Showing 15001 words to 18000 words out of 121675 words

Chapter 6 - MUTUM-DA-DUNIYARSA COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Sep 2024

17142

jagoranci tafiyar amma ta hanyar rubuta jarabawa, daganan zuwa awa d'aya kunada damar yin nazari, zamu dakatar da malamai yau gaba d'aya daga kowanne darasi".
Atare ajin ya d'auki kabbarar *ALLAHU AKBAR!!!*.
Malam mustafa yay musu sallama ya fita.
Nanfa kowacce tashiga duba littatafanta da fatan dacewa.


???????????

Abba kam yana isa katafaren gidansa ya iske su kalifa tsaitsaye a harabar gidan suna jiransa. Babu Wanda ya gaidashi, saima tunzura masa baki da suka shigayi wai sunyi fushi.
Fuskarsa cike da fara'a ya hau fad'in "O shalelen Abba amin afuwa kunji, maza kushiga mota Na kaiku karku makara, Abba yayi laifi ayi hak'uri".
Cikin tura baki Hassan yace, "Amma Abba tunfa d'azu muke jiranka, kabarmu dukmun bushe a tsaye".
"Ai nace ayi hak'uri ko Hassan, Muneer taho kaji". Yak'are maganar yana Kama hannun autansu Muneer.
Kalifa kuwa da Hussain uffan basuceba, shi kalifa ma iyafis ya saka a kunne, Hussain kam yayi cid'in-cid'in da fuska yana wani shan k'amshi.
Ko'a mota Muneer ne kawai ke fira da Abba, amma Hussain da kalifa da Hassan tamkarma babusu a motar.
Ya diresu a makarantarsu mai tsananin k'yau ta y'ay'an manya y'an gata, ya zaro dubu d'aya yabama Kalifa, babu ko godiya yay wucewarsa aji, Hussain da Hassan kuma d'ari biyar2, suma dai babu godiyar, amma sun d'aga masa hannu alamar bye.
Munner ne aka bama d'ari biyu dukda an shiryo masa abinci a lunch box nashi kuwa.
Kalifa ajinsa uku 6angaren sakandire, Hussain da Hassan su kuma aji biyu, Munner kuwa yana firamare 5 ne.
Saida Abba ya raka Munner har sashen y'an firamare sannan yashiga motarsa ya fito daga makarantar................???



Kuyi manage please??????


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu??????_*
[11/21/2019, 2:43 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*



*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce????_*

*_[7.....]_*


..............Kamar yanda malam Mustafa ya fad'a bayan awa d'aya malamin da zaima su jiddah jarabawa ya shigo, sallama yay suka amsa masa tare da gaisheshi.
Ajin yayi shiru kowa yana kallon malam Sulaiman, yad'an tura hularsa baya yana shafa gaban goshinsa da nazarinsu, saikuma yay murmushi ganin duk sunyi tsuru-tsuru sun zuba masa idanu. Zama yay inda aka tanada domin zaman malamai kafin ya kuma maida hankalinsa Kansu.
"Inaga nama canja shawara kawai, zanyi jarabawar da baki".
Kallon kallo aka komayi tsakanin su Jiddah, kowanne a sanyaye ya amsa da,
"Na'am ya mu'allim".
Fita malam Sulaiman yayi, babu jimawa ya dawo shida Malam Shu'aibu da malam mika'il. Nanma su Jiddah gaidasu sukayi. Malam Sulaiman yabasu izinin fita waje su duka, zuwa wajen wata bishiyar dake gaban aji. Ahaka zasu ringa zuwa d'aya bayan d'aya.
Da yawansu sun rikice, dan kowa baisan miza'a tambayeshiba, ga malam Sulaiman gwanine wajen iya zak'ulo tambaya.
Amirar ajin mai suna Shamsiyya jamilu yasaka ta rubuto sunayen kaf y'an ajin tazo saman baranda tana kiransu d'aya bayan d'aya. Hakan kuwa tafaru, bayan tagama rubuta sunan kowa aka Fara, gaba d'ayansu dama su 38 ne a ajin, dan haka aka fara komai a tsanake. Kowa ya fito saikaga yana mazurai, nanfa cikin Jiddah Yakuma d'urar ruwa, (dama ita kwai tsoro) saima Madina ce ked'an k'arfafa Mata gwiwa. Tunda aka kira Bilkisu Ahmad Jiddah takuma tsurewa, dan daga bilkisun sai madina sai ita. Bayan fitowar bilkisu aka kira Madina daga nan sai Jiddah, tamkar wadda k'wai ya fashewa a ciki haka ta shiga ajin, inda kowa ke zama idan ya shigo ta zauna itama.
Malam Sulaiman dake kallonta ya karanto mata tambaya,
*"Malama Jiddah ko zaki iya fad'a mana Kalmar shahada da Manarta?"*.
Dak'yar Jiddah ta iya had'iye yawu, k'asan zuciyarta tana addu'ar Neman nasarar yin bayani cikin nutsuwa, zamanta tad'an gyara cikin sanyinta tace,

*_"SHAIDAWA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH , KUMA MUHAMMADU MANZON ALLAH NE"_*
_Wad'an nan kalmomin shahada guda biyu, sune kofar shiga musulunci, sune kuma rukuninsa mafi girma, kuma ba a yin hukunci da musulusncin mutum, sai da furuci da su, da kuma aiki da abin da suka k'unsa, da wannan ne kuma kafiri yake zama musulmi._
*_MA'ANAR KALMAR SHAHADA_*

_Ma'anar shaidawa da cewa babu abin bauta da gaskiya sai ALLAH, shi ne yin furuci da ita tare da sanin ma'anarta, da kuma yin aiki da abin da tak'unsa, zahiri da bad'ini, malamai sun had'u akan cewa furuci da kalmar shahada, ba tare da sanin ma'anarta ko yin aiki da abin da ta k'unsa ba, ba shi da amfani, kai sai dai ma ta zama hujja a kansa, kuma ma'anar (La Ilaha Illallah) shi ne babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH shi kad'ai matsarkaki mad'aukaki._

Rukunan wannan kalmar (shahada) sune (korewa da tabbatarwa), wato kore hak'k'in bauta daga wanin ALLAH, kuma tabbatar da shi ga ALLAH shi kad'ai ba shi da abokin tarayya. Haka kuma wannan kalmar ta
K'unshi kafircewa d'agutu (shi ne dukkannin abin da ake bauta masa wanda ba ALLAH Mad'aukaki ba, ko da kuwa ya kasance mutum ne (tare da yardarsa da bautar da ake masa), ko dutse, ko bishiya, ko son zuciya, ko sha'awa), da nuna masa k'iyayya da yin kubuta daga gare shi.Wanda ya fad'i wannan kalmar (shahada da bakinsa) amma bai kafircewa abubuwan da ake bauta

musu wanin ALLAH ba (a aikace), to tamkar bai fad'eta
ba.
ALLAH Mad'aukaki sarki ya ce:


"Kuma abin bautarku abin bauta ne guda d'aya. Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi. Mai

rahama Mai jink'ai".(Bak'ara: 163).

Kuma ALLAH Mad'aukaki ya ce:


"Babu tilastawa game da (shiga) addinin

(musulunci), hak'ik'a shiriya ta bayyana daga 6ata, saboda haka wanda ya kafirce wa d'agutu kuma ya yi

imani da ALLAH, to hak'ik'a ya rik'i igiya amintacciya, (wadda) ba ta yankewa. ALLAH kuwa Mai ji ne, Masani
ne". (Bak'ara: 256).

Kuma kalmar (Ilah) tana nufin abin bautawa da gaskiya, duk wanda ya kudurci cewa abin da ake nufi
da kalmar (Ilah) shi ne: Mai halitta, Mai arzutawa, ko Wanda yake da ikon kirkira, kuma ya kudurci cewa yin imani da wannan kawai zai wadatar, ba tare da kad'aita
ALLAH da ibada ba, to hak'ik'a fad'in kalmar (La Ilaha illallahu) ba za ta amfane shi ba, a nan duniya wajen shiga Musulunci, kuma a Lahira ba zata kubutar da shiba daga azaba madawwamiya.

ALLAH Mad'aukaki ya ce:

"Ka ce (da su): "Wane ne yake arzutaku daga

sama da k'asa? ko kuma wane ne yake mallakar ji da gani?, kuma wane ne yake fitar da mai rai daga matacce, ya kuma fitar da matacce daga mai rai? Wanene kuma yake tsara al'amura?" To za su ce: "ALLAH ne". To ka ce (da su): yanzu ba za ku ji tsoronsa ba?" (Yunus: 31).

ALLAH Mad'aukaki ya ce:


"Ko wane ne ya halicci sammai da k'assai, ya kuma saukar muku da ruwa daga sama, sannan (da wannan ruwan) muka tsirar da (shukokin) gonaki masu k'ayatarwa, ba kuwa za ku iya tsirar da bishiyoyinsu ba?, shin akwai wani abin bautawa tare
da ALLAH, A'a, su dai mutane ne da suke kauce wa (gaskiya)".(Naml: 60).
Kuma ALLAH Mad'aukaki ya ce:

"Kuma lallai idan ka tambayesu, "Wane ne ya halicce su?, Lallai za su ce: "ALLAH ne" To, yaya ake juyar da su (daga bauta wa ALLAH)?" (Zukhruf: 87)". Jiddah ta k'are jawabinta cikin sauke numfashi da ajiyar zuciya.

"ALLAHU Akbar". malam uku suka had'a baki wajen ambata. yayinda jiddah keta addu'ar dacewa da tsoron yin kuskure.
Malam mika'il yace, "zaki iya tafiya".
Kamar an bige mata gwiwoyi haka ta mik'e ta fito, a bakin barandar ta zauna kamar yanda su madina sukayi. Murya k'asa-k'asa madina tace, "Ukti mi aka tambayeki?".
Jiddah tai murmushi cikin sanyinta tace, "Ma'anar Kalmar shahada. Kefa?",
"Ni sharud'd'an Kalmar tauhidi guda biyar. Amma wlhy duk saina rud'e ukti".
"Bake kad'aiba ALLAH, har yanzu ni kaina gabana baibar fad'uwaba". Cewar Jiddah tana kar6ar ruwan da madina ta mik'a mata. Sosai tasha ruwan harta d'an samu nutsuwa. Suna zaune a wajen suna d'an ta6a hira har aka gamawa kowa suka koma aji. Bayan fitar malaman kowa ya shiga k'us-k'us da makwafcinsa a kan tambayar da akai masa. Da wannan suka cinye lokacin tashin.


???????????

Sai kusan 9:30am Malam Aliyu yasamu tashi, kansa yad'an rage ciwon amma yanayi k'asa-k'asa har yanzu.
Tashi yay bakinsa d'auke da addu'a, yayi mamakin barcin da yayi, a gaggauce ya mik'e yayo alwala domin gudanar da sallar walha kamar yanda ya Saba, yau barci yasashi zai makara. Koda ya idar d'akin ya kimtsa, ya d'auki filas d'insa Na tea ya fita zuwa cikin gidan dan Neman ruwan zafi. Ta k'ofar cikin gidansu yabi inda Kai tsaye zata kaishi sashen iyalan malam. Shiru gidan babu wata hayaniya, Kai tsaye kicin ya nufa, nanma babu kowa dama baiyu tunanin samun kowanba, yana tsaye zuciyarsa Na tunani d'aura ruwan zafin sai yaji motsi a bayansa.
Waigawa yay da mamakin wanene?.
Maimuna dake bayansa tsaye ta saki murmushin basarwa tana fad'in "Yaya Aliyu ina kwana? mikake buk'ata ne?".
Batare da yayi magana ba ya nuna mata filas d'in daya ajiye.
K'arasowa tayi ciki kicin d'in "Kaje Yaya bara Na dafa maka, asaka kayan k'amshi".
"Eh ki saka, amma miya hanaki zuwa makaranta?".
"Uhm... Uhm wlhy Yaya ciwon......."
Saikuma tayi shiru ta kasa k'arawa.
Kad'an ya kalleta ya d'auke kansa, can k'asan mak'oshi yace, "Ba dole kuyi ciwon maraba kullum kunacin zak'i, yakamata kafin sati d'aya da zuwan jini ku ringa d'agama duk wani Abu mai zak'i k'afa, Ku kuma yawaita amfani da ruwan zafi yayin da yazo...."
Yana gama fad'a ya wuce abinsa tamkar bashi yayi maganarba. Ita kanta Maimuna da kallo ta bishi baki bud'e, sum-sum dashi sai zaro magana, komai girmanta babu ruwansa shi, to ita yaushema tace masa ciwon mara takeyi? "Kai Yaya Aliyun nan ni wlhy harma yaban kunya, a inama yasan Mata na ciwon Mara dalilin period???". Ta k'are maganar da rufe ido.
Shikam gogan naku ko'a jikinsa, hankalinsa kwance ya koma 6angarensu yashiga wanka.

Koda Maimuna tagama dafa ruwan batai gigin d'auka takai masaba, a kicin d'in ta barsa, dan basa Shiga sashen samarin gidan kwata-kwata.

Koda ya fito saiya koma cikin gida ya d'akko filas d'insa, yana shirin fita Maimuna ta shigo kicin d'in hannunta d'auke da kula madaidaiciya.
Kanta a k'asa tace, "yaya gashi inji iya"..
Baice komaiba, yadai mik'a hannu ya amsa yay ficewarsa, saida yafita sosai sannan yace, "kice Mata nagode".
Maimuna ta girgiza kai tana fad'in "ALLAH ya k'yauta, shidai kullum baki 6am, idan kaji yana dogon bayani sai a tafseer ko k'arin karatu kokuma shida Malam".
bakuma dan baya maganarba, danshi ba miskili baneba, kawai dai fahimtace bataiba, dan itad'ince baya sakewa da ita, dadukma macenda ba muharramarsa ba, muharamman nasama taka tsantsan yake dasu, sannan shi ba'a surutun banza dashi Mara ma'ana.

Baimasan tanaiba, dan shi tuni yaje d'akinsa. Tea ya had'a babu madara, sai wasu abubuwa daya zuba wad'anda suka saka turirin shayin fita da wani k'amshi mai dad'i da saka kwad'ayin shan shayin. Saida ya bud'e kular da Maimuna ta bashi yaga fankasune sai miya a robar kular tanata tashin k'amshi, maidawa yayi ya rufe, saida ya shanye shayinsa daya had'a sannan yafara cin fankasun a tsanake.
Bayan kammala cin abincinsa daduk wani uzirinsa yay shiri cikin shadda ruwan makuba mai duhu, d'as taimasa k'yau daka gansa kaga cikakken d'an Arewa, yad'au hularsa Zanna bukar kalar shaddar ya saka. Kafin kace me d'akin ya gauraye da wani mayatacen k'amshi mai sanyaya zuciya da sakata nishad'i.

Tunda ya fito aketa gaishesa a k'ofar gidan, yayinda shikuma yake gaida dattijan da suka girmesa, tuni wani saurayi yazo ya kar6i littatafan hannunsa, agogonsa ya kalla, dan yanason shiga wajen malam kafin ya wuce inda zaije, ganin sha d'aya saura saiya nufi cikin soron, dan yasan malam ya fito yanzu, a zauren farko ya iskeshi shida wasu mutane guda biyu a rukunin kujerun da'aka shirya tamkar falo acan gefen soron kasancewar babba, annan malam ke karatu da d'alibansa dakuma ganawa da b'aki.
Sallamar Aliyu ya sakasu amsawa a tare suka juyo suna kallansa, ya cire takalminsa a gefen kafet d'in kafin yak'arasa shiga rukunin kujerun, hannu ya mik'ama bak'in malam sukayi musabaha, sannan yaje gaban malam ya risina yana gaisheshi cikin mik'a masa hannu sukai musabaha (malam bai amince d'ansa yak'i samun ladan musabaha da shiba, shiyyasa kozai gaisa da yaransa suma yakanyi musabaha dasu tamkar kowa, hakama matansa).
"Ya ciwon kan Ali?".
"Alhmdllh baba". Aliyu yafad'a yana d'an murmushi kafin ya kuma fad'in "Babu wani Abu da za'ai maka? Zanje wajen Mustafa ne".
"Eh to kaje abinka harma ka dawo, dan akwai bak'in da zasuzo inason ka gana dasu".
"To bara kawai nabari saisunzo d'in, daga baya naje wajen Mustafan".
"A'a kaje abinka kawai, dan sai k'arfe hud'u mukai dasu, nikuma akwai inda nakeson zuwa a wannan lokacin, shiyyasa nace musu zasu gana da kai". Malam ya k'are maganar da mik'ama Aliyu key d'in motarsa.
Hannu biyu Aliyu yasa ya kar6a yana godiya kafin ya mik'e yay musu sallama. Yana k'aunar mahaifinsa sosai, akoda yaushe cikin kulawa dasu yake, haka yake masa inhar zaifita inda yazama saiya hau abin hawa, saiya d'auki makullin motarsa ya basa, saboda shi yama kasa sayen motar, dukda Alhamdllh gwargwadon hali yanada y'an kud'insa dazai iya sayen koda k'aramace dai-dai k'arfinsa, to amma akwai abinda ya dakatar dashi daga sayen tukunna.
Da wannan tunanin ya k'arasa inda motar malam take ya bud'e, yayinda Wanda ya kar6a littatafansa sanda ya fito yamatso jikin motar shima ya saka masa a gefen mai zaman banza.
Cikin murmushi Malam Aliyu yace, "Jazakhallahu khairan kamaludden".
"Amin malam". Kamal ya fad'a yana washe baki da rufema malam Aliyu k'ofar.


???????????

Tunda Jiddah ta iso k'ofar gidansu bayan mai napep ya ajiyeta taga babu motar Abbansu sai farin ciki ya kamata, ta sauke ajiyar zuciya tana nufar shiga, da sauri ta dawo baya danta manta batayi addu'ar shiga gidabama (Kai jiddo??).
A yanda ta shigo cikin farin ciki saiya saka Umma dake kwashe dambu a kula murmushi, "Kuluwa ko anyo mana samune yau?".
Dariya Jiddah tayi tana fad'in "Umma mikika gani?",
"Naganki cikin farin cikine ai, nasani ko suruki aka samowa yahaya".
Da hanzari Jiddah ta shige d'akinsu tana dariya. Umma ma dariyar takeyi tanajin dad'in ganin d'iyar tata cikin farinciki akasin sanda suka fita. Kira ta k'walama Jiddah.
Jiddah ta ida cire hijjabinta sannan ta fito.
"Haba yarinya, kinga ina dambu koma kimin sannu". 'Umma ta k'are maganar dad'an harar Jiddah.
Hannu Jiddah tasa a baki tana dariya kafin tace, "O Umman mu kad'ai, ALLAH kece kika bani kunya, amma nasoyin magana, gaskiya yau zamuci dad'inmu, ALLAH ya tsumbula Ummanmu a aljanna".
Umma tace, "Amin Jiddah, tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login