Showing 66001 words to 69000 words out of 177131 words

Chapter 23 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

14801

zaka tausaya min balle cikina ba zai iya dauke abincin nan baki daya ba,"

Da wutsiyar ido ya kalle ni, tab'e baki yayi sannan yace.
"Lokacin da kake min rashin daraja ka manta ai?" Da sauri na kalle shi.
"Amma ai ban tab'a dura maka abinci ba!" Na tambaye shi ina zare ido,
"Ci domin ina da abun yi" babu musu na kalli Chinese bomb din da yake gurin dakyar na had'iye yawun bakina, tun ba aja min kafar ba, na Fahimci akwai dirama.

Tab'a abincin nayi tare da turawa ina jin faduwar gaba.
"Meye alaƙar ku da wannan gayen?"
Da sauri na kalle shi tare da cewa.
"Wallahi ban tab'a ganin shi ba sai d'azun kuma na rantse maka da Allah ban san."
"Bashi ba wanda ya ce zai maka aikin ka dawo mace?"

Ji nayi wani abu ya tsaya min a wuya wallahi na manta dashi baki daya, sosa kai nayi tare da cewa.
"Malamina ne kuma kamar Dan uwana yake, bayan haka ina girmama shi."
"Me yasa ya dage sai yayi maka aiki?"
Sunkuyar da kai nayi, ina kallon yadda yake hada maganin shi. Har ya dawo gabana, tare da d'ago kai yana kallona, kafin yace.
"Ina jiranka?"
Ya fada bayan ya rike kafar da hannun shi. Ya manna min ƙanƙara har cikin tsakiyar kaina naji sanyin.
"Sabida yana sona" cak ya tsaya tare da kura min ido,
"Ya tab'a rungume ka?" Wani irin hautsinewa cikina yayi ina kallon shi. Fuskar shi tayi jajjur, ajiye kankaran yayi tare da kama kafar ya wani irin fisgar shi sai da na fasa kara, tare da hada hannuna biyu na dafe kafad'ar shi.
"Idan ina magana na tsani ayi banza dani, ya rungume ka?"

"Wayyo Allah na, eh sau sau ...sau.." na kasa fada ina jikin ilahirin jikina yana b'ari, ga hawayen da yake zuba min daga ina nuna.

"Kasan waye kai?" Ya kuma jan kafar baki daya na fado kanshi..... (Yo Ni a ganina ba a fara Chakwakiyya ba, amma kunce an fara wasan 🤔 🙄 Wallahi indai da gaske zanyi rubutun nan ban yanke shi ba, Billahi azim ba a fara kome ba, wasan ba a fara ba don Allah mu lallab'a juna domin ba ayi kome ba kuma ba a fara ba..... Keep comments And Vote ni kuma na muku typing gaba gad'i 🤫 domin an hanani ambaton Rashin daraja ba wai na daina bane kawai idan ya motsa🙄🤣 Alqur'an zan yi kuma zan kafta...
#Mai_Dambu....
[7/25, 9:01 PM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1105333540?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=wFWlz0rB5vLnDHBBsgwmy16HrEu27aKV%2BLrvZEc4HZOQhPxrhzXfAzebs68cEFXa4%2BKxqKR8E%2F8iKJMh4QpPwlUHdawDA%2FOu0EVnwQVQ5hDmkOaB8%2Bq4IYKg9xcPDk7D

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ASHIRIN DA BIYAR.

Kifa kaina nayi a kafadar shi ina kuka Sosai, kafar yana hannun shi. Kasa aikata kome yayi ya d'ago kaina.
"Kai ba irin sauran yara bane, kome kashin kuskure ya faru da kai babban tashin hankali ne, rayuwarka abar dubawa ce, ina bukatar ganin ka zama wani abu, dan haka duk dan iskan da ya kusanci inda kake sai na kashe shi." Ya kuma murɗa kafar sai da yayi kara nima na sauke ajiyar zuciya tare da kifa kai na a kafadar shi, dif na dauke wuta.

       A hankali ya d'ago kai na yana kallon yadda kwalla yake sauka ta gefen idanuna,  mik'ewa yayi ya kwantar da ni, sannan ya koma hada sauran maganin ya shafa min, tare da gyara min kwanciya na, a kujeran ya shiga dakin ya dauko duvet ya lullube ni sannan ya rage hasken dakin ya zauna tare da mai da hankalinsa kan aikin da yake yana waya da Dan ba'arensa wanda kusan rabin wayar bakar magana sukewa juna.
"Ina Mamoon?"
Juyawa yayi ya kalli yadda yayi wani lufff a cikin duvet, sai sauke ajiyar zuciya yaƙe.

    "Yana barci"
"Ok amma kana kula dashi kuwa? Kuma idan ya tashi ka bashi wayar mu gaisa mana" 
Datse wayar yayi tare da kashewa baki daya, yana jan tsaki,

        Kasa aikin da yake yi, yayi ya cigaba da kallon Laptop din shi, yana ma rasa me zai yi, mik'ewa yayi tare da mika, sannan ya koma saman kujeran da yake fuskar Mamoon ya kwanta.
..
Mafarkin mutumin nan nake, da ya kamani d'azun sai kuka nake ina kiran "Hammah na zo tafi dani" na fada ina kuka, dake barcin shi bayi nauyi ba, bude idanun shi yayi tare da tashi yana kallon shi, a hankali ya mike tare da zuwa gaban shi ya zauna a ƙasa, a hankali bakin shi yake karato ayatul kursiyu, yana tofa mishi a fuska, tare da shafa gashin kanshi, har yaji ya fara ajiyar zuciya.

          A hankali ya mike bayan ya koma barcin, rike hannun shi yayi tare da gyara kwanciyar shi, ya cusa hannun kasan kanshi. Tsayawa yayi yana kallon yadda yake marairaice fuska yake. Saukar numfashin sa yake ji tare da jin wani irin yanayi yana kara tab'a gangan jikin shi.  Da sauri ya zame hannun shi yana kallon shi.
   Kasa komawa kwanciya yayi ya nufi ban daki ya sakarwa kanshi ruwa, yana me dafa bangon ban ɗakin.
*Anya Yaron nan namiji ne? Anya mata maza ne? Mata maza ne mana baka ga akwai gashin baki ba? Mtseew!*  Yaja tsaki tare da kallon hannun shi, a hankali ruwan yake ratsa shi har ya samu nutsuwa sannan ya fito daure da towel, ya kwanta a gadon tare da rub da ciki, sabida yadda yake jin babu dad'i.

   A yanzun ya kai matakin da ya dace ya ajiye matar auren shi da iyalinsa tunda shi ba yaro bane, tunda ya haura talatin da bakwai, ya wuce a kira shi da saurayi sai dai tuzuru. Toh wacece zata dace dashi? Wacce mace ce zata iya jure bakin halin shi ba Sannun ba Nagode.

      Dakyar barci yayi gaba dashi.
***
Washi gari.

A hankali na mike tare da nufar ban daki nayi wanka da alola na fito na shirya, ina gamawa  yana buga kofar dakin. Fitowa nayi tare da kallon shi.
"Ina kwana Hammah"  share ni yayi tare da juya min baya na nufi falon. Rufe kofar nayi tare da gabatar da sallah, sannan na fito.
"Ka shirya?" Gyada mishi kai nayi, sannan kuma mai da hankali kamar bai da abin fada kafin yace min.
"Ga abinci" wuce shi nayi na zauna na fara cin abincin bayan ya kalli kafar. Ban tab'a kawo zai jifo min tambayar da ta sani kusan kwarewa ba, sai da na furza da shayin bakina.
"Kana son Cigaba da zama da jinsi biyu ne ko kana son tsayuwa akan jinsi daya?"
    Had'iye yawu nayi ina goge bakina. Ganin naki bashi amsa ya sashi mik'ewa, tare da nufar dakin shi ya fito da kayan shi. Yana kallon agogo kou bai gaya min ba nasan ya shirya.

   Nima da sauri na tashi ina tafiya ina dingishi. Kallon agogon yayi sannan ya ajiye kan shi ya nufi dakin ya dauko min kome sannan ya fita da shi, kallon shi nake kawai, can sai gashi sun kuma dawowa da wani mutum ya kwashi kayana shi kuma ya kalle ni kad'an yana me takowa gaba na, a tsuguna ya saka min takalmina, sannan ya dauke ni can, ta mike hana na lumshe idanuna. Shi kan shi wani abu yake ji a ranshi, idan yana tare da Yaron shi kuma ba wai dan Iskanci ba a'a kawai yana yin su kawai kamar sunyi raja'a akan abu daya ne, shi yasa yake ririta al'amarin yaron yake kuma kokarin tsayawa yaron, Har waje haka muka yi ta ratsa mutane. Har gurin motar da zata kai mu jidda, lokacin da zai sauke ni ne wani karamin abu me matuƙar tasiri. Domin a hankali yake sauke,  yana isowa daidai fuskar shi ee shiga niman nawa, cikin wani irin yanayi, ya zuba min idanun shi cikin nawa, ina iya hango wasu sirrika na shi amma babu damar fadar su, ina ganin wani abu na musamman a cikin ƙwayar idanun shi, amma karfin dakiya irinta zaratan maza ya sashi boye min haka, hancina ne ya gogi nashi, bakin shi ya sauka akan goshina. Wani irin yarrr naji kamar tsutsa na tafiya a jikina, shi kan sa wani abu yaji suna mishi yawo,bai san lokacin da ya sauke ni ba, tare da bude min kofar motar na shiga, ya koma gaban motar ya zauna.

    Tunda muka nufi Jidda da motar, yana waya da wani har muka isa garin kusan tafiya me dan tsawo, airport muka nufa, anan muka hadu da Abeed, kallona yayi musamman yadda Mohan yake kaf kaf dani.
"Yaushe ka fara bin maza?" Kallon juna suka yi kafin yace mishi.
"Shine yaron da na gaya maka na kawo shi."
"Kai haba na zata lover kane." Daure fuska yayi sakamakon ganin Abeed yana mikomin hannu, yasan larabawa da fitina yanzun sai ya iya makale mishi akan Yaron shi. Dan hka ya buge mishi hannu yana faɗin.
"Hannun shi yana ciwo" ya faɗa tare da ɗaukata zuwa cikin airport din, shi kuma Abeed yana dauke da kayan mu, sai zuba yake, shi kuwa yana jin shi dan har ya gundura da halin shi.

      Haka suka zauna yayi ta mana surutu yana haɗawa dani, nan kuwa Hammah Mohan harara na yake tare da dauke kai, har lokacin tashin mu yayi.

"Mohan gaskiya ina son Yaron nan naka" ya faɗa lokacin da yaga Hammah ya dauke ni zuwa inda ake duba kome har kayan mu, ana gama dubawa muka wuce, ya kai ni ya ajiye ni sannan ya fito suka kuma sallama.

"Mohan baka ce min kome ba, kasan an Cigaba zaka iya mai da namiji mace please ka bani Yaron wallahi ba zaka sami matsala da Ni ba". Murmushi yayi mishi sannan yace mishi.
"Akwai lokaci" daga haka ya juya tare da komawa cikin jirgin yana yaba girman haukar Abeed. Tab'e baki yayi bayan yazo zama ya hango wani dan kasar Philippines  a kusa dani, wani daure fuska yayi tare da mikar da mutumin. Yana me zabga mishi harara, tare da nuna mishi hanya.

     Zama yayi kusa dani, ni kuma na mai da kaina window, ina kallon yadda jirgin zai tashi, cewa aka yi kowa yasa belt, a hankali ya sunkuya kamar zai hade bakin mu, kafin yaja belt din ya saka min.
"Wato idan nace bana son abu ba zaka kiyayye ba?" Kallon shi nayi tare da sunkuyar da kaina. Huci yake tare da mai da kallon shi kan magazine din da aka ajiye Mishi.

     Ina jin jirgin zai tashi ban san lokacin da na kai mishi cafka ba, na boye fuskana a gefen damtsen hannun shi, shafa bayana yake tare da cewa.
"Nutsu tashi zai yi!" Jirgin na daidaita a sama, na mike a jikin shi.
"Matsoraci kaji kunya." Tura baki nayi ina cewa.
"Toh meye laifina?" Dan na razana ya kama ce min matsoraci.
     ----
Karfe biyu na asuba muka isa dubai, anan ya jani har kasuwa zamani muka yi sayayya, kayan da yayi ta dauka min sune suka bani mamaki.
"Ko baka sone?"
"Allah ya kara budi" na fada ina amsar kayan, wani wando ya miko min crazy pant, da wata ƙatuwar rigar da nake son saka irin su, amsa nayi ina murmushin jin dadi, sai da na d'aga naga wandona na mata ne, kallon shi nayi.
"Ba zan maka dole kasancewa jinsin mata ba, amma wannan wandon yayi min kyau ne, ka amshe shi a kyautana"

      Murmushi nayi tare da sunkuyar da kaina, ina gyara zaman gashin kaina.
"Amma meye amfanin barin gashin nan?" D'ago kai nayi ina kallon shi.
"Muje can a yanke maka " ya faɗa tare kallon yadda na firgita.
"Tsoro kake ji?" Had'iye yawun bakina nayi tare da marairaice fuska nace mishi.
"Iyayena zasu min faɗa" murmushi yayi sannan yace min.
"Dama kana tsoron iyayen ka wancan banzan ya dake ka? Sai na kareraya mishi kafa wallahi." A tsora ce na ware idanuna, daga min gira yayi tare da cewa.
"Meye?"
"Babu" na fada ina girgiza kai,  wato shi bai damu da abin da zai ja min ba, kawai yayi hukunci kawai. Kamar yasan ina tunanin da nake kawai ya tako gabana.
"Kai na musamman ne, ba yau ba na gaya maka kai kyauta ne na musamman, dan haka dole na gaya maka"

   Kallon shi nake kamar wanda aka sanya mishi battery sai magana yake kamar bashi ba.
"Rufe bakin" da sauri na rufe bakin nayi da hannuna.
"Muje" ya faɗa.

Idanuna ne ya sauka akan tv ana nuna wani jirgin kasa, wanda yake bin karkashin ruwa da mutane, dafa shi nayi ina nuna mishi tv. Underground railroad.
"Hammah Mohan dama an a Dubai ne kawai akwai wannan jirgin" kallona yayi sannan yace min.
"Akwai a china, akwai a Singapore, akwai a Japan. Akwai wani dakin da yake bujr Arab dakin yana karkashin kasa ne kuma kina hango kifi mana ko zamu d'aga tafiyar ne muje ka gani" wani ware bakina nayi ina dariya.
"Zan je ko sau daya ne"

    Ja na yayi tare da biyan kudin kaf, sannan ya juya muka fita, wato baki daya rayuwata a Damagaram da Maradi ya kare kai ko Niamey ban tab'a zuwa ba, sai gani a karkashin ruwa ina kallon yadda jirgin kasa yake shiga cikin ruwa, ga kifi yana ta yawo. Cikin wani irin farin cikin nake kallon jirgin tare da kallon shi.
"Hammah ka tab'a zuwa nan? Kai wajen da ban sha'awa yake." Na fada ina hada hannuna, murmushi yayi tare da sako kanshi kafadana.
"Ya burge ka?" Gyada mishi kai nayi kamar wacce aka zabure ni.
"Hammah Mohan! Kasan me gaskiya garin nan yayi kyau kane kar na koma gida," na daura hannuna a  kafad'ar shi karku ga yadda na kara har da dagelgel.

      "Hmm" ya nuna min kafad'ar shi,
"Ai kayi hakuri" na fada ina kallon wata irin kifi me rabi mutum rabi kifi.
"Wayyo Allah, Hammah Mohan? Wannan shine , mermaid?" Jan bakina yayi tare da nuna min wani kifi shima kato, yana zuwa gurin Meemaid din suna watsewa, dariya na saka ina  dawowa ta daya window.
"Hammah sun gudu sun ga babban su." Na fada ina wani irin dariya, kukan da cikina yayi ne na kalle shi kamar zan yi kuka nace.
"Hammah cikina yana jin yunwa?" Na fada a shagwaɓe, murmushi yayi sannan yace min.
"FwpMuje ayi sallah sai a karya" nan ma wancan hotel din ya kai ni, lokacin da ya biya kudin dakin sai da na tambaye shi.
"Hammah nawa kudin dakin? Kuma naji kace wuni daya ne?" Na fada ina kallon shi.
"Kudin ba yawa sai dai zai iya daukar nauyin abincin wata iyali na tsawon wata uku." Ya fada tare da nufar hanyar da zai kai mu kofar elevator......
_Ban zata zan gama da wuri ba wallahi na zata zan kai karfe goma na dare Alhamdulillahi Ubangiji Nagode maka Sosai kuyi hakuri da rashin editing, Insha Allah gobe zai iya kaiwa karfe biyu na rana kafin nayi Posting Insha Allah sabida na goben ne na baku yau da daddare_
Karku manta sharing 😘👏
#Mai_Dambu....
[7/26, 11:18 AM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1105787433?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=Ja9wL7QqFEErjgU2q%2BSBeLU5C48TPF6alEcOeA68MXjwsxZkfzIB%2B1qokdEbQ55KLRjZ93ztdNSly6DP588o1P6bkl7taWFOl0ee6BP9d%2B%2F0Yz5SwmP2bjWvOwHDMKnB

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ASHIRIN DA SHIDA.

Shan gaban shi nayi ina kallon fuskar shi.
"Kace zai dauki tsawon watanin yana ciyar da wasu iyalin?" Tura ni cikin elevetor yayi yana me faɗin.
"Na gaji da tambayoyin, ba sai ka nuna min Dalibin lauya ne." Ya fada min tare da tsayuwa yana kallon gaban kofar,  shiru nayi kafin nace mishi.
"Kasan me? Kawai garin nan ya hadu, amma ya abin yake komawa ƙasa?" Na fada ina kallon shi, gajiya yayi da tambayar toshe min baƙi yayi tare da kallon yadda nake zare ido ina ƙoƙarin sai nayi magana.

      Haka muka shiga dakin tare da kallon ko ina, dakyar na shiga ban dakin nayi wanka da alola bayan na fito na samu baya d'akin amma ga kayana akan gadon dauka nayi na shafa mai, tare da saka kayan sannan na fito ina saka takalmi, kallon shi nayi domin yayi kyau cikin riga da wando sai gyara gashin da yayi, kallon shi nayi sannan nace mishi.
"Kayi kyau, amma kuma kayan nan ya mai da kai wani babba dayawa, ka saka kananun kaya zaka fi ka kyau"
Na fada ina kallon shi, bai kula ni  ba sai aikin gaban shi yaƙe.
"Hammah, zo nan" na kira shi ina   a kujeran sa yake falon. Daure fuska na nayi, sannan na kuma kallon shi, na mishi alama yazo da hannu na.

   Shi kan shi mamaki ya gama kama shi abinda yaron nan ke mishi wallahi yana wuce gona da iri, bai musu ba. Domin ya lura Yaron na jin farin ciki ne dan haka ya nufi gurin shi cikin sauki da salama, ya tsaya yana kallon shi.
"Kawo kunnen ka!" Wallahi a tunanin shi abin arziki zai gaya mishi dan haka ya sunkuya tare da kallon bakin shi.
"Kunne nace" ya gaya mishi haka, mika mishi kunne yayi. Sai da ya gama ja mishi kunne kafin yace mishi.
"Wani ya taba gaya maka kai kyakyawa ne? Toh wallahi kai kyakyawa ne gaka kamar dan dambe gingimemme da kai kamar tsohuwar bishiyar kuka." Wato haka nayi ta yabon shi ina kuma rage mishi wani abun. Kallon fuskana yayi tare da cewa.

"Da alamu yunwa ce ta saka zuba kamar tsohuwar rediyo?" Had'iye yawu nayi tare da shafa cikina, ina kallon shi.
"Idan ka taimaki dan cikina Allah zai gina maka katon gida a aljanna domin yunwa nake ji, kuma Ni kamar mareniya ce" na fada ina had'iye yawun yunwa.

  Jan hannuna yayi muka fita, muna fita ya hango wani mutum da alama shima dan Afrika ne, wani irin juyar dani yayi tare da had'a ni da bango, kafin kaina ya kai bango ya kai hannun shi, tare da daidaita tsayin shi, ya kai fuskar shi kan nawa, kamar zai sumbaci bakina, zato idanu nayi ina kallon shi. Jikinsa ya matse nawa numfashin sa yana dukar nawa, kwayar idanun shi yana cikin nawa, baki daya na kasa cire idanuna cikin nashi mamaki yake bani yadda ya iya juyar dani cikin zafin nama, *Ka manta shi din soja ne* kuma haka ne fa? . Haka mutumin yazo ya wuce da wata baturiya a gefen shi. Sai da ya tabbatar ya wuce sannan ya d'ago ni.
A tsora ce nake kallon shi jikina yana kara sanyi. Kuma na kasa magana, baki daya kamar  wacce baya cinye min bakina.
"Rediyo me jini ya kai yi shiru?" Tura baki nayi ina me Cigaba da tafiya.
"Abokina babu magana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login