Showing 21001 words to 24000 words out of 177131 words
wuce dakin shi, abin shi yana jin kamar zuciyar shi zata buga, zama yayi tare da fashewa da kuka. Ganin kukan ba zai kare shi da kome ba ya nufi dakin shi.. rufe kofar yayi tare da nufar ban daki.
Bayan ya fito ne, ya kwanta a kasa, yana jin kewar gida da iyayenshi.
Haka har gari ya waye, ya kuma fita ko karyawa bai yi ba, yayi tafiyar shi bai dawo ba sai can la'asar sakaliya, yana shiga ya samu Baba Mari ta fito gidan, cikin kulawa ta kalle shi.
"Angona Barka da yamma" kunya ce ta kama shi yace mata.
"Kiyi hakuri Baba ina wuni? Ya aiki da zafi"
"Alhamdulillahi! Ka dawo makarantar ne?"
"Eh wallahi" ya faɗa tare da gotawa ta gefenta, wani irin jan iska tayi da hancin ta, sannan ta bi bayan shi da ido. Haka kawai take jin wani irin abu a ranta dangane da yaron, sai kuma ta share tare da nufar inda gidanta yake, har ta zauna tana tunanin yaron.
Haka suka ci-gaba da zama duk da babu wani kyakyawan mu'amalar da zata nuna maka ana shiri kamar baya tsakanin Ansar da Mamoon, haka bai hana shi ajiye mishi duk abinda yake bukata ba kusan har aka gama zangon karatun suka yi jarabawar da hutu, babu wata kyakyawan fahimta.
A daren yau hada kayan shi yayi tare da tattara duk wani abu, haka kawai yake jin faduwar gaba, dan haka koda ya gama ji yaƙe kamar yayi ta kuka, dan bai san meke faruwa dashi ba.
Haka ya gama had'a kayan shi, sai gashi an dan kira su sakamakon wasu dalilai ba zasu tafi hutu ba, sai watan gaba. Dan dole ya hakura amma a ranshi kewar gida yake, idan ya tafi makarantar dakyar yake fahimtar abinda ake duk da sati biyu ya rage ayi musu hutun, haka dai suka yi ta maida hankali da abinda ya rike su a makaranta.
Yawan mafarkai da tashin hankali na faduwar gaba yasa shi kasa sukuni, abin da ya haifar mishi da zazzaɓin da ya kwantar dashi, Almamoon yana da makon iyaye, ya saka iyayen shi a ranshi. Har gida aka saka mishi ruwa dan yaki zuwa asibitin.
"Likita ka duba shi da kyau, yana yawan kukan ciwon ciki?" Zaro idanu yayi yana kallon likitan.
"Toh dan bamu guri"
Haka ya fita ya basu guri sun jima suna tattaunawa, kafin likitan ya saka mishi ruwa da allurai. Bayan tafiyar likitan Malam Ansar ya shigo ya mika mishi magani.
"Sannun Insha Allah zan tambaya maka damar tafiya gida ko" gyada kai yayi sannan yace mishi.
"Nagode"
Ya fada a hankali, yau kan yadda yake kwance ba lafiya muryan tafi kowa yaushe kamancecceniya da ta mata.
"Yau kam kamar mace ka fito kayi laushi! And anya kai ba mata m.."
Wani kallon banza ya watsa mishi.
"A'a mazan mata ne ba mata maza, ba dalla fita ka bani guri" ya faɗa yana b'ata rai, dan dole ya fita daga d'akin.
---- Washi gari bayan likitan yazo ya cire mishi ruwan tare da kara mishi allurai, sannan ya tafi. Can da yamma Ya fito diban ruwa a kicin suka yi kicibis da Baba itama ta gama abincin zata leka shi ta koma gidanta.
"Ya jikinka Mamoon?"
"Da sauki Baba mari" ya faɗa a sanyayye, sake zuba mishi ido tayi zuciyarta tana wani irin bugawa kamar zata tsage, ta rasa me zata iya fahimta. Shiga kitchen ɗin tayi tana mishi wani irin kallo.
"Waye kai?" Ta tambaye shi,
"Ban gane ba, Baba Ni ne Almamoon fa"
"Ba sunan nakeson ji ba, kai mace ce ko Namiji?"
Gabansa ya fad'i, ya kalli kofar shiga abinka da kuruciya, sai ya rud'e tare da jin kamar an watsa mishi ruwan sanyi.
"Baba don Allah"
"Bani zaka roka ba bayanka zaka Duba, kai mata maza ne?" Kuka ne ya kwace mishi yana girgiza kai.
"Toh amma ai jini ne a bayan wandon ka" ta faɗa mishi. Da gudu ya juya zai fita suka yi kicibis da Malam Ansar, durkushewa yayi cikin matsanancin kunya da kuka.
"Don Allah karku gayawa kowa, ban san na b'ata jikina bane" ya faɗa yana kuka, mutuwar tsaye malam Ansar yayi tare da sake kayan da yake hannun shi yana kallon shi. Cike da mamaki da mugun al'ajabi.
"Toh meye haka yake nufi? Shin kai mace ce ko namiji, ko mata maza ne?"
"A'a ni m.." ya kasa fitar da koda kalama daya ce, sai kuka da yake,.yana ganin kamar yaci amanar iyayen shi.
"Tashi muje asibiti ya faɗa a haukace" inji malam Ansar,
Cikin wani irin kuka me matuƙar ban tausayi, yace.
"Nace bana so! Abinda kuke son sani shine ni." Ya kasa furta kome sakamakon tuno yadda Iyayen shi suka yi ta rokon shi, ta shi yayi ya shiga daki tare da rufe kofar, ya jingina da kofar yana wani irin kuka.
Da sauri ya shiga ban daki ta cire kayan shi, ya wanke wandon ya durkusa ya ci kuka kamar idanun shi zasu fita, "me yasa aka halicce ni haka? Me yasa na kasance haka? Me yasa ba a damu da nawa nau'in ba? Haka zan gama rayuwata? Ko haka ne zai saka na."
Kuka ya sake me mugun karfi tare da zama ya kusa kanshi a tsakanin cinyoyin shi, kunzugun shi ya dauka ya gyara tare da ɗaukar wata gajeren wando ya saka tare da boye kanshi, ya ki fita ma a ban dakin balle ya koma dakin shi.
.... Kallon juna suka yi daga Baba Mari zuwa Malam Ansar.
"Toh amma ina ganin kamar jinsi biyu ne dashi,. Kuma baya son ta faɗa"
Kamar ruwa ya cinye malam Ansar ya kalli Baba Mari, kafin tace mata.
"Baba bana tunanin haka sai dai ina ganin kamar mace ce" ya faɗa a sanyayye, sama da koda yaushe, haka wunin ranar suka yi shi.
Jacader
Tun daga titin da zai kai ka cikin Unguwar zaka Fahimci unguwa ce ta masu hannun da shuni, wato attajirai masu kuɗi, yan siyasa da yan kasuwa, manyan mutane na cikin garin Maradi.
Hukumar yan sanda ne zaka fara cin karo dasu, wanda sun kai kimanin dubu daya, a barbaje cikin unifoam, idan kayi tafiya gaba zaka taradda hukumar jami'an tsaron ko takwana wanda suke sanye da wasu kayan yaki, su kimanin dubu daya.
Gaban su kadan idan ka wuce shigen wato (checkpoint) hukumar kunce bom ne koda za a ratsa tsakanin su a kawo harin bazata, suma kimanin dari biyar da kayan aikin su. Sai gaba hukumar fasakorin shige da fice wato (custom,) suma a nasu checkpoint, su kimanin dari bakwai, idan ka wuce su nan zaka samu get da zai kai ka first get, inda aka saka hukumar immigration, wanda sun kai dari uku a gurin, idan ka wuce get din zaka nufi get me dauke da Ash color wanda aka saka katin Stamp na Niger republic Army. Sojojin ne birji daga sojojin ƙasa, zuwa sojojin sama. Sai daura drum suke ana binciken sirri.
A gaban kadan wasu manyan mutane ne zaune duk wanda zai shiga cikin gidan bayan ya tsallake wadancan checkpoint, sai ya isa gurin su, anan za a saka abu a duba ka har cikin jikinka sai an duba ka,
Idan mata ne akwai jami'an tsaron mata, suke kome na bangaren mata, wani katon legendary house wanda za a iya kiran shi da Mansion, a tsakiyar katon fili, anyi ginin gidan kamar yadda akayi gina shi kamar bujr arab, wato wani hikima irinta fasihai kwararrun maganin duniya aka tara suka gina gidan, idan daga nesa ka hango zaka dauka kamar daukar gidan aka yi aka daura a saman koramar ruwa.
Domin kuwa cikin tsari da baiwa irinta ma'abota hankali suka gina gidan a saman ruwa, kamar an dauki gidan ne aka daura a saman ruwa. Daga nisa kana hango cikin ruwan. Gidan da aka gina kamar gidan sama me hawa biyu, amma kuma Normal mansion ce, sannan anyi tubalin gina zaman a jikin gidan yadda kana kallon shi zaka Fahimci wannan ginin ya kai makura a haduwa, haka roof din gidan yadda kasan kwalba aka saka a saman gidan, gidan kewaye yake da manyan dogayen bishiyar dabino, ta gefen gidan kuwa wani kyakyawan lambu ce me dauke da manyan Swam wato agwagwan ruwa na kasar Austaraliya, lambun dankare yake da kayan ciye ciye, sannan akwai wasu kyawawan dawisu, fararre, daga can ƙasar China aka zo dasu.
Ta gaban gidan kuwa parking lot ne, me dauke da manyan motoci guda biyar, BMW, Phantom, Mercedes Benz, sai Range, da Toyota Tacoma. Sai watan katuwar bike na kamfanin Nissan wacce aka mata ƙatuwar Stamp na sojojin. Gefe can hilux ce 40×40, army color. A jikin kusan da motar wani katon daki ne me dauke da Police Dog, lion dog, wadannan karanunakan ba a cika samun su a ko ina ba sai a China da Japan.
Domin kowani guda daya ya kai girma giant Ram, wato katon rago irin me murdaddiyan kaho. Ko ina ma gidan dauke yake da Cctv. Duk inda ka gifta kuwa.
Can bayan gidan sosai, akwai BQ, inda gabaki daya ma'aikatan gidan suke.
Cikin gidan me dauke da dakuna biyar uku a sama biyu a kasa.
Dakuna ukun saman dakin mamallakin gidan ne, biyu dakin kwana ne, daya kuma dakin al'amuran shi ne, gefen dakin wani study room ne, sai backyard me dauke da yar karamar gurin hutawa me kyau. An Kawata shi da wasu irin kujeru na musamman guda uku, duk yadda aka yi an tsara gidan ne daga mace daya da yaran su, sai abinda ba za a rasa ba.
Daga step din da zai kai ka kasa an shimfid'a India capter. Red and Golden,. Sannan paint na gidan dauke yake da grey color sai minti colour. Dakin farko na sama, wanda aka zuba wasu mahaukatan furnitures daga Korea aka yi oda dinsu, kome na dakin Royal blue ne, sai furnictures din da paint dakin ya kasance cream colour. Daya dakin kuma dauke yake da simple design furnitures, whiter and Black, haka ma labulayen dakin. Fari ne me digon baki.
Sai tiles da aka saka a kasan dakin yayi mugun yiwa dakin kyau. Haka ma wancan dakin shima tiles din shi me kyau ne.
... Dakin kasa kuwa daya dakin dauke yake da kome cream And Golden, yayi masifar kyau haka ma Furnictures din shi. Daya dakin kuwa dauke yake da blue and pink paint, kome na dakin Blue And pink ne, idan ka nutsu zaka ga har kayan wasa an ware.
....
Falon me dauke da ƙatuwar cimma tv, baya kome a kashe yake. Sai falon da yake kawace da manyan sofa, har guda ashirin da hudu,, sabida girman falon.
Kuma ba wai a guri daya ba, a'a kowani kusurwa a jiye yake da sofar shi. Wato kujeru. A can gaba da fakon wata luxury kitchen ne, wanda idan da zaka kira shi da modern kowani suna duk daya ne. Ma'aikata kusan shida ne. Kitchen ɗin suna aikin girki kawai, idan kaga yadda suke aiki zaka Fahimci sun gama gajiya da aikin kawai dan albashin su, sukewa wannan hidimar.
A falon akwai wani hoton family, me dauke da hoton Wani kyakyawan Matashin Soja, dan kimanin shekaru arba'in a duniya, murmushi yake ana saka makon lambar karin matsayi. Kasar hoton an saka Firaministan Mamman Nasir Aghali. Da Major General Mohan Mamman Nasir Aghali. Jarumin sojan kasar Nijar.
Fari kyakyawa ajin farko, dogo murdaddiyan jiki, ma'abocin manyan idanunawa da zunzurutun kwarjini.
A watan Fabrairu waki'a ta faɗa mishi mara dadin ji, ana gab da fara bikin shi wanda ya rage sati Daya a fara, babban da ga Firaministan kasar Nijar, kuma shine kashin bayan mulkin mahaifin shi, sai dai kuma abin tausayin da ya faɗa mishi a filin yaki.
Mamman Nasir Aghali. Shine firaministan Nijar, kuma shugaba me adalci, da son talakawan shi, mutumin da bai dauki duniya da zafi ba. Dan kimanin shekara saba'in da tara, duk da ya girma amma shugaba na gari ne, kuma adalin shugaba.
Da ake matukar kaunar shi a kasar Nijar baki daya, kuma shugaban kungiyar kasashen Afrika baki daya,yana da mata biyu. Yara goma maza uku mata bakwai.
Hajiya Latifah itace matar shi na saurayi da budurwa, kuma buzuwar Agadaz ce wacce al'ummar kasar ke mata lakabi da farar mace alkyabar mata. Duk inda kake niman Jarumar mace idan kayi katarin haduwa da ita ka samu. mahaifinta shahararren dan kasuwa ne mazaunin garin Tripoli na kasar Libya.
Kasancewar ta taso daga wata kasar ta sami ilimin boko sosai me zurfi, haka ta sami na Addinin fiyye da yadda kake tuna, sai dai mace ce da take da d'agawa da son mulki, mace ce da take son Nasaba da kusancin mai kyau, shi yasa bata mu'amala da kananun masu hannu da shuni kuma uwa uba tana da nasaba da Gidaj Sarautan Agadaz tana da yara shida.
Mohan kuma babban Sojar ƙasar shine babban ɗan ta, shi yasa taci alwashin dan ta macen da zata aure shi sai ta haɗa Kyakyawan tarihi da nasaba. Sai Hadder shine yake bin Mohan, yana kasar Faransa yana koyarwa, sai Salman yana kasar Nigeriya, yana aiki a ofishin jakadancin Nijar a Nijeriya,sai Khausar Likitan mata ne na babban Asibitin Nijar da yake Niamey, sai Radiyah, tana karatun ta a jami'a, sai Karamar su Nairah tana matakin sakandiri.
Amaryan Mamman Nasir Aghali Safiya. Tana da yara huɗu duk mata, Mansura, Mahnoor, Hinduh, sai yar karamar su, Tawakaltu.
A zahiran ce zaman lafiya a gidan sai a slow, domin Hajiya Latifah mulki take da Kowa hatta shi kanshi Firaminista sai yadda tayi dashi, sam Safiya bata gabanshi, idan ka ganshi a dakin Safiya ko tazo dakin shi dauki haka a matsayin babban al'amari ne na rabo ya dauko ta, haka yayi mugun fusatatta, domin itama yar babban gida ce, amma aka maida ta kamar baiwa. Dan haka bata tab'a wani yunkurin dan kwatar kanta ba, amma kuma a hankali ta lalata gidan, a zahiran ce sai da ta watsar da Yaran Hajiya Latifah, ta hana su shiga jikin Uwar su, ta kama su duk.ta rike su, kuma bawai dan Allah bane no cutar dasu take na fitan hankali.
Mutum daya ne yafi karfin ta, Mohan Mamman Nasir Aghali, mutum ne mai matukar ilimin addini da na siyasa, duk yadda ka zo Mishi yasan take taken ka. Takai Mohan ba iya ita ba hatta mutanen da suke jikin Mahaifin shi shakkar shi suke, domin ya zamewa Mahaifin shi garkuwa, duk wanda yayi yunkurin cutar da Mahaifin shi tabbas sai dai kayi a wani gurin amma da'iran da yake karyan ka.
Sabida dalilin haka, aka tsane shi babu irin sukan da ba akayi wa mahaifin shi ba, amma zai kira shi yayi ta Mishi fada, daga baya idan suka keb'e yakance Mishi.
"Babana Ka kara himma akan na da, mutanen da suke kewaye dani basu san Allah ba, babu Allah a zuciyar su."
"Insha Allah Abbih zan yi iya kokari na, na baku kariyan da ta dace." Tun lokacin ma bai samu matsayin Firaministan ba ma ake gwagwarmaya da munafukai, lokacin da ya samu Mohan ya kai matakin babba A soja, sai aka yi ta gayawa Uban ai zai Mishi juyin mulki. Ko dar uban bai tab'a ji ba akan Dan shi dan yasan abinda ya haifa.
Duk cikin yara shida na Hajiya Latifah Mohan ne kawai bai juya mata baya ba, domin Hajiya Safiya tayi amfani da abinda Hajiya Latifah take na mulki ta nunawa Yaran ta ai ita babu alamar akwai adalci, a tsakanin su. Kawai tana zaune ne dan su, sabida basu samu kulawar Hajiya Latifah ba. Abinka da dan kulawar da ake badan Allah ba, sai gashi yaran sun juyawa mahaifiyar su baya, tare da nuna mata bata adalcin a cikin rayuwar gidan, bata da lokacin yaranta balle mijinta, abubuwa dai dayawa yaran suka lissafa mata, koda suka gama magana ce musu tayi.
"Kuna da damar da zaku yi kome sabida ku ba zan fasa abinda nayi niyya ba."
Hajiya Latifah bata da lokacin da zata cutar da kai,.ita dai kawai kimarta da mulkin ta take mugun so, daga haka yaran suka juya mata baya. Har rana me kaman tayau.
Al'amarin Mohan Mamman Nasir Aghali, kuwa ranar da aka bashi matsayin Major a ranar wata muguwar ƙaddara ta faɗa mishi na cutar.....
_Hi ya kuke? Kwana biyu zaku yi hakuri gaskiya ina fama da ciwon baya da hannuna. Dan haka gaskiya ba zan iya update daily ba amma Insha Allah idan nayi Posting yau sai laraba kenan, zamuna hutun kwana ɗaya da fatan zaku Fahimce ni...._[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
BOOK ONE
https://www.instagram.com/batool_spices
Fatima Batool enterprise
Yaji
Ginger and garlic
Onion powder
Pepper soup
Curry
Biryani spices
Mixed spices
Indian spices
Arab spices
Chai masala
Baharat blend
Tandoori blend
Thai masala
Garam masala
Provence
Tea spice
Zobo powder
Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Baool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
Wani Al'amari...
BABI NA TARA.
Muhammad Mamman Muhammad Nasir Aghali. Shine asalin cikakken sunan shi, kasancewar sunan shi sunan babans shi da Kakan shi na Uba, yasa aka mishi lakani da Mohan.
Duk inda kake niman mutum me tsaye akan ra'ayin shi Mohan ya kai gurin, yana da dadin mu'amala. Ga son mutane da yawan Alkhairi, sai dai mutum ne da bai da fara'a sosai , wani hali da mohan yake dashi wanda ba kowa yake iya zama dashi ba wato murɗaɗɗan hali, duk wanda zai zauna da shi sai tayi mugun hakuri dashi, kafin wannan lamari babu me iya gane abinda yake so sai Abokin shi daya tal a duniya wato.
Captain Khalil Ibrahim Dan Ba'are, kaf duniya bai da Amini sama da dan Ba'are, bai da abokin arziki irin Dan Ba'are shi yasan Meye Mohan yake so, shi yasan Meye baya so, gashi Allah yayi mishi farin jinin Yan mata, shi kuma baya da lokacin su.
Sau dayawa Yan mata har kawo kansu suke gurin shi,