Showing 81001 words to 84000 words out of 121675 words

Chapter 28 - MUTUM-DA-DUNIYARSA COMPLETE HAUSA NOVEL

18 Sep 2024

17173

Hannunta da ya sumbatane ya maidota hayyacinta, ta Saki murmushin k'arfin hali batareda ta kallesaba.
"Gimbiya gajiyarce har yanzun?".
Kanta ta d'aga masa batareda ta kalleshi d'inba, kamata yay ya mik'ar tsaye.
A hankali tace, "Nagode yaya" ta ra6a ta gefensa tawuce bayi.
Binta yayi da kallo harta shige, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi da girgiza kansa kafin yajuya ya fita.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï

Aliyu bai dawo gidanba sai da gari yay haske sosai, lokacin har Jiddah ta kammala azkar d'inta ta gyara d'akin tsaf tasaka turare, a 6angaren iya gyara da girki batada Matsala, dan mahaifiyarsu tsaye take a kansu tun suna k'ananunsu, zuwa makaranta da suke bai hanata tsayawa wajen koya musu dukkan abinda zai amfanesuba idan sunbar gabanta, gakuma lecture ta musamman da Yaruwaiya taringama Jiddah gabannin aurenta.
Gawayin nan Na kunnawa ta kunna ta saka turare sannan tafito falo, Masha ALLAH tafad'a kwalla Na cika Idonta dajin k'arin k'aunar Uncle Yahya, basuda abinda zasu biya bawannan dashi saidai addu'a, da kowanne dangi zasu zama irin Uncle yahya da zuminci bai lalaceba a wannan zamanin. Saida ta zagaya har kicin da d'ayan d'akin kafin ta dawo tafara d'an kakka6e kurar daba'a rasaba, dan babu wani datti kam. Tana gamawa takoma d'akin da suka kwana tashiga wanka, alokacinne Sheikh ya dawo, jin motsinta a bayi yasashi komawa nasa sashen.

Maimuna ma dai haka ta dage tahau gyaran sashenta tana hawaye, harga ALLAH taji tananin kishin mijinta a yau fiye da ko yaushe, shikenan yazama nasu su biyu, a fili tace, "ALLAH ka bamu zaman lafiya, kasakamin danganar hak'uri nida y'ar uwata, ka kad'e dukkan wata fitina dazata saka mu fitini adalin mijinmu" da wannan tad'anji sanyi a ranta, tacigaba da gyaranta tana Kama dukkan addu'ar datazo bakinta. Tsaf ta kimtsa ko ina, ta shiga kicin tana tunanin miya kamata tayi musu Na Karin kumallo?.

Tsaf Jiddah ta shirya cikin atanfa ruwan hanta da zanen ganye manya ruwan toka, sai bak'i kad'an daya ratsa, kayan sunmata k'yau, dan d'inkin ya zauna d'as a jikinta, aunty Nafisa ce takaima telanta yayma Jiddah d'inkuna na garari, dan basujira lefeba suka had'a y'an kud'ad'ensu sukai Mata kusan kala ashirin danta samu Na kwalliyar amarci, tunda babu Wanda yasaka ran lefen, saikuma gashi an Kai ana gobe zata tare. Su hajiya Jiddah ba'a iya d'aurin y'an gayuba????. Zama tayi tanata juya d'an kwalin a hannu, "ALLAH Sarki Zarah, kullum saikin rok'eni na zauna ta koyamin amma nak'i, yau ga ranar hakan a gareni".
Aliyu dake tsaye a bakin k'ofa yana saurarenta ya murmusa, kafin ya ida takowa ciki bakinsa d'auke da sallama.
Saurin Jan hijjab tayi zata saka amma sai yay azamar rik'e hannunta tareda rankwafowa ta bayanta suka kalli juna ta madubin. K'asa tayi da idonta kunya Na cinta tamkar zata nutse. Hijab d'in ya zare daga hannunta ya maida ya ajiye inda ta d'auka. "Daga yau inhar ba salla ba ko bak'i ko fita na haramta saka hijjab a gidannan madam".
Kamar ta fasa ihu taji, dan wannan dokar tasa tamata tsauri da yawa, ta ina zata iya zama a gabansa ahaka? Ai da kunya......
Tunaninta ya katse saboda jin hannunsa saman kanta yana shafa kitsonta dayay masifar tafiya dashi, musamman ma Wanda ya zubo gaban goshinta da aka tufk'e ya kwanta luf a fuskarta, bakinsa yakai ya sumbaci kan yana fad'in "????????? ?????!
Subhanal-lah!. (Tsarki ya tabbata ga ALLAH.) Juddatulkhair gaskiya kitsonan ya kitsu, ????? ???????!
ALLAHU akbar (ALLAH ne mafi girma)".
Murmushi kawai tayi, aranta tana fad'in irin wannan santi haka? Kujimin mutum.
Shidai sai kuma shafa kitson yakeyi da mamakin yandama ta iya zama aka yisa k'ananu haka.
Ganin santin nashi yagaza k'arewa ta zamo ta durk'usa k'asa tana gaisheshi.
"Lafiya lau Amaryar Aliy, barkanki da shigowa gidan Aliyu. Jiya bansamu danar miki maraba ba saboda kina a yanayin da bai kamata a takurakiba".
Murmushi tad'anyi kanta a k'asa tana kallon k'afarsa zuwa k'afar wandonsa na milk d'in shadda da bata sauka k'asaba sosai.
Kafad'unta ya kamo ya tadata tsaye, "Zauna ni Na d'aura miki d'an kwalin tunda kin kasa ke"..
Jiddah tarufe fuskarta da hannayenta tana fad'in "Na iyafa".
"To zauna ki d'aura Na gani".
"To saika fita".
Y'ar dariya yayi yana zame hannunta data rufe fuskar, yace, "Na takura miki ko?".
Kasa magana tayi, sai kanta data girgiza alamar a'a, shima bai samu bata amsaba ya zaunar da ita a stool d'in madubin yana k'ok'arin Ciro wayarsa a aljihu da ake Kira...........???



_A daina gulmar ya sheikh y'an Groups d'in mutum da duniyarsa??, gashinan baiyi komaiba dai??, duk kunbi kun saka masa ido, shiyyasa yayi kawaici??????¡â??¡â??¡â??¡â_







*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[12/20/2019, 12:01 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*



*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce????_*

*_[43?44]_*


.............Zaman amsa wayar yayi d'an kwallin Jiddah a hannunsa, yanda yake amsa wayar zaisa ka tabbatar shi da malam ne, kusan mintuna uku kafin suyi sallama ya ajiye wayar saman gado yamik'e yana fad'in "Baba na gaisheku ke da auntynki".
"Muna amsawa, yana lafiya shima?".
"Lafiya lau yake". 'Yay maganar yana warware d'an kwalin'.
Duk yanda yaga Maimunatu nayi haka ya lankwasa d'an kwalin kafin ya d'ora akan Jiddah, itadai saima ta hangame baki, dan da farko dukta d'auka wasa yakeyi. Kasa daurewa yayi.
tace, "Kawo Zan iya d'aurawa fa".
"Yarinya kin makaro kuma ai, kedai tsaya kawai".
Babu yanda ta iya dole ta tsaya tana kallon ikon ALLAH itakam. Aiko sai gashi ya d'aura mata, sai dai yanda yay d'aurin dolene kayi dariya, saikace irin tsofaffin yarabawannan Wanda suka k'ware a iya d'aura gwagwgwaro. Hakanne yasaka jiddah saka dariya batareda ta shirya ba, shima dai abin yabashi dariya dan haka ya d'an dara yana fad'in "Wannan bai yiba kawo a sake".
"Nidai Na gode, bara kawai Na d'aura Wanda Na iya".
"Haba hajiyata, d'aurin nan dai duk wanda ya gansa dolene yabani Aword akansa, kinga kuwa yanda kika wani had'u".
Jiddah ta rufe fuskarta da hannu tana dariya, sosai rayuwarsa take birgeta, shi mutumne mai sauk'in kai, kuma haka yakamata kowanne miji ya kasance da iyalinsa kodan shima ya samu farin ciki, MANZON ALLAH har y'ar tsere yanayi da iyalinsa saboda susami farin ciki, amma banda mazanmu Na hausawa, wani zakiga yanata dariya da fara'a a waje, amma da zarar yashigo gida saiya hau kumbura fuska tamkar fulawar da aka kwa6a danyin burodi. Hakan kuma yana k'untata iyalansa sosai, kwata-kwata mazanmu basa koyi da ilimantarwar da addininmu yay mana akan rayuwar aure, kowa tasa yake tsarawa, alhalin kafin ya kawoki gidansa lalla6aki yake da soyayya tamkar kwai a cokali..........
"Tunanin mi kikeyine Jiddah?......"
Firgigit tadawo hankalinta saboda ta6atan da yay, ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in "Babu komai".
"Okay, to tashi muje ki gaida auntynki ko".
Kanta ta jinjina masa, sannan cikin marairaicewa tad'an kallesa ta janye idonta, "Dan ALLAH na saka hijjab? Wlhy bazan iya zuwa gabanta a hakaba".
Murmushi yad'anyi, "Uhm saka, amma fa yau kad'ai".
"Nagode".


Tunda suka fito take kallon tsakar gidan, bawani k'ato baneba, gashi nan dai d'an cif dashi, rayuwa dai ta duniya ya wadatar dasu Alhmdllh, dan bazasu dai takuraba koda ansamu yara a nan gaba, tunda suka iso k'ofar d'akin Maimuna gabanta ke fad'uwa, haka kawai sai takejin tsoro-tsoro, dan bata mance had'uwarta da Hajia Deluwa ba.
Shine ya fara shiga bayan yayi sallama Maimuna dake zaune ta amsa masa, murmushi yamata kafin yay mata alamar tare yake da bak'uwa.
Maimuna data fahimci shida Jiddah ne saita mik'e ta nufo inda yake, hannu ya bud'e mata alamar tazo, kansa tayo gadan-gadan, saida tazo dab dashi saita waske tanufi k'ofa.
Baki bud'e yabita da kallo, tajiyo tamasa gwalo kafin ta bud'e labulen tana fad'in "Amarya shigo mana".
Kan Jiddah a k'asa tad'anyi murmushi kafin tashigo da sallama, Maimuna ta amsa tana kama hannunta suka ida shiga cikin falon.
Aliyu dake zaune yad'ago yad'an kallesu, ganin kan Jiddah a k'asa yake saiya harari maimunatu. Yanzuma murmushi tad'an masa, kansa ya nuna wai shi?. Saita girgiza kanta alamar A'a.
Itadai Jiddah batasan mi sukeyiba, data zaunama saitacema Maimunatu "Aunty ina kwana?".
Zama kusa da ita Maimunatu tayi tana amsawa fuskarta d'auke da murmushi, "Lafiya lau Amarya, ina fatan kin tashi lafiya? Ya kuma bak'unta?".
"lafiya lau aunty".
"To masha ALLAH Amarya, yanzu dai ga abinci, oga bismillah".
Aliyu dake kallonsu yad'anyi murmushi, yayinda acan k'asan ransa yake ambata "Matar kwarai rabin addini, duk Wanda yasamu yagama dacewa".
A filait d'aya Maimun ta zuba musu soyayyar doya, sannan ta had'ama kowa tea.
Har Oga da Uwargida suka fara ci Jiddah takasa, sai juya cokali take a cikin shayin, Maimuna ce tayi magana ganin Jiddah bataci ko sau d'ayaba.
"Amarya kobak'ya sonshi a canja mikine?".
Da sauri Jiddah tace, "A'a aunty".
"To dan ALLAH kici, nanfa gidankine, mukuma y'an uwankine, babu batun bak'unta a tsakaninmu kinji".
"kai Jiddah ta kuma gyad'a mata".
Aliyu dai najinsu baice komaiba.
Da k'yar dai Jiddah tasamu tad'anci kad'an, shima dan Maimunatu tana magana ne idan taga tayi shiru, ahaka suka kammala, Maimuna tafara tattare kayan, hakanne ya saka Jiddah mik'ewa ta tayata, saida suka kimtsa wajen sannan suka dawo suka zauna.
Zama Aliyu ya gyara tareda dai-daita kansa yakoma fuskar babu wasa, hakanne yasakasu suma duk suka nutsu wajen maida hankali a garesa.
Yay maida idonsa a Kansu "Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu".
Atare suka amsa masa.
"Alhamdulillahi, godiya ta tabbata ga ubangijin talikai daya taramu anan wajen matsayin Abu d'aya, wannan ikonsane kuma hakan rubutaccene agareshi tunkan musan zamuzo duniya, shine mai tsara yanda yaso, yakuma tabbata ga Wanda yaso. Da farko Jiddah muna miki barka da zuwa cikinmu, muna kuma miki fatan alkairin samunki kamar yanda muke k'yautata miki zato, kamar yanda na shaida miki tun farko ina zaune da matata lafiya, kuma tanamin dukkan abinda Na buk'ata, idan kinga sa6ani a tsakaninmu saina tsakanin harshe da hak'ori, k'yawawan halayenta yake k'ara girmama k'aunarta a raina kullu yaumin, insha ALLAH indai kika kwantar da hankalinki nasan zaman lafiya zai cigaba da girmama a gidanan. Maimunatu ga Jiddah nan, Y'ar uwarki kuma k'anwa a gareki, kamar yanda Na fad'a miki ina k'yautata zato a gareta, domin mutuniyar kirkice da kowa ke yabon k'yawawan halayyarta, kamar yanda nake k'aunarki a zuciyata itama inajin k'aunarta, yarinyace mai tarbiyya da sanin yakamata, insha ALLAH ina fatan bazaku samu matsalaba koda anan gaba. Nasihar dazan mana gaba d'aya amatsayinmu na iyali shine hak'uri, hak'uri jagorane, kuma katangane ga kowanne bawa, sannan kuma mutuncine ga cikar kamalar d'an Adam, duk inda akace maka wane yanada yawan hak'uri, to lallai zaka sameshi nagartaccen mutumne shi abin son koyi ga kowa, babu wata nasara dake tabbata saida hak'uri, idan babu hak'uri ko ibadar da mukema bazamu jureba, dukanku Na yarda da tarbiyyarku, ina kuma k'yautata zaton samun farin ciki a gareku, ayanzu banida wani makusancin daya kaiku, dan kafin kowa yasan matsalata kune zaku fara sani, hakama a tsakaninku, kunfi kowa kusanci da juna, dan kafin Abu ya sameku wani yataso daga danginku kunma kankushi, so babu kusancin da yakai wannan muhummanci kuwa a tsakaninmu, ina rok'inku amatsayinku Na masu ilimin addini, kunsan dokar ALLAH da abinda MANZONSA ya koyar damu, to ina fatan zamu gina rayuwarmu akan wanan tsarin, dan bai k'yautu ga d'iyan musulmai ba ace yana koyi da wani Abu Na yahudanci, dukkan mai kwaikwayon wani Abu daya fita daga tsarin koyarwar MANZON ALLAH da sahabbansa, to lallai za'a tasheshi da Wanda yake kwaikwayo aranar tashin alk'iyama, to duk abinda zamuyi yakamata mubishi a bisa tsarin addinin islama saimuga mun samu kammu cikin aminci da kwanciyar hankali. Lallai shi kishi gaskiyane, duk kuma macen dazaka ajiye bata kishinkama wannan ba Sanka takeba, to amma muringa tunawa ba kishin matan yanzu ne kishiba, dan wani kishin banda tsantsar jahilci babu komai a cikinsa, kishi mai cike da tsafta shine rige-rige wajen k'yautatama miji tamkar yanda matan msnzon ALLAH suka gunadar da nasu, tananne zakuga miji ya karkata ga son wata, dan ita zuciya Na son mai k'yautata Mata, sannan tanak'in mai munana Mata, harga ALLAH inajin sonku da k'aunarku a raina ku duka, wadda zatafi zama a zuciyata kuma yana a gareku, dan wadda ta kwantarmin da hankali da bani kulawa itace da wannan nasarar, abinda zaisa muji sassaucin kishin juna kuwa shine tsoron ALLAH da danne zukatanmu, mu d'auki rayuwar tak'aitacciya mai yankewa babu shawara, muringa tuna zafin d'aukar rai da kwanciyar kabari da tsayuwar hisabi, duk Wanda ya munanama d'aya acikinmu koda da hararane wlhy sai ALLAH ya tambayesa, dan haka saimu kiyaye, ba shakkan ganin idona zakuyiba, kuji tsoron Wanda ya haliccemu baki d'aya, sannan Ku tayani da addu'ar samun damar yin adalci a tsakinku, dan ina tsoron ranar da za'ace gani natashi cikin mutane masu shanyayyen jiki saboda rashin adalci a tsakanin iyalina. Daga k'arshe ina kuma rok'onmu dan ALLAH muji tsoron ubangiji adukkan abinda zamu aikata a wannan zaman, karmu zama cikin masu shiryama juna makirci ko jifan juna da sharri koda Na maganane, karmu biyema duk Wanda zai kawo 6atanci a zamantakewarmu, koda kuwa acikin makusantanmu ne, karmu biyema sharrin zuciya ta sak'a mana abinda zamu dawo muna Dana sani, muringa tinawa a kowanne motsinmu akwai mala'iku dake biye damu rik'e da alk'alaminsu, kuma Ubangijin al'arshi yana jinmu yana ganinmu, ALLAH yay muku albarka yabamu zaman lafiya da kwanciyar hankali Na har abadan".
Kowacce ta amsa da amin, zukatansu duk sai suka kuma raunana dayin sanyi, aganinsu minene abin zafafawa akan wannan gajeruwar rayuwar da bakada tabbacin kaiwa safiya.......
Aliyu ya katse musu tunani da fad'in "Maimunatu mizakice?".
'Dan murmushi tayi na k'arfin hali tana had'iye hawayenta da suka cika mata ido, "Duk abinda Zan fad'a Yaya ka fad'eshi, sai dai nace ALLAH yabamu zaman lafiya da hak'urin jure yau da gobe, dan itace mai wahalar, insha ALLAHU zaka samemu fiyema da yanda kake tunani, kamar yanda kafad'a hak'uri shine jigon komai Na rayuwa, ALLAH ya bamu mai amfani, yakuma baka k'arfin gwiwar adalci agaremu, dukda Alhmdllh kakai ayaba maka, dan nidai Zan iya bugar k'irji ako ina nace mijinmu adaline, ya banbanta da maza da yawa dakan wulak'anta matansu aduk lokacin da zasu k'ara aure, sannan kuma bakaimin romon bakaba nacewa k'addarace ta sakaka k'arawa badan kasoba, kafito kanka tsaye kasanarmin sonta kakeyi shiyyasa zaka aurota, kaga hakan dakayi ka k'ara Mata kima da daraja a idona, sannan baka tozartaniba yanda Zan kalli k'ara aurenka a matsayin gazawata ba, kabi dukkan sharud'a da matakan da kowanne musulmi adalin magidanci yakamata ace ya d'ora gidansa akai, dan maza da yawa suke gur6ata zaman lafiyar gidansu tunkan aure da bayan shugowar amarya, harga ALLAH ina k'aunar y'ar uwata a matsayinta Na musulma kuma Mace, abinda zai k'ara sakamin ita arai kuma shine zamantakewarmu cikin aminci babu cutar da juna ko k'untatawa, ALLAH yabamu zaman lafiya yakuma k'ara mana tsoronsa koda gujema azabar wuta".
Amin, jiddah da malam suka fad'a. Sannan ya d'ora da fad'in "ALLAH yaymiki albarka, yakuma k'ara muku k'arfin gwiwa bisa k'yak'yk'yawar niyyarki".
Nanma Jiddah ta amsa da amin.
Ya maida kallonsa ga Jiddah itama, "Jiddah fa mizakice?".
Kai Jiddah ta girgiza, cikin sanyinta tace, "Duk abinda yadace kun fad'a, fatana ALLAH yabamu k'warin zukatan aikatawa da hak'uri, sannan nima harga ALLAH Aunty tashiga raina saboda k'yak'yk'yawan halinta da awannan zamanin yay k'aranci ga mata, akanyi dogon bincike kafin asamu mace irinta, wadda miji zai k'ara aure sannan ta kar6i matar da hannu biyu dakuma zuciyar musulinci, nagode sosai aunty, halayyarki na gari da ya sanarmin tunkan shigowata gidannan tabbas nagansu a yanzu a gareki, ALLAH yabani ikon koyi da nagartarki".
Murmushi Aliyu yayi sannan ya amsa da amin. "To Alhamdullahi matana nagodema ALLAH Na gode muku, sai maganar kwana, Yaya kuke ganin za'ayi?".
Itadai Jiddah k'asa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login