Showing 150001 words to 153000 words out of 177131 words
ita kanta ta san gaskiya ya gaya mata, ita kanta ta tausaya mishi, ta kuma tausayawa yarta, dan haka ta ce mishi.
"Insha Allah zan kokarta na nuna mata matsayinta." Ta fada mishi.
"Nagode sosai" ya mike tare da barin gidan, sannan ta kira Khalil ta gaya mishi, kin yarda yayi da nuna mata gaskiya haka cutarwa ce, domin da a bata mishi abotar shi da Mohan, mutuncin shi da Maimunari take gani ya zube.
Bayani tayi mishi tare da gaya mishi gaskiya ita kanta bata son haɗin, dan haka suna gama wayar ta kira Jalilah ta ci Ubanta da kyau sannan ta gaya mata a abinda yake faruwa. Yar banza dai gata tana ihu da murna, tana faɗin.
"Nice zan auri Ya Mohan! Wayyo Allah na, dad'i kashe ni" ta faɗa tana ihu, takaici da bakin ciki ya sa Hajiya Nuratu ta kai mata duka, cuno baki tayi tana faɗin.
"Ni wallahi ina son shi dama"
"Kaniyar ki da soyayyar yaci kaniyarta, toh shi ba sonki yake ba sakarya kawai."
"Koma meye ni ina son shi" ta fada tana tura baki, dan babu abinda ya dame ta, takaici kamar ya kashe Hajiya Nuratu, domin bata jin a ranta wannan shine hanya bullaliya, abu uku da yake hana mace zaman lafiya a gidan mijinta K'iyayyar Uwar miji, k'iyayyar dangin miji, k'iyayyar miji, wallahi bata fatan ta zauna da Mohan a wannan yanayin na zuciyar shi tana tare da wata. Amma ya ta iya sam Jalilah bata da hankali.
"Umma Idan na aure shi sai na sashi ya manta da Maimunari, wallahi sai na mantar." Make mata baki tayi,
"Kin ci gidanku, ana gaya miki gabar kina yamma, dan kaniyarki ba zaki tab'a iyawa ba, sadaukarwa da matar shi tayi shi kawai ya ishe shi mutuwa da rayuwar shi, ke kin san so? Kina son shi ne sabida yana burge ki ko? Toh ita ta sadaukar da kome nata ne domin shi, dan haka kar na kuma jin kince kina son shi zaki mantar dashi kome!"
Cikin jin haushi ta mike tare da barin gurin ita ta sha alwashin sai ta mantar dashi kowa ma, balle kuma Maimunari. Dan haka ta juyar da kanta lallai zata mantar dashi kome har da soyayyar Maimunari.
**
Diffa.
"Ina sonta Baba, wallahi ina kaunar Maimunari, don Allah Baba ka gaya min me yasa kace na rabu da Ita" sunkuyar da kai yayi sannan yace mishi.
"Ka hakura da ita Hisham mahaifinta ba zai baka ita ba, koda kuwa zaka mutu ka dawo! Ka kyale su ba zaka tab'a samunta ba."
"Baba don Allah ka gaya min meye yasa!" Shiru yayi sannan yace mishi.
"Kasancewar shi Baroro, mutum ne da yasan kan shi, kuma yasan abinda zai yi ya kare kanshi. Ni kuma Mahaifiyata bororo ce mahaifina Bazabarme, shima kuma yasan kanshi, sai dai shi yana rayuwa ne a daji mu kuma muna rayuwa a cikin gari, wani shakara ana bikin sallah, na hadu dashi. Wallahi da farko bani da burin zaluntar shi, sai dai lokacin mun nuna mishi muma bororo ne, yasa ya amince da mu.
Dan haka bayan sallah mun bishi har inda suke anan muna zauna na tsawon wata shida sai dai muzo cikin gari mu koma, ba dan kome ba sai dai Allah yayi mishi baiwar Ilimi na iya sarrafa Alqur'ani yayi abu dashi, dan haka zaman mu bamu tab'a nuna mishi mun zo cutar dashi bane domin ma bama da wannan alamar a ran mu. Abinda yasa muka shiga wannan al'amarin sai dan yadda muke son mu shiga harkan siyasa da wasu abubuwan. Dan haka muka mai da hankali gurin daukar wasu sirrin Alqur'an, bayan mun gama sai muka fara zuwa muka yi fashi, bayan mun yi fashin shine muka gudu tare da kai cunen shi.
Lokacin da ya samu labarin abinda muka yi, shine ya maza ya bar dajin. Aka yi ta niman shi. Bamu kuma haduwa ba, sai a hanyar Mali ya tafi da wata mace, itama kamar bafulatana ce. Dan haka matukar ka matsa kana son Yar shi zai iya tozarta ka, don Allah ka bar mishi yar shi."
Cikin bakin ciki ya kalli mahaifin shi, sannan yace mishi.
"Toh meye ya had'a ka da Abbun!" Kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Shi wannan Sa'a yafi Ni, shi yasa nayi alƙawarin sai naga bayan shi"
"Lallai ka fini son kai, dan haka koda za a dawo maka da gawata, wallahi sai na auri Maimunari, shi kuma Ubanta dole yayi hakuri ya bar Ni da ita."
"Ka hakura ka bar mishi yar shi." Mikewa yayi tare da barin gurin.
"Na rigada na yanke hukunci sai dai a kawo maka gawata, amma tabbas sai na tafi ga abar kauna ta. Idan taurin kai da zuciya dabi'ar ka ce, toh ba makawa na gaje ka."
Daga haka ya fice daga dakin da Ubanshi yake, yana kara bibiyar layin Benazir, da ya karba a gurin yar ajin su. Tunda ya saka a kan google ya samo kasar, dan haka ya kwantar da hankalinshi ya gama hada kome zai nufi Zurich.
***
"Baba Mari Sannun kina ta hutawa!" Na fada ina zama, murmushi tai tare da kallona.
"Yo ni da kun mayar dani Nijar da na huta, na gaji da zaman garin nan" ta faɗa tare da kallona.
"Hmm! Babu inda zaki muna tare" shigowa Abie yayi Benazir tana kuka tare da fada mishi ita a'a, don Allah ya amince duk da bana jin English amma na Fahimci kamar an b'ata mata rai ne.
"Don Allah abie kasa baki wallahi na fasa auren shi" gutsiran apple nayi tare da kallon ta.
"Me yasa toh? Idan kinsan baki son shi me yasa zaki bar shi yayi ta wahala?" Na tambaye ta a fusace,
"Addah Munah, ban da bakin munafunci me yasa zasu hada kanwar shi da Hammah Mohan? Wallahi na tsane shi baki daya, ba zan kuma aure shi ba"
Wani abu naji ya tsaya min a wuya, kafin na had'iye tare da sake murmushin takaici, sannan nace mata.
"A'a karki b'ata soyayyarki akan wani banza da bai san hakkin so ba! Dan haka ki gyara tsakanin ku da Dan Ba'are, bai da matsala" na cigaba da cin apple din, shi kan shi Abie dariya yake mata domin tun d'azun take mishi bori ita kuma gashi nan tazo na gwatsale ta.
"Addah Munah! Haka zaki ce?"
"Toh don Allah me zance miki? Shi yasan me yasa ya gaya miki ai? Tunda Kinga ya iya gaya miki toh sako ya baki, dan haka ki ajiye batun zaki b'ata soyayyar ki dashi, domin babu amfanin haka, tunda yana sonki kuma babu amfanin kiyi fushi dan kawai Mohan zai auri kanwar shi. Sai kiyi fatan Alkhairi ba wai kizo kina cewa kin fasa ba."
"Addah Munah!"
"Kinga karki b'ata soyayyarki, domin kuwa wasu na niman damar da kika samu amma basu samu ba."
Ina gama fadar haka na tashi na bar musu gurin, na nufi can backyard, na zauna a kujeran da yake gurin, kwalla ce ta shiga zuba min ina sharewa amma kamar sake tulo shi ake wato har Mohan yana da kwarin gwiwar aure..
*Don Allah yau ku barni na huta na gaji baki daya👏🏼 wallahi*
#Mai_Dambu..
[8/14, 10:44 AM] Joindah: https://www.wattpad.com/1115269487?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=I5OLVif069AImr78w%2FlEumcHUFhhjB3GL%2BklLGDEG2mX72ge1I4j4pFlSrPzq7qgVMUX54J2flC9h4g6fi2m%2FvewJigtCSmbiskTJxpG%2BKNCCPD6AHygfMZwtAY2jz%2F0
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA SITTTIN DA ƊAYA.
"Wato nice zai tozarta nice zai mai da ba kome ba, bayan faffutikar da nayi dan na same shi amma sake subuce min yayi, meye nayi mishi? Dama duk abinda yake fada min karya ce, dama ba zai tab'a tayani kuka ba, lallai yanzun na gane kuskure na."
Sosai nayi kuka nayi bakin ciki tare da zama gurin, naki shiga cikin gidan domin kar a ce min ma nayi kuka dan na damu da Mohan, na san ina son shi amma ban zaci haka daga gare shi ba, wacece irin k'iyayya Ammyn take min haka da ta gwammace ta rabani da abinda nake so! Babu damuwa na bar mata Mohan ba zan kuma damuwa dashi ba.
Dafa kafadana Mommy tayi bayan ta zauna.
"Bayan na tafi na barki zama cikin kad'aici yana daga cikin abinda Dr Khalid yayi yaki akan shi domin na tsani zama cikin jama'a, bana son magana da kowa. Kinsan yadda nake ji a lokacin. Ismail ya lalata min kome na, ya rabani da iyayena da kome nawa, uwa Uba na rabu da abinda na haifa, sau uku ina samun ciki da zaran nayi mafarkin abinda na bari zai lalace.
Ina da yakinin hakkin abinda na bari yake bibiyata, ban wartsae da haka ba, kawai na fara fuskarta matsala daga Mahaifiyar shi, nasan yadda kike ji, amma ba zan iya cewa ga yadda naji ba, Maimunari nayi kuka na roki Allah ya dauki rayuwata da halin da nake ciki da Surukata, ta tsane ni dan ban haifa mata jiki ba,.gashi Yaron nata iya shi daya Allah ya bata, Maimunari ina gaya miki ne dan na yarda dake, amma a lokacin idan da zan ga mutuwa zan so shi sama da kuncin da nake ciki.
Khalid sai da ya juya min baya sabida mahaifiyar shi, ba dan kome ba sai dan ya dakata farin ciki, nasha tambayar shi dalilin da yasa yake kin kulani. Murmushi yake kawai, domin karfi da yaji hajiyarshi ta dawo Paris, kuma haka yake kokarin ganin ya kyautatta mata amma baiwar Allah nan, bata fasa gasa ni ba. Haka na hakura da ita har Allah ya amshi rayuwar ta, ban tab'a fushi da shi ba, domin da ya fahimtar dani yana hana ne domin kar ta tsananin ta, k'iyayyar da yake min ya sani kara kaunar shi. Hajiya tayi fatan taga abinda xan haifa sai gashi ina da cikin Benazir Allah ya amshi rayuwarta, kin san me? Tana da kirki amma saboda son da takewa D'anta yasata juya min baya, Maimunari duk tsanani yana tare da sauki, duk wanda kika ga ya zama wani toh kafin ya isa gurin waye shi.
Na sha zama na duba wata irin ƙaddara ce take bibiyar rayuwata? Na zata kawai dan abinda ya same ni ba zan kuma fuskarta wani matsala ba, sai gashi bayan rasuwar Hajiya Khalid yan uwan shi sun kuma juya mishi tunani, su dai lallai yayi aure, a lokacin bani da wanda zai tsaya min sai Allah, nafi yarda da cewa hakkin abinda na bari yake bibiyata.
A lokacin na kuma bazara rayuwar mutane, ba dan kome ba sai dan yadda nake kokarin na kyautattawa dangin Khalid haka bai saka sun kaunace Ni ba, idan har zamu je hutu Nijar haka xan hada musu shatara na arziki, amma ashe duk abinda nake musu ba, bai musu ba su dai kawai Khalid ya auri yar dangi kin san yadda hankalina ya tashi, haka kawai suka kirkiro bala'i da tashin hankali a tsakanin mu, ina ji ina gani abu kadan zanyi ya fusata Khalid, gashi har lokacin Benazir nake goyo, gashi babu wani nawa, bani da kowa sai shi. Shima ya juya min baya.
Munah ina ji ina gani na zama mahaukaciya, karatun da yake biya min ya daina, dan inda nake jin dadi ya katse min, sabida kawai yana son auren wata Yar uwars shi, ban kuma tsinkawa dashi ba, sai da aka gama kome ana jibi daurin auren ya gaya min, haka na saka shi a gaba nayi ta kuka, amma bai saurare ni ba, haka suka yi al'amarin auren su. Ranar da ya tafi Nijar dakyar ya ajiye min abinda xan bukata na sati Uku, amma da ya tafi sai da ya share wata biyu, a lokacin na ga tashin hankali da damuwa, bani da kome sai da ta kai ina fita bakin hanya ina rokon abinda xan ci Ni da Yarinyana, sannan na kawo mana gida a girki.
Haka bai saka na samu sassaucin rayuwa ba, domin kuwa idan yarinya bata da lafiya, haka zan ta roko ina Bara."
Goge kwallar da yake zuba tayi sannan tace min.
"Ban rike shi ba, domin har lokacin ina mishi fatan sauki da salama, ina cikin wannan yanayin wata baturiyar London ita ta taimaka min na samu aiki a wani gurin girki, ban boye mata ba ina karatun likitanci, haka ta kuma nima min damar na koma makarantar, ita kuma Yarinyar da nake goyo ta gaya min na dinga kaita gidan reno, haka ce ta faru da dan albashin da nake samu nake rufa mana asiri, bayan wata biyu ya dawo, ashe ya kamawa matar wani gida mai kyau, dan haka sau daya yake leko ni, haka zai yi tafiyar shi ba tare da nasan yana yi ba, ana cikin wannan yanayin har muka shekara uku, yana zuwa min kullum da yamma, ko da safe. Benazir tana da shekara uku da rabi da watanin ranar yazo min a hargitse,. Yana kuka tare da niman yafiyana haka na yafe mishi. Bayan na yafe mishi muka koma kamar da.
Wai ashe fada suka yi da matarshi har ta kai shi ofishin yan sanda, ban gama kaduwa ba sai da naga yan sanda sun kawo sammacin shi nan na gane da gaske sun rabu, amma ban wani damu can ba, domin halin rayuwar da suka jefani dai Allah ne kawai ya sani.
Haka suka yi ta sintiri yana ƙoƙarin kare kanshi,kafin matar dai ta bar kasar sai da aka raba dukiyar shi gida biyu, aka bashi rabi,
Ke duk wanda ya yarda da Allah bazai tab'a tab'ewa ba, haka dai na zuba mishi ido, bayan haka yayi ta lallabani muka daidaita, amma ban tsira ba a gurin dangin shi, cewa suke nice na raba su.
Bani Mantawa bayan haka ya faru da wasu watanni muka zo bikin sallah, wallahi a ranar sai da nayi danasanin kasancewata a cikin su, domin kiri kiri suka yi ta zagina da cin mutuncina. Haka ya shigo gidan ya samu abinda suke min. A ranar na Allah ya dawo min da shi, domin birkice musu yayi tare da nuna musu ai duk aiken da yake musu daga Faransa, ba shi yake turowa ba,
Nice shine har suke cin mutumci na, yayi musu bori tare da alqawarin ba zai kuma musu alkhairi ba ya gaji, sannan a gaban mutane ya kira mayar matar shi da suka rabu aka yi magana. Ya gaya musu tunda muke dashi ban tab'a kai karan shi ba, duk da abinda zai min Baba fushi da kawo karan shi, amma ita yar uwar shi ta kai karan shi, wallahi sai da jikin su yayi sanyi sannan yayi alƙawarin ba zai kuma. Dawowa cikin su ba, ba zai kuma waiwayar su ba. Na sha wahala da dangin mijina, amma da yake Allah ba azzalumin sarki bane, sai gashi suna ganin mu, a raye amma babu yadda suka iya, koda ya rasu takardun shaida na filayen shi da wasu abubuwan shi da ta dangance su. Wallahi sun rike, sauran abubuwan kuwa suka matsa lallai sai da aka raba aka cire musu nasu, basu da gadon shi amma haka suka yi ruwa suka yi tsaki, Maimunari. Ina ji ina gani suka addabi rayuwata da na Yarana, zuwan Babanki na samu sauki domin gani suke dan abinda ya rage na hakkin su Yumnah kamar wata tsiya ce yau a kawo min korafin ana niman taimako gobe ma haka, hmm Allah ya taimaka asibitin da nake namu ne tare dashi muka gini badan haka da shima sai sun kwace.
Toh ban san meye baban ki ya gaya musu ba, amma naga sun shafa min lafiya, ban sani ba ko zama zai kuma had'a ku da Mohan, amma ki sani dole sai kinyi hakuri da mahaifiyar shi, sai kin dauke kanki daga kanta, matar da zai aura sai kinyi hakuri da ita, mutane sun kashi gida hudu ne.
Na farko babu ruwan su da kai idan kayi zasu zage ka, idan baka yi ba zasu zage ka, kuma babu me sauya musu ra'ayin su akan ka, kuma babu ruwan su da alkhairi ko sharrin ka. Dan haka dole ka yi hakuri da su domin can dama ba sa yinka kuma babu mai sauya musu alkiblan su akan ka. Sannan suna iya mu'amala da kai kota wani fuska,. musamman idan suka ji ana maganar baka da kirki zasu biyo ka su bincika basu son ka amma zasu duba wannan labarin da kuma waye kai.
Na biyu kuma suna sonka zasu zageka kuma da zasu ganka zasu makale maka, babu domin duk inda suka ganka kai nasu ne, da ka bada baya kai ne tsinannen su sannan idan b'taanci ya fito sune.masu yayyata shi da yadawa a duniya, sannan su addu'a suke Allah yasa kayi ka za domin duniya ta zageka. Babu ruwan su, da kai amma sun fi kowa yayyata sharrin ka, dan haka idan zaka kira makiyi toh su ba zaka kira su makiya ba, su ne ake kira mahassada, suna tare dakai amma basu kaunarka, suna ganin ka zasu ji ran su ya b'aci, ko magana kayi zasu juya zancen ka, ko dariya kai zasu juya shi. Irin wadannan idan kayi sallah biyar da ya wajaba akan ka toh alatilas ne ka saka su a cikin addu'arka wanda zaka hada da falaki da nasi. Sune asalin Original mahassada.
Na uku suka kaunar ka da zasu ga an tab'a ka sai inda karfin su ya kare, amma su suna iya kasancewa basu zama tare da kai, kuma ba ka san su ba. Su din masoya ne na hakika, kuma da wani abu zai had'a ka da su zasu biyar duk wani sharrin ka su fadi Alkhairin ka, irin su basu zama a jikin ka, koda zasu zauna a jikinka ba zasu tab'a fadar alkhairinka akan idanun ka ba, kar haka ya zame maka d'agawa sannan wani abinda baki sani ba irin su basu tab'a nuna miki suna yin ki akan idanun ki, sannan idan da zaki yi wani abu na kuskure baki sani ba, su zasu kare ki, idan da za ayi abu dan ranki ya b'aci su zasu hana shi isowa gare ki, su a cikin rayuwar ka baka san inda suke ba, da zaka yi kuskure zasu kiranka su gaya maka haka irin su suke, a duk inda suke suna maka kauna ce domin Allah da Manzonsa.