Showing 54001 words to 57000 words out of 177131 words
saka min" na fada ina matsar kwallan, bai saurare ni ba, ya kuma dangwala audugar ya manna min.
"Wayyo Allah na zaka kashe wallahi sai na huta kafin ka kuma saka min wayyo ni wayyo zafi don Allah ka saka min a hankali."
Kamo ni yayi tare da juyar dani, ya matse ni yadda ba zan iya motsi ba, yana wanke min ciwon ni kuwa sai kuka nake da rikici. Shigowar Malik zai gaya min Ansar ya zo, ya tsaya baki sake yana raba idanun shi akan mu, d'ago kai Hammah Mohan yayi tare da d'aga mishi gira alamar lafiya.
Cikin wani irin yanayi da ban mamaki ya kame guri guda ya sara mishi tare da cewa.
"Jami'an soja mai lamba C210 mai igiya uku Malik Moussa Abzin yake magana Yallabai"
Lumshe idanun shi yayi yana jin wani abu yana yawo a jikin shi tun daga tafin kafar shi har tsakiyar kanshi, tsigar jikin shi sai mik'ewa yake, d'ago kai nayi ina kallon fuskar shi wacce take kara fidda wata irin kwarjini. Shagala nayi ina kallon shi.
Bayana yana jingine da kirjin shi, hannun shi daya yana tsakanin cikina da kirjina, daya hannun shi kuma yana rike da almakashi.
Jinjina kai yayi tare da kallon Malik irin ina jinka. Nutsuwa Malik yayi a karo na biyu ya fadi abinda ya kawo shi, da sauri na fara ƙoƙarin mik'ewa a jikin shi, kai hatta sunan malam Ansar tsoro yake bani, balle kuma nayi ido biyu da shi.
Gyada kai yayi alamar ya shigo da shi. Yana makale dani, har lokacin bai barni na mike ba, fuskar nan ta kuma had'ewa shigowa malam Ansar yayi yana dingishi. Tun kafin ya idda sallamar shi kalmar ta makale a wuyar shi yana kallon ikon Allah.
"Almamoon" ya faɗa a sanyayye, cikin wani azzababben kishi, ya tako da karfi ya manta da ciwon kafar shi, yana zuwa ya tsaya a gaban mu jikin shi yana kerma, kokarin fisgo ni yayi amma ya kasa.
"Tashi ka haura sama" a mugun kidime na juya ina kallon shi, fuskar ku kusan tana gogan juna, hancin shi har yana gogan goshina, d'ago kai nayi ina kallon bakin da yayi magana, tare da kura mishi ido, ina jin sautin Muryan shi har cikin jinin jikina.
"Nace tashi" kara ware idanuna nayi ina kallon shi bakina cike da mamaki. Can kuma sai gashi ya daure fuskar sama da baya, da sauri na mike na haura sama. Nunawa malam Ansar guri yayi tare da kallon shi.
"Ba zama nazo yi ba, abinda na kawo na zo dauka"
Cikin renin hankali irin ta namijin duniya yace mishi.
"I thought abinka yana jikinka" ya faɗa cikin wani irin isa, kamar ba shi yayi maganar ba.
"Poor" inji Malam Ansar.
Kamar bai ji abinda yace ba, ya kuma Cigaba da kallon yatsun hannun shi.
" Malam ka bani yaron can domin ni na mishi hanyar samun damar zama a cikin ku." Ya fada cikin karaje da fusata.
Juyawa yayi tare da kallon inda zai ga yaron, bai ga kowa ba. Ya juya tare da tab'e baki yace mishi.
"Ban ga yaron ba, yana ina?" Ya fada yana kallon malam Ansar wanda ya cika kamar an watsa mishi yiest.
A fusace ya mike Mohan ya mike tare da sakala hannun shi dukka biyu a k'ugun shi, suran shi ta zaratan sojoji ta kuma bayyana sama da farko, ya fito giant din shi, ya tsaya a gaban Ansar duk da shima ba kad'an bane amma Mohan ya kere shi.
"Akan me yasa kake cutar da shi bayan kasan kana bukatar shi a tare da kai?"
Wani irin duba yayiwa Mohan sama da kasa, kafin ya fashe da dariya. Mai karfi sosai sannan yace mishi.
"Ina son shi! Ina kaunar shi! Tun daga lokacin da na fahimci shi mata maza ne, na fara kaunar shi dan haka matsa min a hanya na dauko shi"
Shiru yayi tare da matsa mishi a hanya ya wuce sama, bai hana shi ba, komawa yayi ya zauna yana tuno abinda ya faru jiya, ok dalilin da ya sa kenan ya datse mishi kofa a hannun? Lashe bakin shi yayi yana kallon yadda zasu kaya.
Can kuwa sai gashi nan ya fito da Almamoon yana jan shi, shi kuwa sai kuka yake yana faɗin.
"Ni kam ba zan je ba, ka kyale ni" na fada mishi ina kuka.
"Ba zan ba zan cigaba da ganin ka cikin suffar maza ba muje idan ka ga gatar da na shirya maka iya ni da kai a duniyar mu sai kasha mamaki."
"Bana son" na fada da karfi ina kwace hannuna.
Na nufi gurin Hammah Mohan, yana zaune ya aza daya kan daya yana jin mu,. Rike kafar shi nayi ina kuka.
"Don Allah karka bari ya tafi dani". Na fada ina kuka. Malam Ansar yana zuwa ya fisgo ni, tare da d'aga hannu zai mare ni, Ya rike hannun.
"Masoyin gaskiya ba tab'a dukar abinda yake so, manufar ka mai kyau ce, amma dukar ba zai iya canza kome ba. Kai kuma ka bishi ku tafi."
Ya fada min yana kallon yadda na sake baki, jikina yayi mugun sanyi, haka ya nuna min hanya. Had'iye yawun da ya tsaya min a wuya. Ina kallon shi, na kasa magana, kawai saka kai nayi zan fita.
"Amma irin wannan al'amarin iyayen shi sun sani?" Ya tambaya yana kallon yadda Ansar yake jan hannuna. Cak muka tsaya, wasu irin kwalla ne suke zubo min, a hankali ya mike tare da takowa gaban mu. Ya zare hannun malam Ansar da ya rike hannuna. Sannan ya saka hannun shi ya riko k'uguna.
"Hatta kare idan yana tarayya da shi ba zan tab'a barin shi yayi haushi ba balle kuma shi Yaron ka koyi yadda ake martaba dan adam sai ka dawo na baka shi......
_Barka da Sallah! Na cika muku alkawari.......😘😍saura kuma ku nuna min naku alkawarin.... Karku saka rai zaku samu update nan kusa domin sha'anin aikin sallah_
#Mai_Dambu...
[7/21, 6:14 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA ASHIRIN.
Wani irin sanyin naji tun daga kafana har tsakiyar kai na, kokarin mai da kuka na, ina kallon shi. Kara kawo hannun Malam Ansar yayi,.da sauri ya kifa kaina a kirjin shi tare murɗe hannun shi sai da yayi kar'a, so nake naga abinda yake faruwa amma fir ya matse kai na a kirjin shi, dan haka baki daya na kasa aikata kome.
Cire kaina nayi tare da kallon yadda ya murɗe hannun.
"Sake shi kaji" na fada ina kallon shi.
"Almamoon! Ni ka ciwa zarafi? Ni ka wulakanta? Almamoon ko yagar namar jikinka nake bai dace ka min haka ba. Amma babu kome." Ya kwace hannun shi yana me barin gidan. Yana fita Hammah Mohan yana kara birkice min, domin kwanciya yayi min alamar bai da lafiya, baki daya na tsora ta.
Ya ciwon shi ta dawo sabo fil, sai shegen taurin kai kamar tsohon jaki.. daga rana zuwa dare kamar zanyi hauka, domin sai yayi kamar zai fadi kasa, ina tare shi zai ture ni ya falla a guje.
Washi gari.
A dararre na wullakila idanuna ina niman shi, hango shi nayi a saman table din cin abincin gidan.
"Sauko ko na zane ka" na fada ina gyara hannun riga,
"Dama ciwon bai kyale ka bane shine jiya har da..."
"Assalamu alaikum!"
"Yawwa Hammah Malik dubi abinda mutumin nan yake yi, kana ganin shi kamar wani robot sai rashin mutunci wallahi kayi wani abu ko na sab'a mishi sauko idan ba haka ba zan zane ka"
Kallon shi Malik yayi da alama ciwon ne ya kuma dawowa, dan haka ya kira malamin ranar, yayi mishi bayani. Riko hannuna yayi tare da jana gefe yana fadin.
"Kaga ka tafi makarantar ka, zan ji da kome" gyada mishi kai nayi na nufi daki na dauki kayana, kallon shi nayi cikin tausayawa nace mishi.
"Allah ya baka lafiya"
Na fita daga gidan. Motar da yake kai ni makarantar na shiga, duk da bani da nutsuwa, amma zuciyata bata so zuwa ba, naso na zauna a jikin shi har naga halin da zai yi.
Hana motar aka yi ta shiga makarantar, ina zaton basu san darajar me motar bane, dan haka na sauka a bakin get na shiga makarantar da kafa.
Ina shiga aji na zauna a nutse, ina sauke ajiyar zuciya.
"Almamoon ashe kuma likafa ta cigaba ashe ka fara aikatau a gidan manyan mutane shin aikatau na aikin gida ko kuma aikatau na bin bayan ka?" Duk sai na muzanta, sunkuyar da kai nayi ban ce kome ba, haka malamin ya shigo yayi mana darasi bayan fitar shi. Naji ana ta dariya a cikin ajin. Sosai fa,
Mik'ewa nayi na kuma jin sun kwashe da dariya, da sauri na fita daga ajin duk inda na wuce dariya ake min.
"Almamoon Isma'il Wodaadabe, tsaya ka ciwo abinda aka rubuta a bayan ka" cak na tsaya ina jin wani irin tsoro yana kamani, nasan dai ba haila bace tunda sati Daya da ya wuce nayi gama.
Cire min takardan da aka rubuta Kalmar Mata maza da manyan Haruffa. Jikina har wani irin rawa yake, na juya zan bar gurin.
"Mamoon" juyawa nayi na kalle shi.
"Kad'an daga cikin abinda kayi min kenan, kuma baka ga kome ba domin yanzun aka fara."
Dariya ya bani na tsaya sosai a gaban shi ina faɗin.
"Idan na kula ka ban san darajar kai na bane, amma idan har ka cika namiji ka tari Mohan Mamman Nasir Aghali ka ga yadda ake wasan kura da lusari irinka."
Na juya zan bar gurin ya fisgo ni,cikin fushi na kai hannuna zan mare shi, sai kuma na fasa ina kallon cikin idanun shi.
"Wallahi kaci albarkacin girman ka da nake gani da yau na mare ka a cikin makarantar nan, kuma na rantse da Allah sai na baka mamaki."
Nayi tafiya na na barshi tsaye cikin mamaki.
"Dan daudu zai bani mamaki" murmushi nayi na cigaba da tafiya, domin bani da abin da zan gaya mishi, koda na gaya mishi ba zai ji haushi ba, kuma koda ma mishi a aikace ba zai damu ba, duk wanda ya cutar da kai ba zai tab'a jin zafin dan ka rama a lokacin barshi ya manta abinda ya aikata, haka na kyale shi. Sake tare ni daliban shi suka yi.
"Kai dan dan daudu, me bin maza kawai lalatacce mara hallaci." Ban kula su ba, sai ma keb'ewa da nayi zan bar su a gurin dan basu min kama da masu hankali ba.
Ina barin gurin su, na samu kasar bishiya na zauna, ina son nayi kuka amma ba zan iya ba, bana son nayi kuka yanzun so nake na iya shanye kuka na, gashi ban san halin da Hammah Mohan yake ciki ba.
Bayan an koma aji na mike tare da shiga aji, na zauna ina sauraron darasin shi. Har ya gama zai tafi.
"Dalibai ku kasance masu tsentseni da sanin ya kamata, karku zama butulu marasa halacci."
Murmushi nayi ina kallon shi, sabida ya daina bani mamaki sai dariya.
"Kai waye kakewa dariya?" Ya tambaye ni, ware idanun nayi cikin dariyar renin hankali nace mishi.
"Ina dariyar yadda mutane suke manta waye su? Kamar Ni dai." Na nuna kai na ina dariya. Mik'ewa nayi zan fita, ya tare hanyar fita.
"Ansar Yusuf, ka bani hanya na wuce na Barka kayi rayuwar ka baka isa ka hanani tawa rayuwar ba, Ansar kayi yadda kaga ya dace amma karka shiga cikin abinda babu ruwan ka" na fada ina me barin ajin.
Da sauri na fita a makarantar.
Ban samu motar da yake zuwa dauka na ba, dan haka na tari abin hawa, sai dai ina shiga da malam Ansar nayi tozali, kamar zan fasa dan wani irin tsoro ne ya kamani, sai na shiga na zauna ina kallon shi. Kamar da wasa madadin su kai ni inda na faɗa sau suka wuce dani wani gurin.
Wani asibiti muka nufa, ban mishi musu ba, har muka shiga cikin asibitin. Tare da nufar office din wani likita, kamar Balarabe ne. Muna zuwa ya mika mishi hannu suka gaisa, Kafin ya fita.
"Ko zamu je na duba ka?" Murmushi nayi domin a yanzun nake kara hango Malam Ansar shi ya dace da kasungumin mahaukaci ba Hammah Mohan ba. Mik'ewa nayi zan fita ya mike shima.
"Kazo ka zauna na duba ka."
"Ba zan iya ba, kuma wallahi ka kuskura ka tab'a ni sai ka yanke ka." Na fasa wata Kwalba da tasa shi tsorata, na fita abina daga dakin. Na samu baya nan da haka da sauri na fita a cikin asibitin. Kamar zan tashi sama haka na bar harabar asibitin, ina isa bakin hanya ana kiran sallah la'asar, Dakyar na sami abin hawa. Na fada mishi inda zai kai ni.
Ina shiga malam Ansar yana isowa da gudu ya biyo mu.
"Malam karka tsaya sace ni yake son yi don Allah mu tafi" na fada mishi ina me jin kwalla na cika min idanuna, ai kuwa driven ya taka motar da gudu, muka bar ganin shi. Tafiyar kusan minti arba'in ya kawo mu unguwar lokacin da ya tsaya na bashi kudin shi na juya zan tafi.
"Malam kudin yayi yawa"
"Jeka kawai" na fada mishi ina ƙoƙarin shiga cikin kofar get din farko.
Rike hannuna malam Ansar yayi, a tsora ce na juya. Ina ido hudu dashi na fasa ihu, ina ƙoƙarin kwace kai na.
"Don Allah ku fito ku taimake ni, zasu sace ni" kafin sojojin su fito ya shaka min abu a hancina, komawa nayi tare da zuɓewa a jikin shi. A hankali na fara ganin kome yana juya min bibiyu kafin na koma tare da lumshe idanuna.
"Hammah Mohan" na fada a hankali.
Fitowa sojojin suka yi lokacin har ya saka Ni a motar shi, ina da gudu ya bar Unguwar. Danna wani abu suka yi take ilahirin sojojin gidan suka fito. Suna masu hango motar tana tashi da kura.
"Meye ya faru Fahad?"
"Wallahi wani da bamu sani bane ya dauki Alm.."
"Haukar banzan kuke kenan? Tsayuwar Uwar me kuke?" Inji Malik,
Ai kuwa kamar wanda ya ankarar da su, suka rufawa motar baya da hilux, amma kafin nan ya b'ace musu, kamar zasu yi hauka.
Koda suka dawo sun sami Major General Mohan Mamman Nasir Aghali a tsaye yana kallon su. Baki daya aka rasa wanda zai sauko a cikin motar zunzurutun yau sun ganshi a cikin unifoam. Yana jingine da bike kanshi sanye da hular yaki, fuskar shi tayi jajjur. Yana kallon agogon hannun shi. Tab'a bluetooth din shi yayi.
"Ina jin ka? Number guy din? Ka gayawa dakin iko, su bani bayanin inda yake nan da minti biyar"
A fusace ya kuma daka mishi tsawa.
"Dan Ba'are! Wallahi na rantse da Allah sai na harbe duk wanda ya kuskura ya shiga tsakanin mu da My Maid idan ka sake na kuma kiranka wallahi sai na dakatar da kai"
Ai sojojin da basu nimo Almamoon ba sai gasu sun zube a gaban shi cikin tashin hankali.
"Yallabai wallahi" yatsar shi ya saka a bakin shi, tare da nuna musu hanya.
A hankali ya hau kan bike din, tare da saka hular kwanon shi, ya taka machine din ya jata da mugun gudu, yana bin bayanin da ake gaya mishi. Sai da yayi tafiyar minti Talatin kafin ya isa asibitin da Almamoon ya gudo, cikin isa ya tsaya yaran shi suka iso, tare da taka mishi baya da bindiga a hannunsu, irin duk wanda ya kawo mana wargi zai sheka lahira.
Wani irin tafiya yake cikin jarumta da Izza, tare da jin shi din a bakin aikin shi yaƙe. Matashin sojan da yayi zarra sama da sauran manyan sojojin da suke saman shi. Duk inda suka wuce bin su ake da idanu, sabida yadda suke takon a nutse baka jin kome sai karan takun takalmar su, kai.daga dakuna sai leken su ake, cikin isa da jin kai ya isa bakin kofar da aka gaya mishi nan Almamoon yake, dukar kofar yayi da kafiran takalmin shi, budewa kofar tayi daidai ana ƙoƙarin cire kayan Almamoon wanda yake kwace kamar gawa.
Wata Ɓoyayyen ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tsaya cak yana kallon fuskar Almamoon da kwalla ta bushe akai. A hankali ya ja wani kujera ya zauna yana kallon yadda Nurse din cikin dakin da kuma likitan suka yi tsuru tsuru.
"Ina yake?"
Fitowa Malam Ansar yayi tare da da kallon shi babu tsoro a fuskar shi ko nadama. Mik'ewa yayi tare da nufar shi.
"Wannan shine kashedina da kai na karshe karka tab'a Yaron nan tunda ba kai ka kawo min shi ba" inji Malam Ansar,
"Idan na ki fa?" Ya tambaye shi a gadarance.
Tare da nufar Almamoon, yana ƙoƙarin daukar shi. Wani allura ya dauka ya suka a wuyar Almamoon, kafin ya juya ruwan. Mohan ya kai mishi wani irin duka akan hannun..sai da kashin hannun shi tayi kara, yayi maza ya zare alluran. Takowa yayi gaban shi yana kallon shi. Da hannun daya ya d'ago shi.
"Idan ka kuma tab'a ko inuwar shi, wallahi na rantse da Allah sai na aikaka lahira, ina kyale ka ne sabida karatun shi nasan zai fi son shi a matsayin shi ne ba kowa ba, idan ka sake raina ya b'aci, hmm" ya faɗa tare da barin gurin shi ya juya zai dauki Almamoon.
"Wallahi ka rubuta ka ajiye, sai na raba ka dashi, wannan alƙawari na ne"
Daukar maid din shi yayi tare da tsayawa cak, yace.
"Ni kuma nayi maka alkawarin barinka a raye domin