Showing 42001 words to 45000 words out of 177131 words

Chapter 15 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

14793

kudin hannuna dukka, sannan na shiga dama kamar ni ake jira.

    **
Isar dare nayi dan haka ban yi gangancin nufar gidan Hammah Mohan ba, na nufi gidan Malam Ansar domin zan kafta mishi rashin mutinci.

    Ina shiga na samu Baba tana sallah isha, zama nayi bayan nace mata.
"Wash tsohuwa bayana"

Tana idar da sallah ta mike tana murmushi.
"Sannun Angona, yau kai ne a gidan mu?"
"Tsohuwa gani nan dai"
Ban daki ta shiga ta hada min ruwan zafi,sannan ta fito. Na shiga nayi, ina fitowa ta ajiye min abincin da man shafawa me gurguwa.

A hankali na shafa sannan na zauna muka shiga hira muna gaisawa.

"Daga ina kake?" Tsam nayi da hannuna kafin nace mata.
"Naje ganin gida ne."
Kura min ido tayi kafin tace min.
"Wani gari?"
"Damagaram"

"Almamoon kana dauke min kewar Y'ata, maganar ku tafiyar ku, murmushin ku.. Almamoon idan. A ganka sai naji ina ma kai jininta ne, duniyar nan cike yake da azzalumai marasa imani, ya shigo ya lalata min rayuwar Y'a yasa kowa ya guje ta.

         Kimanin shekaru goma sha tara kenan rabon da naji muryanta. Ina kewarta saboda ita na kasa komawa ko ina, na kasa bin mijina da Yarana na kasa komawa Libya gurin dangina. Ina kewar Zainabu."

Rike hannunta nayi domin ta bani tausayi, nace mata.

"Me yasa mi Addah Zainabu?" Kwalla naji ya cika min idanuna,

   "Wasu daga cikin kabilar Fulani suna da wata muguwar al'ada wacce matukar ta faɗa kanka shikenan. Rayuwar mutum ya lalace"
"Baba Mari wata al'ada ce haka? A'a Almamoon kai ne yau a gidan mu"

Juyawa nayi na watsa mishi kallon banza, kafin na mai da kaina gurin Baba Mari. Da take kuka. Nima tsintar kai na nayi da kuka domin duk yadda aka yi labarin ba me dadin ji bane.

  Hakuri muka yi ta bata, har tayi shiru. Sannan ta gaya mana muguwar Al'adar fulanin, kallon ta nayi cikin rawan jiki nace mata.
"Baba kina nufin da auren wani akanta ya dauke ta yayi zina da ita?" Na tambaye ta kuka na kwace min. Domin am very shock, tana matar wani zaka kwanta da ita? Taya zaka iya zama da matar aure bayan kasan igiyar wani na kanta, ban san me yasa na tsinci kaina da kuka kamar Ni aka yi wa laifin. Dan ma taki ta gaya min sauran abinda ya faru.

   Shima Malam Ansar haka ne, jikin shi yayi mugun sanyi.
"Almamoon zo na baka sakon ka" kamar ba zan taso ba, na mike domin ina cike da shi kuma na sami yadda zan kafta mishi rashin mutinci,  muna fita ya tsaya a gabana.
"Ya isa haka kukan nan, meye ya kawo ka nan?"
"Kai me yasa baka gane bayani da Yaren da muke yi? Me yasa ka je ka sami Iyayena da maganar da tsakanina da kai ne? Kai baka da lissafi ne? Kome aka ce nake gayawa Iyayena? Nasan ciwon su da darajar su, karka kara zuwa gaban iyayena da maganar banza domin idan ka kuma zan baka mamaki dole ne sai nayi alaka da Ni?

     Wallahi ka kuma duk abinda na maka kai kasayawa kanka, duk abinda kayi min ban tanka maka ba, sabida bana son damuwa amma akan iyayena wallahi za a jimu da kai domin na nasan darajar iyayena, shine abinda ya kawo ni gidan ka, kuma zan kwana gobe na wuce don't think that ko ban san me nake yi bane ina sane dashi ka fita idanuna"

Na fada zan juya riko hannuna yayi tare da matse ni a jikin motar shi.
"Ban ji kome ba, ban ji haushin ka ba, sai ma burge ni da kayi. Amma kasan me? Zo na nuna maka wani abu." Jan hannuna yayi har cikin gidan shi, ya kunna Laptop ɗin. Yana me nuna min wasu abubuwan. Kafin yace min.
"Ina ta tura musu sako ne, sabida matsalar ka, kayi Hakuri nayi laifi zan k'iyayye gaba, amma is very important ayi maka aikin na. Domin kafi karfi ta jinsin mata."

Cikin tsannanin takaici nake kallon shi kamar zan fasa ihu.
"Toh impossible" na gaya mishi tare da barin falon shan gaban yayi tare da had'a hannun shi guri guda.
"Please and Please listen to me, idan na kawo maka zancen shirme kayi tafiyar ka, amma abinda zanyi yana da matukar muhimmanci a rayuwarka."

"Look ba zan yi ba, kuma idan ka nace sai na maka abinda ba ka zata ba, dalla bani hanya na wuce ban tab'a ganin mutum me mugun shiga abinda babu ruwan shi ba sai kai.

         Ina ruwan ka da lifestyle dina? Meye matsalar ka sa rayuwata? Ina ruwanka dani ne? Yes Ni mata maza ne, doesn't mean you have right to enter my personal life.  Kayi rayuwarka nayi nayi nawa dole ne sai ka shiga rayuwata? Don Allah don Allah don sanka da Allah ka rabu dani"

   "Dan ban da arziki? Kodan ban da kome?" Ya tambaye ni a sanyayye, takaici ya sani rike k'uguna da hannu bibbiyu, ina kallon shi.
"You see, ji abinda ka fada? Ji abinda ya fito daga bakinka? Kalli kalaman ka marasa dad'i da kyau. Yayi maka idan ka dagama kayi tunanin kome a kaina tunda baka san yadda ake gudanar da rayuwa ba, kana tare dani but kana drag din rayuwata."

     Na juya a fusace zan fita. Jin shi nayi ya wani k'amk'ame ni, kamar wani zai kwace mishi ni,
"Don Allah don Allah karka tafi Almamoon, nasan za ayi nasara akan aikin da za a maka."

Kasa motsi nayi ina matukar tausayin shi, amma bawai ina jin shi bane a raina.

  Zare hannun shi nayi tare da juyawa nayi ficewa ta, daga falon. Idan na cigaba da zama zan iya kafta mishi rashin mutinci. Dan haka ina fita na nufi dakin Baba Mari, na kwanta.

     ***
Tun da Almamoon ya bar gidan, yake zaune a bakin kofar shiga gidan, ya zuba tagumi hannu bibbiyu, yana kallon ta inda zai fito.

      Duk sun zagaye shi, domin sun san Almamoon kawai yake jira.

    Har dare bai tashi ba, yana gurin Malik kuma baya nan, dan haka babu wanda yayi tunanin sashi yayi alola ko sallah kamar yadda yake kullum, tunda ya zauna yake kallon kofar harabar.

   Har dare ya raba, yana zaune a gurin. Yana ta gyangyadi, wasu irin kukan abu yaji ya bude idanun shi, bai ga kome ba, dan haka kamar yaro karami da ya rasa uwayen shi haka ya mike tare da shiga falon gidan, ya zauna a saman center table dake na Kwalba ce me ƙarfi.

   Haka ya zauna kamar maye har kusan asuba, kafin barci ya dauke shi a saman gurin. Washi gari masu aikin gidan ne suka ganshi a gurin.

      Tsoro ya kama su, dan dole suka hakura da aikin domin sun san idan Malik ko Almamoon. Yazo zasu sha wahala musamman Almamoon ma baki daya yake shuka musu tijara.

       ***
Ina sallah Asuba na tashi, tare da shirya kayana.
"Sai yaushe?"
"Insha Allah zan na zuwa Asabar da lahadi."

"Toh Allah ya nuna mana" haka na tattara na bar gidan, domin bana son na hadu da Malam Ansar, zai iya karya min zuciya, jiya kwana nayi da tunanin shi, sabida yadda yake damuwa da ni. Sam Ni ban damu dashi ba.

Amma shi ya daurawa ranshi damuwa a kaina.

       *
Na isa gidan lafiya.
"Assalamun Alaikum"
Zubur ya mike tare da zuba min ido, tashi yayi ya juya tare da nufar sama da gudu, irin ta me cikakken kuzari, yake tsallake step by step, har ya haura dakin shi, bin bayan shi nayi da kayana na ajiye su a d'akina.

    Sannan na nufi dakin shi yana gani na ya dauke kanshi. Takawa nayi har gaban shi. Juyawa min baya yayi, durkusawa nayi a gaban shi tare da riko hannun shi.
"Kayi hakuri na dawo da dare ne sai ban karaso nan ba, muje na baka abincin kaji"

     Daura kanshi yayi akan cikina, tare da k'amk'ame ni, wani irin abu naji ya mike a jikina yarrrr, da sauri na ture kanshi, ina me kallon kofar. Daidaita tsawo na nayi ina kallon shi. A karon farko da kwayar idanuna ya faɗa cikin nashi.

      Wani irin abu naji yana shiga cikin nawa, lumshe idanuna nayi tare da jin wata irin faduwar gaba. Lashe bakin shi yayi yana me kumshe idanun shi, janye idanuna nayi akan shi, tare da mik'ewa, kawai naji ya riko hannuna.

   Kallon shi nayi bakina a sake, na kasa magana sai sunkuyar da kai da nayi. Zuciyata tana wani irin bugawa da sauri da sauri. Kwace hannun nayi ya kuma fisgo ni, tare da yi min dabaibayi da hannun shi.  Ina son nayi magana amma baki daya kome na bakina ya kare, ga wani iskar da yake cika min bakina, kwalla ne suka cika idanuna. Dakyar Allah ya bani sa'a na kira sunan shi da cewa.
"Hammah"

Lumshe idanun shi yayi yana me kara rike ni gam a jikin shi. A hankali ya birkitani daga gaban shi zuwa saman gadon. Wani abu naji ya daki kirjina. Ina ƙoƙarin mik'ewa ya kuma danne ni. Sai na tuna wani hira da naji a gidan Radio BBC Hausa da Baba Yake sauraro. inda me tambaya yake cewa a hada shi da likita yayi mishi bayani shin mahaukata suma suna da sha'awa akan mata ko maza. Nan likitan ya yi bayani tare da cewa.

"Halitta ce sha'awa, kuma tana jinin kowani irin jinsi mutum ko dabba, dan haka suma mahaukata suna da ita."

      Wayyo Allah na, na faɗa a raina da sauri na fara ƙoƙarin kwace kaina. Amma ina haka ya danne ni, tare da niman kwayar idanuna.
"Hammah don Allah tashi kaji, ya hakuri ka tashi bani da karfi irin naka."
Kamar wanda yaji abinda na faɗa mishi sai gani nayi ya tashi a hankali, tare da janyewa daga jikina, da sauri na dira a gadon ina niman hanyar fita waje, ai kuwa ya biyo Ni.

    Allah ya hada ni da bindi, domin duk inda nasaka kafa yana biye dani, har niman faduwa yaƙe idan yana bin bayana, haka na dafa mishi abincin duk da babu dad'i domin har yanzun ban iya girki ba, kuma dai sai a hankali baki daya rayuwana ban tab'a shiga cikin al'amarin girkin Inna sosai ba, ina yi amma ba wai ina nufin na iya bane. A'a Kawai ina yi ne sabida kar na mutu da yunwa.

Ina juye mishi na zuba nawa na fara ci, kamar yadda nake ci. Rike hannun shi nayi sabida nashi cin a haukace ake yinta, ina ci ina nuna mishi. Haka shima yake ci a hankali yana kallona.

Har na gama ci na sha ruwa sai cin nashi yaƙe, kuma abin da j fahimta shine bai san koshi ba, yayi ta durawa kamar yaro karami,dauke filet din nayi, wani irin narke min yayi da fuska sai da tsigar jikina ya mike min, ina ganin kwayar idanun shi cike da wani irin maiko, yana tara kwalla.

Murmushin jin dadi nayi tare da cewa.
"Kaga idan kaci kadan sai kasha ruwa, sai ka bar inda iska zai shiga, fadar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne, a raba ciki kashi uku daya abinci daya ruwa daya kuma iskar da zaka shaka, idan kuma ka nace sai ka cika cikin ka ina zaka samu inda zaka sha ruwa?"

Kura min ido yayi yana me lashe bakin shi pink dashi, kurawa bakin idanu nayi gasu da wani irin fadi dai dai misali. Ga gashin bakin da ya zaga bakin, sai karan hancin shi, dara daran idanun shi masu matukar kyau da haske.

Mik'ewa nayi zan tafi ya riko hannuna, juyawa nayi ina kallon shi.
"Kana son wani abu ne?"
Shiru yayi yana kallona, a hankali na janye hannuna daga nashi. Ina barin kitchen yana biyo ni. Da sauri na fice kamar dama haka yake jira, sai ji nayi ya fad'i a bayana nima na fadi, ina jin wani irin yanayi a jikina, juyawa nayi na ina kallon shi, sai zare ido yaƙe.

"Tashi a kaina babu kyau kaji" kamar wanda ya san ma'anar haka ya mike da sauri, yana me d'agani. Kafin na Fahimci nufin shi ya dauke ni cak. Ya wuce dani sama, yana zuwa bakin kofar ya kwala Ni da kasa ji kake timmmm. Yayi wucewar shi cikin dakin abinshi.
"Dalla dube shi basamude a gurin zaka karya min k'uguna."

Na fada ina jin kwalla a cikin idanuna. Ganin ban taso ba ya kuma juyowa zai sintume ni da sauri na tashi ina zare idanu.
"Yanzun ka makani da kasa kace zaka kuma daukata ai ko daga birnin mahaukata irinka nake na zan yarda ba balle daga birnin masu hankali na fito."

Na fada ina mishi mugun kallo, tsayawa yayi.
"Kuma ka bar kallona katon kawai"
Da sauri ya sunkuyar da kanshi, karasawa nayi gaban shi, tare da tsagalgale shi da masifa, ina yi da baƙi, hannun nayi, wato d'ago kai yayi tare da kallon bakina. Sannan ya fashe da kuka. Zaro idanu nayi ina kallon shi.
"Toh kayi hakuri" na fada mishi ina mi d'age kafana ina share mishi kwallar da yaƙe, murmushi yayi tare da kai hannun shi kan hanci na, yaja da karfi zunzurutun mugunta.

"Auchewww! Kaga mugunta sake min hancina.....
*_🤣🤣🤣🤣🤣 Mahaukaci kenan, sorry wallahi mun fasa Chakwakiyyar rashin wutar lantarki 🤣🤣🤣 Wallahi sai a hankali domin kuwa ban san iya adadin lokacin da zamu dauka kafin mu samu wutar ba, so please zaku ji Ni shiru idan kunga update toh wallahi mun sami wuta ne idan baku gani ba sorry nagode sosai da ta'aziyar da kuka min Allah Yasaka da Alkhairi nagode sosai_*
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
https://www.wattpad.com/1099088650?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=4lwvUq4CDNgGO6G8hSqWOpKF0xTz1GVp6y7Sxeme%2Fg5OCwGdT5AJbfyarf93zolA7FBbhl2FOh%2FpFU0pdrB84Lq2xdZkHArH%2Bvs7uiWokSFzxRJ27Z5Ikm4Ezg7evEig
Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA SHA BIYAR.

"Sake min hancina!" Na maza na kwace kaina a hannun shi ina lailaya hancin nawa, kamar zanyi kuka. Harara shi nayi tare da cewa.
"Maza zauna a nan na shiga ban daki na yi wanka." Na nuna mishi inda zai zauna na shiga ban dakin.

Sai da na shirya sannan na fito, na same shi yana zaune kwayam.
"Kayi hakuri kaji na Barka kai ɗaya a daki."

Bai kula Ni ba, kamar yadda ban saka rai zai amsa ba, haka na cigaba da uzurin gabana, ban kuma bin takai shi ba, domin abubuwa da zanyi na maganin shi yana dayawa, dan haka na shiga haɗawa ina kaiwa ban daki nasaka shi ya cire kayan shima da kokuwa, haka na samu ta cire na fito na kira Hammah Malik yazo yayi mishi wanka Tunda suka fara yaƙe rawan sanyi.

    Har suka gama ya fito, na shafa mishi addu'o'in, sannan ya kwanta, ban yi tsammanin zai yi barci haka ba, sai gashi yayi dan haka ma na fita na barshi a dakin nayi sallah, ina idarwa na kuma leko shi, ina dawowa na samu bai farka na, dama Baba ya gaya min zai ta yawan barci.

  ***
Kasa zama yayi ya kasa tsayuwa. Kallon Mutallab yayi sannan yace mishi.
"Kasan me? Ba zan iya boye maka abinda yake raina ba, amma wallahi ina masifar kaunar Almamoon" ya faɗa a sanyayye, yana kallon yadda Mutallab ya sake baki, mik'ewa yayi zai fita Ansar ya riko hannun shi.
"Don Allah saurarre ni mana" fauce hannun shi yayi yana zare mishi ido.
"Shika min hannuna, da alamu ka haukace? Ba banza aka yi ta muku kallon masu soyayyar jinsi ba, ashe da gaske ne soyayyar jinsin kake ina zaka kai..."

"Dalla ka min shiru, ka bude banzan bakin ka sai maganar banza kake yaron nan mata maza ne!" Ya fada da karfi, zaro idanu Mutallab yayi tare da had'iye yawun.
"Kasan me yasa na gaya maka? Saboda ina son Yaron ne kuma zan taimaka mishi ayi mishi aikin ya tsaya a mace, wallahi ina masifar kaunar shi. Please my Friend kai ɗaya ne zaka taimaka min shi yasa na maka maganar please"

    Ajiyar zuciya yayi yana kallon shi, Kafin yace mishi.
"Ban san me zan ce maka ba, amma na tausaya maka. Kuma idan na boye maka yadda rayuwa take yana da hatsari, idan yaron nan yana son ganin shi a mace falillahamdu idan kuma ya fison ganin kanshi a matsayin mata maza TOH karka tirsassa mishi ayi abin da zai saka kowa damuwa."

       Riko hannun shi yayi sannan ya ce mishi.
"Na sani, amma abin mafi alkhairi shine a dawo dashi jinsin da ya fi karfi idan aka ce lallai sai an jira ra'ayin shi ba zai yarda ba."  Shiru yayi na wani lokaci  kafin ya cigaba da cewa.
"Tukun kasan inda yaron nan yaƙe? Kasan a inda yake rayuwa? Yana tare da dan primer minister ne, kuma abin takaicin tunda yagan shi ya makale mishi.

     Wallahi ina tsoron kar yaje a lalata goben shi! Ina tsoron kar abin duniya yasa a lalata mishi mutuncin shi, don Allah ka taimaka min ta yadda zan shawo kanshi."

    Shiru Mutallab yayi yana gyada kai kamar kadangaren da ya sha rana.
"Yaushe kenan zamu hadu da Almamoon din, tunda kaga kun kusan komawa makaranta?"

   Ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanun shi yana kallon yadda Almamoon shi zai koma da yan nonuwa a kirjin shi yana takun kauna a dakalin zuciyar shi. Tashi yayi zaune yana faɗin.
"Insha Allah ranar friday"

         Wani irin murna yake ji sabida yana hango yadda zai yi da Almamoon indan Allah ya nufa ya zama nashi. Kuma yadda zai sarrafa santalelen cinyoyin shi,(da gaske ashe su Mom Sayeed da Maman Sadeeq basu yi karya ba hauka kake tuburan team Ansar 🤣🙆🏾‍♂️😭)

***
Zaune take tana ta haɗa aikan da ka kawo mata daga gidan ministan harkokin wajen tana gani tana murmushin mugunta domin haɗin na musamman ne, dan haka ta kira Babban matakin mai tuka jirgin saman fadar.

"Maza ku shirya gani nan zuwa Maradi zani"
Kashe wayar tayi tare da ɗaukar jakarta tana me jin a ranta shi kenan daga wannan haɗin Insha Allah Mohan Mamman Nasir Aghali ya tafi har abada.
.... Dakin Hajiya Lateefah ta shiga daga bakin kofar ta shiga matse kwallar fuskarta tana faɗin.
"Hajiya yanzun don Allah ba zaki ki ga jikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login