Showing 63001 words to 66000 words out of 177131 words

Chapter 22 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

17129

ta amai, kakarin yaji ya farka. Yana tashi ya rungume ni, na cigaba da sheka mishi amai a jikin shi da jikina, sai da nayi aman tas a jikin mu, sannan ya daura kaina a kirjin shi ina jin kwalla na zuba min. Shafa bayana yake tare da cewa.
"Sannun"
Murza kai na nayi a kirjin shi, ya tab'a wani abu, sai ga nurse sun shigo, dan haka ya basu guri suka gyara min jiki shikam fita yayi daga asibitin ya koma gida yayi wanka tare da wanke kayan, sannan ya mai da wasu kayan, ya dawo asibitin ya same ni jingine.

Gashi kayan ya fidda kirjina, sau daya ya kalle ni bai kuma kallona ba, ya mai da hankalinsa gurin rubutun da suka yi.  Kallon shi nake bako daya ya cika min idanuna. Hada min tea yayi tare da zama yana diba da karamin cokali yana bani a baki, amsa nake ina me kallon shi. Har ya gama ya bani magani, sannan ya dawo inda kafana yake yana matsa min su. Mamaki yake bani babu ruwan shi da magana tun sannun da yace min bai kuma magana ba.......

_🙄 Wallahi Na kusan fara rashin Daraja hmmm bana son na dauke labarin daga Wattpad kuma wallahi idan na cire zan dakatar da rubuta shi baki daya ne na Fara na kuɗi na shi kuma zai kai Okada Insha Allah ku bani had'in kai bana son ma fara book din kudi na dakatar da Wannan kuma bana son na sayar da labarin! Idan kuka bari na dakatar tabbas zamu ji babu dad'i bana son haka shi yasa nace kuyi comments da Vote idan babu Insha Allah Ranar Monday Zan fara KISHI a tsakanin zubda jini........iya comments da Vote kawai na bukata domin akwai mutanen da suke buƙatar Bororoji ya koma na kuɗi amma nace a'a kuyi wani abu ko nima na fara rashin Daraja kuma ba iya Pagen nan ba all Pages da masu zuwa👏🙄 Wallahi na iya rashin Daraja na fitar hankali musamman akan Zanen kaddara ta 🤸😒😏😡_
[7/25, 9:44 AM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

_Eh toh nayi ritaya daga Rashin Daraja! Sai dai kuma an koma Gaba gad'i🤫_

BABI NA ASHIRIN DA HUƊU.

Kura mishi ido nayi, ina son ya kuma ce min koda Sannun ne amma fir yaki kallona, da na gaji da zaman kurame yana miko min tea din na dauke kai na. Sake tura min cokalin yayi na kauda kaina. Ajiye kofin yayi tare da mik'ewa yana duba maganin da zai mika min. Shima naki kallon shi sai ma ƙoƙarin sauka akan gadon da nake yi.

    "Ina zaka?" D'ago kai nayi ina son kallon shi amma yalwataccen gashin kaina ya hanani ganin shi sosai. Sake yunkuri nayi tare da zamowa zan fad'i, cikin wani irin kulawa ya tare ni.
"Gida zan koma" na fada mishi ina maida numfashi.
"Ok ince kana da kudin jirgi?"
D'ago kai nayi ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, tare da kokarin kwace jikina, a hankali ya mai dani saman gadon, sai shesshekar kuka nake? Daukar rigar shi yayi tare da wayar shi ta fita. Bai damu da halin da nake ciki ba. Koda ya fito shekar isa yayi tare da fesarwa. Sam bai iya rarrashi ba, asalima kanen shi basa rikici wannan da alamun shine auta a gidan su, shi yasa bai rena kuka. A hankali yake walking a cikin  harabar asibitin hannun shi zube cikin aljuhun rigar shi. Karar wayar shi yaji sannan ya dauka.

   "Ya?" Ya tambaya,
"Ya me jikin?"
"Am think da sauki"
"Mohan anya kana kula da lafiyar shi kuwa?" Inji dan Ba'are,
"A'a Alhaji ina ganin me zai hana ka kwashe min albarka tunda ka bani aiki na gaza" ya faɗa tare da shafa kanshi,

"Toh tunda haka ne ai gwara Ansar yazo gare shi" ya caka mishi bakar magana yadda shima zai ji zafi, tsaki yaja tare da katse kiran, yana me jin haushin Dan Ba'are kuma yadda yake ji da zai same shi dan Ubanshi sai ya kirb'a mishi naushi a fuskar shi. Da dan sassarfa ya nufi cikin asibitin.

Yana shiga ya same ni na cusa kaina a tsakanin cinyoyina ina kuka, banging kofar yayi da dan karfi wanda ya razana ni. Na d'ago kai ina kallon shi wani b'ata rai yayi sama da koyaushe.
"Oya dauki tea ko na zane ka" ya nuna min kofin, kallon shi nayi naga yana niman inda zai zauna. Bayan ya leka inda yake saka cajin shi. Wayar cajin ya dauko. Ban manta ranar da Malam Ansar ya zane ni ba, jikina yana rawa na dauki shayin. Na kafa kai na fara sha, yayi sanyi toh kuma  sai na fara jin zan yi amai.

   "Idan ka sake ka min amai sai na zane ka" ya zaro min idanun shi. Gyada mishi kai nayi tare da kurb'an ruwan tea din, ina sha ina shafa wuyana. Ina gamawa na je ajiye cup din kawai ya fadi kasa, ya tarwatse. Kafe ni yayi da ido.
"Kayi hakuri ba da gayya bane"
" A cikin albashin ka" ya faɗa min tare da dauke kan shi. Tunawa da nayi, ina aiki dashi ne dan na saya mana gidan da zamu zauna na budewa Babana shafi saura kadan na karasa kudin gidan ban san lokacin da na fashe da kuka ba. Domin nasan kawo ni asibitin ma da kudina ne.

       "Hammah Mohan" a masifance ya kalle ni, sunkuyar da kai nayi ina kallon kasa. Share ni yayi ya cigaba da duba wasu takardun shi, yana turawa a Laptop din shi, da na gaji kwanciya nayi ban san lokacin da barci yayi gaba dani ba.

             Jin ya daina sauraron kananun kukan shi ya sashi d'ago kai, sai ganin shi yayi yana barci.mikewa yayi tare da gyara mishi kwanciyar shi, ya lullube shi sannan ya koma ya cigaba da aikin shi. Wayar shi ce ta dauki kara, ya kurawa Number ido, wanda ya saka.
"Abbu" cikin sanyin jiki ya dauka tare da sallama.

"Babana ka kyauta? A ce tsawon lokaci bamu nime ka ba kai ma ba zaka nime mu ba? Toh duk inda kake ina son ganin ka cikin sati me zuwa kana jina?" Gyada kai yayi kamar yana gaban shi yace mishi.
"Afwa Abbu Insha Allah"
"Khalil ne ya bani Number ka da ba zaka tab'a niman mu ba, ina kewar ka."
"Nima haka" ya faɗa a sanyayye, kafin suka yi sallama,

   Har zai ajiye wayar yace mishi.
"Abbu don Allah karka gayawa kowa na sami lafiya kawai ka bari na zo da kaina."
"Insha Allah" ya faɗa a sanyayye kamar Mohan din, kashe wayar yayi tare da kura mishi ido, yana kewar shi sosai. A fisge ya kalli inda Almamoon yake kwance yanzun dai ganin likitan da yake son ya kai Almamoon ya fasu kenan.

         Tunda sun tattauna da Dr Hisham Hadid, ya haɗa shi da wani likita a China Dr Zenrog Chuo a garin Yunnan, amma babu kome insha Allah zai fara tuntubar iyayen yaron dai yana komawa dashi gida gaban iyayen shi zai kai shi kuma su saka idanu akan shi.

         Kaf idanun shi yayi akan hotunan da Dan Ba'are ya gama hada mishi kome, murmushi yayi sannan yace.
"Best friend like no other" yana gama abinda zai yi ya Laptop din ya fita tare da zaga garin.

Bayan fitar shi da awa daya na farka, tashi nayi sakamakon ciwon cikin da ya dame ni, sosai nake jin ciwon kamar zan yi hauka. Haka nayi ta fama har nurse biyu suka shigo. Ganin basu shawo kan matsalar ba suka fita, sai ga likitan sun zo dukkan su mata ne..

   Sun jima a kaina kafin suka shiga tambaya na.
"Al'adar ki dama haka yake miki da ciwon ciki?" Gyada masu kai nayi. Tambaya ma marasa kan gado sai dai abinda na Fahimta suna min kallon mace ce sai da Dr Hisham Hadid ya shigo ne suke gaya mishi.

Nan take gaya musu matsalar da nake fama dashi na jinsi biyu sai na zama abin al'ajabi a cikin asibitin domin sun gama tare da saka min ruwa da allura, na fara barci. Bai shigo ba zai karfe bakwai na dare.

Lokacin kuwa ina jin kamar na jika jikina baki daya, kuka nake sosai domin babu kowa a tare da ni, kuma bana son daurawa nurse din damuwa, shigowar shi ya same ni ina shashekar kuka. Takowa yayi a hankali yana kallon fuskana.

          "Ya ilahi sowie me kake bukata?" Ya tambaye ni,
"Ban daki zan shiga ina son na gyara jikina."
"Ok ok!" Ya shiga ban dakin ya gyara min ko ina, sannan yazo ya d'aga bargon tare da taimaka min zan sauka idanun shi ya sauka akan farin zanin gadon.

      "Me...me...me.. zan gan..." Kura mishi ido nayi domin bai san halin da nake ciki ba. Sai yau ban san yadda aka yi kunya ta kama Ni ba, na fashe da kuka tare da komawa zan zauna. Cak ya d'agani tare da nufar hanyar ban dakin ya ajiye Ni a bakin jacuzzi tub din da ya cika da ruwa me zafi, sannan ya fito cikin kyankyame ya tattara zanin gadon,  ya bude wardrob din dakin ya ciro wani ya shimfid'a min sannan ya kawo ban dakin bayan ya buga kofar, gyaran murya nayi. Na nutsa ruwan zafi ina jin wani irin dad'i kamar zan yi ihu domin jikina ciwo yake kamar an murkad'e ni.

     A hankali nake wanke jikina bayan na gama na daura babban towel, a hankali na bude kofar bayan na rufe kaina, ganin zanin gadon nayi tare da tsugunawa na dauka. Sannan na shiga ban dakin na fara ƙoƙarin wankewa. Hannun shi naji a saman nawa.
"Ba aikinka bane, ko nace ba aikinki bane aikina ne ko kina kokarin b'oye yanayin ki ne?"

              A hankali na fara ƙoƙarin tashi a tsugunon, amma dake shi din Kamar bishiyar kuka ne sai wani kewaye juna muke. Da sauri na juya, kamar zamu shige jikin juna. Ya tsare min hanya, jikina ne ya shiga rawa,
"Relax!" Ya fada min yana niman kwayar idanuna, babban damuwar hannuna daya yana kan towel din kaina da na rufa daya kuma yana rungume na kirjina, domin har kwanjina yake.
         Lallubar hannu na yayi tare da daura min pant da audugar matan, yana ƙoƙarin na d'ago kai na yaga yanayin da nake ciki amma fir naki asalima kokarin rike towel din nayi tare da cewa.
"Hammah" ƙaran wayar shi ya sa shi juyawa zuwa waje, da sauri na jingina da kofar jikina yana wani irin rawa, tare da lumshe idanuna, na dauki Pant ɗin na daura audugar na saka, sannan na bude kofar da niyyar fita, ashe shima yana bakin kofar yana son ya buga kofar dai gashi ya buga goshina,  cikin wani irin tsoro naja da baya tsantsi ya kwashe ni.
       "Hammm!!!" Na fada da karfi tare da sake towel din kaina, na tafi da baya na kirjina kuwa na rike gam, wani irin riko ya kaiwa k'uguna,  a tsorace na fada kirjin shi tare da sauke wata irin ajiyar zuciya. Cak ya d'ago ni, wani irin rawa jikin shi yake karon farko da ya kusanci wani abu me sunan kusanci. Shima din na mata maza,  a sanyayye ya kai ni bakin gadon yana kallon yadda gashin kaina ya baza fuskana na da jikina baki daya naki yarda mu kalli juna ma balle naga katob'arar da muka yi, wucewa ban dakin yayi ya wanke kayan da na b'ata, kafin ya fito har na gama shiryawa kuma ina kyautatta zaton ya bani damar ba shirya ne, dan haka ina gamawa ya fito.

   Ya shanya kayan a ban dakin, ya zo ya zauna yana kallon yadda nake juya kafana, mik'ewa yayi yana me zama a bakin gadon ya shiga tausa min kafar, kwanciya nayi tare da lumshe idanuna, a hankali barci yayi gaba dani.

     ***
Niamey.
Yana wayar ta shigo bata san da wa yake ba, dan haka yana gamawa ya zuba mata ido.
"Mai gida dawa kake waya haka ka saukar da kanka kamar shine sama da kai?"

Bai yi mamakin maganar ta ba amma yayi al'ajabin yadda take Mantawa da halin da Yaron su yake ciki.
"Kina waya da su Haddir kuwa?" B'ata rai tayi tare da cewa.
"Idan ma sabida su ka tsayar dani sai an jima, Lateefah" cak ya tsaya.
"Kaga Ni zan tafi bikin yar gwamnar Jahar diffa wacce dan ministan ilimi ya aura sun turo min katin dinner zan tafi!"

     "Allah ya shirya ki" ya faɗa cike da mamaki, domin kuwa yasan halinta.

    "Assalamu alaikum! Sannun Yallabai, kai ɗaya ne?"
"Eh Safiya"
"Yallabai ga wasu takardu ko zaka Duba mana su na kwangila ce."
"Toh kin san dai na dauki hutun karshen shekara idan na sami lokacin xan duba."

"Yallabai yana da kyau ka duba, nasan da ace Hajiya Lateefah ce da ka duba amma dake Ni bani da arzikin ka duba shine ka ajiye min." Ta fada tare da mik'ewa tana me son fita.
"Idan Allah ya kai mu nan da wata me zuwa zanje duba Mohan" ta faɗa tare da kallon shi ko yanayin shi. Bata rai yayi tare da mik'ewa yana jan tsaki, murmushin jin dadi tayi tare da bin bayan shi da ido.
"Har yanzun tarkona yana kan kama kurciya."

Ta fita daga falon, tana me jin lallai tana da Sa'a shi yasa ta rike wuyar primer minister.

   ***
Damagaram.

"Malam yau watan Almamoon biyu bai zo ba bayi aike ba?" Inji Innar shi.
"Insha Allah duk inda yake zai dawo cikin amincin Allah"

Shiru suka yi sannan suka shiga wani zancen duniya,

   Sosai yake nuna mata fa'idar yarda da ƙaddara me kyau kalmar kyau, tare da labarta mata abinda yake faruwa.

   ****
Riyadh.

  Wasu kwanakin da suka tawo Alhamdulillahi naji sauki sosai asalima kokarin barin kasar muke,domin dai ina fita waje daga haka bana zuwa ko ina.  Ranar wata Alhamis aka sallame ni, sannan muka shiga cikin garin Makka nayi Umrah, bayan mun gama muka juyo.

     A hankali nake takawa shi kuma sai sauri yake, wani dan kasar Mali ne ya riko hannuna.
"Kai dan kasar Mali ne?"

    Juyawa nayi ina kallon Hammah Mohan yayi nisa.
"A'a Ni daga Nijar nake!" Na fada mishi ina ƙoƙarin kwace kaina,
"Toh me ka zo yi?" Ya tambaye ni, yana ja.

"Sake ni na tafi" ina kara bin hanyar da Hammah Mohan yabi, dake lokacin dare ya fara, domin bayan sallah isha ne.

"Hammah Mohan!!!" Na kwala mishi kira ina tsalle, haka mutumin ya cigaba da jana haka kawai ban san shi ba.

   Bai juya ba, amma haka kawai yake jin kamar akwai matsala dan haka ya juya tare da dubawa ko ina bin shi. Da sauri ya ware idanun shi babu Yaron shi. Baya ya dawo yana niman shi, can nesa yajiyo muryan shi. Da sassarfa ya isa gurin lokacin da mutumin yake kokarin shigar dani wani lungu, bayan ya daki kafana wanda naji karan shi har cikin ruhina.
"Wayyo Allah Hammah na ina kake" na fada da mugun ƙarfi,d'aga hannu mutumin yayi zai mare ni, aka rike hannun shi, tare da murɗa hannun sai da yayi kara, sake murɗe hannun yayi tare da cewa.

"Kafin ka zalinci mutum ka fara duba waye a tare da shi, ba iya shi ba!"

"Hammah kyale shi na yafe mishi." Sabida yadda naga zai cire mishi hannu, sake jijjiga shi nayi ina magana.
"Karka kashe mana" na fada ina zaro idanu, sabida yadda mutumin ya kai kasa baya motsi,
"So What! Idan wani ya tab'a hannun ka hukuncin shi a cire hannun shi, idan yayi kuskuren tab'a jikin ka wallahil azim mutuwa ya cancanta ba rayuwa ba." Ya fada min da karfi, a tsora ce naja baya, ina girgiza kai.

    "Ban yi deserved  haka ba matsayina mai maka aiki ne kuma na gama, don Allah karka janyowa ƙaddara ta, wata masifar."
Cikin fushi ya fisgo ni,
"Wayyo kafana" a rikice ya kuma durkusawa yana kallon kafar, musamman wuyar kafana da ya kumbura sosai, a hankali ya ciro min cambus din kafana, sannan ya mika min, ina shirin mik'ewa nayi yayi sama dani. A tsora ce na kalle shi. A raina ina faɗin.
*I do not know how you are destined to bring me into your world, but one thing I know is you are my life, I will continue to follow you like a slave I will stay by your side like a dog and my Lord, I will stay with you until you open for me the door of your heart to respect your cause*
(Ban san yadda aka yi ƙaddara ta kawo ni duniyar ka ba, sai dai abu daya na sani kai ne rayuwata, zan cigaba da binka kamar baiwa zan zauna a gefen ka kamar kare da Ubangida, zan ta zama da kai har lokacin da zaka bude min kofar zuciyar ka girmama al'amarin ka)

Tafiya yake hankalin shi kwance, bai damu da ina da nauyi ba, bai damu da ni din ina da tsayi ba, kawai abinda ya sani yana tafiya ne a tsakanin wasu abubuwan na musamman, sannan bai ji kome ba sai ma wani irin nutsuwa da yake samu, abu daya yake damun zuciyar shi baya iya hakuri idan yaga wani ya taba Yaron har cikin zuciyar shi yake jin abin, sabida shi yake dauke kai akan Ansar dan haka yana shiga masaukin abinda yayi ajiye shi yayi,

Ya koma cikin dakin ya dauko katin shi ya fita, can sai gashi da kayan dauri, a hankali ya tako har gabana ya zuba kayan sannan ya koma dakin shi yana me rage kayan jikin shi ta fito sanye da wandon Nike, sai farin Singlet ya fidda tarin muscle din shi, da sauri na sunkuyar da kai na, yana zuwa ya durkusa tare da janye kafar wandon jikina sama.

Sannan ya cire min daya takalmin, ya zauna sosai bai kuma min magana ba, ya haɗa kankaran a cikin wani towel, ya koma gefe yana mai kallon tv, had'iye yawu nayi cikin tsoro, karar kofa muka ji ya mike, can sai gashi da kayan abincin, ajiye min yayi tare da cewa.
"Oya cinye min"

Kallon abincin nayi tare da kallon shi kamar zan yi kuka nace.
"Hammah ko jaki ne ni ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login