Showing 159001 words to 162000 words out of 177131 words
zama yadda ya dace insha Allah"
Ya fada yana shafa kanshi, domin yayi wallahi yana jin matukar suka had'e toh ba makawa sai ya bi da ita yadda bata zata ba, sai ya nuna mata shi
namiji ne da ba'a rena shi cikin sauki, duk zai iya hakuri da kome amma ya tsani rashin kunya, musamman irin bata da ta rena shi lokaci guda, bayan yana ji a zuciyar shi da gangan jikin shi tana haukar son shi, shafa fuskar shi yayi yana murmushi.
***
Ranar beenah ta sha fada a gurina, su Mommy watsar da mu suka yi, ranar da muka cika kwana biyar Abba da Abbu suka zo, abin ya bani mamaki. Amma ganin su bai rage kome ba, sai kara min kaunar Yaron su, na gaishe su ina kuka.
"Allah ya miki albarka, Ubangiji ya raya abinda kika haifa, Ubangiji ya shiga al'amarin ku"
"Amin Ya Allah, Amin Yallabai"
Mikewa nayi na koma dakin ina kuka.
"Ka ga ikon Allah! Yarinya ta raba gardama,kaga yadda ta dauko Ubanta, har da Kakanta. " Inji Abba,shi kam Abbu kiran matar shi yayi suka gaisa. Sannan ya gaya mata gashi a gidan su Maimunari, tare da sabuwar Amaryan da yayi,
Nan suka shiga wasa,har aka kawo min wayar, sannan suka gama maganar su ne manyan, akan nan da wata wata biyu zasu tawo bikin Beenah da Khalil, anan suka ci abincin rana da na dare, sannan suka wuce,
...
Tana gefena tana waya, wallahi bana jin me take cewa, domin maganar ciki ciki ake yin shi da salon shagwaɓa. Make ta nayi tare da kallon ta.
"Ki kula min da Widad zan shiga ban daki" na fada mata ina nufar ban daki, juyawa tayi gurin Yarinyar tana mata wasa tana waya, bayan na fito, Naji tana sauke nishi a hankali.
Fisgar wayar nayi tare da sakawa a kunnena.
"Khalil karka b'ata albarkan aurenka daga waje, duk abin da zaka yi ka jira ta shigo gidanka meye na wasu abubuwa haka?"
Na cilla mata wayar ta, mik'ewa tayi tana tura baki.
"Idan ke ba zaki kula da masoyinki ba, ki bar ni na kula nawa saurayin"
"Zo nan!" Na kirata, tana zuwa na rike kunnenta.
"Na makale a zuciyar shi ce, sabida soyayyar mu babu kazamta,ina rungume shi duk lokacin da naso, sau daya na sumbace shi ranar da muka sami sab'ani, ke soyayyar ku shirme ce. Ni tawa dashi guba ce domin idan muka hadu tabbas Allah ka dai yasan me zai faru" sannan ba ture ta, dariya ta saka min tare da cewa.
"Matar nan baki da alkibla, shekaranjiya kina ce kin tsane shi yau kuma kina haukar son shi. Duk wanda ya shiga tsakanin kuzari mutu wallahi"
Share ta nayi, na cigaba da rarrashin Widad da bata gajiya da rikici.
Haka Mommy ta shigo da kayan da aka kawo mana, akwati hudu, tsayawa nayi ina mamakin wannan al'amarin, kayan yarinya kuwa babu laifi, wai dan ba a can na haihu ba, da na ga kayan jaririyar. Har da sarkar farin gold,
**
Ranar da suka dawo ya mikawa Ummul Aiman hoton Babyn.
"Yallabai yarinyar nan tafi Baban ta kyau, dube hanci har baka. Shine baka kawo mana ita ba."
"Wallahi da na turawa Ubanta kamar zai yi kuka. Tausayi yake bani." Ya fada yana cin abincin shi.
"Gaskiya ya kamata ka gaya Mishi inda suke haka ba hujja bane."
"Insha Allah, zan gaya Mishi meye zaku yi na sunan dan na gayawa Khausar taxo ku tsayar da magana." Ya tambaye ta,
"Eh duk yadda kace"
Abu ne na kuɗi dan haka ya ware masu kudin da zasu bukata, dan haka aka shirya gagarumin walima,bayan an bawa wata gidan abincin daukar nauyin girkin walima, dan haka gefe guda haka suka yi ta zirga-zirga ita da Yar gidan Babban liman da ya bata, dake budurwa ce, gashi Radiyah bata gidan tana Nigeria, hoton yarinya aka bawa wasu masu yin aikin foste suka masu aikin dake an zuba musu kudi har da kalanda, memo, book, cup ba tangaran, stickers na mannawa a bayan waya, da abubuwa dayawa. Su kuma suka shiga hidima aka raba kaya sosai.
Lokacin da Khausar ta nunawa Hajiya Lateefah tace mata.
"Ammyn kalli wannan yarinyar ta min kyau!"
Kura mata ido tai yana kallon hoton Yarinyar da ya daki zuciyarta.
"Wacece ta haifi me kama dani"
"Ai baki sani bane, ai gobe gidan nan akwai walima dukda su yau ne suna mu gobe ne zamu yi namu matar da kika tsana ce, jinin ki Allah sai ya raba gardama gashi kowa yasan yadda Hammah Mohan yake kama dake shine Allah ya tashi sai ya sakawa Maimunari jininki me mugun kama dake."
Sake wayar tayi tare da dafe kirjinta, tace.
"Ta haifi cikin?"
"Toh dama kin kifar dashi ne? Ta haifi Maryam Sunan Nahnah, Kinga kuwa dole gidan nan ayi shagali"
Kirjinta ne yayi mata nauyi dan haka tana rike da shi, sai kallon ta take.
"Ammyn ya dai?"
"Babu kawai ina mamakin kamar da yarinyar tayi ne da mu, anya ma Yar Mohan ce?" Cikin bakin ciki da takaici tace mata.
"Ammyn Ubangiji ya dube ki da rahamar shi" ta kule dakin ta, domin tana bin na Ammyn zata fadi abinda Allah zai kama ta.
Washi gari aka yi walima kuma dake bata da kunya sai gata har a gurin tana gayawa mutane, yar Mohan ɗinta ne, gashi bata san inda yake ba, surutu irin mara hankali tayi ta sake yi shi.
Bayan an watse kayan da aka kawo na suna da mugun yawa Khausar da Ummul Aiman wacce suke kira Small Mom, suna ganin kaya, tace mata.
"Small Mom, mun hada kudi zamu mishi sayayyan namu kayan, amma ina ganin zata zo bikin Kanwar ta."
"A'a dota Abbunku yace ba zata zo ba, domin tana arba'in zata koma makaranta, kuma idan tazo zata zama abin nunawa a cikin dangi dan haka kawai tayi zamanta da yarta, idan zasu koma sai a koma mata da kayan."
**
Bayan suna da kwana ashirin, Mommy suka fara hidimar su, da shiga kasuwa sayayyar kayan Beenah da ita amaryan.
Jego ya amshe ni, idan ka ga yadda nayi kyau nida yarinya na kamar me,Bama fita Baba Mari jegon da yake min, dan haka na samu kulawa ainun.
Lokacin da muka cika kwana arba'in, Abie da Mommy da Baba Mari, da Yumnah aka bari a gida, bayan an kawo min Nanny wacce zata zauna har sai sun dawo. Yumnah suna tsakiyar karatun gama primary school ne,Ni kuma Abie ya nima min makaranta zan cigaba da aji. Duk wanda ya kalle ni ya san na samu nutsuwa kibar da nayi ta boye tsawon da nake da ita.
Ranar da na fara karatu, ranar n hadu da Malam Ansar, murna kamar zanyi yayya, har gida ya kawo ni na nuna mishi Yarinya na, haba bawan Allah haka ya dauke ta yayi ta hidima da ita. Washi gari haka ya kawo maka kaya niki niki.
A lokacin nake gaya mishi ai mun rabu da Mohan, dan haka karatu ne a gabana, kuma shima ya bani goyan baya, dan haka muka kuma dinkewa sama da baya.
... A can Nijar kuwa bayan an daura aure ne.
Anyi shagali sosai ranar budar kai wata Al'amarin ya faru.
Domin kuwa Baba Mari ta rike hannun Beenah ta mikawa Nahnah, ita kuma Nahnah ta kurawa Baba Mari ido.
"Mariya!"
"Mairamu!" Sai suka sake salati tare da fashewa da kuka.
"Mariya kina raye?"
"Mairamu kina nan da ma?" Komawa cikin gidan aka yi babban falon Abba aka zauna.
"Maza ku kira min kowa, har da Mohan da yazo, kowa karku bari har da Wancan kafiran."
Bayan minti talatin aka haɗu, kallon Mohan tayi sannan ta kalli Jama'ar falon tace musu, domin har da iyaye mazan.
"Mariya kanwata ce Yar baffana."
Share kwallar idanun ta tayi sannan tace musu.
"Zuri'ar Shehu Usmanu Wodaadabe, babban zuri'a ce fa ta haɗa yammacin Afirka zuwa gabashin Afirka, domin shi din daga kasar Libya yake kuma bafulatani ne na Usul Bororo,"
(Zaku yi hakuri domin zamu leka 75yrs ne da suka wuce! Da fatan zaku bude kanyar ku, ku fahimci bayani.)
.....
75yrs ago.
Shehu Usmanu Wodaadabe ya na da tarin dukiyar dabobbin musamman shanu da raƙuma, ba a batun kananun dabobbin,
Yana da mata uku, Maimunari itace Uwargina suna kiran ta da YADIKO Munari, yana da Mai bin mata Hajara Hajjo suna kiranta Yawuro, sai ta Ukun itace Amarya suna kiran ta da Inno, sunanta Ramatu.
Dakin YADIKO Munari ita ke da Yara maza, rai shida. Kafin mata biyu.
Iro, Kalamu, Isuhu, Dahe, Kabiru, Ya'u, sai Deja da yar karamar su Laure.
Dakin Hajo tana da yara mata biyar namiji daya.
Kuluwa, Sa'ade, Sakina, sai Rabi'atu, fatsuma, da Garbati.
Dakin Amarya tana da yara biyu domin ita wabi take, Sulaimanu da Tanimu,
Dukka yaran shi nan doka sha shida, Allah ya albarkace su da tarin ilimin addinin musulunci, kuma suna bada taimako irin na laluran rashin lafiya, dan haka sai ya zama na sun yi shura a rugar baki daya. Domin daga Libya sukan tafi Mali zuwa burkina faso, suna yawo sosai.
Sannan Shehu Usmanu Wodaadabe yana da Kane maza biyu, Abdullahi da Abbas, Abbas yana burkina faso, Abdullahi yana Mali, kuma dukkan su da iyalin su.
Duk shekara suna zuwa Libya, bikin al'adar Wodaadabe, dan haka lokacin da suka zo aka tsayar da magana yar Abbas aka bawa Iro mai suna Sadiya, shi kuma Kalamu aka bashi Yar gidan Abdullahi mai suna Dayyiba. Haka aka sha bikin su,bayan sun amince da junan su.
Sai ya zamana duk shekara ana wannan haɗin,kuma ana zaman lafiya.
Bayan wasu shekaru kamar ashirin da Biyar, duk da ana zumuncin amma yayi rauni.
Zuwan da suke duk bayan shekara daya, sai ya koma bayan shekara biyu ko uku, ya zama gidajen baki daya uku auren zumuncin da aka a tsakanin su yayi baya,
Amma kuma a Zuri'ar Shehu Usmanu Wodaadabe, ba a daina auren ba, a wannan dakunan.
Dakin Hajo sun yi aure yaranta a wasu gidajen..
D'ago kai tayi sannan tace musu.
" A cikin Zuri'ar iro nice nayi saura, ban sani ba ko akwai wasu dangin nawa! A Zuri'ar Isuhu dakin YADIKO Mariyah ce tayi saura ban sani ba ko a kwai Sauran! Amma a Zuri'ar gidan Ya'u Mamman ne yayi saura ban sani ba ko akwai sauran." Sunkuya da kai Abie yayi tare da cewa.
"A Zuri'ar Kalamu Ni da kanwata Amina muka yi saura dakin YADIKO"
"A Zuri'ar Sa'ade mune muka saura dakin Hajo" inji Abban Khalil dan Ba'are
Take dakin ya dauki kabbara.
( Mu Cigaba)
Bayan kamar shekaru ashirin sai iyayen mu suka fara ganin ya dace a hada yaran su aure.
Dakin YADIKO da dakin Hajo, aka ware matasa maza da mata.
Dakin Amarya aka ware yaran suma.
Dan haka aka kira Sa'ido aka ce mishi an bashi auren Hauwa'u, yar gidan Baba Isuhu. Shi kuma ɗan dan Baba Tanimu ne. Kasancewar Baba Tanimu ya rasu,
Girgiza kai yayi tare da cewa.
"Ni Ummul khairi nake so! Ita zan aura idan ba ita ba sai dai a fasa wannan haɗin"
Hauwa kuma yar gidan Baba Garbati ce dakin Hajo.
"A'a Ummul khairi an bawa Na'ibi ce."
"Hodijam! Wallahi dan anga kasata rufewa Baffana idanu za a bani abinda bana so, toh wallahi ba zan amsa ba. ko a bani Ummul khairi ko kuma na tafi da ita!"
Iyayen su tsawatar mishi amma bai ji ba, dan haka suka dauki Hauwa suka bashi, ita kuma Ummul khairi aka bawa na'ibi. Kanwar Sa'ido Aminatu aka bawa dan gidan .
Dan haka babu wanda yasan manufar shi, sai ranar da aka daura auren, Ummul khairi da Na'ibi, Sa'ido ya dauke ta ya tafi da ita.
Iyayen mu dayawa ransu ya b'aci, dan haka abin sai ya zamana ya tab'a kowani dakin. Domin dakin mu, baffan mu yayi mana fada maza da matan mu, sannan yace kar yaji kar gani.
Bawan Allah nan bai tashi dawo da Ummul khairi ba, sai da tasha bakar wahala da tsohon ciki ya dawo da ita.
Ana aka gujeta kowa ya gudu ya barta, ashe daman can akwai wani Buzu daga Nijar yana bala'in Sonta shi ya daukota ya dawo da ita Nijar bayan ta haihu ya aure ta, "Mamman kai ne!". Jikin kowa a gurin sai da yayi sanyi.
Bayan wata biyar anzo bikin kanwar Sa'idu, dakin su Ummul khairi Ya Ado ya dauke Yarinyar akan idanun Sa'idu, mai suna Deja. Ya tafi da ita, bai dawo ba sai da labarin mutuwar ta,
Wannan abin ya fara ne daga dakin Baba Tanimu, sai gashi ya shigo har dakin mu, inda Hammah Babba ya dauke yar Baba Kalamu. Maimunari mahaifiyar (Abie da Innah)
Shima Faizo kanin Maimunari ya dauke ni," kin ji ko? Allah ya nufa ba a shegu zan haife ku ba, amma abinda kuke yi dattin zina ce ta lalata min ku! Sabida ita zina masifa ce, kuma dattin ta kashe zumuncin yake kuma ya kashe min zumuntar ku tun mahaifana"
Bayan na shekara biyar Allah ya nufa na dawo gida, nima sai ba gudo Nijar gurin Ummul khairi, anan na hadu da mahaifin su Lateefah shima Buzu ne.
Sai ya zamana baki daya Zuri'ar mu ta watse, kowa ya kama gaban shi, gwara Maimunari naji labarin Hammah Babba ya aureta kafin suka rasu. Amma ban san inda take ba, ranar da naga Maimunari naji a jikina Yar Uwata ce, domin kamar yadda wancan take haka itama take. Labarin Zuri'ar mu da fadi take amma mu nan yan dakin Iro, Isuhu, da Kalamu duk mun hadu dakin Sa'ade gaka, dakin Tanimu kai ne Mamman, Sulaimanu kuma Yar shi mai sunan. Bilkusu wani Bazabarme ne ya aureta, tana da D'anta shima ban san shi.
"Wa'adin Ansar yana nan raye." Inji Abie.
Sharce kwalla Baba Mari tayi.
Sannan tace.
"Baffana yayi saurin aura min Ja'e ne, gudun kar abinda ya faru da sauran ya faru dani, tunda dan Uwana Hammah Babba ya dauke Maimunari, ashe muna namu wayon ne Allah ya shirya mana nashi hikimar, bayan na haifi yara maza da mata, na aurar da su, sai gashi Zainabu ta samu manema dayawa har da wani likita a birnin , mun saka burin son tai karatun boko, abubuwan farin ciki sun faru(babu amfanin dawo da baya muje kawai ba)
Bayan ta gama karatunta aka saka Bikinta."
Har inda abie ya kwamushe ta, (toh kunji ba kunga illar ramuko kenan wallahi dukkan su zuri'a daya ce)
"Haka muka gudu sabida abin kunyar da zamu aikata, idan yar mu ta dawo, bayan mun tafi mahaifinta ya rasu, na manta cewa Allah zai bima kowa hakkin shi, sai gashi dan Maimunari yazo ya dauki fansar uwar shi."
#mai_Dambu
[8/16, 5:52 PM] Yar Kasuwa👳🏻♀️: https://www.wattpad.com/1116237086?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=uJKhfsFaHx1OnFijgRnQ5anbrgbu69dYpl9OGkwca9A2nKghpFbmd3OLH0az9UZXH%2BXwtjoqsjLlfz094p%2BjC%2B2BV7NWPll8LKXfhlmC%2F4I7zE2IA9ygXh%2FB85HrSw%2B0
HAKKIN MALLAKATA
#Mon-Aug-2021
BOROROJI
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza..
BABI NA SITTTIN DA SHIDA
Ya tafi da ita bai tashi dawo da ita ba, sai da cikin shi haka yasa muka gudu, bayan rasuwar Mallam na dawo garin aka ce min suma.basu nan!"
Kukan Ammyn ne ya tsannanta, tace.
"Nahnah Yayanki ne ya dauke kakar Maimunari? Shi kuma Uban Maimunari ya dauke Zainabu, me yasa ban san tarihin mu na taya zanyi ta d'agawa."
"Baki ga kome ba, tunda gashi kin raba zumunci Allah ya haɗa kin raba, dake ke shaidaniya ce" inji Nahnah.
Addu'o'in aka yi tare da niman kariyar Ubangiji akan abinda ya faru Shekaru saba'in baya,
Sannan Mohan tace.
"Don Allah ku taimaka min ku aura musu junan su, ko bayan sallah isha ne,"
Kallon suwaye aka mishi.
"Mommy da Abien mu."
Kunyar haka yasa Mommy ta gudu, aikuwa bayan an tashi an rufe taro da addu'a,
Aka nufi masalaci, sallah magarib. Mohan ya tsaya waliyin Abie, Khalil ya tsayawa Mommy,
Haddir da Salman sune suka biya sadakin.aka daura aure cikin mutumtaka.
A ranar kowa yasan matsayin shi, musamman Primer minister, da a daren ya ajiye aiki shi. Mohan kam bai iya magana ba, domin abin yazo mishi bazata, ta ko ina Maimunari yar uwar shi ce, kai ba zai ya jiran ya ganta ba, domin yasan zai bata mugun wahala. An kai amarya d'akinta, bayan watsewar abokan Ango.
Wato ma'ana idan na leka gidan Amarya. Duk wani abinda ake na al'ada sun yi (😂🤣🙄 BENAZIR bata san tsohon tuzuru ta aura ba, amma bari mu leka dakin ko🤨😜)
Wato shi tuwon girma miyar Nama ce, domin kuwa Khalil ya gaya mata gaskiya (😎🤓 Alqur'an na rasa yadda zan rubuta kome)
Yar gidan Mommy da Marigayi ta zata auren shan minti ne, sai da aka gama tab'ayya, sannan ya zaro bayani daga karamar hukumar wandon shi, ya shiga zungure ta,....(na fecce bani da damuwa da ita)
***
Washi gari da safe, kiran Umma yayi kamar zai yi kuka.
"Umma don Allah kizo"
Haka ta nufi shashin su, daga bakin kofar kawai ta tsaya.
"Umma ki shigo mana".yana sanye da Jallabiya ruwan milk, tana shiga taga matasai a kasa, ga Beenah can a kuryan gado, ta makure, sai kuka take ta dunkule.
"Fita ka bani guri." Ta kore shi ban daki ta shiga ta hada mata ruwa me shegen zafi. Sannan ta zo ta mika mata towel tace mata.
"Tashi kinjin" ta juya mata baya,a hankali ya zuro kafarta tana kuka, sannan ya daura towel din, da kifa akan gadon. "Kin gama daurawa"
"Eh " tace a raunane, sannan ta juya tare da taimaka mata suka shiga ban daki, sai da ta gasata sosai, ta gabata cire towel din, sannan ta fito ya same shi a falon fada tayi ya mishi tare da cewa
"Zan dauke ta, tunda baka da girma sai na jikinka. Kai ko kunya baka ji ba, ka saka yarinya a gaba kamar abinci, wallahi kaji kunyar ka, ina dalilin kasaka yarinya karama a gaba kamar ka samu babbar mace, toh ya kare dan ita ba tuwo bane da zaka saka a gaba kana ciki kamar ba zai kare ba, ce maka akayi haka rayuwar auren yaƙe? Dan haka kar na kuma jin labarin ka adabi rayuwar ta haka" kunya ya yasa shi sosa kanshi. Tana fita can sai gata da magani har zuwa dakin ta kaiwa Beenah,da tea mai kauri. Haka ta sata tasha. Dan ta same ta akan abin salla ne, tana sha ta koma ta kwana, ita kuma ta fito ta same shi a falon yana zare ido, kwafa yayi mishi tare da shigewa ta barshi a gurin yana zare ido.
Tana fita shima ya shiga dakin shi yayi wanka ya shirya tsaf, sannan ya fita tare da kiran Khalil suka tafi yawon gaida Surukai, sai wani sheki yake yana wani jim kanshi kamar akan shi aka fara aure (😎🤓 irin yaci sabon d....🤨😜) Ko kallo bai