Showing 69001 words to 72000 words out of 177131 words

Chapter 24 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

14811

ne?" Kara dauke kai nayi ina kallon cikin Elevetor da muka shiga. Daukar wayar shi yayi tare da dannawa ya manna a kunne, kafin ya fara magana,

    Buzanci ya juya baki daya kamar babu Hausa a bakin shi ko French, haka yayi ta hiran har muna fito, ganin kofar ta bude naka hannun shi mu tafi wayar ta fadi kafin na dauka ya taka, kamar zai bugani da kasa ya dauki wayar yana kallon yadda screen din shi yayi daga daga, gashi suna magana me muhimmanci ne da Hammah Khalil. Ranshi yayi mugun b'aci,
"Kasan abinda ka aikata min? Kasan Meye kayi? Me yasa baka da hankali ne? Kalli wayar yadda kayi min da ita? Wallahi baka jin magana mara hankali kawai, kuma a cikin albashin ka zan cire kudin wayata na baka sauran canjinka"

       A mugun tsora ce nake kallon shi jikina yana rawa, sabida har jijjiyar kanshi mik'ewa yayi,  da sauri na fita tare da yankawa da gudu, saka wayar yayi a cikin aljuhun shi yabi bayana, yana fitowa bai ganni ba, sake fitowa yayi ya hango ni, ina tafiya ina share kwalla.

      Bin bayana yayi tare da da karamin gudu, har ya isa jin ina kuka sosai ya sashi kallon yadda nake kokarin share kwalla da suke zubo min. Abinda na Fahimta shi mutum ne da bai iya rike ka ba, a lokacin da yayi fadar a lokacin yake manta kome. Rike hannuna yayi tare da cewa.
"Abokina kuka kake?" Ya tsare Ni da manyan idanun shi.
"Don Allah ka mai dani gida zan ga Innah" na fada tare da fashewa da kuka,  na fada ina fisge hannuna, ganin na saka hannuna dukka biyu a cikin aljuhun wandona yasa shi bina tare da gyara tsayuwar shi, kauce mishi nayi, ban san mota na zuwa ta bayana ba, sai da naji ya fisgo ni tare da had'a ni da jikin shi.  Yana bin fuskana da idanu. Musamman yadda na razana.. hannuna daya a kirji ina zare idanun.
"Zan cigaba da baka kariya daga yau har ranar da zan mai da ka gaban Innah." Mai da kaina nayi gefen kirjin shi ina kuka.
"Toh kukan na me?" A tsiwa ce na d'ago kai.
"Baka ce zaka tab'a min albashi" na ba" na fada ina tura baki.
"Really"
"Kwarai" na fada ina kallon shi, ga kwalla na zuba min. Shi kam ya manta da wata batun albashi, amma dake yana niman rigamar ya kare sai ya kura mishi ido, sannan yace mishi.
"Toh Yanzun kai me zaka yi da kuɗin da baka so na tab'a"  da sauri na dawo gaban shi tare da rike k'uguna. Sam na manta da abinda zai fito bakina.
"Zan biya sauran kudin gidan da zan saya mana, zan budewa Baba na kanti, zan sayi Laptop zan sayi waya. Kuma saboda wasu yan iska ne zamu bar unguwar dan dayan ya tab'a tab'a."

   Wani irin caccuma yayi min wanda ya sani tuna abinda Shege yayi min. Jikin shi yana rawa yace min.
"Gaya min ina ya tab'a maka"
"Hammah sake ni idan har da gaske kai abokina ne!" A hankali ya sake ni, fuskar shi tayi jajjur. Cikin wauta na fara kallon shi sannan nace mishi.
"Idan kana min haka wani sai ya dauka kana jin haushin dan an tab'a ni, kuma ai ba wani gurin ya ta b'a ba, duw..." Toshe min baƙi yayi tare da kallon cikin idanuna,, yana wani irin haki. Hannuna ya lalluba tare da sakawa a kirjin shi, yadda zuciyar shi take bugawa kamar zata fito. Dakyar yace min.
"Anan na saka ka! Ajiye ka nayi anan karka kuma bani labarin anyi muka wani abu domin babbakewa zanyi a cikin kirjina"

     "Toh Yanzun idan ka babbake taya zaka rayu? Zaka gaya min gaskiya ko sai na tara maka jama'a" na fada ina had'a index fingers dina yana dan bubbuga su da juna, ina mishi kallon tsokana.

     Kura min ido yayi cikin damuwa kafin ya riko hannuna, muka koma hotel din, muna shiga kai mu gurin cin abincin, inda ya kai ni babu mutane a cikin gurin, an rubuta VIP. Waiter ne ya tawo tare da memo na abincin, ya ajiye mana cikin girmamawa. Dauka nayi ina kallon abincin da yake rubuce, shi kuwa Hammah ya harde kafa yana kallona.

     Kallon Hammah nayi sannan na tura mishi memo din ina faɗin.
"Ban ga kome" dubawa yayi sannan yace mishi.
"African dishi" ya nuna mishi kome sannan ya ce mishi.
"Da fruit" haka ya juya kuwa can ba shafa cikina ina faɗin.
"Hammah Mohan, wallahi yau sai na biya bashin yunwar da cikin yake bina, kuma ko zai fito sai na dura."
"Cikin ka zai fashe" gwalallo idanu nayi waje kafin nace Mishi.
"Inji wa? Ai danyen fata bata fasuwa" na fada ina kara tabbatarwa.

     "Danyen fata yana fasuwa, sosai kuwa amma waye ya gaya maka?" Ya tambaye ni yana kallon fuskana,
"Innah ta mana." Murmushi yayi karami sannan yace mishi.
"Innah tafi ni gaskiya" sabida yaso ya gaya mishi wata magana amma sanin cewa Yaron shi bai da cikakken kirki yanzun sai ya kuma kara tambayar shi, zuwa an jima reni ya shiga tsakanin su. Ya sa shi gasgata Innah da yaso tace mishi. Akwai a jikin kuma tsaf zai fasu sai ya share zancen.

    Bai gama nazari ba aka kawo abincin, kallon shi yake yana kallon yadda yake had'iye yawu, dan haka ana gama shirya musu table din yace mishi.
"Don Allah karka cinye da table din" gyada kai nayi, ina me daukar cokali, ina faɗin.
"Bismillah" na fara diban abincin wani irin motsi kunnena yayi, bayan hanjin cikina yace kururu.
"Karka damu ku gama ihun ku, yau zan cakaku da Abincin" ba fada ina kara cika bakina da Abincin.

    Wato abin ya fahimta, yaron yana da barkwace sai dai rashin abokin da zai zauna da shi suyi hira tare da raba matsalar shi da shi,  Yaron yana da kuruciya da wauta, gashi da ban dariya duk fushin sa idan yayi mishi abu zuwa an jima zai bashi dariya, d'ago kai nayi ina kallon Hammah Mohan da yake kallon yadda nake cin abincin.kunya ce kuma ya kamani, na ajiye cokalin ina faɗin.
"Ya hakuri na manta da kai ne baki ɗaya."

Girgiza min kai yayi sannan yace mishi.
"Cigaba"
Murmushi nayi mishi tare da ware fararren hakorana. Girgiza kai yayi ya fara shan fruit din yana kallon hannun shi, wayar hannu shi take haske amma babu halin dauka sabida ya bugu da kasa. Har muka gama kallon abincin nayi ina sauke ajiyar zuciya.
"Yanzun haka zamu bar abincin?" Na fada ina kallon shi. Bai kula Ni ba, ya fara kokarin mik'ewa nace mishi.
"Hammah kawo kunnen ka" na fada ina yafito shi da hannu, ya gaji da shirmen yaron nan, zama yayi tare da kallona.
"Kawo mana shawara zan baka"
.kawo kunnen shi yayi na kai bakina ina dan karewa kar maganar ya fito.
"Kaga mu ce su biya mu rabin kudin mu tunda bamu cinye abincin ba ko me ka gani?"

       Tashi yayi yana kallon shi idan ya bashi amsa kamar ya biye mishi ne suyi ta hauka, idan kuwa ya kyale shi ya manna mishi haukar shi daya ne dan haka ya mike tare da ciwo kudin ya saka a cikin memo din ya tawo inda nake ya d'ago ni, yasan sai na iya raba kudin biyu, aikuwa bai gama d'aga ni ba, nace mishi.
"Wallahi sai na raba biyu."

     Jana yake ina kai hannuna.
"Wallahi zan sab'a maka" kwace hannun nayi ina tura baki.
"Haka kawai mutum bai cinye abinci ba ace sai ya biya Alqur'an Ubangiji da na koma sai na kwashe kuɗin." Na fada ina tura baki. Bai san ƙaddara da ta haɗa shi da Mamoon  ba, amma baki daya ya hautsina mishi lissafin shi. Daga nan fita suka yi cikin garin Dubai, inda suka nufi wani shagon sayar da waya, anan ya hango irin tashi, a ciki kuwa akwai inda ake gyaran waya Sosai dan haka ya nufi  gurin ya mika musu, basu jima ba suka gaya mishi abinda za saya.
"Kai haba kudin a kasa kake diba? Gaskiya gwara ka sayi sabo kawai" na fada ina hararan mutanen.
"Kasan Allah, karka hada ni da mutane." Ya fada min kamar zai make ni, dan ya fara gundura da halina.  Juya mishi baya nayi tare da kallon wayoyin da suke jere.  Juyawa nayi gurin Hammah Mohan na janyo shi ina nuna mishi wayar. Na sake shi tare da nuna mishi wata Sumsung S4.
"Yayi maka ne?" Kallon shi nayi sannan nace.
"Eh amma nasan ko dukkan albashina na dauka ba zai saya min ba. Ba yanzun ba idan na koma gida zan Nime wata yar Vivo, dan naji kace sai ba biyaka kudin wayar ka, shi yasa ba ce maka kawai ka sayi sabuwa."

          A hankali ya kalli me sayar da wayar ya nuna mishi, yana daukowa ya mika min.
"Karb'a"
"Hmm, kawai ka barshi domin ka ga idan na koma Maradi zan koma makaranta ne, kuma hostle zan koma. Sannan kuma zan je ganin gida iyayena ina kewar su." Na fada kai na a ƙasa.

     "Karb'a." Ya mika min lokacin ya mika master card din shi, kamar yadda nayi tsammani haka ce, domin kuɗi ne me mugun yawa, tura baki nayi bayan naga yawan kuɗin. Can nace mishi.
"Ina fatan kyauta ka bani? Domin ni dai ba zan iya sayan wayar nan ba, tunda ba kudin ce dani ba"

"Zaka zauna dani na wata uku kafin nan na fanshe kudin aikina." Ya fada min yana tafiya kamar ba a bakin shi maganar ta fito ba, wani Jahilin tsalle nayi, tare da dawowa gaban shi, ina raba ido.
"Ba ka sami lafiya ba?"
"Eh amma ai na saya maka waya kuma na biya kudin gyaran wayar toh me?"
"Ungo maza mai da musu bana son Alqur'an bana son, kawai ka bani sauran canjina na koma gida."
"Auw haba?"  Aikuwa na takarkare murya na fasa mishi kara, sai da ya toshe min bakina, tare da ɗaukata ina, watsal watsal da kafana kamar Yaro dan shekara uku. Haka ya fitar dani daga shagon. Aikuwa na koma inda ya tsayar dani na fashe da kuka.
"Wallahi ba zan yarda ba, sai dai ka rike wayar haka kawai zaka tab'a min kudina saura dubu dari bakwai na gama biyan kudin, kace ba zaka kyale Ni ba sai ka fanshe?"

   "Kwarai sai na fanshe kudina." Ya kuma faɗa min, kuka ne ya kwace min, muna tafiya sai kallon mu mutane keyi.

"Kaga akwai wani wasa da ake yi casino zan baka aron kudina  idan kaci zaka iya samun sama da dallar Amurka dubu dari uku a lokaci guda, amma sai ka nutsu zan na gaya maka Number kana sakawa, sannan kuma idan aka canza shi zuwa CF kudi ne ne shegen yawa, sai ka biya kudin gidan ka."

   Kallon shi nayi naga nima yake kallo.
"Caca zan buga bayan haramun ne?"
Janyo Ni yayi jikin shi.
"Karka damu akwai abinda nake son muyi a gurin muje ko ba zaka yi amfani da kudin ba amma kuma zaka ga sabon rayuwa"  ya shigar Kawata min gurin babu shiri na amince, muka nufi wani hotel tare mu aka kayi tare da nuna mana inda zamu sauya kaya.
Kallona yayi sannan yace min.
"Almamoon ina son tausaya min kayi shigar mata?" Wani tsalle nayi kamar wani dan biri. Ina rufe kirjina.
"Kai haramun ne" na fada mishi,
"Toh babu damuwa bari na fita na nimo wata baturiya" ya juya zai fita da sauri na rike hannun shi.
"Amma daga yau karka kuma sani nayi shigar mata, domin ni ba mace bane" na fada mishi ina me sunkuyar da kaina.

         "Good boy" ya faɗa min, wani daki ya nufa bayan ya buga kofar dakin, wani dan daudu ne ya bude kofar.
"Dame zan taimaka maka karjejjen kato"

"Sauya min shi a cikin nan da awa daya" ya tura ni.

       Shiga katon dakin muka yi, da yan mata kafin kace me sun taru a kaina, sai da suka kwashe min albarka kafin suka nuna min wani daki na sauya kaya, haka nayi ta sakawa idan na kalli madubi da sauri zan dawo mishi shi.

Dakyar ka sami wata gown iya kwanjina, golen sannan suka dauko takalmin da yar pose, yan kunnewa, aka saka min wato dan daudu nan da ya rike fuskana ya shiga min paint, sai da naji kamar abu ake loda min a fuskar dakyar ya gama. Sannan ya dauko wata jacket ya daura min a ƙafadana yana faɗin.
"Kin fito kamar wata Jaruma." Murmushi nayi mishi sannan  na fito, ya juya bayan shi yana waya kamar kuma me muhimmanci ne.
"Eh mana shi ne daidai da aikina kafin na iso inda zan kammala baki daya, kawai zan yi amfani da hakan ne ka gane kawai ka saka ido akan sauran sai mun iso Insha Allah." Karan sautin takalmi da yaji ne ya sashi juyawa. Tare da zubawa sarautan Allah ido, duk da yasan cewa Yaron mata maza ne amma wallahi yau ganin shi cikin kayan mata ya kara kwadaita mishi son lallai yaron ya koma mace.

       Takowa yayi tare da mika min hannun, a hankali na saka a cikin nashi, muka fita a hankali domin ban iya tafiya da takalmin ba kamar zan fad'i. Shi yasa ya kange ni a jikin shi har cikin inda ake buga wasan.

     Kamar zanyi kuka haka nake kallon gurin, saka min abubuwan da zan buga wasan aka yi ya ajiye Dalar Amurka har guda bakwai, sannan ya saka a gabana. Yana faɗin.
"Kai me Sa'a ne kayi amfani da sa'ar nan idan suka baka wasan ka dauki wancan silallar."

    Gyada kai nayi, a hankali yana gaya min ina bin abinda yace kafin minti talatin cinye gasar,  a  hankali ya shiga tara min kudi ko awa daya ban yi na na zama attajira a gurin an cika min kudi a gaba na. Tab'a kunnen shi yayi tare da cewa.
"Ba'are fara" 
Nan kuwa wani katon mutum ne ya fito, tare da kallon shi.
"Dama tunda na ga ana ta cin mutuncin gasar nasan Mohan ya farmake mu. Barka da zuwa." Ya fada cikin French,  mika mishi hannun yayi tare da cewa.
"Wasan bai kare ba, ita Yarinyar zaka saka nima kuma zan saka abinda na mallaka. Domin zamu gwada kwanji ne?"

     "Thomas jefferson ba wannan ne ya kawo ni ba, kawai akwai abinda ya kawo ni sai dai matuƙar kasa ni magana zan karya kashin hakarkarinka na kuma Cigaba da wasa na, na jima da ajiye aikin soja kawai ina da yakinin wata rana kasata zata bunkasa." Ya fada yana kallon mutumin.

     "Toh haba, lallai ku tattara mishi kudin shi, na zata kana aikin ne har yanzun, muje ka sha ruwa" ya faɗa mishi.
"A'a kasan bana son giya." Haka ya ja hannuna muka nufi inda mutumin yake zaune, a hankali hira ta sarke a tsakanin su, ina gefe duk a takure nake.
"Cire rigar jikinka ka nufi wancan table din, ka zauna"

A hankali na cire jacket din na kudi inda yace na zauna,  ina zaune sai ga wani dattijo, zama yayi yana kallona. Matsowa kusa dani yayi tare da cewa.
"Yan mata daga Afrika?"
"Eh" na bashi amsa ina kallon yan matan da suke rawa naked, nan ya zauna yayi ta min shirme da shiririta, har wasu mutane suna shigo gurin. Mikewa yayi suka fita. Mikewa yayi tare da zuwa inda nake ya mika min kofi tare da wani kwaya ya mika min bayan ya bar gurin dai ga mutumin.
Ajiye kofin nayi bayan na zuba lemon Kwalba a cikin kofin, na mika mishi sannan nima na sha nawa, a hankali muka hira dashi har ya mike tare da mika min hannu, kallon Hammah Mohan nayi ya gyada min kai.

     Bin bayan shi nayi, muka tafi yana tangadi har dakin da yaƙe, muna shiga ya zube akan gado. Bayan kamar minti goma, naji an buga kofar, budewa nayi na gan shi.
"Babu abinda yayi maka? Toh maza wuce gani nan zuwa."

Yana shiga na bar gurin domin da kayan aikin ma'aikatan hotel din ya shiga ya gama abinda zai yi ina club ɗin sai gashi, ya mika min hannun na mike tare da nufar inda muka ajiye kan mu, muka sauya.  Kallona yayi bayan na saka kayana na fito rike da jakar da ya saya min waya.

   "Me yasa baka da account Number? Yanzun da kudin nan sai dai na tura maka" kallon shi nayi sannan nace mishi.
"Kudin nan zan kai asibiti da makarantun gwamanti tare da gidan marayu, akwai mutane masu makamanciyar rayuwata  basu ci sau uku a rana ba, ma idan na basu zasu yi farin ciki."

        Jan abinda na daure gashina yayi dashi bayan ya cire hular gashin mazan da yake saman kan nawa, ya zare min gashin. Ribom din da na kama gashin da shi ya ha, gyararren gashin ya sauka har gadon bayana.
"Me yasa baka son ayi maka aikin komawa jinsin mata?" Saka hannuna nayi tare da hautsina gashin kaina ina murmushi.
"Nafi son wannan yanayin" na fada ina kallon shi.
  Shima hautsina gashin yayi yana faɗin.
"Kuma kayi kyau ba a jinsin mata"
   Tsayawa nayi ina kallon shi kafin nace mishi.
"Ai kafi ni kyau"
"A'a ba dai fika farin fata ko"

   "A'a kawai ba zaka fada bane"
"Gaskiyar kenan"

        Na gaji gashi lokacin sallah yayi dan haka muka nufi inda muka kama, muka yi sallah bayan mun isar yace min.
"Pizza kake so ko Shawarma"

   Mika nayi tare da cewa.
"Duk wanda aka kawo min matukar ba zan yi asarar shi ba yayi min" na fada ina shafa cikina.
Yayi a waya can dai gashi an kawo min, shi kan Coffee ya sha abin shi.
"Kayi sauri domin an jima zamu bar kasar nan."

"Hammah duk dai saurin unguwar zoma dole sai an haihu dan haka ka jira na gama cin abincin mana" na fada ina koda pizza a bakina. Share ni yayi tare da mai da hankalin shi kan yanayin da yake ciki, na son lallai ya shiga Nijar yau din nan.

        Haka na gama dakyar shima dan yayi min barazana zai tafi ya bar ni, yasani mik'ewa da sauri na bi bayan shi, muka nufi hanyar gida.

     Tunda muka iso airport, yake yawan kallona,
"Yanzun idan muka koma dole sai na maka aikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login