Showing 141001 words to 144000 words out of 177131 words

Chapter 48 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

17156

cikin sauki batare da sunyima fatar mutum lahani ba😘 sister's duk ynd zanbaku lbrn soap dinnan yawuce nan domin zaku iya anfani da zallar sabulun batare da kunma bukaci cream ba🥰Amare gareku akwai hadinku na musamman wnd duk wacce tayi anfani dashi dawuya ango ya iyaganeta😁wani abunma saikungani da idanku👏gamasu nankarwa kuyi kokari kujaraba mg's domin Yana rageta sosai inkuncigaba da anfani da soap dinma saidai kuduba kuga Babushi😊duk wani prblm na skin kugwada soap dinnan Insha Allah zakuyi😂
Kayanmu bana bleaching bn organic ne nagyaranjiki zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkune anyisune d natural abubuwa
Soap price:3k
Maiso should chat:08062991548
Call 08064532391
Muna maraba damasu siyan daya kosari🙏

Be part of the glow team🤭say nooo to pimples, black spot,acne,sunburn,nd all skin prblms🙏

Mg's lv you guys fisabilillah🤭```
___________________________________
"Kai tsafe kari ke da wanin Allah, Ni kuma Alqur'an na rike da Allah ka yarda wani abu ya same ta, sai duniya sun ji mu. Gabanka da Mamman Nasir Aghali ya tsaya a can muku yarinya ta kuwa kashe ku zanyi daga kai har d'an ka "

Yana gama fadar haka ya juya tare da barin gidan, ina Hisham ya kwaso wannan masifar ai yasan waye Sama'ila Wodaadabe, wannan ai Bala'i ne da kanta, waye ya aike shi niman bala'i. Tabbas duk da yana son zama shugaban ƙasa, ya hakura dan yasan Sama'ila sanin hakika, yasan Waye shi. Ya kuma san dalilin da ya saka shi barin gidan amma bai zata Almamoon Yar shi ce ba, ina zai kai bala'i haka, idan ya kuma zuwa billahi azim sunan shi gawa, ko abinda dan shi yayi mishi bai kai kashedin da Uban Almamoon yayi mishi ba.

***
Niamey.

Yadda Hajiya Latifah ta hana kowa sukuni da firgice, yasa aka fara mata addu'o'in.

"Mohan ka dawo da ita wayyo Allah na, zasu kashe ni. Don Allah ya dawo da ita, wayyo Allah na."

    "Meye ya faru?"
"Alhaji nasa ya saki matar shi ce saboda Shegiya ce an samar da ita ta aure."

B'ata ta daina ganin abinda yake gani tare da kallon su.
"Meye ya faru?"
Gaura mata mari Primer minister yayi sai tayi tambul, kafin ta zauna da kyau..
"Alhaji marina kayi"
Cikin tsuma ya mike tare da watsata waje.
"Kije na yanke igiyar aurena baki daya akanki, Allah ya bi mishi hakkin shi na cutar da d'anki da kika yi"

Ya fada tare da juyawa tana ihu tana kome, kifa hannu Mohan ya a fuskar shi, kamar ba sadauki ba yana kuka me ban tausayi.

"Kayi hakuri, baka yi sa'ar uwa ta gari bane." Ya fada tare da shiga dakin shi ya kwanta, kowani dan adam yana da nashi ciwon mai illa ko mara illa, tashi ciwon ya zama tarihi na tsawon shekaru saba'in da wani abu, abinda mutane suka kasa fahimta akan wannan al'amarin shine rashin karban ƙaddara da uzuri. Shi yasa tafiyar Ƙaddara take rugu rugu da zukatar su.

  **
Kwana biyu ina kwance, ranar da na farka kallon Innah nayi, sannan na dauke kaina. Shigowar Dr Zainab ya sani ce mata.
"Mommy don Allah ki taimaka min ina son na tsarkake jikina"

     "Toh" haka ta taimaka min ta had'a min ruwan zafi, nayi wanka tare da gasa jikina, sannna na fito ina tafiya a hankali, sake mai dani tayi tana faɗin.
"Zaki lalace muje na guda ki da kyau."

     Haka ta dawo dani ban dakin ta dubani sannan ta zuba min ruwa me zafi da wasu magunguna ta sani na zauna a cikin shi. Hawaye ke zuba min, har na gama na fito, sannan ta had'a min shayi me kauri ina sha ina kuka, ina idarwa na wanke bakina, na zauna  na gabatar da sallar da ake bina sannan na daura da addu'o'in, wanda badan Ta rufe min bakina ba, Allah kadai yasan Irin Bala'in da zan janyo musu.

   "Wallahi addu'o'in da nayi ne, Ni na mishi Allah ya juyar da shi kanki, don Allah karki yi addu'a. Ƙaddara ce ta faɗa min amma wallahi na sha zuwa niman ki aka ce sun tafi dake?"

"Wacece ke?"
"Sai kin tambaya ne? Ai balagazar da ta kasa yarda da ƙaddara ce ta tafi bata kalli abinda ta haifa ba, ta bishi da mugayen fata gashi Allah ba azzalimin sarki bar ga kayan ki nan tunda ta bude ido ta san meye soyayya masifa da bala'i da rashin jin dadin rayuwa suka sakota a gaba, an ce miki Allah abokin wasan kine!"

"Ya isa haka Aminatu!" Abie ya daka mata tsawa.

"Uwata kiyi hakuri, gamu nan iyayen ki dukkan mu biyu, don Allah kiyi hakuri."

     Tashi nayi tare da bude kofar, na nuna musu hanya.
"Uwata!"
"Ismail Wodaadabe da Dr Zainab Mustapha Ja'e, zaku iya barin gurin nan ko sai na fita na bar asibitin?" Na fada ina kallon su.

    "Zamu fita! Amma kiyi hakuri kinji"
"Idan na shigar da karan ku zaku fadi abinda yayi muku kyau a gaban ka, Sai na rusa"

      Na taka gaban su, ina murmushi na cigaba da cewa.
"Sai na saka an muku tofin altsine, sai na hanaku jin dadin rayuwa, kuna kallon jama'a zaku zama abin kyama,  sai na saka ku kuka kamar yadda kuka jefa rayuwata. Daren amarcina daren da mijina ya amshi martabata, kuka ja min uwar shi ta kore ni ko wanke janabar jikina banyi ba. Wallahi Billahi azim sai kunyi kuka."

"Idan haka zai sanyaki farincikin na shirya taranki, amma karki tozarta mahaifiyar ki"

"Mahaifiyar wa? Ni wallahi na tsane ku, bani da Uwa Ni Shegiya ce ku fita bana son ganin ku" haka ayita ihu ina bala'i, tare da koran su. Suka fita baki daya.

Idan nace muku bani da lafiya zaku ga kamar karya ce, amma tabbas na haukace. Haka na rubuta karar da nake, na Abie da Mommy, gashi kullum ƙarin ruwa ke min sai da nayi sati biyu. Kafin na uku aka sallame ni,  gidana da yake nan Maradin ba nufa, kuma baki musu magana, haka kullum zasu zo. Amma bana kula su.

Ranar Asabar na nufi Niamey, tare da maka su kotu, na kafe lallai sai an yi shara'ar, kuma na ce Ni zan tsayawa kaina.  A hankali maganar ya shiga yaɗuwa kamar wutar daji, Surukar shugaban ƙasa tayi karan iyayenta sakamakon samarda ita ta hanyar da bai dace ba, haka yayi sanadin da Uwar MG Mohan tasa ya sake ta a daren Auren su. Sannan na samu goyan bayan wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam, tare da goyan bayan yan siyasa,  ta kowani gefe an sami taimakon da ya dace kuma sun tsaya min, wannan ya kara min kwarin gwiwa.

Shi kan shi Mohan yana can bai da lafiya, bai san wainar da ake toyawa ba, haka na zauna a niamey har ranar da za a saurari karan, Abie a ranar ya ajiye aikin shi, ya shiga kotun.  Ina zaune kaina sunkuye, labarin ya zama abin yayyatawa, ko ina na duniya so ake aga  shari'ar.

     A hankali kowa shigo, kafin aka fara gabatar da kara, kirana akayi, bani da lafiya amma dan bakin naci haka ina tashi ina niman faduwa. Na nufi inda zan tsaya, koda na nufi gurin kifa  kaina nayi.

Ina jan numfashi, gashi har microphone aka saka mana sabida mutanen da sukayi dandali na son jin yadda zata kaya.

***
Da sauri ya shiga dakin tare da cilla mishi jaridar.
"Matarka tayi karar iyayen ta, a kasar jaridar ka duba"
an b'ankad'o sirrin Primer minister ashe ba dan Alhaji Muhammad Aghali bane shege ne.

Mikewa yayi tare da ɗaukar jaridar, ya nufi Part din Ammyn.
Ya ajiye mata.
"Mijinki abin alfaharinki, ya sake ki amma mun roki arzikin ya zauna dake, gashi nan an b'ankad'o sirrin shi, kin b'ankad'o sirrin yarinyar da babu ruwanta, Allah ya bankado namu sirrin, shi yasa hausawa suka ce Kunyar mara kunya asara ce. Dole ya ajiye mulkin domin wannan kadai ya ishe shi zuciyar shi ta buga."

Yana fadar haka ya nufi inda motar shi take, ya shiga Office din Abbu ya nufa, cikin kwanciyar hankali ya same shi suna tattauwana ne, da yan jaridu, kuma ya tabbatar da cewa adawa ake dashi shi yasa ake son bata gwamnatin shi. Bayan tafiyar su ya kalli Mohan.
"Me ake ciki?"
"Kome ya lalace"
"A'a mun kira Allah, kuma ya amsa mana, kaje ka dakatar da Yarinyar."

"Taya Abbu?"
"Tana sonka! Kai namiji ne maza tashi kaje, ko bamu yi aikin gwamnati ba zamu iya rike wasu har da jikokin mu, dan haka zan ajiye aikin da fatan zaka ajiye aikin soja"

Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Insha Allah"

.....daga nan yakira Khalil suka nufi kotun, shima kuma primer minister ya kira a dakatar da shari'ar, amma fir Maimunari taki, ta kasa magana sai haki ga hawaye da yake zuba mata,. Duk me Imani idan ya ga yadda take son magana amma ta kasa, sai dukar kirjinta take, tana kuka.

Daidai shigowar Mohan.
"Ya Mai Shari'a, ka tambaye su Meye nayi musu haka suka rusa min tushe na!"

Kafin ta kara sani kalma ya isa gabanta.
"Maimunari Isma'il, primer minister ya kira yace wannan matsalar ta cikin gida ce, dan haka kotu ya maida ku gida ku sulhunta a can."

"Wannan ba adalci bane, wannan son kai ne.wato dan ban da kome.." bakin shi naji a saman nawa, ya d'ago ni cak yana sumbatar bakina, har ya fito dani daga koyun daukar mu ake, yana zuwa gurin motocin da aka ajiye ya sauke ni, dukar shi nayi tayi.
"Ina ruwanka. Meye matsalarka sani Ni, ka kyale ni." Na juya tare da nufar inda motar Ansar yake na shiga tare da cewa.
"Mu bar nan."

Haka ya fita Mohan ya rufa mana baya, sai da muka kayi tafiya me nisa, sannan na nace.
"Sauke ni" gefen hanya ya tsaya na fita tare da nufar cikin sahara babu takalmi, ihu nake ihu nake tare da zama akan kasar ina dukar kasar na rasa meye zanyi, yana tsaye shi kanshi sai da yai danasanin kuntatta mata. Yyi amfani da sirrin ta da yaji a bakin Innah ya kuwa Hajiya Latifah, bai zata idan kome ya fito zata cutar da kanta ba haka dai yanzun.

A haukace ya yi parking sannan ya fita, tare da nufar inda nake.

Yana zuwa ya rungume ni, kuka nake yana shafa bayana.
"Kiyi hakuri"
"Hammah Mohan me yasa?"
"Soyayyar mu daga Allah ne, wallahi ban ji kome ba akan ki, sau soyayyar ki da yake kara samun matsuguni. Raina,"

"Hammah na, zan mutu"

"A'a bazaki mutu ba, sai dai mu mutu a tare." Kuka nake na rasa meke min dad'i, a hankali ya d'aga ni, daukata yayi cak ya kai ni bayan motar ya shiga ya zauna tare da daura ni a jikin shi.

"Khalil muje"

Haka muka tafi tare da barin Ansar a gurin, kasa aiwatar da kome yayi, haka yabi motar da ido. Kafin ya shiga nashi yana me barin gurin, shafa wuyar shi tayi yana jin abinda ya rike mishi wuyar har yau yana damun.

   ** Gidan shi da babu wanda ya san da shi daga Ni dai shi sai Khalil muka san da zaman gidan, ya kai ni, Khalil yana ajiye mu yayi tafiyar shi. Shi kuma ya wuce dani sama, inda dakin shi yake, tunda ya kwantar dani a gadon bana iya kome daga amai sai barcin wahala, kuma shi yake jinyata. Ranar da na cika kwana uku a gidan ya dauko min Mommy, ina ganinta na fara ƙoƙarin Mik'ewa.
"Karki matso kusa dani, karki zo inda nake, wato ka dauko min ita ko? Hmm shi kenan." Na fara ƙoƙarin tashi, haka suka min allura tare da ƙarin ruwa, tana kallon yadda na zabge, sai wani bau da nayi tare da cikar da nayi daga Kirjina, ni kaina nasan na kara girma ta kirjina, tunda ta saka min ruwan na ji dama dama,  a hankali na cigaba da samun sauki. Kwana na goma sha bakwai, ranar ya fita na bar gidan tare da ajiye mishi wasika.

    ***
Daga nan airport na wuce, na nufi Maradi, na hada kome nawa, sannan na tafi makarantar mu, dakyar shugaban makarantar ya bani transfer, bayan na loda mishi kudi masu yawa, sannan na bi motar dare zuwa Damagaram, na kwashi kayana da takarduna musu muhimmancin,  na fito na nime motar da zata shiga Libya.

       Dakyar na samu sannan yana tashi muka dauki hanya, na bar kome na bar kowa nawa, na mike tafiyar ƙaddara, wanda tunda ba fara ban tsaya ba har yau, na manta rabona da farin ciki. Na manta rabona da nayi dariya, haka kome nawa ya lalace, ina ji ina gani sun lalata min gobe na.

     ***
Yana dawowa gida ya shiga dakin.
Akan pillow ya sami yar takardan.
*Nagode sosai! Sai dai nasan dama kayi min nisa kuma karambani ne irin nawa yasa Ni fadawa SOYAYYA da mai kyakyawan tushe kayi hakuri na tafi Allah ya had'a mu a darulsalam matar ka Har abada Maimunari*


Kaina na mugun ciwo wallahi...
#Mai_Dambu
[8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1114000208?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=9erIrydatIuPkJseZal69xUkMstLsWx8GyFdlSLeJfq8JZ7%2BWyAuXyBi3TFONZWvmJKNlkO3cngr4M2Sk%2BLQ9DhqVJ2mn36fvlalGIeTBV4qaMAzYIkNfoxokz2fxpjv
🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA HAMSIN DA BAKWAI.

HMMM NIDAI YAR KALLO CE!


Zuɓewa yayi akan gwiwar shi, ya rasa meke mishi dad'i baki daya, wayar shi ya ciro. Ya shiga gurin kira, ya kira Abie.
"Abie ta tafi" ya faɗa kamar yaro karami. "Kuka zaka yi?" Ya tambaye shi yana murmushi,
"Karka damu, zata dawo Insha Allah ba zata tsallake boda ba, zata dawo."

"Abie Mommy tace tana da juna biyu! Abie rayuwar su da abincin ki ta!"
"Karka damu zata dawo, baka yarda dani bane?"
"Na yarda da kai"
"Kwanta kayi barci zata dawo Insha Allah. Sai dai idan ta dawo ka rabu da ita kayi watsi da ita"

"Ba zan iya ba"
"Zaka iya, domin zata cutar da kai da abinda soyayyarta. Ka cigaba da hakuri Mahaifinka ma kayi ta bashi hakuri. Itama Mahaifiyarka ka bata hakuri."

      "Toh" ya faɗa, Abie ne ya kashe wayar ma.
*
Bayan sun gama wayar yayo alola tare da ɗaukar Alqur'ani, addu'o'in kawai ya shiga yi yana ambaton sunanta. Bai tashi ba zai da yaji a ranshi Allah zai amsa addu'o'in shi sannan ya mike tare da turawa Dr Zainab sako.
*_Ina kara baki hakuri don Allah ki taimaka mana da addu'a ke uwa ce Maimunari tana bukatar addu'o'in ki._*

  Sannan ya mike tare da fitowa falo yana labarta musu tafiyar Maimunari.

    ***
Tafiya muka yi bana kare ba, dab zamu fita bodin Nijar, mu shiga hanyar Libya, hukumar shige da ficce suka kamani, nayi juyin duniyar nan amma fir suka ki sake ni, karshe wayata suka amsa suka duba Number Hammah Mohan.

  Aka kira shi. Kamar a mafarki ya ji kiran dan haka bai b'ata lokaci ba, ya kira Dan Ba'are, aka yi magana da hukumar sojojin sama, aka bada jirgi. Har bakin bodar yazo daukata, sai da yayi kome sannan ya shiga inda aka ajiye ni, na kifa kaina da hannuna.
"Tashi muje" mik'ewa nayi a hankali, ya dauki jakar kayana ya fita dashi. A hankali naga yana tafiya. Da gudu na bishi tare da rungume shi ina kuka. Tsayawa yayi yana sauke ajiyar zuciya. Shi kanshi dan Ba'are goge kwallar da yake zuba mishi yayi.

      Muna shiga cikin jirgin yayi mishi magana da buzanci.
"Ka dauki matar ka ku bar kasr nan."
"Taya?"
"Zaka iya mana"
"Zan bar Abbu cikin kad'aici ne"
"Toh ai Ammyn tana kan bakanta sai ka auri yar masu kudi."

"Toh nagode! Amma ka tattauna da Abbu duk yadda yace"
Haka suka yinta hira ina jikin shi a kwance, ina shaƙar kamshi turaren shi, har muka isa Niamey.

     A hankali ya dauke ni, muka wuce gidan Abie, Khalil na parking ya wuce dani dakin da ya tab'a kai ni, lokacin karfe biyu na rana, haka ya kwantar dani. A hankali ya janye rigar jikina yana kallon shafaffen cikina zuwa maran bai ga alamar kome ba, babu alamar cikin fa. Maida kanshi yayi kirjina da ya cika. Murmushi yayi yana shafa kirjin, su kam ya yarda dan sun dauke kome, har wani kumbura suka yi, addu'o'in yayi mata tare da shafe ta, sannan ya fito ya sami Abie.

Mika mishi fura da nono yayi, a hankali yake sha. Shigowar Khalil shima Abie ya mika mishi.
"Abie zama haka babu dad'i fa? Kayi aure mana"
"Hmm"
"Ko Mommyn mu zamu maka bikonta."

   "A'a Nagode"
Duk yadda suka so amma fir yaki, haka suka gama suka bar gidan.
.... Karfe biyar na yammacin na farka sannan na nufi ban daki nayi wanka, sannan na fita na nayi sallah, ina sallah naji shigowar shi. Bayan na idar na kulle kofar,  haka nayi ta zaman daki ga yunwa ga zazzaɓin da ana magarib nake fara shi dai gari ya waye, nake samun sauki.

  Cikin dare na farka nayi ta buga kofar dakin, na kasa bude kofar, karshe balle kofar kayi, suka kai ni asibiti. Anan na kwana.

***
Washi gari.
Ya shiga gaishe da Hajiya Latifah, tana zaune. Abun duniya ya dame ta, sunkuyar da kai yayi sannan yace mata.
"Ammyn ki yafe min"
"Zan yafe maka amma sai ka min alƙawarin ba zaka tab'a dawo da Maimunari rayuwar ka ba, idan kayi min haka wallahi na yafe maka."

       Da sauri ya d'ago kai yana kallonta, kafin ya sunkuyar da kanshi.
"Naji"
"Alhamdulillahi! Allah yayi maka Albarka ka tafi Maiduguri akwai Yar Kawata ka nimo aurenta."
"Toh"
Ya fada mata, haka ya fita ya nufi shashin mahaifin shi ya gaya mishi, yadda suka yi.
"Toh Allah ya kyauta"
"Amin amma kafin nace ina son zuwa naga Nahnah naji ance min bata da lafiya."

"Karka sake ka gaya mata kome ka barta Allah ya bata lafiya."
"Toh insha Allah."

    Haka ya shirya ya tafi Agadaz babu shiri. Duk da ya samu jikinta da sauki, amma sai da ta mishi maganar Maimunari, yake yayi mata.
"Zata zo Insha Allah"
"Akwai labarin da zan baka, naji labarin abinda ya sami Mamman Nasir, gaskiya ce babu bincika karya ba. Amma kuma ai Nasir ya rike shi da Amana.

Shekaru saba'in da wani abu baya.
Duk wanda ya xaga Afrika yasan bayan wasu kabilun babu kabilar da ta kai Fulani yaɗuwa a nahiyar Afirka"

Ajiyar zuciya ta sauke nauyin kafin tace mishi.
"Karka damu, idan ka shirya kazo kai da iyayenka ka iyayen yarinya, zamu yi magana da kai. Akwai abinda na gani a tattare da Yarinyar. Kayi min fatar na samu lafiya zan gaya maka yadda kome yake har ita yarinyar ta san waye Mahaifinka, sannan itama uwarka ta san waye Mahaifinka."

Ba haka yaso ba, amma haka ya bar gidan bayan ya cika ta da Alkhairi, sannan tayi mishi addu'o'in ya tafi.

***
Bayan wata uku.
Cikina ya shiga na huɗu, ina kwance bana shiga harkan su, amma yau da ya kasance juma'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login