Showing 51001 words to 54000 words out of 177131 words

Chapter 18 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

14794

daukewar gani na, na tafi zan fadi yayi maza ya taro ni, daukata yayi tare da nufar cikin gidan dani, da sauri.
Yana isa dakin kasa ya kwantar dani. Yana kallon yadda gefen fuskana ya sha mari, shafawa yayi. Yana kallon yadda nake kwance. Tashi yayi ya ma rasa me zai min, kawai ya fita can sai gashi da ruwan sanyi ya samu fuskana ya juye min baki daya, a firgice na farka tare da dafe goshina, kai na yana mugun sarawa.
Zama yayi tare da riko hannuna yana kallon yadda nake ajiyar zuciya.
Tashi nayi tare da nufar ban daki na, hada ruwan wanka, sannan na cire kayana na fara, tunawa nayi ban dauko wani abu ba, na fito daure da towel a kirjina. Da sauri na nufi inda dama kayana yake na dauki yar abin da zan dauka na na koma ban d'akin.
"Karka je ko ina ganin nan fitowa"
Na gaya mishi ina turo kofar, na cigaba da abinda nake, lokacin da na fito kusa gashina me bala'in yawa ban daure shi ba, na fito haka zube a kirjina, zama nayi ina tattara su,sannan na daure su baki daya, na kuma gyara shi yadda ba zaka tab'a dauka ina da sumar a kaina ba.

Kallon inda nake bai yi ba, alola na koma nayi sannan na zo na sashi yayi.
A tare muka yi sallah, muna idarwa na fito falo da niyyar niman abin da zamu ci na rana, sai ga Malam Ansar ya shigo gidan, daidai ba fito ina gyara wandona, kallona yake cike da tashin hankali lokacin da Hammah Mohan ya fito zip din gaban wandon shi a bude. Rigar shi botir din a balle. Cikin fusata ya nufe ni tare da zare belt din wandon shi. Wani irin mugun tsoro ne ya shige ni dan ba a tab'a duka na ba, kawai ya dage ya tsulla min belt din shi a gadon bayana sai da na daka tsalle, lokaci guda ya haukata Ni da duka.
Rarrafawa nayi ina ihu tare da cewa.
"Don Allah Hammah Mohan ka taimake ni" na nufi ne shi tare da k'amk'ame kafar shi. Jikin yana rawa, tare da kerma ilahirin jikina b'ari yake kamar za a zare ruhina, sabida yau ne karon farko da aka zane ni ban san dukkan ba.

Jin bulalar bata kuma dauka a jikina ba ya sani kara k'amk'ame shi ina kuka me shiga jiki. A hankali ya janye kafar shi daga rikon da nayi mishi, ya murɗe malam Ansar da bulalar a wuyar shi kamar zai kar shi, idanun shi sun yi wasu irin jajjur, jijjiyar goshinsa sun mike rad'a rad'a, jikin shi wani irin rawa yake kamar an saka mishi mazari.
Kakarin malam Ansar ya sani, d'ago kai na, ganin yadda Hammah Mohan ya shake shi, da sauri na mike.
"Sake shi ya hakuri bar shi na yafe mishi." Na fada ina kuka.
Sake shi yayi ya fadi, sannan Hammah Mohan ya dawo bayana ya rungume ni yana kallon Malam Ansar. Tare da mishi gargadi da idanun shi da suke cike da b'acin rai.
"Wato dan na hukunta ka shine zaka saka ya kashe ni?"
Bude baki nayi zan yi magana ya juyar dani muka koma cikin dakin. Zama nayi a bakin gadon ina kuka kamar me, ban san ya aka yi ba sai mika min hannu yayi tare da jana zuwa ban daki ya nuna min ruwa, gyada kai nayi. Na fara ƙoƙarin cire kayana ya fita daga ban ɗakin.
Ashe fita yayi bayan ya cire key din dakin ya rufe Ni ta baya, ya samu malam Ansar bai bar gidan ba, damke wuyar shi yayi tare da jan shi kamar kayan wanki ya watsa shi a waje, sannan ta nufi yake ya shiga kwallo shi, baki daya Sojojin ganin abinda Mahaukacin mai gidan su yake yasa kowa ya shiga hankalin.
"Yallabai karka kashe shi." Inji Malik yana rungumo Mohan. Ture su yayi domin ranshi yau yakai kololowar baci, haka ya wulakanta Ansar kamar yadda ya zane Almamoon. Sannan ya nufi cikin gidan lokacin na fito daga wanka zazzaɓi ya rufe ni, na kwanta tare da rufa bargo. Ina rawan sanyi. Fita yayi daga dakin ya nufi dakin shi, can sai gashi dauke da wasu abubuwan yana zuwa ya damu ina kwara amai zazzaɓi yayi mugun rike ni, kai hannu yayi zai ja bargon na rike ina girgiza mishi kaina, kyale Ni yayi tare da ajiye min maganin, har zai tashi na rike hannun shi.
Tare da juya mishi baya ya sha fa min. Musamman yadda bulalar ya fasa min jikina, yadda ya lakato maganin yana shafa min sai da naji hannun shi har cikin jini na yake yawo, tun daga tsoka har ɓargona ina jin hannun Hammah Mohan, yana gama shafa min ya mike tare da barin d'akin mik'ewa nayi na na cire towel din. Ina shafa maganin daga Ni dai pant, ina bin ko ina inda Bulalar ya fasa ina shafawa, sai a lokacin wani tunani ya zo min taya Hammah Mohan ya fahimci ina bukatar man zafi... Na d'ago kai zan yi nazari shi kuma ya bude kofar sai shigo baki daya na fasa wata irin ihu domin dai tsirara nake........😁🤣😜 Ayi sallah lafiya wallahi ko bashi naci sai haka kai Jama'a.... Babu ranar da ba zan ga Sakon Auta ba🙄🙄🙄 ga Yan Bororoji fans ga Mama Mai Voice! Ga Kawar Mommy na, ga Jikar kulu, Aunty Safiya Jos, Sister Fatima Sabo, Aunty Zully, Da My Kawata Mom Abdul, Da Rano 🤣 😂 Lalalala Aunty Mamieh shekaranjiya har da fushi, A'isha Durling har da kirana tsohuwa, Aunty Khalil kan cewa tayi ta hakura dai na gama rashin daraja na ta karanta😁🤣😂🤣😂 Wallahi wannan labarin da alamu sai ya ci kaniyar Kwarkwarah... Fatan Alkhairi 👏 ayi sallah lafiya Allah ya maimaita mana ina jiran goron sallah....💞💓❤️Team One Love 😍😘❤️
Mai_Dambun ku ce har kullum.
[7/20, 9:06 AM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

*Barka da Sallah Ubangiji ya maimaita mana*

BABI NA SHA TARA.

Da mugun gudu na danne kofar, tare da sake wata irin kara, me had'e da kuka.
"Ashhhhhh! Ohhhh Auwshhhhhhh" ya faɗa tare da banging kofar, sai da na kuma faduwa, ashe na rufe da hannun shi ne, ina jin ya bar jikin kofar na koma ban dakin na dauko kayana, na saka kafin na fito da sauri. Yana zaune tare da zubawa hannun idanu, zuɓewa nayi akan gwiwa ta, na sake wani irin kuka tare da jin nadamar me yasa na matse mishi hannu, riko hannun nayi tare da sakawa a bakina ina tsotsa su, can na kuma mik'ewa zuwa kitchen na dauko kankara na saka a cikin towel na nad'e shi sannan na shiga matse mishi hannun. Duk abinda nake idanun shi kumshe bai bude ba, sai leka fuskar nake jijjiyar goshinsa sun mike sosai.

Mik'ewa nayi ina kallon shi kafin na  shiga inda first aid box yake na dauko na mishi dress din hannun sannan na koma na shiga duba hannun.
"Kayi Hakuri" sai lokacin ya bude idanun shi tarr akai na.
"Kayi hakuri kaji"
Lumshe dara daran idanun yayi, tare da gyara kwanciyar shi, haka nayi ta kula da hannun a binka da farin fata sai gashi gurin yayi jajjur bayan ya kumbura, shafa mishi man zafi zanyi yayi maza ya rike hannuna. Idanun shi har lokacin bai bude ba. Sai tauna bakin shi yake tare da lumshe idanun shi duk da a rufe suke, amma haka bai hana shi yin yadda zan Fahimci yana jin matsanancin zafi ba.

   "Kayi hakuri ka ji, nasan da zafi amma haka shine mafita domin zaka ji dadin hannun" a Sannun a hankali yake zare hannun, tare da kauda kanshi yana me jin kamar ya kurma ihu, domin shi kad'ai yasan yadda yake ji.

Shigowar Hammah Malik yaga halin da muke ciki.
"Subhanallahi taya haka ya faru"
"Eh wallahi garin garin garin" nayi ta maimaitawa sabida wani irin kallon da yayi min wanda ya sani jin saura kiris fitsari ya zubo a wandona, kai ban tab'a ganin mugun kallo irin na yau ba. Sannan ya juya ga Malik, ya zuba mishi ido. Shima kuma kamar mara gaskiya shan jinin jikin shi yayi tare da cewa.
"Sir ko zamu kai ka asibiti ne?"
"Ok bari na kawo mishi jacket din shi ya daura akan kayan zai fi kyau kam a kai shi asibitin."
  
       Da sauri na haura sama na dauko mishi rigar Black yayi mishi kyau sosai, ga gashin nan irinta buzayen asali ta wani nad'e akan shi, ba zaka tab'a kallon fuskar shi ka dauka bai da lafiya ba. Saboda kullum cike yake da kwarjini da kamala, haka muka nufi asibitin domin yaki bin Malik sai da nace mishi.
"Toh muje"
Haka ya saka kai ya biyo mu, baki daya ina walwala ne amma bani da nutsuwa domin kuwa ina tsoron malam Ansar sosai,haka aka gama duba mishi hannun shi, sannan muka dawo gida.

    Zuwa dare sabon zazzaɓi ya rufe mu dukkan mu, dakyar na shiga dakin shi tare da taimaka mishi yayi wanka, amma yana fitowa yanki jiki ya fadi, gashi tikeke, haka nayi ta jan shi.

"Ko zan kira Hammah Malik ne baka da lafiya" lumshe min idanu yayi yana kallon yadda nake son kuka nima zazzaɓi nake ji.  A hankali ya dafe jikin gadon tare da rike Ni da karfi sai da na kusan faduwa, sannan ya mike dakyar ya faɗa gadon, tare da fisgo ni jikin shi. Hakoran shi suna haduwa da juna.

               A hankali na saka kafana na janyo bargon na lullube shi, sannan na gyara kwanciyar shi, kafin na fara ƙoƙarin zamewa a jikin shi, wasu irin kananun surutai yake tare da faɗin.
"Zasu harbe ni, karka bari su same mi."

Ya fada tare da matse ni a jikin shi, yana ƙoƙarin boye fuskar shi a jikina, tsoron kar ya cutar dani ya sani fara mishi addu'o'in, can naji yana sauke ajiyar zuciyar, sai barci me mugun karfi ya tafi dashi. A hankali na gyara mishi kwanciyar shi, kafin na fara ƙoƙarin saukowa a gadon ya rike hannuna, haka na dawo na kwanta a  gaban gadon, hannun shi cikin nawa, haka nima barcin ya dauke ni.

    -.02:30am farkawa yayi yaji hannun shi da na Almamoon a sarkafe da juna, a hankali ya zare nashi tare da mik'ewa ya nufi ban daki yayi alola sannan yazo ya gabatar da sallah da yake kanshi, zama yayi yana addu'o'in wanda duk kusan rabin shi kuka yake hannun shi a sama, bayan ya idar yaji Almamoon yana nishi a hankali  a hankali. Tare da kuka yana surutu shima. mik'ewa yayi tare da nad'e abin sallah.

    Yana ajiyewa ya nufi gaban gadon, a hankali ya durkusa zai dauke shi, bakin Almamoon ya sauka akan kuncin Mohan, tare da sauke mishi wani irin nishi me tab'a jiki da jini, sabar shi yaji sama yana kallon  fuskar shi, musamman yadda ya daura kanshi a daidai kahon zuciyar shi, wannan ne first time da ya tab'a ɗaukar wani a hannun shi.  Ko mace bai tab'a rikewa ba indai ba jarirai bane.

    A hankali ya haura gadon ya kwantar dashi, yana me gyara mishi kwanciyar shi,,.bayan ya ja mishi bargon shi, ya zo zai dai fuskar shi zai gyara mishi kwanciyar shi musamman wuyar shi da ya kwanta a karkace, sai ji yayi Almamoon ya kuma damke wuyar shi.

   A hankali ya kwace rikon ya gyara mishi kwanciyar shi ya fita daga dakin yana mamakin meye ya kawo mishi wani jikin shi? Yasan ya samu lafiya amma baya son koda wani a cikin gidan ya san lafiyar shi lau. A hankali yake takawa cikin wata irin kasalalliyar yanayi, ya fita daga dakin ya nufi dakin shi, ya zauna tare da dafe goshinsa yana jinjina karfin k'iyayyar da Hajiya Safeeya take mishi meye yayi mata da zafi haka? Ba dan Almamoon din ya zubda maganin ba tabbas da wani mara imanin ne zuba mishi maganin zai yi, meye ya tsarewa mutane da suke burin su kashe shi? A iya sanin shi dai bai da matsala da kowa amma meye ya kawo haka?

  Akwai dalilin da yasa Almamoon yazo ina Khalil da Malik? Amma ko yau kwana biyu yasan Khalil ya tafi amma zaman me yake a cikin gidan nan da yayi shi domin ya kawo matar shi gidan, wato wacce zata zama mallakin shi.
  ***
Tun da asuba na tashi jikina babu dad'i, dan haka na sauka a gadon na shiga ban daki ina mamakin taya aka yi na dawo sama gadon ni da na ke kwance a kasa. Lumshe idanuna nayi bayan nayi alola zan yi sallah ya shigo. Shima ina ga alolan yayi yazo tadda ni.

      Kallon yayi na wani lokaci kafin ya juya ya fita, rufe kofar nayi na gabatar da sallar, ina idarwa na mike tare da nufar kitchen na mana abun karyawa, ina gamawa na kawo zan ajiye, na hango shi zaune ya daura dogayen kafaffun shi a saman hadaddiyar center table din falon yana kallo.
"Hammah ina kwana?" Na dai fada ne amma ban sani ba ko zai amsa,
Bai kalle ni ba ya cigaba da abinda yake, mik'ewa nayi na nufi gurin shi da abincin, ya kawar da kanshi, Cigaba nayi da tsayuwa.
"Ga abincin ka ni tafiya makaranta zanyi" na fada ina tura mishi baki..share ni yayi ya cigaba da kallon shi.
"Wai ma waye ya kunna maka tv? Bana ce kayi ta kallon Tashoshin musulunci bane, na kuma ganin ka kunna labarai sai na cire kunnen ka" na fada ina zare mishi ido. Kallon Yaron yayi daga sama har ƙasa.
*Wannan Yaron akwai karfin hali!*
Ya fada tare da mik'ewa yana me nufar hanyar table din, sake baki nayi tare da nufar shi da abincin.

   "Ina wasa da kai ne? Wato zaka mai dani karamin mutum na kawo maka abincin ka taso ka bar ni dashi" na fada da karfi ina zare mishi ido sannan na cigaba da cewa.
"Sai na gayawa Hammah Khalil dan na lura kafu shakkar shi, tunda ka rena ni"

*Kan Uba! Wato Dan Ba'are ya gaya mishi ina shakkar shi kenan dan Uban shi? Lallai zan ci kaniyar ku daga kai har dan Ba'aren*  ya faɗa tare da bin Almamoon da wani mugun kallo kasa kasa.

   "Maza dauki cokali kaci abinci." Na fada a ikonce, irin nice gaba da shi.
*Wai Ni dan abun nan yake min ihu? Abinda bai fi nayi loma daya da shi ba! Zan kama dan Ba'are sai naci Uban shi dan banza mara mutunci*
Babu musu ya dauka ya fara ci yana kallon fuskana, tari ya fara na bashi ruwa ya sha, sannan nima na dibe nawa na dawo falon ina ci, kad'an yaci sanan ina gamawa na nufi hanyar kitchen na ajiye kayan, a gurguje na gyara gidan, sannan na tawo tare da rike hannunshi muka haura sama, na bashi magani da addu'o'in da nake tofa mishi. Dakyar yasha yana niman kwara min amai.

              Ko ta kanshi ban bi ba, na dauki jakata na fita ina me shafa sumar kanshi na fita da sauri. Sabida na kusan makara.

   Lokacin da na iso makaranta, an kusan shiga aji dan haka ina isa bakin kofar shiga naga dalibai sun tsare hanyar.
"Lafiya kuka tsaya a tsatsaye kamar mama maza?" Na tambaye su ina nufar hanyar shiga aji..
"Ai har kai Almamoon malam Ansar zai nemi ya taimaka maka ka saka a mishi dukar kawo wuka?"
"Haka ya gaya muku?" Kallona suka yi tare da cewa.
"Idan na haka ba toh meye kayi mishi?"
"Tunda ku nan uwayen shi ne me zai hana ku rama mishi" ban tab'a zata zasu iya duka na ba, amma dai gashi sun rufe Ni da mugun duka.

     Dakyar aka kwace Ni na sha mugun bugu, kasa zama nayi domin abokan malam Ansar sun goyi bayan daliban, dan haka aka kore ni zuwa gida, kuka yana cina amma kuma na kasa yi,tafiya nake kamar wanda kwai ya fashe mishi a cikin shi. Ina isa bakin get na samu motar haya, ya kai ni gida, ina isa bakin get din farko aka dauke ni a wani motar zuwa cikin gidan, ina shiga gidan na hango shi yana tsaye ya zubawa dabbobin shi ido hannun shi a cikin aljuhun farin jeans din shi na kamfanin Next, sai bakar riga me kyau me dogon hannu, ya daura wata mara nauyi akan rigar cikin fari tass na saman.
     Hadaddiyar gashin kan shi ya dauka har keyar shi,
        Kwalla ne ya shiga zuba min ina jin kirjina yana bugawa da mugun gudu. Na shagala da kallon shi kwalla na zuba min.

     Yayi nisa gurin tunanin yanayin da ya tsinci kanshi,  da yadda yake rayuwa babu lekowar iyaye. Lumshe idanun shi yayi lokacin da yaji kamar ana kallon shi, a hankali ya juyo tare da kallon yadda yake tsaye kamar an dasa shi a gurin. Takowa yayi har inda yake ya hango Bakin Almamoon a fashe. Kura mata ido yayi tare da kasa motsi sakamakon tawowa da Almamoon yaji ya wani rungumo shi yana kuka kamar ranshi zai fita.
"Hammah Mohan, don Allah ka mai dani ni gurin Innata, bata tab'a duka na ba, amma sabida malam Ansar na sha dukka sau biyu."

Na fada ina kuka tare da jin ko ina na jikina yana ciwo,  janye ni yayi a hankali yana kallon yadda fuskana ya kumbura, sai jinin da yake fita ta hancina. Ga goshina da ya fashe, cire rigar saman yayi tare da saka min a bayana sabida yadda suka yaga min rigar jikina, ya lullube ni da shi, dake saman rigar ce, rike hannuna yayi tare da wucewa dani cikin gidan.

         Ruwan sanyi ya dauko ya bani na sha, na sauke ajiyar zuciya. Bai magana balle ya ce min nayi hakuri, haka ya zuba min ido, sosai sannan ya mike tare da nufa sama, can sai gashi ya kuma saukowa da kayan first aid box. Duk da hannun shi yana ciwo bai hana shi nutsuwa ya shafa min idean ba, lokacin da ya saka min spirit ne na shiga tsalle ina wash da rike hannun shi.

   "Don Allah ka barni na huta, idan na huta sai ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login