi kansa Uncle yahya abin yay masa wani gingiringin, su zarah kam sunrasa mizasuyi, ba?in cikin halin da abbansu yake ciki, ko farin cikin ku?in da ?ar uwarsu ta samu. Hajia hindu kam ai tana cikin ru?ani, a ganinta wannan shari'ar batayiba, ita kuma ?a?anta shikenan su tashi a tutar babu, kai ina da sake al?ur'an.
Umma da yara gida suka nufa gwiwa a sake, Uncle yahya kuwa yabi jami'an tsaro dake tare da abba.
Kasuwa aka fara zuwa babban shagonsa dake dan?are da kayan kicin, nan take mahukunta suka fara ?iyasta abinda ke cikin shagon da shagon kansa, dan tuni yazama mallakinsa dama.
Har magriba suna cikin kasuwa ana cakusawa, daga ?arshe akaima shago da kayan ciki ku?i naira milyan ashirin da biyu, sai cinikin ciki dubu ?ari tara da wasu canji a sama, amma basu cika miliyan ?ayaba, hakanne yasa akabarsu a miliyan 23 kawai.
Sallah kawai sukayi aka nufo gidansa, dama tuni su ashir sun kawo dillalalai ana zuwa maganar ku?i kawai akayi, ansaya naira miliyan bakwai shima gidan, ku?i sun kama miliyan talatin kenan, saura miliyan goma ake nema kenan harda na Jiddah.
Hindu dai kuka take rurus yaranta na tayata, wanan wace iriyar masiface, shikansa Abban kukan zuci yake, shikenan yau tashi tagama ?arewa, ?ar kwanciyar hankalinsama ?ayace sune ku?in da akace yabama jiddah, yasan insha ALLAHU hannunsa zasu dawo, dan kar?ewa zaiyi koda karfin tuwone.
Komawa akai da abba station, Uncle yahya yawuce gida jikinsa a sanyaye.
Sunbar Hajia Hindu na neman yin ?aramin hauka, dan taci alwashin sam bazata amince da wanan tsarinba. A daren ta kira ?aninta tantirin ?an isaka yana zaune a legas tace yataho kano gobe-gobe.
Ba?a?en magana yafara sakar mata dan basa shiri sosai dama, ta dakatar dashi tanai masa bayani dalla-dalla, jin zancen ku?ine saiya kwantar da hankalinsa, atake yay mata al?awarin baro legas shida yaransa da adaren ranar.
Wannan shine ya?an saka mata kwanciyar hankali, dan tasan bazasu tashi a tutar babuba dai kenan suma.
???????????
Jiddah duk batasan hidimar da akeba, dan Umma ta hana kowa ya sanar mata, amma su Aunty Nafisa dasu Aunty Sauda duk an sanar musu da halin da ake ciki, dukda abinda yay musu kasancewarsa mahaifinsu hakan bai hanasu shiga tashin hankaliba da tsananin damuwa.
Washe gari aka ida tattare ku?in dake bank accaunt ?in Abba da wani gidansa dake karkasara ana haya, ku?i sukakai miliyan talatin da shifa da ?yar, baida wata sauran kaddara sai gidan dasu Umma suke ciki, shima sai akayi cinikinsa miliyan uku da rabi, yamayi darajane saboda a cikin tsohuwar anguwa yake wadda gidaje keda daraja komai lalacewarsu, dukda ma dai gidan fes yake, ballema anmasa fenti lokacin bikin Jiddah da alhaji garba.
Dabarar da Uncle yahya yayi itace ro?ar al?ali a saka gidan dasu Umma suke ciki a lissafin ku?in jiddah, hakanne yasa aka ?eba ku?in Alhaji garba miliyan ashirin da biyar aka dan?a hannun su ashir, sauran miliyan sha shida da takardun gidan dasu Umma ke a ciki aka dam?ama Uncle hayha, saura dubu ?ari biyar Abba zai cikama jiddah, anbashi sati ?aya yakawo cikon ku?in Jiddah rabin miliyan.
A ranar aka sako Abba da yamma li?is suka taho da Uncle yahya daya ?akkoshi da nufin ajiyeshi gida, shikuma yakoma yakai ?u?in Jiddah banki, dan canne kawai zasu tsira sai ?ura ta lafa kuma asan abinyi da su.
Zuciyar Uncle yahya a tsarkake take, dan haka yayma abba rakiya har cikin gidansa da aka sayar wanda hajia hindu take ciki.
Abin mamaki saiga hajia hindu taimusu tarba mai nuna alamun damuwa da halin da Abba yake ciki, harda rungumeshi a gaban yara babu ko kunya. Da wanan damar Abba yasamu damar gwargwa?a mata wata magana. Kanta ta jinjina masa sanan ta sakesa tana kallon Uncle yahya.
"Dama dawowarku muke jira yahya, dan harma munfara ha?a kayanmu, kwanaki biyu kawai suka bamu mubar gidanan, dan ALLAH kozaka taimaka mana da kimtsa kayan ?akin Abban kalifan".
Kallonta uncle yahya yayi, kamar zaice wani abu saikuma ya fasa ya?an kalli agogonsa, yamma tayi lis, ga ku?innan da yakeson kaiwa banki "Hindu inaga mubar aikinan zuwa da safe, yanzukam dare yayi gaskiya".
"To shikenan hakanma babu damuwa, amma taimakamin ka dakkomin wani akwati dake sama a cire takardun gidan Jiddah karsu shiga ruguntsumi".
Uncle yahya bai kawo komai aransaba, ya maida kallinsa ga Abba dake zaune su Hussain sun zagayeshi, "Babu damuwa, wannene ?akin?".
Da hannu ta nuna masa, babu musu ya nufi ?akin kansa tsaye, sa?af-sa?af hajia jindu tabi bayansa, yana shiga taja ?ofar ta rufe.
Da sauri Uncle yahya yajuyo yana ?wala mata kira da ro?on ta bu?esa, amma ?iri da muzu ta?i.
Dawowa tayi wajen Abba tana fa?in "Nagama aikin da kasani Abban kalifa".
Da sauri Abba yaja hannunta sukabar gaban yaran, "Yauwa hindu, abinda yasa nace mu kullesa saboda mu samu mubar gidanan, dan ko sama da ?asa zata ha?e bazan bama jiddah wa?annan ma?udan ku?inba, maza duk abinda yadace ki ha?a mu kama hanyar kamaru, dagacan zamuyi sudan, munbar Nageria kenan har abada".
"?ari bisa ?ari na gamsu da jawabinka, amma muyi ha?urin asubanci, dan yanzu dare yafara, tafiya da wa?annan makudan ku?in ha?arine Abban kalifa".
Shiru Abba yay yana nazarin maganarta, zuwa can yace, "To babu damuwa, yanzu dai ki ha?a mana dukkan abinda yadace, a yanzu mu lodasu a mota, ko yara karki sanar musu komai".
"Hakan yayi amma kuma matsala ?aya, idan Yahya yakira mana ?an sandafa?".
"Kwantar da hankalinki, saida na tabbatar yabar wayarsa a mota sanan".
Da?i ya kama hajia hindu ta rungume abba cikeda ?oki.
Duk bugun ?ofar da Uncle yahya keyi basu bu?eshiba, harma yagaji ya bari, hankalinsa yayi matu?ar tashi dajin bayanin da Abba yazo yamasa a bakin ?ofa.
Idanunsa na zirar da hawaye yace, "Yaya karka aikata haka, Jiddah fa ?iyarkace data fito daga jinin jikinka, miyasa zaka aminta da cigaba da zalintarsu suda mahaifiyarsu, kana ganin adalcine gudun da zakayi ka barmu saboda dukiya? Baka tsoron ita wadda zaka gudun da ita taci amanarka?, wlhy nasan jiddah zata iya barmaka ku?innan, amma sh........"
Cikin daka tsawa Abba yace, "Ya isheka haka munafiki, babu abinda ya isa dakatar dani wlhy".
"shikenan naji yaya, Amma makomar auren maman Nafisa fa?".
"Aurenmu na nan munafiki babu mai rabashi, bazan ta?a yadda bakin inna ya biniba, tunda tace idan na saketa ALLAH ya isa ko bayan ranta to bazan saketanba balle kaje ka aureta, dan nasan burinka kenan a kulum, saidai ta mutu da aurena wlhy".
"Yaya karkayi haka dan ALLAH, wanan zaluncine wlhy, ka tausayama baiwar ALLAH nan koda a wanan ga?arne".
Tsaki Abba yay yabar masa bakin ?ofar.
Sosai hankalin Uncle Yahya yakuma tashi, haka yaha?ura ya zauna yana ?ulla abinda zai fisheshi, gashi wayarsa na a mota ya bari.
Cikin dare saiga ?arayi sunyi dirar mikiya a gidan Abba, tun Uncle yahya najin hayaniya sama-sama harya fara jiyo magiyar da Abba kema ?arayi da ro?onsu.
Zuwa can kuma yajiyo