Showing 21001 words to 24000 words out of 121675 words
Nabel magana ma ya za6o maka mai k'yau".
Washe hak'wara kalifa yayi yana rungume Abba da fad'in "Kana birgrni Abbana......"
"Abbanmu dai". Cewar Hassan cikin jin haushi.
Kallonsa Hajia hindatu da Abba sukayi, yayinda kalifa ke antaya masa harara kafin yaja tsaki da fad'in "Jealousy".
Hassan ya ta6e baki shima yana hararar kalifan "Jealaus d'in Ubanmi za'a maka, gaskiya Abba muma ka siya mana phones, nidai nafasa sai munkai js3 d'inma, ai gashi Aisar nan suna dashi".
Hajia Hindu dake dariya tace, "Y'an biyun Abba da gaske dai kishin kukeyi da babban Yaya".
"ALLAH ya kiyaye wlhy Mom, kibarma hura masa wannan k'aton kan nasa".
"Kai dan Uwarka waye mai k'aton kan?". Kalifa ya fad'a a fusace yana mik'ewa zai kaima Hussain dayay maganar duka. Amma sai Abba yay nasarar tarewa.
"Haba yaran Abba minene abin fad'a anan, ya Isa haka to abar maganar, kowa za'a saya masa indai wayace. Kai Auta mikake buk'ata?". 'Abba ya k'are maganar da kallon Munner daketa kallonsu kawai'.
"Abba ni sonake ka siyamin motar da muka gani ni da mom ranar, nace ta sayamin saitace kud'inta bazai kaiba".
Jinjina kai Abba yayi yana maida kallonsa ga Hajia Hindu. Da ido tai masa alamar anyi haka.
Murmushi yayi, "To Auta mom zata rakani na saya maka insha ALLAH".
Sosai Munner yake murna shima.
Haka dai suka cigaba dacin abincin kaya-kaya tamkar wasu kaji. Bayan sun gama kowa ya kama gabansa.
Sayayyar da Abba yay alk'awarin yimasu Munner ce ta saka hajia Hindu sauka daga fishinta Na kwananda Abba yaje yayi a gidan Umma. Dan suna shiga d'aki ta rungumeshi.
Sosai yaji dad'in, shiyyasa ya kudiri aniyar kokartawa ya siya musu duk abinda ya alk'awarta musu..................???
(Humm?????¡â??).
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[11/23/2019, 11:01 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[9......]_*
...........Alhamdulillah komai ya kankama Na shirin tafiya taron su Jiddah, Wanda Abba baimasan anayiba, sai Ana gobe tafiyarne Uncle yahaya ya kirashi ya sanar masa.
Masifa yaytayi akan shifa bayason gantali, yagaji da yawon da Jiddah take zuwa Ana fakewa da addini, yarinya balaggiya ce zata tafi har wata uwa duniya Abuja, to bai aminceba.
Banza Uncle yahaya yamasa, daga k'arshema ya yanke wayar, koda yaje gidansu Jiddah da daddare cemusu yay kawai Abban ya amince.
Sosai Jiddah taji dad'i, dan dama gobene tafiyar tasu, duk abinda yadace Uba yayi Uncle yahaya ne yaje makarantarsu yay Mata, (dama idan irin haka ta taso shine ke musu, bama sabi takan Abba).
Tun a Daren ranar suka farajin kewar juna itada su Zarah, kad'an-kad'an saisuce gobe iyanzu kuna Abuja Yaya Jiddah, wlhy zamuyi kewarki".
Umma da ita kanta takejin babu dad'i tai dariya, "to in banda abinki walida yaune tafara tafiya? Kuma wataranfa gidanma aure duk zaku tafi, baga Nafisa ba kamar bata zaunaba".
Duk kasa magana sukai, sai hawaye dake zirara a kumatun kowaccensu, duk sanda Umma zatai musu zancen tafiya gidan aure duk saisu shiga damuwa, tunaninsu tayaya xasu rabu da juna? Tayaya zasu barta ita kad'ai?.
Umma ta ta6e baki tana fad'in "Tofa, ta6arar tazo? To kunga bara nayi nan ALLAH ya bamu alkairi".
Umma ta shige d'aki abunta, tana shiga itama ta share hawayen da suka mak'ale mata cikin ido. (??aure yak'in Mata).
Suma bayan sun gama shashshare hawayensu suka tashi daga tabarmar suna kaye-kayen tsakar gida kafin su shige d'akinsu. Acan d'inma babu mai magana, jikinsu duk a sanyaye sukai shirin barci, kowacce ta kwanta da tunanin. (??zakuyi bayani indai aurene).
Abubuwa da yawa ke saka su Jiddah kuka idan suka tuna zasuyi sure. Na farko rabuwa da juna da kuma Ummansu farin cikinsu. Na biyu wane irin miji zasuci karo dashi? Mai irin halin Abbansu ne kokuwa Wanda yafi nashi muni? Na uku tayaya Ummansu zataji dad'in rayuwa babusu a kusa? Tunda suka tashi sune take gani taji dad'i, k'aunar da take musuce tasakata hak'urin zama da mahaifinsu dukda munin halinsa da rashin k'aunar da yake nuna musu da ita kanta, to ta Yaya bazasu damuba a yayin da suka tuna zasu tafi su barta cikin kad'aici bayan ita ta zauna danta gusar da nasu kad'aicin a lokacin da suke matuk'ar buk'atarta.
Haka kowaccensu taita sak'awa da kwancewa har dare yay nisa, ganin sun kasa barci Jiddah tace su tashi suje suyi alwala suzo suyi salla.
Wannan shawarar sukabi, suka fito domin d'aura alwala, Umma dake sallar itama duk tana jiyo motsinsu. Godiya taima ALLAH daya bata y'ay'a irinsu Jiddah, dama akance Ubangiji baya had'ama bawa zafi biyu, idan ta k'untata wajen mahaifinsu saitaji sauk'i da farinciki a garesu, itako tayaya zata jahilci ni'imar Ubangiji buwayi gagara misali, shima dayake a cikin duhun kai ALLAH ya ganar dashi gaskiya.
¡ï¡ï¡ï¡ï
Washe gari duk sukuku suka tashi, gashi ranar lahadice babu makaranta, haka dai suka taimakawa jiddah ta shirya kayanta kala biyu sai Uniforms d'inta kala buyi suma (tafiyar ta kwana uku ce kacal, ko hud'u).
Bayan sun gama Karin kumallo Uncle yahaya ya iso, dan tare zasu tafi, k'a'idar makarantar su Jiddah ce inhar tafiya irin wannan ta Kama saida muharraminka, basu yarda tafiya iya malamai da d'alibaiba, kowacce zatazo da muharraminta ne aje dashi, sauk'insu ma koda tafiya ta Kama ta k'etare to lallai makwaftan Najeriyane irinsu Cameroon, Niger dadai sauransu, mafi yawanci kuma duk tafiyace ta mota balle ace babu kud'in biyan jirgi.
Har makaranta Zarah da Walida saukai mata rakkiya, sun iske malam mustafa da malam Bilal (kanin M. Aliyu) sai malam mika'il da sauran d'aliban da za'ayi tafiyar suma da y'an rakkiyarsu. Basu wani 6ata lokaciba suka shiga motar da za ayi tafiyar.
Har suka fice su Walida basubar d'agama Jiddah da Uncle yahaya hannuba, itama Jiddah Na d'aga musu, yayinda Uncle yahaya suke k'ara birgeshi da k'arajin k'aunar yaran, dan tarbiyyarsu da zumincinsu Na birgeshi, sosai yayarda da maganar man ta bahaushe dayake cewa mace itace ginshik'in zuminci, dan inhar babu ita saikaga kan y'ay'anka kowanne da inda yayi.
Wannan shine zuwan Jiddah Abuja Na uku, dan haka bata wani damu da 6ata lokaci wajen kallon hanyaba, hasalima ramuwar barci tashigayi, sa6anin abokan tafiyar tata dake hira a hankali, su Uncle yahaya dasu malam mustafa ma hirarsu sukeyi wadda ta danganci rikicin rayuwa da ta'addancin dake faruwa a duniya kullum Ana cewa musulmaine.
Sun Isa Abuja k'arfe uku Na Rana, dan kokad'an basuyi guduba, tafiya sukai a tsanake babu wani cida zuci, sun tsaya a Kaduna masunyi salla, sunkuma dad'e kusan Awa d'aya da wani Abu.
Tuni Jiddah ta tashi, dukda ba hira takeba tana sauraren hirar ta 6angarori biyu, y'an uwanta d'alibai da malamsu da iyayensu.
Sun Isa Babbar makaranta ta Arabic da akeji da ita a ciki da wajen Nageriya, dan akwai d'alibai cikinta harda Na k'etare, sannan ta had'a k'abilu daban-daban. Makarantace da duniyar ilimin addinin Islam keji da ita matuk'a, dan duk Wanda yaje nan lallai yakai abin kallo da tutiya ga al'ummar musulmai, makarantace tundaga nursery har zuwa University, guda biyuce makarantar, ta mata ce a farkon shiga layin, sai ta maza acan k'arshe wanda nisansu yakai zaka iya hawa mashinma, babu yanda za'ayi namiji ya shigo sashen mata, hakama mata basuda hurumin shiga sashen maza, akwai tsaro sosai a makarantun mai ban sha'awa da tutiya ga al'ummar musulmi. wani taro dasu jiddah sukazo a makarantar suka sauka, amma lokacin anma d'alibai Hutu, sai y'an manyan kawai suka tarar y'an jami'a, amma wannan Karon d'alibai Na nan.
Bayan y'an wasu abubuwa da suka gudana aka kai su Jiddah masaukinsu a cikin hostel. Tarba suka samu ta mutunci ga d'alibai y'an uwansu, sai kaf-kaf akeyi dasu. Hakama sauran d'aliban da suka halarci taron daga k'asashe daban-daban.
Dukda wad'annan abubuwan hankalin Jiddah naga tunanin Ummanta da y'an uwanta, kad'an-kad'an saita ayyana "komi sukeyi yanzu?". a zuciyarta.
Yawan murmushinta yasaka wata d'aliba Mai suna kemi tambayarta cikin harshen larabci, (dan yoroba ce, bakuma tajin Hausa, ita kuma jiddah bajin turanci takeba sai tsinta-tsinta da ake koya musu a makaranta dakuma Wanda y'an uwanta ke koya mata).
Murmushi Jiddah tai Mata, kafin tace, "babu komai".
Badan kemi ta yardaba tabarta.
Ranar dai haka suka kwana cikin d'alibai, inda da daddare aka gudanar da lecture mai ta6a zuciya da ruhi, wadda aka sakama suna *_TARBIYYAR MUSULMAI A YAU!!_*.
sosai wannan lecture ta shigi su jiddah da sauran d'alibai, k'arfe sha d'aya aka tashi kowa ya nufi makwancinsa. Da k'yar jiddah tasamu tayi barci, dan kewar su Zarah ta addabi zuciyarta matuk'a.
Washe garima bayan Sallar Asuba ankuma yimusu lecture, ita kuma Mai taken *_YAYA YAKAMATA MU RAYU A MATSAYIN MUSULMAI?!!_*.
Itama dai tashigi su jiddah sosai, dan har kuka wasunsu sukasha saboda jin kura kurai da al'umar musulmai suke tafkawa a cikin zaman takewar rayuwa, wadda a yanzu mafi yawancinmu bama kare hak'k'ok'i da dokar da addininmu ya sharad'd'anta mana mu rayu, kowa gaban kansa yakeyi da abinda yay maisa a zuciya. (Ya rabbi ka gyaramu muda halayenmu??????).
Sosai ake shiryama zuwan manyan bak'i wannan taro, an gyara k'aton fili da akan gudanar da makamanta wannan taron, mazaunin d'alibai, mazaunin manyan bak'i, Na iyaye, da d'alibai irinsu Jiddah daga kasashe 10 na Africa.
K'arfe kusan 9am su Jiddah suka fito daga hostel, tuni har waje ya d'inke da jama'a, manyan bak'in da aka gayyata duk sun iso.
Malam Abdul-ra'uff Adam Maina yana d'aya daga cikin manya-manyan malamai da akeji dasu a wannan wajen, tun kusan k'arfe takwas na safe ya iso shida tawagarsa, dan haka komai dake gudana a wajen akan idonsune, tundaga fitowar d'alibai da isowar sauran jama'a bak'i.
K'arfe 10 waje ya nutsa, dan mafi yawan wad'anda ake jira sun iso, acikin d'aliban makarantar aka tada wata tafara karatun alkur'ani cikin nutsuwa, tsitt kakeji wajen yayi kowa Na sauraren zazzak'ar muryarta. Bayan itama wata takuma zuwa tayi, daganan wani malami ya kar6a yana jan doguwar addu'a da fatan alkairi ga kowa tareda mik'a gaisuwar barka da zuwa ga manyan bak'i irinsu malam Abdul-ra'uff Wanda shine farkonma ambata.
Komai yana gudanane da harshen larabci. (Da banaji Nima danaga idi, rahoton da bai d'aukuba. ????)
Malam Andul-ra'uff shine Wanda ya fara gufanar da jawabi awajen taron, tareda yima kowa fatan alkairi Na musamman, daganan sauran manyan bak'in daya kamata su tofa nasu suma suka tofa.
Taro yafara gudana bisa jagorancin lectures daga malamai daban-daban da suka fito a sassan k'asashe, kowa da taken tasa lecture d'in mai shiga 6argon jiki.
Su Jiddah dai sunata saurare da d'aukar darussa, lallai wannan taro ya cancanci a kirashi Na *k'arama juna sani* .
Zuwa k'arfe d'aya aka tafi gudanar da sallah dakuma bama bak'i filin cin abinci da hutawa.
Su Jiddah duksun koma hostel domin gudanar da sallar zuhur suma.
Zuwa k'arfe 2 aka daddawo aka d'ora daga inda aka tsaya, akuma wannan lokacinne aka bama su Jiddah dama suma, an Fara kiransune makarantu-makarantu suna gudanar da karatun alkur'ni Mai girma, sannan kowacce abata damar yin bayani akan wani Abu cikin mintuna biyar.
Koda akazo makarantar su Jiddah sai malam mustafa yace Jiddah ta tashi.
Gaba d'aya jikinta rawa yakeyi, dukda ba yaune Karon farko data Fara halartar taro irin wannanba, saidai wannan ya banbanta saboda yawan jama'a, gashi kowa ya zubo mata ido, cikin takunta Na sanyi da nutsuwa ta isa inda ake buk'atar ganinta, kanta a k'asa bata iya kallon kowa saboda ta Saba ko yaushe fuskarta sanye da nikab. Koda ta tsaya agaban microphone d'inma kanta Na a k'asa, tad'anyi shiru Na wasu seconds kafin tayi gyaran murya, ahankali muryarta tafara ratsa lasifikan da ambaton bismillah tashiga karanto suratul Al-anfal.
Bawai dan Jiddah tafi kowacce d'aliba iya karatu bane zata burgeka, a'a nutsuwa wajen karatun da yanda zak'in sautin muryarta ke fita wajen fidda kowanne harafine yasaka zukatan bayin ALLAH nutsuwa, masana Na fassara kowacce aya daki-daki idan ta karanto a zukatansu.
UBANGIJI yaba jiddah matuk'ar murya mai sanyi wajen jan k'ira'ar alkur'ani Mai girma, idan tazo ayar dake gargad'i, saikaji muryarta Na rawa alamar tahowar kuka, har sai tasaka handkerchief d'in hannunta ta share idonta. Dad'in sautin muryar tama ya hana a dakatar da ita, saida takai aya ta 68 sannan malam yasamu damar dakatar da ita, yayinda hawaye masu d'umi suka wanke fudakarta, handkerchief tasa tana tsanewa kanta a k'asa, yayinda shashshekar kukanta ke fita a hankali daga cikin lasifikan.
Guri fa yayi tsit babu Mai kwakwkwaran motsi, dan kukan Jiddah ya raunana zukatan jama'a da yawa, ita kanta batasan miya k'arfafa kukan nataba ma, bayaninma da kowa keyi Na mintuna biyar ita sai hak'ura akai aka barta.
Malam Abdul-ra'uff Kama sai ajiyar zuciya yake saukewa yana k'arabin Jiddah da kallo, yayinda ransa ke hamdala da samun irin wad'annan y'ay'a acikin al'ummar musulmai.
Malamin dake kiran sunayensu yay gyaran murya yana fad'in,
???? ? ???? ? ?????? ? ??? ? ?? ??????? ??????? ???? ??????? ???????? ? ??? ???? ???? ?????.
???? ?????? ??? ?????? ??? ????? ?????? ? ???? ??????? ??? ? ?? ?? ??? ???? ???? ?????? ?????? ???? ?????? ??? ????? ??? ? ??? ??? ????? ?? ???? ? ??? ??????? ????? ???? ?? ??????. ??? ????? ??? ?? ??? ?? ????? ??? ??? ?? ??? ?????.
"Masha ALLAH malama Jiddah, irinku sune al'ummar musulmi da musulinci ke buk'ata, ALLAH ya albarkaci rayuwarki. ina taya iyayenki farin ciki da samunki matsayin d'iya, wannan wa'azine a garemu, yanada k'yau idan kana karanta alk'ur'ani karingajinsa har cikin jininka, ma'anarsa da abinda yake magana akai, ta wannan hanyarne tsoron ALLAH da k'arfin imani zai kuma yalwatuwa a zukatanmu. kamar dai yanda mukaga malama Jiddah zakari yaro ta tsinci kanta a ciki yanzu".
"Kuma sauran d'alibanmu ALLAH ya albarkaci rayuwarku gaba d'aya".
A take wajen ya d'auki kabbara ta d'alibai da ambaton Amin.
Dad'i ya kama Uncle yahaya sosai, sai nanata godiyar ALLAH yake a zuciyarsa, da takaicin d'an uwansa daya gaza fahimtar baiwa da ni'imar da ALLAH yay masa ta samun wad'anan yara.
Jiddah kam wajen zamanta takoma ta zauna tana cigaba da sauke ajiyar zuciya.
Abubuwa masu muhimmanci sun cigaba da gudana har zuwa k'arfe 3:40pm, lokacinne kuma taro ya tashi lafiya, cikeda addu'oi ga d'alibai da iyayensu.
*washe Gari*
Washe gari kam an gudanar da lecture ne, wadda gaba d'ayanta malam Abdul-ra'uff maina ne yayita, sosai tsohon ya birge Jiddah, jitake inama ita jininsace. Bayan kammala lecture d'in malam aka bada k'yauta gasu Jiddah, wadda cikin amincin Ubangiji tasamu babbar k'yauta da saka sunanata a jerin d'alibai uku da za'a tantance su wakilci Nageria musabak'a dazata gudana a k'asar saudia ta y'an shekaru 20 zuwa k'asa.
Wannan Abu bak'aramin farin ciki yasaka malam Abdul-ra'uff maina ba, ganin d'aya daga cikin d'aliban yankinsa kuma yarensa tasamu wannan dama.
Yayinda Jiddah ke gudanar da godiyarta ga ALLAH da jigogin wannan taro sai kuka ya sark'e.
Malam Abdul-ra'uff yay murmushi yana ambatar "sarkin kuka kenan" akan la66ansa, shi kansa malam mustafa murmushi yayi, yayinda uncle yahaya idonsa yacika da hawaye, dan shikam ya fahimci kukan Jiddah da biyune.
Yau kam antashi karfe 1pm, yayinda manyan bak'i sukayi haramar tafiya.
Sukuma su Jiddah sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu