Showing 114001 words to 117000 words out of 121675 words
abubuwan Suna taimakawa sosai ka gwada".
"Abinda muka fa?a dai-dai ALLAH ka bamu ladansa, wanda mukayi kuskure ALLAH ka yafe mana, ALLAH ya sakama malaman mu da alkairi damu gaba ?aya.
??????????? ??????????? ????????????? ???????? ???? ??? ?????? ?????? ?????? ?????????????? ????????? ????????.
*Subhanakal-lahumma wabihamdik, ashhadu an la ilaha illa ant, astaghfiruka wa-atoobu ilayk.*
_Tsarki ya tabbata a gare Ka, ya Allah, da yabo gare Ka. Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafararka, kuma ina tuba izuwa gare Ka._
*(Wanan Addu'ar Tashi daga Majalisi ce, (Domin Neman Yafewa Ga Abin Da Ya Gudana A Cikin Majalisin. A'isha, ALLAH ya yarda da ita, ta ce: MANZON ALLAH, tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, bai taba zama a wani majalisi ba, ko ya karanta Alkur'ani, ko ya yi wata sallah face ya cika da wadannan kalmomi. (Sai A'isha ta ce: Ya MANZON ALLAH! Na lura cewa ba ka taba zama a wani majalisi ba, ko ka yi karatun Alkur'ani, ko kayi sallah face ka fadi wannan kalmomi. Sai ya ce; "Kwarai. Duk wanda ya fadi wani alheri sai wa?annan kalmomi su zama kamar hatimi ne ga alherin da ya aikata, wanda kuma ya fa?i sharri, sai su zama kaffara ne gare shi)*.
Tuni Sheikh Aliyu ya sulale yabar massalacin, yabar mutane da tattauna wanan lecture ta yau, koda yaje yima malam sallama ma sai wani sunkuy da kai yake tamkar yana gaban surukinsa, shi malam ma dariya ya bashi, amma saiya danne baiyiba, yasan dai wannan lecture ?ince ta yau takawo wanan sinne kan, haka Aliyu yake da tsananin kunya, ALLAH ya bashi sani kuma bai gazaba wajen bayyanama mutane, sai dai ko fa?ar yake zaka sameshi mai tsananin jin kunya a garesu. Shiyyasa inhar malam yasan Aliyu zaiyi wa'azi a wajen da zasu kasance inuwa ?aya to bayama kallon inda yake, dan kuma sakashi a wata kunyar zaiyi, yauma fitowa yay daga massalacin tunda Aliyu yafara bayanin magungunan can, daga soro ya zauna yana saurarenshi yana murmushi.
???????????
Kasan cewar cikin Maimunatu ya tsufa sosai sai dukkan kulawar Aliyu da jiddah suka koma kanta, yanzu haka kowanne dare a sashenta yake kwana bisa amincewar Jiddahn, dan koda ranar girkintane idan yazo wajenta zai kusan raba dare, idanma yana da bukatarsa daya samu nutsuwa zai tsaftace jikinsa yakoma wajen Maimuna ya karasa kwanan. Bawai dan Jiddah batajin damuwar hakan bane ta hakura, a'a a ganinta wannan adalcine, dukda har yanzu bata san ra?a?a?in koda laulayin cikiba Maimuna na bata matu?ar tausayi, tanada tabbacin da ace itace a wanan yanayin babu abinda zai hana Maimuna sadaukar mata da Aliyu harta haihu, dan ayanzu hakanma ranar girkin Maimunan idan yakasance ranar batajin da?i sosai, kuma bazata iya kar?arsa ba, Aliyu kuma yanada bu?ata takan amince masa yaje ga jiddah ya samu nutsuwa, haka itama idan Jiddah na al'adah Aliyu yanada bukata kuma lafiyar Maimuna ?alau takan yarje masa yaje ga Maimuna ya damu nutsuwa, wannan adalcin nasune ke ?ara dasa masa ?aunarsu mai yawa a cikin ransa, shiyyasa kullum burinsa ya faranta musu da soyayyarsa da kuma abinda ALLAH ya hore masa, sanan ya tsare musu mutuncinsu bisaga ha??o?in da ALLAH ya ?aura masa.
Randa kuma ALLAH ya kawo sa?ani a tsakaninsu sukan zauna su fahimci juna wajen warware abin, dan kowa dai yasan zama na yau da kulkum sai ALLAH, tsakanin harshe da ha?orima ana sa?awa balle zaman kishi kona mata da miji. Amma idan aka sanyama zuciya salama sai kiga komai yazo da sau?i, to hakane ga zaman su Jiddah, Sa?ani yakansha gittawa harma Aliyu ya fahimta ya zaunar dasu yamusu nasiha da sauraren tushen lamarin, atake kuma zaibama mai gaskiya ha??insa ya nunama mai laifi kuskurensa, shima kuma yakan samu da?anin tsakaninsa dasu, wanan kam daduk wadda yasamu sukan yitane a ?aki su ka?ai batareda ?ar uwar zamanki tajiba kota sani, kuma ko afusaka bazata saninba, saboda kowanne ya iya takunsa daga Aliyun har matan nasa.
Lokacin daya iso gidan saiya iske Jiddah na kuka rungume da Maimuna daketa mur?ususu. Hankalinsane sosai ya tashi, bai wani zauna jan jikiba ya ?akko hijjab ya sakama Jiddah da Maimunan suka fiddata mota, asibitin dake kusa dasu wanda Maimuna keshan kwanci sukaje.
Haihuwace gadan-gadsn dan haka suna zuwa aka shiga da ita ?akin haihuwa, kasancewar asibitin na ku?ine baya rabo da ma'aikata.
Jiddah sai kuka take, tama kasa tsayuwa waje ?aya, ganin a rikice take Aliyu ya kamota ya sakata jikinsa ya rungume yana lallashinta.
"Addu'a take bu?ata Jiddah, kiyi hakuri kibar kukan, muyi mata fatan ALLAH ya sauketa lafiya kinji".
Kanta kawai ta iya ?aga masa, tareda ?ara lafewa a jikinsa tana sauke tagwayen ajiyar zuciya............???
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
[1/1, 5:11 PM] ??Noorunnisa??: *_Typing??_*
*_??HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_??MUTUM DA DUNIYARSA....!!??_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????_*
*_[65?66]_*
............Hajia hindu dai shirinta tai tsaf domin tafiya, Sai dai kuma ita ka?ai zata tafi bada yaraba, ?an ku?in da ake tarama Abba na dubiya tasaka Kalifa yabi duhun dare ya lalubesu tas, shima saida ya ?iba rabonsa sanan ya kawo mata sauran.
Kafin ta kwanta kamar wasa ta gwada Number ?aninta harisu kamar yanda ta saba, yaukam saiga waya ta shiga kamar almara, jikinta har rawa yake ta fara fa?in hello-hello tunkan a ?aga.
Sai da takusa tsinkewa ne aka ?aga wayar.
Cikin mamaki tace, "Wanene? Ina kuma mai wayar?".
Dariya yaron harisu yayi irinta basawa wadda harta tsorata Hindu, saida yayi mai isarsa sanan yace, "Wanan yakwana biyu a barzahu. Halan kece yayarsa da tai mana hanyar samun ?an canji".
Zumbur hindu ta mi?e dan bata fahimci maganar tasa ta farkoba, tace, "Eh wlhy nice, tun washe gari nake nemanku a raba ku?in amma wayar ta?i shiga, dan ALLAH ina harisun yake?".
Wani wawan tsaki yayi yace, "ke wai halan kanki baya kawo wuta ne, kajimin mumun mata, nace miki yana barzahu, bara na miki gwari-gwari danna kula ?wa?walwar kifi gareki, dama Oga haris baizo amsar ku?i danya raba dakeba, yazo amsane ya ware abinsa, shiyyasa ya saka miki Number busy yanda kokin kirashi bazaki samuba. Duk wahalar da mukasha wajen amso ku?in nan muka wanke ?afafunmu tundaga legas mukai masa rakkiya amma yay nufin cin amarmu, muko bazamu iya ?aukaba, sati hu?u kenan muka caccake cikinsa da wu?a muka aikashi gidan kowane shege da shegiya (lahira kenan), yanzu kema na ?auki wayarkine danki daina wahalar nemansa ma, kisamu gobe kisa ai masa addu'ar uku data bakwai data arba'in, wainar da za'a bamu kirabama almajirai, muna miki gaisuwar ta'aziyyarsa fa, kuma karki damu sai da mukai masa salla kafin mu jefashi ruwa......"
?itt ya yanke wayar.
Ihu kawai hajia hindu ta dage ta fasa, ta kware baki tana rusar kuka da kiran "Wayyo ku?ina, shikenan na mutu, Harisu ka talautani..."
Wanan ihune yay sanadin tashin su Umma a barci, sukazo suka rufu akan hajia hindu ana tambayar miya faru?.
Batareda tasan mi takeba tashiga sakin surutai akan yanda ta ?ulla makirci da haris aka amshe ku?in Jiddah, harma da dukan da Abba yaci wanda gashinan ya zame masa sanadin doguwar jiyya.
Wannan lamari yayi masifar girgiza su Umma da Abba dake cikin ?aki kwance yana saurarensu, jiyay hawaye kawai suna gangaro masa, matar daya fifita fiye da kowace ta aiko masa ?arayi? Wadda yay burin guduwa da ita suci ku?in tare, dama abinda ta ?ulla masa kenan shiyyasa ta lalla?ashi subari sai da safe su wuce, tini wutar kan Abba ta ?auke gaba ?aya, yaji komai yamasa ?if, bayajin sautin komai, baya ganin komai sai duhu, daga haka bai sake sanin inda kansa yakeba kuma.
************
Washe gari Uncle yahya yasa aka kama hindu, dai bata cancanci cigaba da zama batareda ta fuskanci hukunciba.
Abinda yabata matu?ar tsoro da mamaki shine ko damuwa su kalifa basuyiba, sai Munner ne kawai ke kuka da ri?eta.
Abba kam saida aka kaishi asibiti, dan jininsa yayi ?ololuwar hawa sama.
???????????
Alhamdulillah ALLAH ya sauki Maimuna lafiya gabannin asubahi, sai dai tasha matu?ar wahala abin tausayi, ta haifi babynta Namiji mai kama da Sheikh Aliy masha ALLAH, bayan sun shiga sun dubata tana barci suka fito suka barta.
Rige-rigen ?aukar jariri akai tsakanin Aliyu da Jiddah, ALLAH yabama Jiddah damar kar?a, shiko ya ha?a da Jiddah n da jaririn duk ya rungume, Jiddah ta ?ago tana kallonsa fuskarta ?auke da murmushi ta furta,
??????? ????? ???? ??? ???????????? ????? ?????????? ??????????? ???????? ?????????? ?????????? ???????.
*_Barakal lahu laka fil mawhubi laka, wa shakartal wahiba, wa balagha ashuddahu, wa ruzikta birrahu_*.
_ALLAH Ya yi albarka ga abin da aka azurta ka da shi, kuma Ya sa ka godewa wanda ya baka (shi), kuma Ya sa shi ya rayu har zuwa ga matukar karfinsa, kuma a azurta ka da biyayyarsa._
Aliyu yakuma rungumeta yana amsawa da "Ameen ya rabbi Noorunnisa, nagode sosai, ALLAH ya kawomin kema ta tsatsonki".
Murmushi kawai tayi tana sumbar goshin yaron, yanda takejin ?aunar mahaifinsa haka shima takejin tasa ?aunar.
¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï
Tunda gari yay haske bayan Aliyu yadawo sallar Asubahi yafara sanarma Malam, daganan sai Aunty Ru?ayya da Aunty Siyama da gidansu Maimuna.
Kafin kacemi labari ya gama zagaye dangi, zuwa tashin hantsi duk masu kusanci dasu sun iso asibitin, lokacin kuma Maimuna ta farka daga barcin datai na hutawa.
Zuwa ?arfe sha biyu aka sallamesu suka koma gida tareda babynsu abin sha'awa, fuskar Aliyu kawai zaka kalla ka tabbatar yana tareda tsantsar farin ciki. Addu'oi dai yaro ya shashi tuni har yamasa hu?uba da suna Muhammad. Maimuna kam yanda yaketa nuna mata tattali har kunya abun yake bata, duk mintuna ka?an ya kirata yace ya jikinta da babynsa.
Dukda Jiyyar Abba haka Umma ta fisge tazo tayi barka ita da maman sadiq, hakama su Aunty Nafisa tazo tayi, haka su aunty Hannatu duk sai da suka kira a waya sukaima Maimuna barka da shi kansa Aliyun.
*_Bayan sati ?aya_*
Ranar da yaro ya cika sati da haihuwa aka ra?a suna a masallaci, da yamma akayi walima.
Su Jiddah ansha hidima, dan kuwa tayi lis da gajiya, tunda akayi haihuwarnan bata samun kanta, koda yaushe cikin hidima take, danma su Aunty Siyama na taimakonta da wasu ayyukan, da dare kuma Sheikh Aliy yay mata tausa har tayi barci yana jera mata sannu da saka albarka.
Washe garin sunan Maimuna ta koma gidan malam wankan jego badan Aliyu yasoba, ko Jiddah saida ta shiga damuwa, harda ?ar kwallanta kuwa.
???????????
Bayan sati ?aya da sunan yaron Maimuna aka shiga kotu da hajia hindu wanda tagama jigata da fita hayyacinta wajen kwalawa .
Zan iya cewa wanan zaman kotu yazama silar tone-tone ne masu tada hankula, dankuwa hajia hindu bata ?oye komaiba gameda yanda suka ?ulla kar?e ?u?in itada ?aninta, sai dai tace ita batace su dokeshiba.......
Kafin ta rufe baki wata murya a cikin kotun tace, "?aryane, tunda kika iya shirya kasheni shima zaki iya sawa a kasheshi".
Gaba ?aya jama'ar kotun juyowa sukayi domin son ganin mai maganar.
Zaune yake cikin ?ananun kaya, fuskarsa lullu?e da hular rigar sanyi ?atuwa dake a jikinsa. Babu mai ganin fuskarsa....
Al?ali ya yanke shirun da fa?in kowaye mai maganar ya fito.
Tunda ya taso kowa ya zuba masa ido, kansa a ?asa babu mai ganin fuskarsa har yanzu, idanun hajia hindu kai kace fa?owa zasuyi ?asa wajen son ganin wanene shi?in?, sai zufa ke keto mata a kowanne sashe na jikinta.
Bayan an nuna masa ya tsaya a akwatin kotun Al?ali yace ya bu?e fuskarsa.
Wani murmushi yasaki kafin ya janye hular kansa fuskarsa ta dattijantaka alamun yanada shekaru ta bayyana. ?ara hajia hindu ta ?walla tareda zubewa a sume, da sauri jami'ar tsaro taje ta yayyafa mata ruwa ta farfa?o.
Hajia hindu sai sambatu take tana fa?in "Wlhy karku aminta dashi fatalwane, na rantse da ALLAH ba mutum bane fatalwane.
Banda murmushi babu abinda mutumin keyi, yayinda dukkan jama'ar kotun suka zuba musu ido sunason jin mike faruwa?.
Tsawatarma hajia hindu Al?ali yayi, dan haka ta nutsu tana ma?yar?yatar tsoro.
Al?ali ya gyara zamansa yana fa?in, "bawan ALLAH kai ?in wanene?".
"Da farko dai ya mai shari'a sunan SHAZALI, ni ?an asalin garinan ne, anan natashi nai wayo har zuwa samartakata, bayanan ne nabar garin kano dalilin rabani da akai da ita Hindu aka aurar da ita ga wanina, takaicin hakanne ya sakani barin kano, amma sai sonta ya hanani sukuni a inda nake, hakanne yasani yin waiwaye adon tafiya, na dadawo kano rama abinda mahaifinta yaymin, dan iyayenta sunce bazan aureta bane saboda tantirine ni, gashi babu wanda yasan sana'ata, babanta ya ha?ata aure da ?an abokinsa badan tana sonshiba. Da wanan damar nayi amfani wajen jawo ra'ayin hindu muka cigaba da soyayarmu a ?oye da auren nata, harma takaimu ga fara aikata zina. wataran mijinta yazo ya iskemu awanan halin, shine ya saketa, tareda ?wace abinda suka haifa, amma sam ya?i sanarma iyayenta abinda yasa ya saketa, saidai yace kawai zamanne ya ?are. Wanan shine cikar burina daman, Hindu tacigaba da zaman zawarci a gidansu, yayinda nikuma na maidata tamkar wata matata, ana cikin haka wata hanyar samu tazo mini, banyi ba?in cikin jawo hindu jikinaba na biya mata makka. Tayi mamakin a ina na samu ku?in, dan nidai tasan ko sana'a banida ita sai kame-kame. Amma koda ta tambayeni saina ?ata rai akan ta rainani, ha?uri ta bani taje ta sanarma iyayeta, Koda wanan magana taje kunnensu sai suka ?aryata, musamman babanta, amma mamanta sai ta nuna murnarta har tana jifan baban hindu da kalmar yanama ?iyarta ba?in cikin cigabanta. Wannan magana ta ?ata ransa yace ya zare hannunsa daga kan hindu da harisu ?aninta dayazama ?an iskan gaske. Bata wani damuba muka tafi saudia aikin hajji, saida mukaje can nake sanarmata ma'anar zuwanmu saudia, dan satar ku?in jama'a ?an aikin hajji zamu rin?ayi, da farko ta?i, amma dana kalamayeta da da?in baki saita amince muka fara, kafin kacemi mun tara ku?i masu yawa, duk abinda muka samu wani abokina mazaunin saudia yake amsa yana tura mana ta banki. Dalilin ha?uwarmu da Alhaji Zakari kuwa ?akinmu ?aya ni da shi, wataran sai naji Alhaji zakari yana waya da labarin miliyan hamsin dayaci a banki zai fa?a?a kasuwancinsa, tunda naji wanan batu sai hankalina ya tashi, dan haka nasami hindu da batun na yarda su ?ulla soyayya da Alhaji Zakari dan muci ku?in, da farko ta?i amincewa saboda tana sona sosai, saida nagama lalla?ata da da?in baki akan ai muna tare bamu rabuba, kuma zamu cigaba da Mu'amularmu sanan ta amince. tashiga jikin Alhaji Zakari har suka ?ulla soyaya tun'a can, muna kuma dawowa aka ?aura musu aure dashi, shirinmu shine bayan kamar wata ?aya mu mallake ku?in tasa ya saketa. Sai dai tun bayan aureta da Alhaji Zakari muna tare muna cigaba da mu'amularmu, cikin farko data samu nasan nawane tabbas, dankuwa inada hujjata, abin da?i kuma saita haifi namiji kamar yanda Alhaji Zakari yake buri, wanan ne yakuma sakata ?in yarda tarabu da Alhaji Zakari, nayi-nayi amma ta?i, sai dai tace mudai cigaba da tarayya, bazanyi takaici kojin kunyar fa?ama duniya abinda basu saniba, abinda yasa zan fa?a kuwa danya zama izina ga ?an baya masu a?ida irinta Alhaji Zakari yaro, dukda ?yautar da ALLAH yay masa saiya bijire masa, ya manta ALLAH shike bada haihuwa ga wanda yaso, yakuma hana wanda yaso, sanan shike bayarwa daga jinsin dayaso, mutane da yawa zasuyi mamaki idan nace su Kalifa ba ?a?an Alhaji Zakari yaro baneba, indan kacire autansu dabansan sunansaba........"
Tuni kotu ta rikice da ?ananun magana, Abba kam yama daskare acikin WheelChair ?in dayake ciki, hakama Uncle yahya dasu Umma da Jiddah.
Al?ali ya buga gudumarsa alamar ayi shiru.
Tsit kotun tayi aka maida hankali ga Shazali daya cigaba da fa?in,
"Tabbas ?a?ansa duk nawane, zama a iya gwada jinsu daduk dalilan da zasu tabbatar da hakan, bayan ta haifi ?an biyu ne na matsa mata akan a kashe alhaji zakari mu kwashe ku?in, amma sam sai tace bata yardaba, wai ba yanzuba, tabi ta tsarani da zance na yarda da ita. Sai dai danayi bincike saina gane wayo tamin, ni tama saka a kasheni saboda taci ku?in ita ka?ai. Ban nuna mata na saniba har tayi ?ulla-?ullarta a motata da nayi shirin yin tafiya a lokacin, daga baya muka canja komai na biya wa?anda tasaka