Showing 45001 words to 48000 words out of 177131 words

Chapter 16 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

14787

Mohan ba? Hajiya abinda kike fa Allah"

"Fitar min a d'akina!" Inji Hajiya Latifah, tana nuna mata hanya. Kamar da gaske ta saka kai zata fita.
"Inda yaso ya mutu ko ya rayu, ohon shi" ta faɗa da karfi tare da jin kamar zuciyar ta zata buga dan bata kaunar a kira sunan Mohan a kusa da ita balle kuma sauran Yaranta.

     Da wani shu'umin murmushi ta bar falon tana jin a ranta shi kenan ta karewa Mohan Mamman Nasir, zata biya yaron da yake tare dashi kudi na fitan hankali.
  
Tana fitowa ya hadu da Primer minister, da Manyan yan jam'iyyar shi. Dake tana shirye da ta tozartashi tace mishi.

"Yallabai ina son zuwa na duba jikin Mohan"

Wani irin duba yayi mata tare da cewa.
"Ba yau ba"
Ya cigaba da abinda yake, juyawa tayi tare da komawa gida, har ta nufa gidan ya dawo tana cewa.
"Yallabai sai yaushe?"
"Jibi Insha Allah"
"Dama magani zan kai mishi, kuma yana da muhimmanci, tun da laluran nan hauka ce ai dole a duba lamarin don Allah ka barni na duba shi"

"Ba zaki ba nace" ya daka mata tsawa da yasa ta juyawa da gudu,

Caaa suka mishi da ido, yana jin numfashin sa yana hawa da sauka.
"Yallabai Mohan...."
D'aga hannu yayi alamar baya son jin koda kalma Daya ce daga bakunan su. Mik'ewa yayi yana me d'aga wayar shi ya mikawa Mai bashi Shawara na musamman.
"Ka musu bayani gobe zamu zauna yau bana jin dad'i."
Ya nufi hanyar da zai sada shi da cikin gidan shi. Yana jin kamar zuciyar shi zata buga.

Daga kasar zuciyar shi kaunar danshi yake kokarin tasowa mishi amma kuma k'iyayyar yaron yana kara danne mishi kin yaron.

   Yana shiga falon shi ya zube akan sofa, yana jin wani irin kewar yaron a ranshi, amma Yarasa me yasa yake jin zafin yaron.
Chef Judge  ya fado mishi a rai, baya mantawa ko wancan juma'ar sai da yace mishi.

"Yallabai munufarka tana da kyau sai dai  kuma da na jikinka ake maka yankan baya, sannan ake niman ganin bayanka, Yallabai nasan ba ilimina ya kawo ni nan ba, Allah ne ya kawo ni nan, kai a tunanin ka bayan mun hadu a Saudiya na gaya maka wannan yaron da kuke tafe dashi zanen ƙaddara zata iya raba tsakanin ku.

             Kuma kai ma baka manta ba, na gaya maka yaron ka yana da taurari masu karfi da zai hadu da wanda yake da irin taurarin shi da duniyar su. Yallabai Yaron ka yana cikin mawuyacin yanayi wanda a cikin gidan ka aka fara, sai dai kuma Allah yana sane dashi kuma yana sane da kome, idan yaso sai ya kawo mishi dauki kuma ya bashi wanda zai tsaya mishi. Ina tausaya mishi, duk da na daina na tuba amma bana jin dadin yadda rayuwar d'anka ya koma. Allah ya hada shi da mutanen kirki masu tsoron Allah.  Yallabai Yaronka shine jigon mulkinka kayi wani abu akanshi ya dawo kusa da kai, Yallabai ina ga baka tab'a jin ana fadin Yan baiwa ba ko? Toh d'anka yana cikin su, domin kuwa idan yana tare da kai kowa tsoron shi yake babu wanda ya isa ya takaka, idan baya tare da kai kuwa wallahi jikin su na rawa zasu nemi bataka idan ka shirya zan duba Al'amarin shi Insha Allah za a dace"

   Duk da yana jin zafin kiran sunan Mohan da Shugaban alkalan alkalai yake amma haka bai hana shi jin abin a ran shi ba
.toh waye yake niman bayan shi? MEYE! Mik'ewa yayi bayan sun idar da sallah jumma'a ya mika mishi hannun shi.

"Nagode idan ina son karin bayani zan Nime ka, alkalin alkalai" inji Primer minister,
"Nagode sosai Allah ya tsare gaban ka da bayanka"

Lumshe idanun shi yayi yana kara nazarin abinda yake faruwa, na farko tunda Mohan ya fara jinya mutane dayawa suka shiga rayuwar shi kuma suna abinda suka gadama bai isa ya hana su ba
  Na biyu tunda babu Mohan aka fara mishi bore kamar zasu shi Office din shi.

Na uku kowa niman daura mishi laifi yake kome ya faru niman a cutar dashi ake? Ya rasa gane abinda yake faruwa,.ya rasa gane dalilin da yasa aka juya mishi baya, a yanzun yana da shekaru masu yawa akan mulki amma bai tab'a jin ko ya cutar da kowa ba, amma shi kullum niman hanyar cutar dashi ake, kasa fahimtar kome yayi, sai ma dage kirjin shi da yayi yana kara tausayin kanshi.

Yana kuma jin kamar akwai masu bibiyar rayuwar shi da ta iyalin shi, idan ba haka ba me yasa za a mishi wannan abun?
     ***
Maradi.
Addu'a ake mishi yana kara mingirawa kamar maciji, duk ya jima kamshi ciwo, sai rike kanshi yake, da sauri na mike zan kai mishi dauki domin yana cutar da kanshi, rike ni Malik yayi cikin wani irin sassayan kallo, ya rike hannuna. Fisgewa nayi na fada kan Mohan,  wani irin duka ya kaiwa kirjina, sai da naji kamar raina zai fita sakamakon dukar nonuwana baki daya da yayi.

    "Hyaiiiiiiii! Haaaah" na sauke wata irin numfashi tare da jin kamar an cika min iska a bakina da kirjina, tafiya nayi zan zube Malik ya tare ni, daidai shigowar Dan Ba'are, shima ya kai mun wani irin riko, suka kwantar dani a kasa, yayinda Mohan yake ta amai.

   "Alhamdulillahi yau zamu bari zuwa gobe ku kula da Yaron yayi kokari wallahi"

       Bai kai aya ba,Dan Ba'are ya dauke ni da gudu ya fita dani Sakamakon jinin da nake fitarwa ta hanci da baki, baya ganin gaban shi domin kamar dirka yake a step din, har asibiti ya kai ni.

      A guje ya fita dani, Yaran shi da suka rako shi suna ganin shi aka bude kofar motar da sauri ya saka Ni sannan ya shiga yana me daura kaina akan cinyar shi.
"Taka motar"
Ya fada da karfi, haka suka fincike ta a guje.

       Daidai fitowar Malik da Malam.
"Yanxun ya za ayi da mara lafiyan?"
"Zan kula dashi" ya faɗa kamar zai fashe da kuka, domin wani irin yanayi yake ji na takaicin yadda Dan Ba'are ya mishi shigan sauri haka kawai zai wani dauki Almamoon ai haka bai dace ba ina laifin ya kuka da Mohan shi ya kai Almamoon toh idan kuma wani abu ya faru da.....
.......... Chaiiii.....🙄 Ga masu bukatar a tallata musu Hajar su kofa a bude yake a tuntube wannan Number,08130269641
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 
                   
~The Journey of Destiny💔~
 
Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

_*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Domin samun labarin masu kayatarwa na Hausa danna Link din nan a sha sauraro lafiya....

_Gaisuwar wannan shafin naku ne baki dayan ku Makarantar  BRRJI👏 Nagode sosai_

BABI NA SHA SHIDA.

Iskar bakin shi ya furza domin yasan dai duk abinda zai ayi almamoon namiji ne, dan haka ya juya tare da sallamar malamin, ya shiga cikin gidan. Yana me kara jin babu dad'i baki daya, ji yaƙe kamar yayi ta kurma ihu.

A yau yayi danasanin fara aikin soja, domin yana ganin kamar kasancewar shi a aikin ne ya ja mishi kaddararren wahala,haka ya taimakawa Mohan sannan ya koma bakin aikin shi dan bai ga dalilin da zai saka shi zama a jikin Mohan ba, tunda shi ya janyo haka.

     ***
Muna isa asibitin da gaggawa aka amshe ni, yana rike da gadon da ake turani har bakin kofar shiga dakin da za a duba ni.

          Tambayar shi nurse tayi yayi mata bayani, sannan ta shiga cikin dakin, suka mai da hankali akan duba lafiyar ta, rigar Jikinta suka nime tsagawa, likitan ya ce musu.
"Ku dakata ba sai an raba shi da kayan shi ba, idan aka duba daga wajen ma yayi."

Inji likitan yana ƙoƙarin had'a alluran da zai mata, haka suka gama abinda zasu har suka sami nasarar farfaɗowa ta, amma take likitan yayi min alluran barci.

   Lokacin da aka fito dani, mikewa Dan Ba'are yayi yana kallon su. Kamar me ciwon baki yace musu.
"Ya......ya.... Ya...."
"Yallabai da sauki ya samu barci, idan ya farka zuwa jibi zamu sallame shi"

     Gyada kai kai yake tare da kallon keken majiyanta, har dakin da aka kwantar da Almamoon ya shiga. Zama yayi yana kallon fuskar yaron, wanda kullum yake zagaye da saje, kusan ma dabi'ar shi,  sajen har kusan kumatun shi. Yana barci kamar wani mage, ya samu auduga. Dan cuter face din shi ya kuma fitowa sosai, gwanin ban sha'awa.

             A hankali ya shafa dan bakin shi nan (Ni kuwa nace bakin tsiwa ba🙄😩da bakar magana) haka yayi ta shafa bakin  shi yana murmushi, bakin yayi mishi kyau dan karami kamar bana namiji ba, murmushi ya sake tare da shafa kanshi yana me kallon window dakin yana kallon mutanen da suke shige da fice daga asibitin.

Yana jin ina ma da ace Almamoon mace ce, da yau zai gabatar da kan shi sabida kar yayi sake reshe kama ganye, kuma idan ma bai yi haka ba, taya yana ganin dama zai wuce shi, murmushi yayi sannan ya zauna tare da riko hannun shi yana kara jin wani irin nutsuwa a tare da Yaron,  haka kawai yake kara kallon nasibin yaron, yana kara jin yaron a cikin zuciyar shi lungu da sakon cikin zuciyar shi.

    Wani irin bugun zuciya yake ji a duk lokacin da ya kalli fuskar yaron ji yaƙe kamar dan shi aka halicci Yaron,. Shafa kanshi yayi tare da jin wani sabon nutsuwa akan shi. Yaron baki daya yayi tafiyar bazata da rayuwar shi. Murmushi yayi.
           ---
Kallon shi tayi kafin tace mishi.
"Malam Ansar ko zaka kai Ni naga Mamoon ne zuciyata taki yarda da halin da yake ciki, ko zaka kai ni"

Yadda ta damu sosai ya kalli Baba Mari kamar zai yi kuka, yace mata.
"Baba idan muka je ba lallai su barmu mu shiga ba, amma tashi muje"

   Babban mayafinta ta yafa, tare da bin bayan shi, har Jacader.

   Lokacin da ta ga gidan da Almamoon yaƙe zuciyarta sai da ta girgiza, dake sun san Ansar basu hana shi, shiga gidan ba. Asalima kamar an bashi pass ne, yana shiga suka haɗu da Malik kallon juna suka yi kafin Ansar ya fito daga motar shi yana faɗin.
"Ina Almamoon na kawo kakanshi ta gan shi ne dan ta damu"
Murmushi yayi irin me ciwon nan, sannan yace mishi.
"Yana asibiti babu lafiya"

         Cakume wuyar Malik yayi kamar idanun shi zasu fado.
"Me Mahaukacin ku yayi mishi? Kunga abinda nake gudu ba? Kunga dalilin da ya sani nake gudun zaman Almamoon a cikin gidan nan ko? Wallahi idan wani abu ya same shi. Sai na kashe wancan Mahaukacin"

      Dukar da aka kai mishi a baya yasa shi sake Malik.
"Kyale shi Fahad, ba laifin shi bane yana da iko da Almamoon."
.wayar shi ya ciro tare da kiran dan Ba'are ya tambaye shi suna ina ga kakan Almamoon tazo ganin shi. Yana gaya mishi asibitin ya gayawa Ansar.

Shima yayi amfani da kalmar kaka ce saboda yasan idan suka ji haka zasu bar shi ganin Almamoon. Yana gaya mishi sunan asibitin ya shiga motar shi da sauri, ya bar gidan kamar zararre, dama kuma ai zararren ne (🙄🤸😁🤣)

   Koda ya iso asibitin, dakyar ya sami dakin da aka kwantar da Almamoon bayan ya gama shan bakar wahala, yana shiga ya kura mishi ido, yana mai da numfashin sa, tare da goge gumin goshin sa, kafin ya kalli dan Ba'are, kasa mishi tijara yayi domin irin karfaffan mazan nan ne, da shi da Mohan fadi kawai Mohan zai nuna mishi da cikar halittar jiki irinta mazan da suke daukar karfe. Idan Mohan ya saka mata matukar ta kama shi idan zai d'aga hannun, toh rigar zata iya darewa, sabida tarin kwanjin shi.

         Takowa yayi tare da kai hannun shi zai dauki Almamoon, yaji an rike hannun. Tare da mai dashi baya, sake kai hannu yayi zai dauki Almamoon, ran Dan Ba'are ya b'aci dunkule hannun yayi zai sauke mishi naushi Nurse ta shigo.
"Nazo duba mara lafiyar ne zamu mishi allura"
Sauke hannun shi yayi yana kallon Almamoon, Nurse tana gama abinda zata yi ta fita, wani azazzaben dambe ya kaure a tsakanin su, karan buge buge ya farkar dani.

Kallon su nake kafin na tashi dakyar. Na nufe su tare da riko malam Ansar. Bakina yayi nauyi ina son nayi magana amma na kasa, dakyar na koma bayan shi na rungume shi. Tare da zaga hannuna kirjin shi.
"Ya isa Hammah ANSAR" na fada a hankali, kamar ba zan iya magana ba, cak ya tsaya kamar an zare mishi duk wata kusarin shi. Ji yaƙe kamar tunda yake ba a tab'a kiran shi da suna Yaya ba, baki daya gwiwar shi tayi sanyi sama da kullum. Yau shi Almamoon ya kira Hammah ko mafarki yake ne?

     Anya ba mafarki yake ba? Indai da gaske ne shi Hammah ANSAR ne, toh tabbas Almamoon yana rungume dashi kenan. Wani bahagon naushi Dan Ba'are ya kai mishi. A fuskar shi sai da ya kufa a kasa, tare muka fadi.

"Almamoon rabu da munafuki" inji Dan Ba'are,
"Hammah Khalil! Ka daina dukar shi, bana jin dadin haka."  Na shiga tsakanin su. Muna kallon juna. Tafiya nayi luuuu zan fadi suka tare ni dukkan su biyu, ɗauka ta suka yi tare da mai dani gadon, suna kallon fuskana. Lumshe idanun nake ina kuma buɗe shi.

    "Ya Hammah Mohan yake?"  Na tambaye su a gajiye, gyara kwanciya na suka yi sannan Dan Ba'are yace min.
"Ana ta lafiyar ka waye yake ta Mohan?"
Sam ban ji dadin abinda ya faɗa ba, dan haka na tashi zaune.
"Zanje naga halin da yake ciki"
"Baka isa ba, wallahi sai na falla maka mari, kuma mun zo da Baba Mari ne"

        Komawa nayi na kwanta, haka ya fita can sai gasu tare sun shigo d'akin, suna shigowa dan Ba'are yana fita.
"Sannun kaji, Allah ya baka lafiya ashe baka da lafiya ne"
Gyada mata kai nayi ina jin kwalla na cika min idanuna, shafa kaina tayi tare da cewa.
"Zan zauna da kai kaji"
Gyada mata kai nayi, muna cikin haka Malik ya shigo tare da kallona.

       Murmushi ya sakar min, na maida mishi nima.
"Ya jikin naka?"
"Da sauki"
"Allah ya baka lafiya"
"Amin Ya Allah, ina ka baro Hammah Mohan? Kasan bai da lafiya kake barin shi babu wani a kusa dashi? Kasan yadda rayuwar shi take cikin hatsari ka bar shi shi daya a gidan? Ku mai dani gidan kawai nayi jinyar  a can"

       "Ba zaka kuma komawa gidan ba, domin ina kaunar ka" juyawa nayi na kalli Malam Ansar.
"Ba zaka tab'a samun yadda kake so ba,dan haka babu ruwanka dani."
"Kayi hakuri dama nazo duba halin da kake ciki ne, kuma Alhamdulillahi, zan koma domin na bar Fahad a jikin shi."

Gyada mishi kai nayi, tare  murmushi.
Haka ya tafi ba tare da na yarda mun kuma magana ba, sabida bana son yadda yake kallona.

     Hankalin su Baba Mari da Hammah ANSAR ne ya dawo kai na.
"Baba Kinga shi taurin kan bala'i ce dashi dan haka ki saka baki mu koma gida dashi."

"Hmm" na fada ban kuma magana ba sai ga Dan Ba'are da manyan ledojin shi guda uku, ya ajiye min.
"Sannun bawan Allah Ubangiji ya saka da Alkhairi, Sannun da tallafan rayuwar shi mun gode"

Cikin wani irin murmushi yake kallon mu, irin yayi katon bajinta. Dariya ya bani irin wanda ake yin shi a cikin rai haka, na kalle shi nayi murmushi. Zuba hannu Yayi a cikin aljuhun wandon shi yana kallona. Janye idanuna nayi daga kanshi ina kallon Malam Ansar da ya cika ya batse.
"Hammah Khalil ka tafi ka duba halin da Hammah Mohan yake ciki kaji"
"Toh babu damuwa, duk yadda kace haka zamu yi, Baba sai an jima. Kai kuma be careful" ya saka kai ya fice daga d'akin.

"Baba kin gani ko? Hidima suke mishi waye ya sani ko wani abu ne yake shiga..."
Fisge ruwan hannu na, nayi tare da sauka a gadon na shiga tura shi har kofar dakin, ina kai shi gurin na ce mishi.
"Kar na kuma ganin ka a nan idan ba haka ba hmm"

      Na nuna mishi hanya tare da banke kofar..
"Mamoon,.kayi hakuri nasan babu dad'i."
"Baba kina ji yana zargina shi din waye shi? Meye na tsare mishi da yake zargina? Ina dalili zai saka Ni a gaba"

    "Kayi hakuri" haka tayi ta rarrashinsa, dakyar yayi hakuri, sannan ya shiga ban daki yayi alola da wanka ya fito, tare da gabatar da sallah.

Yana idarwa ya zauna yana kallon kayan da Dan Ba'are ya kawo shi.  Flast da ruwan zafi. Sai kayan ciye ciye.

    Haka na zauna na ci kadan sauran na turawa baba. Tana ci tana kallona.
"Me yasa meka?"
Kasa magana nayi tare da kasa kallonta.
"Ina tambayar ka? Kasan jikinka ba karfi ne dashi ba, kai asalima baka da nau'in karfin maza, don Allah ka  daina saka kanka cikin kasada kaji, ka daina cilla rayuwar ka cikin damuwa, malam Ansar yana da laifi gurin sakawa lallai sai kayi abu dole amma ka tab'a bibiyar me yasa yake maka haka? Sabida yana kaunarka gani yake baka cancanci zama a inda za a tab'a lafiyar ka ba. Don Allah karka tab'a min zuciya, wanda aka yi na shekaru sha ma bai warke ba, idan wani abu ya same ka ba zan tab'a yafewa kai na ba.[7/15, 4:04 PM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1099611906?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=B2xbg56NQ%2Bj7itiadIMLq5S6mXv9S%2FsKyYdkh0H8PJKgwqgLqD%2Fo961ZM5LierkVHLwx3qEwMnG%2BOkvdE6rc9D1tbKk2fSwjLb0oWove1cVKshUkIo7LVOxrft0MhTCk

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

_*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Domin samun labarin masu kayatarwa na Hausa danna Link din nan a sha sauraro lafiya....

BABI NA SHA BAKWAI.

    Kwalla ne suka cika min idanuna, na kalli Baba cikin kuka nace mata.
"Amma ko ma yayya ne dole yayi min uzuri, tunda nima mutum ne me rayuwa, taya zai dinga jifana da abinda ya fito bakin shi? Shin wannan adalci ne ko son Zuciya? Baki daya na kasa gane mishi bai da aiki sai gaya min maganar da ta fito bakin shi wallahi ki gaya mishi ya daina ko na kafta mishi rashin mutinci."

Na fada ina share kwallar da sune zubo min,
"Kayi hakuri"

Baki daya malam Ansar yaci uwar rena min hankali, dan yaga bana mishi magana ne wannan karon ya isa haka. Kuma zai ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login