Showing 123001 words to 126000 words out of 177131 words
supplie de m'épouser !"
(Ina son ki sosai! Ina kaunarki ki, zan so ki da dukkan numfashina, ba zan taba barin ki kiyi kuka ba da dukkan karfina, zan kare ki da dukkan rayuwata. Maimoon, zan ba ririta Al'amarin ki fiye da kowa, Zan yi dariya da dariyar ki, zan yi kuka da kukan ki! ni ina son ki da dukkan rayuwata! Ina son ki da dukkan zuciyata, Maimunari ina son ki ina rokon ki da ki aure ni!). Fasali yaja tare da kallon mahaifiyar shi, sannan ya taka har gaban ta, yace Mata.
"Ammyn idan ina tare dake Mantawa nake da ita, idan ina tare da ita tunawa nake dake, sabida babu mace da ta cancanci na d'aga darajarta sama dake," sannan na cigaba da cewa cikin Faransa. Tare da komawa gaban Maimunari.
"J'élèverai votre dignité et votre valeur devant tout le monde, j'élèverai votre cause devant tout le monde ! je vous respecterai je respecte votre famille aussi longtemps que vous restez avec moi!"
(Zan d'aga darajar ki da kimar ki a gaban kowaye, zan ririta Al'amarin ki a gaban kowaye! zan girmama ki na girmama danginki matuƙar zaki zauna dani!)
A hankali ya mika min hannu, tare da kallona. Baki daya jama'ar gurin tafi suke mishi, sabida yadda yake amayar da soyayyar shi, kamar wanda aka sakawa wani abu.
Idan ka cire Hajiya Lateefah da jikinta yake rawa, bata kaunar ta b'ata kome, Amma tabbas idan ranta ya kai dubu ya b'aci sosai, domin har duhu duhu take gani.
"Maimunari! Gani a gaban ki, ga jama'a a zagaye damu. Maimunari ina kaunar ganinki cikin farin ciki da! Bani hannunki na saka miki."
Wani irin kuka nake mara sauti,ina kallon shi. Tare da mika mishi hannu nawa, a hankali ya rike tare da saka min zuben danyen zinari wanda aka saka mishi dutse mai daraja akan shi na lu'ulu'u, tafi gurin ya dauka ina kuka tare da kallon shi, mika min karamin akwati Dan Ba'are yayi na cire zoben azurfa har da agogon shi an daura mishi madubin dutse mai daraja, haka na cire zoben na saka mishi, kwalla na zuba min, sanan na cire agogon na saka mishi, tare da kifa kaina ka gefen hannun shi ina kuka, a hankali ya taka har gaban Hanan ya dauki zoben da aka tanadar domin ya saka mata ya riko hannunta, ya saka mata, karfin hali take kawai amma ta gama firgita bata cikin hayacinta, kallon zoben take. Jikinta har rawa yake,. Duk abinda ya bukata ba ita ya bawa ba. Wa wancan kaskantarciyar ya bawa!
Hatta kayan da ta saka ita ce ta zab'i na jikinta amma daga baya ta tura mishi kalar jan yaki kulata, ita da kanta ta zab'i jan bracelet diamond, amma ai gashi ta gani a jikin Maimunari. Kallon uwarta tayi hawaye na tsinkewa daga idanunta, da kyar ta samu tabbar gurin ba ita daya ba. Hatta Hajiya Lateefah da take jin kamar ya cire zucuyarta ta huta, kallon mu tayi, tana kara jin tsana da bakin cikin kamar ta shiga filin tayi ta dukar Mohan da Maimunari.
A hankali aka saka kida mara sauti dan haka. Ya cigaba da cewa.
"A lokacin da duniya ta manta da Alkhairi na, da aikin da nayi dan kasata da al'umma ta, sai Allah ya bani Khalil Ibrahim Dan Ba'are a kusa dani, sannan ya haɗa ni da munafukai a kusa dani wanda dasu ake kashe ni kullum. Sai ga shi Allah ya kawo min matar da ban tab'a zata zan same ta cikin sauki ba.
Sai gashi ta shigo rayuwata bayan irin bakar wahalar da tasha a gurin wasu, bayan bakar azabar da tasha a hannuna, Maimunari tayi faman jinya dani ta bauta min sama da yadda nawa na jikina. Ammyn tayiwu kin manta dani amma ita saboda ni sai da aka shaka mata cocin." Ya kura min ido, ganin ina kuka sosai..kafin ya cigaba da cewa.
"Sai da tayi wata daya a kwance sakamakon tab'a mata huhu da yayi, duk sabida ni. Ko makaranta ta nufa bata zama sabida ni akan lokaci zata dawo.
Ita tayi ta nima min magani lokacin da iyayena suka manta dani, lokacin da kowa ya manta da rayuwar da nake sai Khalil da ita suka fahimci ina bukatar na rayu! Maimoon nagode sosai! Don Allah Karki juya min baya."
Ya fada bayan ya tawo gabana yana goge min fuska na.
"Dayawan masu son aurena, sai da na sami lafiya suke haukar su a kaina, amma ke da a lokacin aka nime aurenki nayi imani zaki amince, nasan da haka zaki yarda da aurena ba tare da jin ina cikin hauka ba, zaki zauna dani ba tare da kyankyame ba. Duk wacce zata zauna dani ta nuna min kauna bayan kece. Ga Mohan a gabanki ga Mohan baya tare da wata matsayi ko muƙami. Ga Mohan a gaban ki shi ba kowa bane, ga Mohan a gabanki ba dan kowa bane, don Allah ki aureni."
Ya kuma dukawa. Wani irin kuka ne ya kwace min, tare da mika mshi hannu ya mike, a hankali na tsaya a gaban shi.
"Na amince!" Takowa yayi tare da rike hannuna, yana kallon yadda nake kuka. Kan shi ya kai daidai kunne na.
"Nagode!"
Hanan kan sulallewa tayi ta bar gidan, da motar su tana wani irin kuka. Ba tare da ta kalli ganbanta ba, ta daki wata mota. Aikuwa na bayan ta da yake Binta ya dake ta, karshe dai can motar ya hantsila. Aka shiga kokarin ganin an ceto rayuwar ta.
.
Haka aka Cigaba da shagali mutane na bani kyautattaka wanda shi ke taya ni rikewa, mahaifiyar Hanan da mahaifinta suka fita, sannan Ammyn ta bi bayan su.
Ba a tashi a gurin ba sai karfe bakwai saura aka tashi, wasu suka wuce masalaci, ni kuma muka wuce cikin part din shi. Anan muka yi sallah tare da cin abincin, muna idarwa sai gashi.
"Tashi muje na ajiye ki, zamu wuce asibiti"
"Lafiya?" Na tambaye shi a tsora ce.
"Wancan mahaukaciyar yarinyar ce tayi hatsari"
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, muje na ganta."
"A'a muje na kai ku gida kawai"
Haka muka fito bayan ya cire jacket din suit din shi ya daura min, sannan muka fito da kyaututtukan da na samu,muka nufi gidan. Koda muka isa babu wanda yayi wani dogon magana kasancewar mahaifiyar shi tana ta kiran shi. Sai da ya kwashe min kayana tsaf sannan ya kai min cikin, ya fito zai tafi nace mishi.
"Nagode"
Hannun shi ya zuba a aljuhun wandon shi.
"Godiya kawai! Na zata zan samu koda pick ne a goshina" sunkuyar da kai nayi tare da kai bakina na sumbaci daidai saitin zuciyar shi, sannan na juya da gudu ina tattare gown din jikina, rike Ni yayi tare da kai hannun shi dukka biyu, ya janyo ni gaban shi, duk da ina da tsayi amma Mohan kamar mashi yake, domin yana dawo dani gaban shi, d'agani yayi na sumbaci goshinsa. Wallahi a tunanina bakin shi zan sumbata, sai gashi na kare da goshinsa. A hankali ya dire ni.
"Ki kula min da kanki"
Gyada mishi kai nayi sannan na, tsaya sai da ya tafi, kafin na shiga cikin gidan.
**
Wato asibitin kuwa wata shegiyar bala'i ake, domin Hajiya Karime shake Hajiya Lateefah tayi tana kuka.
"WALLAHI ba zan yarda ba, idan yarinya ta ta mutu sai na kashe kowa, har dake ban da rashin girman da kika nunawa Yaranki. Ace kamar ki har Mohan zai ajiye wacce zai zab'a baki gaya min ba,ya saka mata abubuwa masu tsada"
Sai da Nahnah ta kifa mata mari, tare da cewa.
"Eh ya zab'eta, yarinyar da bata kyamece shi ba lokacin da yake laluran hauka itace bata dace da shi ba? Yarinyar da tayi sanadiyar samun lafiyar shi! WALLAHI ban da wannan shirmen da zan ga iyayenta a daren yau za a daura musu aure da Muhammadu, naga ta karshen haukar ku, mahaukatan banza.
Ai wallahi idan Muhammadu bai auri yarinyar nan ba,sunan shi butulu, domin duk wacce zata sadaukar da rayuwar ta da karatunta sabida Muhammadu ba karamar son shi take ba, dan haka kar naji kar na gani, matukar ba daga yarinyar za a samu matsala ba, wallahi ban yafe muku ba, duk wanda ya Kuskura ya raba wannan haɗin ko ya shiga tsakanin su, Allah ya isa Ban yafe mishi ba, Ubangiji ya kawo rabon da zai kashe shi har lahira."
Ta fada bayan ta zauna tana haki, a hankali ya shigo ya same su sunyi jungun jungu, zana yayi a kusa da Nahnah..
"Ka maida Maimunari?"
"Eh! Na kainata"
"Kaji tsoron Allah indai zaka juya mata baya, tun wuri ka rabu da ita don Allah"
Rike hannun ta yayi, tare da cewa.
"Nahnah wallahi ban tab'a. Jin a raina zan juya mata baya ba, ban nime ta dan na wulakanta ta ba, asalima ina mata wani irin kauna ce, mara algus. Nahnah meye ribata idan na wulakanta ta, Ina son Maimuna."
Rike hannun shi tayi tare da cewa.
"Allah yayi maka Albarka." Daidai fitowar likitocin, a yadda suka yi bayani babu wani abinda ya faru da Hanan buguwa ce kawai tayi a goshinta, sabida da daka seat belt, sai damuwar da yake damunta, Mohan najin haka yayi musu sallama tare da Nahnah suka bar asibitin, Khalil da ya kawo mahaifiyar shi, nan ya same su, ana kulla sharri domin har sun kuma dinkewa, amma suka yi kamar basu ji su ba. Bayan tafiyar su suka shiga tattaunawa, daga Hajiya Lateefah har Maman Hanan a jikinta suka kwana, washi gari tana farkawa tayi ta kuka tana kiran Mohan.
Yana barci aka kira shi, babu yadda ya iya haka ya taso yazo, tana ganin shi ta mika mishi hannu, karasawa yayi ya rike hannun ta. Haka tayi ta sauke ajiyar zuciya. Karshe dan Iskanci a jikin shi tayi barci. Iyayen kamar su zuba ruwa a kasa su sha.
Da gangan suka sami likita tare da cewa kar ya sallame Hanan bayan an tula mishi kudi me shegen yawa.
**
Tun daga ranar da ya dawo dani sai da muka yi kwana biyar bai kirani ba, bai nime ba, idan na kira shi zai ce min nayi hakuri yana Busy. Karshe dai ba tafi asibitin da kaina bayan na mata sayayyan kayan masarufi, ina shiga ward din na same Iyayen a tsaye, suna gani na suka mike. Allah cikin ikon shi sai ga Abbu yazo dubata, shine suka maida kudirin su, cikin sanyin jiki na gaishe su. Sannan na shiga d'akin, na same shi zaune ta zuba mishi kafaffun ta, yana karanta mata story book. Wani irin sanyi jikina yayi a karo na biyu.
"Hanan ya jikinki?" Banza tayi min.
"Bana son damuwa baki ji tana tambayar ki ba!."
" Da sauki" ta faɗa tare da harara na.
Ture kafarta yayi tare da ja min kujera na zauna, shigowar Abbu yasa ni mik'ewa, ba kuma gaishe shi.
"Ya iyayen ki?"
"Suna lafiya"
"Masha Allah, Hanan ya jikinki?"
"Da sauki Abbu"
"Toh Allah ya kawo sauki zan koma. MG Office dinka yana jiranka fa! Nayi hakuri naga kamar baka Fahimci haka ba, dan haka gobe ka shigo Office akwai aiki sunyiwa Khalil yawa."
"Insha Allah!" Bayan fitar shi ba kalle su, sannan na mika mishi kayan da nazo dashi.
"Allah ya baki lafiya" na mike zan fita ya ajiye kayan tare da fisgo ni.
"Meye nufin ki? Ina ta miki magana sai share ni kike!"
"Toh kayi hakuri." Na fada mishi ina ƙoƙarin janye jikina, sumbatar kumatuna yayi tare da wuyana duk da hijab ne a jikina, da sauri na ture shi. Dariya ya saka tare da cewa.
"Muje na goge laifina da nayi"
Haka muka fito, ya kalle su yadda suka cika fam.
"Ammyn bari na ajiye ta a gurin aikinta?"
Budar bakin Maman Hanan tace mishi.
"Toh Hanan kuma fa? Kasan likitoci sun ce ba a son ka barta ita ɗaya."
"Idan ta mutu fa kabarinta daban nawa daban, idan ta so.ta Cigaba da kwanciyar ta a nan, babu abinda zai canja. Domin daga gobe zan koma bakin aikintae Insha Allah,tayi ta kwanciya idan Mohan ne zai bata lafiya, ina da abin yi daga yau bani kuma dawowa."
Babu abinda ya dame shi duk da mahaifiyar shi tana tsaye bai hana shi fadar abinda yake ran shi ba, yayi tafiyar shi tare da rike hannuna. Muna fita na fisge hannuna.
"Wato bani da daraja, shine ka share ni na tsawon kwana biyar, ba dan nazo ba haka zaka Cigaba da jinyarta, ni kuma na mutu ko? Nagode" na fada bayan na juya zan tafi.
"Toh kiyi hakuri mana! Ke nifa kina burge ni! Hmm wallahi tafiyar tafi maganar ban sha'awa!" Da sauri na juya tare da bin shi zan buga mishi jakata.
Rike hannuna yayi yana dariya. Bayan ya kai bakin shi kunne na.
"Insha Allah wata me zuwa Abbu zasu tafi nima min auren ki duk da nasan an bani ke, sauran kuma a daura auren, kinsan Allah! Yadda nake tausayin ki. ba zai hanani amsar hakkina ba, dan haka ki nutsu sosai, domin akwai karamin yaki a gabanki, namiji nake sosai kuma girma nake dashi daga cikin wandon na," da sauri nan juya tare da cewa.
"Subhanallahi!" Tare da niman hanyar guduwa, riko ni yayi tare da bude min motar na shiga ina kauda kaina, haka muka nufi gurin aikina, sai dariya yake min tare da kallon yadda kunya ta kama ni.
Alhamdulillahi duk wani farin ciki da annashuwa na samu, Mohan yana aiki amma idanun shi yana kaina, kome namu kusan a tare muke, a gurin aiki idan ba meeting ba, ba zaka tab'a ganin mu Bama waya ba, haka tasa har an saka min ido, Abie kuwa bani lokaci yayi, dan na maida hankali akan abinda nake shima kuma yana taimaka min. Gyara rigar shi ta Alkalai yayi tare da kallona.
"Yau zan shiga aiki a kotu ko zaki ajiye wayar ki mi shiga tare!"
"Toh Abie" na kashe wayar bayan na tura Mohan sako, muka fito tare, ban san me dai ba yana gana ina binshi a baya.
"Tsaya" yace min, da guda wani katon kadangare ya nufi kaina,sai da yazo dab dani, kafin ya tsaya cak. Ya kasa motsi.
"Koma inda aka turo ka" da gudu ya kuma juyawa, abinda ya kusan sumar dani kenan, sai da ya tab'a ni.
"Kuyi hakuri da Typing errors din da suke cikin rubutun domin babu editing 🤷🏼♀️🙋🏾♂️*
Mai_Dambu
[8/9, 3:16 PM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1112772393?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA HAMSIN.
Jan wani irin numfashi nayi tare da niman zuɓewa kasa, ya riko hannuna.
"Ke tashi matsoraciya kawai." Kiran wasu lauyoyi mata yayi tare da gaya musu maza su kai ni asibiti, idan kuma zasu iya taimaka min ba sai mun je asibitin ba.
Amsawa suka yi da toh suka kaini Office din su, suka taimaka min na farka, sannan suka shiga bani ruwa, kasa sha nayi domin na gama razana, shiru nayi tare da jingina kaina da bango. Har ya fito, hankalin shi yana kaina, yana zuwa ya ce min.
"Tashi muje"
Haka ya saka ni gaba muka nufi gidan shi, cire kayan shi yayi tare da saka wasu kayan, ya shiga min rubutu a jikin allon karfe, ya nutsu yana rubutun da tawwadar mai zafi,sabida tana tafasa ce ake rubutun dashi, yana gamawa ya wanke min da ruwan zamzam mai zafi dan har yana tiriri. Ya mika min fuskar shi babu alamar wasa yace min.
"Nasan kina addu'o'in neman tsari, amma sha wannan makiyan shi sun rub'anyan da! Ta ko ina aika zakina samu, dan haka nake kyautata zaton an fara bibiyar ki, maza sha ba mutum ba ko ifiritu yake, zai ganki ya barki sai dai a kare a makirci da munafunci ba boka ba ko malami ne, idan ya nace zai tab'a miki wallahi kwayar idanun shi tsiyayyewa zasu yi.
Idan kuma aka dage na miki sharri hauka mutum zai yi domin da bakin shi zai magana."
Sai da ya gama min bayani, sannan ya bani wani Magani nasha, kafin na kwanta a dogon kujeran falon shi, bai tashe ni ba. Sai da aka yi azahar na tashi nayi sallah sannan ya mika min abinci.
Awaran madara soyayya sai yaji da dafaffen nama wacce aka dafa ta da madara, har karasa yadda daɗin shi yake, sai shinkafar da aka dafa da ruwan kwakwa. Ina gama ci. Ya kalle ni.
"Duba wayarki mutumin ki ya shiga kotu sau uku yana niman ki"
A kunya ce na dauki wayar na kunna, sakonni shi kawai suke shigowa, kiran shi nayi.
"Kina ina?"
"Ina gidan Abie kazo ka ɗauke ni"
"Toh gani nan"
"Kina son Mohan kamar yadda yake sonki" sunkuyar da kai nayi, ina wasa da cokalin hannuna.
.. hira muka sama sama har ya iso, harara ta yayi sannan yace min.
"Kin kyauta min!"
"Zauna kaci abinci"
"Toh Abien Moonah" ya faɗa a zolaye, murmushi nayi na zuba mishi. A hankali yake ci yana kallona.
"Muna nake kika yi girkin nan ba? Domin nasan baki iya girki ba"
"Subhanallahi! Maimunari, dama baki iya girki ba?"
Taka Mohan nayi tare da hararan shi.
"Wash ta taka min kafa, Abien Moonah kaga zata cire min yatsu."
"Gulmar ka ya ja maka" ya faɗa mishi haka.
Wayar shi ya dauka bayan ya danna wata lamba yace.
"Akwai yarinyata zata fara zuwa daukar darasi Insha Allah Asabar da lahadi. Sauran ranakun idan ta taso aiki.zata zo"
"Abie har da Auta"
"Toh su biyu ne"
Hararan Mohan nake kamar idanuna zasu fadi kasa, mutum ya zama gulmammame,
Haka muka sha hira sannan muka mishi sallama, bayan mun kuma hanya yake ce min.
"Yau naji kamar nayi hauka da aka ce min kin suma, ina meeting na fito muje na ajiye ki a gida sai na koma domin ni suke jira."
"Toh Sarkin gulma"
"Eh na yarda"
Haka ya ajiye ni a gidan, na samu auta ta gama abincin, cikin tsokana nace mata.
"Kwashe kayan shirmen ki nan ba ci zanyi ba, naci me dad'i a gidan Abie na"
"Wallahi baki isa ba har dare shi zaki ci"
Haka dai yanayin yake tafiya, ban san wanda ya gayawa Ansar anyi baikona da Mohan ba, sai kirana yayi yana faɗin.
"Munnah amana bai ce haka ba, ashe kuma anyi baikon ku baki gaya min ba? Amma har yau ban cire rai da samun ki, domin nasan ke allura ce cikin