Showing 147001 words to 150000 words out of 177131 words

Chapter 50 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

14829

zaku ji ni 😏🤸 kwana biyu ban kafta rashin daraja ba, wallahi har kaikayi nake ji😂🤣
#Mai_Dambu.
[8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA HAMSIN DA TAKWAS.

Kura mata ido yayi yana mamakin yadda Allah ya daura mata son kanta, sunkuyar da kai yayi yana kallon shaddar jikin shi.
"Zan nima maka maganin ko kurwanka ta kama  ta sake maka shi, Insha Allah wannan masifar da me yayi kama."

     Bai ce mata kome ba, haka dai ta gama masifar ta, yayi mata sallama ya bar gurin. A cikin kwanakin bai da lokacin kanshi domin tun da ya rabu da Maimunari ya ajiye aikin soja, sai ya koma kasuwanci, kuma dama yana kasuwancin bai mai da hankali bane. Amma yanzun da ya mai da hankali yana ganin Cigaba sosai.

     Yau da la'asar ya shirya zuwa duba Maimunari, yana isa da kayan marmari da ya kawo mata,ya samu basu asibitin. Ya tambaya aka ce ba. A  san inda suka tafi ba,bai kuma tabbatar da ya rasa Maimunari ba sai da yake gidan Abie ya samu a rufe nan ya gane cewa sun tafi da ita wani gurin ne, haka ya kira Khalil ya gaya Mishi. Amma babu wani labari, da ya sami Abbu da zancen cewa yayi.

"Ban san inda suka tafi ba, amma koma yayya ne ai Mahaifiyarka ta bukaci haka, dan haka idan na isa kuma na haife ka ka kyale musu yar su ta huta, ita ba matar ka bace Yanzun sannan kuma ba zai yiwu uwarka tana tozarta su ba, dan haka na gargade ka da ka fita hanyar ta, ko kuma na sab'a maka."

  "Amma Abbu!" D'aga Mishi hannu yayi tare da cewa.
"Itama iyayenta suna SONTA, kuma babu wanda zai yarda ayi ta wulakanta Mishi d'a. Dan haka ka tafi ka zauna da uwarka ita ka barta da nata iyayen, saboda kai ta saka su a kotu, saboda kai ta wulakanta su, duk sabida soyayyar ka. Indai har zata aikata haka saboda tana son ta dawo rayuwarka amma uwarka taki meye yasa ba zaka kyale ta ba? Me yasa ba zaka hakura da ita ba? Tayi kokari tayi kokari. Don Allah ka kyale ta ta huta Ubangiji ya bata wanda ya Fika kai ma Ubangiji ya baka wacce ta fita."

       Jikinsa ne yayi mugun sanyi, sannan ya mike a hankali tare da nufar hanyar waje.
"Insha Allah na hakura da ita, Nagode sosai Abie"

    Tun daga ranar yayi wani irin sanyi, magana ma bata dame shi ba, baya harka da kowa sai Khalil shima sai yana gari,.ana cikin wannan yanayin me niman auren Radiyah, suka turo har an gama magana, amma mahaifiyar yaron ta tawo da kanta, har gurin Hajiya Latifah.

   Bayan sun gaisa tace mata.
"Hajiya Lateefah nice Mahaifiyar Safwan kawai jiya Mahaifin shi yace min sun zo nima Mishi auren yarinyar da yake nima bai gaya min ba sai da suka gama magana. Toh gani nan nazo na gaya miki gaskiya. Bana son had'a zuri'a dake! Ba dan kome ba sai dan mijinki shege ne bai da asali"

"Keke!"
"Ke yi kasa da muryanki! Indai har uwa irinki zata kashe auren danta ranar da ya kwanta da matar shi, meye laifina dan nazo akan a fasa auren dana da Yarki a? Dan haka ita da kika saka ta wulakanta iyayenta.  Kin ga ina son kaina da arziki ba zan so dan da na haifa ya maka ni a kotu saboda yar ki ba.

    A takaice dai ba zan tab'a barin shi ya auri yar ki ba, da ya auri Yarki wallahi gwara ya mutu bai yi aure ba, balle kuma ga mata kaca kaca."

            Ta mike tana kad'a keyn motar ta,  tare da ɗaukar jakarta, har zata fita tace mata.
"Wallahi kamar yadda kika saka iyayen Maimunari kuka haka zaki yi kuka ga yara mata gasu nan a gabanki"

       Sannan ta fita, yadda kuka san gumki haka ta koma, tana cikin wannan yanayin, Khausar ta shigo dauke da jakar kayanta, niki niki.  Idanunta cike da kwalla,

     "Lafiya!" Ta tambaye ta, zama tayi cikin shashekar kuka, tace.
"Hajiyarsu Abdullahi tasa ya sake ni" ta faɗa hawaye na zuba mata, daidai lokacin da Radiyah take shigowa da nata kayan, kallon su uwar take cike da mamaki.

"Akan me?" Ta tambaya bakinta na rawa.
"Ban sani ba."  Mikewa tayi tare da fita. Dake dama an ce wanzab bai son jarfa, sai gata har gidan Surukar Khausar, ta samu ma suna magana  akan Khausar ne.ta shiga cikin gidan.
"Hajiya Marwanatu lafiya Abdullahi ya sake Khausar?"
"Zauna mana Hajiya Lateefah,ai abin ba na tashin hankali bane"
"Akan me zan zauna"
"Toh ita Yar gidan Babban alkalin bata da zuciya ne? Ko ba haihuwarta aka yi ba? Kinga indai har ke zaki iya sakawa dan gwal irin d'anki ya sake yar mutane bayan kuma kuna da abin kunyar meye a cikin dan nace dana ba zai zauna da yar da aka haifi Ubanta shege ba?"

"Wallahi karya ne, sharri aka mishi."
"Malama fita mana a gida, domin duk nan babu mahaukaci irinki,.dan haka maza a tafi a nimawa yaran ya'yan asali masu kyakyawan nasaba"

Asalin koran wulakancin suka mata tare da gaya mata ai ko mata sun kare babu wanda zai auri yar yaranta, taje itama yaji yadda iyayen yarinyan da ta wulakanta take ji!"

"Wai dan akan Maimunari kuke wulakanta Ni?"  Ta tambaya kamar zata fashe da kuka.
"Kai kunna mata wayar nan ta gani"

Muryanta ne ya fito fili lokacin da take cin mutuncin Maimunari a asibiti.
"Wallahi na rantse da Allah matukar ina raye babu ke babu Mohan. Yar karuwa ribar dadiro. Yar matsiyata an ce miki arzikin iyayenki zai saka na hakura ki zauna d'ana ne? Ko ance miki cikin da yake jikin zan yarda na d'ana ne? Toh ai bari na gaya miki tun wuri gwara ki nemi uban cikin jikinki, yar matsiyata jinin kazamta."

"Kai kashe min idan ina jin wannan abin ji nake kamar na tattara yaran da Abdullahi da Khausar suka haifa kamar a watsar da su mota ya bi ta kansu" inji Surukar Dr Khausar,

     Wani irin abu taji a kirjinta zuwa kanta, dakyar ta d'aga kafarta cikin tashin hankali tace.
"Hajiya Marwanatu, don Allah karki wulakanta jikokinki"
"Ke kika iya wulakanta abin cikin yar mutane! Bayan d'anki ya yarda na shine? Toh ai dan mu ba jahilai bane da mun baki abinda ya dace, dan haka fitar mana a gida Allah ya wadaranki"

    Kasa magana tayi ta fita, dakyar ta shiga mota aka fita da ita, baki daya ta rasa fahimtar mene faru, a cikin yan kwanaki ƙalilan kome ya lalace mata. Ji take kamar tayi ta zuba ihu, amma babu hali.
**
Tunda suka isa Geneva, wato Zurich, Abie bai da lokacin kan shi sai na sintiri zuwa asibiti. Kuma Alhamdulillahi domin wannan karon ma ya kuma gayyato likitan da ya dubata, shi ya kuma dubata. Amma wannan karon an yi mata aiki a zuciyarta, dan ma damuwar ya hadu da laluran ciki ne. Haka yayi aikin cikin nasara.

Bayan kwana uku masu kyau, ta fara motsi, a hankali kuma ta farka baki daya, sai dai tun daga ranar. Abie yake mata addu'o'in yana bata a ruwan zam-zam tana sha, abinda ya haifar mata da komawa tayi sanyi. Magana ma sai kayi da gaske take yin shi. Sai nasiha, tare da bata tarihin magabata,

Sannan ya kawo mata irin daukaka ta Khalid bin Walid, wanda Allah ya mishi kirari da saifullahi Ma'asum, sabida yadda yayi adawa da musulunci, sannan ya dawo yayiwa Musulunci hidima yayi adawa da kafirci, tare da kawo mata misalai dasu Nusaiba, Rabi'atul adaweyya, irin su Ummul Salma, karewa ya kafa mata suratul Maryam har dasu mujadala, da yadda mata suka yi gwagwarmaya a musulunci, sai ga Maimunari tana kuka tana rike hannun shi yace mata.
"Lokacin khalifancin Umar, Allah ya yarda dashi, yace an taba zuwa yaki aka kamo bayi aka kawo su, yace yana tsaye sai ga wata mata a cikin su, an daure kafarta da hannunta da Sarka na karfe, yace dan matar ne ya b'ata, bata iya tashi tayi tafiya rarrafe take tare da ciro mamarta duk inda ta ga yara na wasa sai da durkusa ta nemi D'anta, wasu malamai ma sunce an ce matar bata gani, haka tayi ta niman D'anta. Balle ke da dukkan mu mun san mun yi miki laifi, mune iyayenki mun baki hakuri amma bamu tsira ba, haba Uwata ai bawa baya wuce ƙaddarar shi."

   "Abie kayi hakuri." Iya abinda na iya fada kenan na kwanta,.ina kuka mai mugun cin rai, amma a sanyayye.
"Kina kukan kin rasa Mohan ne ko kina kukan abinda muka miki ne?"
"Dukka Abie"
Na fada mishi haka, fita yayi tare da gayawa Baba Mari ta tsaya dani.
....
Sai da nayi sati biyar asibitin sannan aka sallame ni, koda na dawo gida ma, gasu Benazir da Abie ya mai da ta makaranta, Yumnah ma haka, idan suka dawo kuma shi yake karantar damu a gidan, a hankali na Fahimci iyayena suna min wata irin soyayya da yasa basu iya tsawata min, musamman Mommy bawai bata fada bane a'a kawai tausayina ne yasa kullum sai ta kirani a waya,kuma koda na dauka daga Sannun sai Sannun da ya jiki da sauki, shikenan. Babu abinda yake hada ni da ita, kuma zata b'ata lokaci tana saurarona, bawai bana son iyayena bane, kawai ni dai ina da yakinin sun tafi sun barni babu wanda ya damu dani sai yanzun da na girma suka damu dani, idan ta ga nayi shiru, tayi min magana nace mata hmm! Sai ta kashe wayar ta kira Benazir ta turo ta d'akina.

  Duk da halin da nake ciki ban tab'a tsanar su Benazir ba, asalima jin su nake kamar mun fi haka kusanci, bana son naga Beenah tana rab'ewa idan ta ganni da Abie muna zaune, sai naji kamar sabida Ni aka raba su da Mahaifiyar su.

Yanzun haka ta shigo dakin tana waya da Mommy, zama tayi tana kallona.
"Mommy gata nan dai tana karatu ne"

"Toh Toh kyale ta, karki dame ta, amma ya Babyn ku? Yana lafiya?" Dariya ta saka tare da cewa.
"Lafiyan shi lau, Mommy baki ga Yadda Adda Munah ta koma ba, zan dauka miki hotonta."

Kashe wayar tayi tare da zuwa zata dauke ni na buge wayar ya fadi can, kallona tai tare da juyawa ta dauki wayarta, ta ga ya tsage.

"Addah Munah! Ba laifi bane idan kinyi fushi da Mommy, amma kuskure ne babba wulaknta Uwa. ciki ne a jikinki, kuma zaki so idan kina haife shi ya mutunttaki ko? Wallahi da ace Daddy ne ya saya min wayar nan ba zan tab'a miki magana ba, Amma wannan wayar Mommy ce ta bani ranar da na cika shekara sha takwas, ko da wasa ban tab'a barin shi ya fadi haka ba, sabida ina son Uwata duk abinda zai fito daga gare ta mai kyau ne,"

   Fita tayi daga dakin can ta dawo tare da wata jaka, ta shiga zazzage min shi baki daya a gabana, tana kuka.
"Dairy ɗinta ne baki daya, labarinta ne a nan baki daya,  soyayyarki ce a nan baki daya. Zaki tozarta mana mahaifiyar mu, idan baki sonta Kice baki kaunar ganin mu, yau zamu bar miki gidan Abien ki, domin ba zan cigaba da kallon ki, kina tozarta min mahaifiyar ba."

Tana fadar haka ta juya ta fita daga d'akin, tana kuka.

   Da Abie suka haɗu. Ya riko hannunta har falo ya zauna da ita, goran ruwa yasa aka kawo mishi ya mika mata tasha. Tana shashekar kuka.
"Abie ita me yasa bata farin ciki? Allah ya bar mata Mommy da kai! Mu kuma Allah ya dauke Daddyn mu!"

Wani irin lumshe idanun yayi, tare da bude su akanta.
"Abie a duniya akwai na biyun uwa?"
"Babu!"
"Toh meye yasa take wulaknta Uwa?"
"Sabida laifin da muka aikata? Kuma har yau Mommynku bata zauna da ita ba, kuma tana bukatar kulawar ta."

"Wannan shine matsalar ta?"
"Eh ina zaton haka!"
"Insha Allah zata zo, ta zauna da ita har ta haihu..
*HMM! BAN SANI BA KO A PAGES DA SUKA WUCE NA RUBUTA CEWA HAJIYAR MOHAN TAGA TSIRAICIN MAIMUNARI DA HAR YA ZAMA ABIN MAGANA AKAI KUNGA WANNAN BOOK DIN FREE BOOK NE! SABIDA KANANU MAGANA INSHA ALLAH VERY SOON ZAN KAMMALA SHI AMMA KAFIN NAN NI MUTUM CE DA NAKE TSAYAWA AKAN MAGANA TA DA KUDI NAKE NIMA DA BA ZAN YI BOROROJI FREE BOOK BA. AMMA DAKE WASUNKU BUTULCI BA WANI ABU BANE A RANSU WAI HAR SUNA MAGANA AKAN ABINDA BAN FADA BA INSHA ALLAH WANNAN ZAI IYA ZAMA NA KARSHE! WALLAHI DUK WANDA YAKE BIN BOOKS DINA KARYA YACE NA B'ATA MISHI LOKACI BAN YI POSTING KODA NA KUƊI NE, HMMM MAJI MA GANI AN BINNE TSOHUWA DA RAI. ALHAMDULILLAHI DA KUDIN KU ZAKU SAYI BOOKS SAI AN GADA MA AKE MUKU POSTING WANDA NA B'ATA LOKACI ANA GAYA MIN MAGANA AI BA WANI ABU BANE DABI'A CE TA DAN ADAM BUTULCI ALLAH YA BAKU HAKURI MASU BASIRA NI DA NAKE RUBUTAWA KU YAFE MIN KAR NA LALACE DAN NACE AN GA TSIRAICI YAR UWARKU MAIMUNARI!*

Dan haka ina ga babu amfanin na cigaba da Posting a WhatsApp.
#Mai_Dambu
[8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1114877151?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=z9ZOtX44qohxpFic26GH%2Fsn4B4gALffG4rhIwdZgrEOLvK6sIq9knb%2FFjtTVFnjyKKX0u8D3JU062TWZvHMQK0nMVrMzF9JRvFiItDn%2BYZJxkFtAoVCSwYFXCySTxhIc
🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA SITTTIN.

"Amma" rufe min baƙi tayi, bayan ta kashe karatun.
"Me yasa baki da Fahimta? Ki godewa Allah Kinji, abinda ya jarabce ki a kai kuma ki kara mishi godiya yana sane dake, karki yarda son zuciya ya saki, fadawa fushin Allah."

   Gyada mata kai nayi ina wasa da rigar jikina,sabida ina jin motsin abin cikina,

"Kina fushi da Abie har yanzun ne?" D'ago kai tayi tana kallona,
"Amma ai kina sonshi, tunda gashi har kina zaune a karkashin inuwar shi, kawai kuma shirya kanku ko kuma wannan abin ya shirya ku"

Mikewa tayi sakamakon shigowar shi, tana faɗin.
"Allah ya shirya ki"
"Amin Ya Allah" ya faɗa bayan ya zauna yana kallona, cikin murmushin jin dadi yace min.
"Ga Budurwan da nayi sunan ta, Grace" kallon Mommy nayi wacce ta tsuke fuska,
"Don Allah? Na ganta Abie amma ai babba ce ko" na tambaye shi ina leka wayar hannun shi.
"Eh talatin da biyu fa"
"La ba wata babba bace, toh gaskiya zamu je mu ganta."
"Haba Kinga kuwa baturiya ce, sai a haifa miki kane farare"
Cikin zolaya nace mata.
"Mommy kece babbar kawar Ango, tunda nasan bai da abokai sai ke"

"Karki kuma saka ni cikin shirmenku" ta wuce fuuuu, aikuwa muka saka dariya, sannan nace mishi.
"Abie me yasa ba zaka gaya mata kana Sonta ba?"

"Ina jin tsoron ta ne"
Kallon shi nayi kafin nace mishi,
"Babu wani tsoro kawai ka gaya mata gaskiya, itama tana sonka fa"
"Da tsufana"
"Itama ta tsufa ai"
"Toh Allah ya sa mu dace"
***
Agadaz.

Kallonsu tayi sannan tace mata,
"Kinsan girman baki uwa? Kinsan yadda Allah yake amsa bakin uwa? Da nace duk wanda ya shiga tsakanin Alhaji da Matar shi ban yafe ba shine kika kashe mishi aure yanzun kin dibo jiki akan Nuratu zata bar D'anta ya auri Kanwar Maimunari"

   "Nahnah yarinyar da Shegiya ce? Sannan taya ma zan so ya had'a zuri'a da mayu, tunda ya sake ta yaron nan bai kuma samun sukuni ba, dan haka nake zargin kama mishi kurwa tayi"

     Kallon tayi na wani lokaci, kafin yace mata.
"Idan har akan Shegiya ce toh ai kuwa Allah ne ya nufa zan haife ku a silar aure, har na auri buzu. Amma duk wanda yake cikin Zuri'ar mu yasan me ya faru a shekaru baya. Hmm Nuratu ki bashi yar ki Jalilah, Allah ya bada zaman lafiya"

   "Nahnah wallahi Mohan ba zai zauna da wata mace ba, Maimunari yake so ki saka baki ta barshi ya dawo da matar shi."

"Wallahi ba zai sake ta ba, Insha ALLAH ba zai sake miki yar ki ba na rantse da Allah." Ta fada jikinta na rawa. Cikin takaici Nahnah ta kalle ta, kafin tace mata.
"Dalla rufe min baki, Ni nace kar ku raba yaran nan amma sake baki da imani shine kika saka ya wulakanta yar mutane. Wallahi ki saka ido kiga abinda Ubangiji zai yi dake tunda baki da imani" shiru tayi cikin yanayin na jin haushi domin duk inda taje niman auren Mohan,kin bashi aure ake.

    "Ni dai ku taimaka min don Allah"
"Hmm! Allah ya gani ba zan yarda ya maida min Y'a bazawa ba, amma babu yadda na iya tunda Nahnah kin saka baki."

"Toh nagode"
"Nuratu kiyi hakuri"

    Kamar mahaukaciya ta fado d'akin, tare da shake wuyar Hajiya Latifah, tana kai mata duka.
"Kun kashe min yarinya na, wallahi sai kun mutu kuma, ba zan yarda ba." Ta fada tare da rufe Hajiya Latifah da duka, sosai ta haukace musu, sai da maza suka shigo aka fitar da ita.

"Wallahi sai na kashe su, tubda suka kashe min Y'a, wallahi sai kashe su wallahi ba zan yarda ba, idan har suka shiga hannuna sai sun mutu."

        Haka aka yi ta dambe da ita, cikin kuka Hajiya Latifah tace.
"Yau na shiga uku, meye nayiwa Karime da zata kashe ni?"
"Sharrin da kuka nemi kulawa yar mutane, shine Allah ya maida muku kaidin ku kanku, Alhamdulillahi da abin ya koma kanku. Wallahi Nahnah kin sani abinda ba zan ki ba. Amma da ba zan yarda Mohan ya auri Jalilah ba, yarinyar da tayi jinyar d'anki ma baki kaunace ta ba, sai yar da baki shiri da Uwarta sabida banbancin ra'ayi."

   "Kiyi hakuri"
"Shi kenan Nahnah" ta faɗa idanunta yana cika da kwalla, domin Uwa ce ba zata iya mata musu ba, amma wallahi da Latifah ne ba zata tab'a yarda ta bawa Mohan yarta ba.  A cikin kankanin lokaci aka shirya kome, haka Hajiya Nuratu ta kira Mohan ta gaya mishi, sunkuyar da kai yayi sannan yace mata.
"Umma ba zan sake ta ba, sai dai har ga Allah wallahi Maimuna nake so, don Allah ki ce karta shige min, karta dame ni. Karta shiga rayuwata. Wallahi zan aureta ne kawai sabida ke da Nahnah da kuma Abba sai kuma Khalil ba zan iya cin zarafin ta ba, domin abotar mu dashi gaskiya ce. Kuma ba zan iya juyawa akan abotar mu ba, ba zan iya cutar da ita ba, dan kamar su Radiyah take. Amma ki bata hakuri domin zuciyata yana gurin Maimuna"

Yana gama fadar haka ya juya tare da barin falon,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login