Showing 171001 words to 174000 words out of 177131 words

Chapter 58 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

14812

Ya tambaye ta a gajiye,
"Kai"
"Toh Zainah" haka bawan Allah nan ya raba dare akan matan nan, sai da suka dauki lokaci kafin ta samu nutsuwa, wanka yayi da ruwan zafi ya zo ya kwanta,  karfe shida ya tashi yayi sallah asuba, sannan yayi nafilla da yake kafin sallah asuba. Yana idarwa ya tashe ta, bude idanunta tayi sannan ta zuro kafarta kasa, tare da ɗaukar towel dinta ta shiga wanka. Bayan ta idar ta fito ta gabatar da sallah asuba, sannan ta kwanta a gefen shi.
"Hammah barci kake ji?"
"Ke kuma rigima kike ji?"
"A'a kawai kai nake so"
"A'a kayana dai kike so"
"Kai Hammah meye haka" ta faɗa a shagwaɓe,
"Zainah na gaji wallahi, kuma ina son ma huta koda na awa biyar ne gaya min meye kika sha ne?" Ai kamar ya zage ta, ta fashe da kuka tana faɗa cewa.
"Idan ba lalura ba me zai saka na zama haka, ka hada ni da ciki me jaraba kace min ina rigima"

Tashi yayi zaune bakin shi dauke da sunan Allah, ya d'agota yana fadin.
"Alhamdulillahi! Kanin su Yumnah ne a jikin ki?"
Murmushi yayi tare da rufe fuskarta.
"A'a ai dole ayi ban ruwa, wannan kyakyawan dashen, Tabbas yana bukatar ruwa domin yayi yabanya"

    Ai kuwa bawan Allah nan ya dage tare da aikin Alkhairi da aikin lada.

   ....
Khalil ya gaji sosai, dan haka matar shi ta taimaka mishi yayi wanka sannan ta dauko kular da ta kawo mishi na abinci, sai da yaci ya koshi sannan ya zauna suna hira sama sama, ganin zata fara barci ya sashi dole ya taimaka

_Zaku yi hakuri a madadin three pages zai zauna a biyu, domin zan cigaba da typing ɗin FREE Pages din kishi._
#Mai_Dambu
[8/18, 8:23 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: HAKKIN MALLAKATA
#wed-Aug-2021

BOROROJI

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA SAB'ANI DA ƊAYA.
-----------------------------------------------
Ina kuke matan alfarma muna da kayan ado da kawa... Musamman turaren kaya wanda zai yi awa ashirin da hudu a jikin kayan ki, muna da scentball wanda ake wurga shi a wardrob sannan muna da Oil mai dan karen kyau da dad'i! Ina uwar gidan ina Amarya, maza garzayo kar a baki labari kayan mu free order! Sannan ina uwaren gida da amare nesa tazo kusa, muna da kayan Mata ingantattun masu kyau, Muna da gumba mai kyau yar asali, muna da hadin kazar amare mai kyau yar asali sannan muna da Sha daka mai kyau na amare da uwargida! Akwai parkege na amare mace da ta yarda da kanta Hajiya taɓa Ni ta wannan Number:08130269841 sayan na gari mai da kudi gida*
Kaza
Tara bala'i-
Gumba bucket ƙarami-
Gari-
Hatsabibiyar zuma
Hatsabibin gari
Zobe-
Tsumi-,
Maina ya rikice
Zazzogau
Haɗin gigita shi
Maƙale mata

    Sayan na gari mai da kudi gida..... Sai kun zo muna maraba da ku

_______________________________
Cikin kaunar da soyayya mai karfi Beenah ta kula da al'amarin mijinta, shi kuma ya nuna mata yayi kewar ta, anan take shafa mishi Mommy na da ciki.

  Dariya yayi ta mata, yana cewa.
"Eyye kice zamu yi wasu kanen!"

    Gyara kwanciya tayi a jikin shi tana cewa.
"Eh mana, Allah yasa ta haifa mana yara maza dukka."
"Kuma kyakyawan irin ku!"
"Kwarai Abie ne ko Mommy kasan shi yafita kyau domin shi baki ne ita kuma fara ce, shi yasa Addah Munah tafi mu kyau.

         Kaga Baby Widad mana yadda Allah yayi mata kyau ba Uba ba Uwa ba, kamar na boye kayan ta."

Sumbatar wuyarta tare da rungumo ta, ta baya yana shinshina gashin kanta, har barci ya dauke su.

Da asuba bayan sun yi sallah suka kuma komawa, barci.

  ***
Bayan  kwana uku, suka tattara sai Nijar, inda suka yadda zango a Niamey, Khalil ya wuce da matar shi. Mommy kan ita dangana ta akayi da asibiti. Domin laulayi take sosai.

       Yumnah da Innah suka dawo gida, tare da Baby Widad, abin tausayi yarinya da iyayen ta amma ta zama marainiya, dan ma bata damu da nonon uwar ba, ga Innah tana tattalinta haka sata take ganin Innah kamar uwarta.

    ... Umma Khalil sun je har asibiti suna gaishe da Mommy, sannan suka nemi a basu Widad. Abie bai hana su ba, sai dai yarinyar taki fir musamman da Hajiya Latifah ta nace dai ta dauke ta, nan yarinyar tayi ta kuka. Haka yasa Abbu yace mata,
"Kina son Yarinyar kika shegenta ta tun bata bata taka doron kasa ba, ai ban zata da kanki zaki ce a baki ita ba, na fi daukar cewa k'iyayyar uwarta ne zai damammali yarinyar ashe ba haka bane "

Wani irin kunya ce ta kama ta, karshe haka ta sunkuyar da kai, bata iya mika hannunta ba.
"Hammah Mamman, kayi hakuri ta dauki gudar jinin Mohan, haka zai kara mata imani da tsoron Allah, kuma tayi tuba irin wanda ake son musulmin kwarai yayi."

"A'a ai babu amfanin bata, yau Maimunari tana fuskarta rayuwa ce sabida ita, da yau bata rabata da mijinta ba, taya har wani zai samu damar cutar da ita?" Ya tambaye su ranshi a b'ace,

"Amma kuma ƙaddara karban shi ma ibada ce" inji Innah.
"A'a ban da irin wannan,.domin Kuwa son kai ya shigo cikin al'amarin na yarda da ƙaddara amma ban yarda akan cewa kaddara ce tasa Lateefah kashe musu aure ba a daren idan aka yiwa Nairah ko Radiyah ya zata ji?"

    "Kayi hakuri duk abinda ya faru ya faru, sai dai a tari gaba. Allah ma muna mishi laifi ya yafe mana balle dan Adam! Dan haka itama Maimunari nasan da tana nan zata yafe mata, ai ba wani abu bane jarabta ce" Abie ya fada tare da sake murmushi, yana kara bawa Abbu hakuri, ita kam Widad tana jin muryan Abie ta shiga mika mishi hannu, daukarta yayi yana cillata.

"Ni dai karka karya min kishi ace nice na ƙaryata da gayya!" Inji Umman Dan Ba'are,
"Ai da narasa matar so! Wannan fararren idanun kamar na larabawan Libya!"
"Abie amma ai tafi Matarka kyau, kuma tafi Ammyn kyau"

Inji Benazir da shigowar su kenan.
"Nifa dama ina kulata ne sabida tana kama da Mohan, amma ban da haka, akan me zan damu kaina da ɗaukar mummunar mace"  rufe baki Benazir tai tare da cewa.
"Abie! Da bakinka kake fadar haka? Kaga yar fara balarabiyar Libya da nijar, bafulatanar Mali da Burkina faso. My Bororoji baby"

   Amsar yarinyar tayi tare da rungumo ta, sannan ta sake sautin kuka me ban tausayi, tana kara rungumar yarinyar a jikinta, tana jin wani irin kaunarta yana cika mata zuciyarta.
"Allah ya bawa Mahaifiyarki lafiya yasa ta tashi da kafarta."

"Amin Ya Allah, Allahummah Amin." Inji Hajiya Latifah da tayi laushi gwanin ban tausayi, haka suka yi ta amsawa da Amin.

      **
Bayan kwanaki ƙalilan aka sallami Mommy zuwa gida ya Cigaba da jinyarta, kullum su Benazir suna hanya sai da Mommy tayi mata tas tace bata son ta kuma zuwa mata, taji da kanta itama.

     Haka ta hakura domin da Khalil ne yayi magana toh sai ya hadu da rigima sosai zata yi ta kuka, tayi ta fushi tare da kin cin abincin, sai idan dan cikin ta ya isheta da juyi nan ne zata shiga  niman abinci kamar mahaukaciya,.sai ta gama ci zata zauna tayi ya bakin rai kamar zata fashe.  Sai da ya zauna ya gaya mata duk abinda take yaron cikin ta yana dauka.

Shine ta rage wasu abubuwan, dan ma tana shiga gurin Umma, kuma itama tana yawan gaya mata tayi ya rage wasu abubuwan na rikici, da saurin fushi domin yaro yana dauka domin har ta kawo mata wata kirsa wanda ya faru lokacin khalifancin sayyidana Umar, Allah ya kara yarda dashi. Yace akwai wata rana yayi tafiyar rangadi izuwa wata shashi na yankin da yake shugabanci, yace sai ya hango wani yaro ya shiga gonar mutane, yana ta musu barna,kuma abin da aka noma bai kai a cire ba, sai ya daka mishi tsawa bai saka yaron ya razana, suka kad'a suka raya yaron nan yaki  gonar, sai Amiril Muminina ya tambaya suwaye iyaye nan aka gaya mishi ai iyayen yaron mutanen kirki ne, mahaifiyar shi tana aikin jinya mahaifin shi kuma babban mai koyarwa addinin Musulunci ne.

    Dan haka yace yana son ganin iyayen yaron, dan haka baka raka shi ya tafi yaga iyayen yaron, nan ya tambaye su Meye yasa dan su ya kasance haka, iyayen suka ce basu yi kome ba, saima bautar Allah da kuma kyakyawan mu'amalar su da mutane, sai ya Amiril Muminina ya dubi uwar Yaron yace mata.
"Wannan yaron ba haka kawai yake wannan rashin jin ba akwai wani abu, ko lokacin kina dauke da cikin shi wani abu bai faru dake ba?"

Sai tayi shiru, na wani lokaci kafin tace.
"Eh wata rana na fito aikin jahadi da nake yi na jinyar mutane da kuma amsar haihuwa,  lokacin ina da tsohon ciki, sai na ratsa ta wani gona, anan na hango Randa cikin farin ciki na karo kuzarina dan na isa ga Randa, gashi ana zafin rana sosai.

     Koda na iso sai na iske randan nan babu ruwa a cikin shi, bakin ciki da takaici ya sani na fusata, har sai da dan cikina ya juya nayi tir da alawadarar manoman da suka bar gurin randan babu ruwa. Daga nan na dawo gida wannan shine abinda ya faru!"

     Shiru Amiril Muminina yayi sannan yace musu.
"Tabbas b'acin ranki shine ya shafi yaron har yake lalata amfanin gona domin babu shafin shaidanu a tattare da shi, lokacin da ranki yab'aci akwai jinin da ta fita ta cikin zuciyarki wanda zai digq akan mahaifar yaron, shi kuma ya wuce dashi cikin jikin yaron shi yasa yake ganin abinda yake aikatawa na wani abu bane."
Dan haka Malaman tarbiyya a Musulunci, sun yi kokarin fito da wasu abubuwan da yaro yake dauka, musamman akan matsalar yaron can, wanda suka tabbatar wannan abin ya faru da shine ta hanyar jini , wanda yake had'e da mahaifar shi, da wannan suka kara da cewa.

Matukar yaro yana rashin ji ko fitina ko rigima haka kawai, ko yawan kuka da wasu abubuwan, duk Yaronki yana dauka a cikin ki, karamin misali me yasa ake cewa babu kyau sauraron waka idan kina da ciki!( Akwai wata member na grp dina, wacce take gaya mana cewa, babban  D'anta sun yana da shekara goma a duniya ya sauke Alqur'ani, ta kara da cewa wallahi yaron ya kasance mai sanyin hali da kyawawan halaye, tace sabida tun ina da cikin shi ', aka bani addu'ar da Annabi Ibrahim yayi lokacin da ya kawo Hajara da D'anta ya roki Allah ya albarkaci Zuri'ar shi. Tace ayar yana cikin suratul Ibrahim, sannan tace sai daya a suratul Maryam,inda Mahaifiyar Nana Maryam tayiwa yarta da kuma bakacen da tayi,tace wallahi ban yi bakace ce ba, amma na roki Allah ya shirya shi tun daga cikina bana jin ko sautin waka, sai karatun Alqur'ani da wa'azi, ta kara da cewa Alhamdulillahi Ubangiji ya amsa min addu'a ta, domin wallahi ko cikin unguwar mu mutuntta yaron ake, ni kaina da nake uwar shi mutuntani ake, Ubangiji ya shirya min shi, dan haka yana da kyau tun daka cikin ki fara nima musu shirya da taimakon Ubangiji Allah zai tsaya miki! Wallahi sai naji matar ta burge ni ainun)

     Dan haka Umma ta gaya mata gaskiya akan tarbiyya, har take gaya mata idan zata ci abu ta fara da bismillah, idan zata zauna ta zauna da bismillah (🙄😎 gaskiya ya kamata na ajiye rubutun novel haka mu koma Islamiyyan, domin dauko tarbiyya a Musulunci)

       Duk dani ladubban musulunci, Umma tana daurata, duk da ta lura yarinyar ma ba tayar baya bace akan ilmin addinin Musulunci, amma itama tayi nata kokarin kuma itama Benazir tana dauka.

***
Berlin, Germany.

Goge mata jiki yake yana kallon yadda take kwance bata ko motsi, murmushi yayi sannan ya gyara mata kwanciya, yana shafa kanta, kafin ya mike tare da nufar ban daki yayi alola. Sannan yazo ya gabatar da sallah, bayan ya idar ne, ya dauko yar karamar Alqur'anin shi ya fara karantawa, idan ya gama kula da ita sai ta dauko Alqur'an ya fara karatu yana rage mishi kewa da kad'aici,.

   Babu wacce yake tausayawa kamar Yar shi Widad, domin tayi karama da ɗaukar maraici, gashi baya tare da su. Ga halin da Uwarta yake ciki duk sai yaji damuwa yayi mishi yawa, yaji kamar kan shi zata buga, kome ya tsaya mishi cak.   Duk sai yaji kamar babu wani amfani a rayuwar shi, tunda wacce yake dominta gata nan kwance, duk fadi tashin da yake yanayi ne sabida ita, amma baki daya. Sai yayi ya sare, tunda suka zo ake gwaje gwajen,, har yau basu ce mishi kome ba, kuma basu kuma dawowa kanta ba, sai dai kuma ana zuwa ana mata allurai da saka mata ruwa. Wannan kawai ya kara mishi kwarin gwiwar suna sane dashi,  likitan da zai duba su, ba dan kasar bane kuma idan zai zo yana bin kasashen kusan biyar kafin ya iso, shi yasa  suke dakon jiran shi domin duk abinda ake mata shi yake bada umarni, sannan yana daga can ake tura mishi duk wani bincike da aka yi nata, shi yasa ma yace zai zo domin zai tsallake wasu ayyuka masu muhimmanci amma haka ya tsallake su, kuma ya saka zai zo nan da wata biyar da wasu kwanaki.

            Yana idarwa ya mike tare da rike hannun ta, ya saka a fuskar shi, yana kallon yadda take ko numfashin bata ja, dai na na'ura, baki daya jikin shi yayi sanyi...
#Mai_Dambu
[8/19, 1:39 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: HAKKIN MALLAKATA
#thu-Aug-2021

BOROROJI

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA SABA'IN DA BIYU.
---------------------------------------------
*Ina kuke matan alfarma muna da kayan ado da kawa... Musamman turaren kaya wanda zai yi awa ashirin da hudu a jikin kayan ki, muna da scentball wanda ake wurga shi a wardrob sannan muna da Oil mai dan karen kyau da dad'i! Ina uwar gidan ina Amarya, maza garzayo kar a baki labari kayan mu free order! Sannan ina uwaren gida da amare nesa tazo kusa, muna da kayan Mata ingantattun masu kyau, Muna da gumba mai kyau yar asali, muna da hadin kazar amare mai kyau yar asali sannan muna da Sha daka mai kyau na amare da uwargida! Akwai parkege na amare mace da ta yarda da kanta Hajiya taɓa Ni ta wannan Number:08130269841 sayan na gari mai da kudi gida*
Kaza
Tara bala'i-
Gumba bucket ƙarami-
Gari-
Hatsabibiyar zuma
Hatsabibin gari
Zobe-
Tsumi-,
Maina ya rikice
Zazzogau
Haɗin gigita shi
Maƙale mata

    Sayan na gari mai da kudi gida..... Sai kun zo muna maraba da ku

________________________________
Shafa kanta yayi tare da goge mata hannunta. Yana jin saukar kwalla daga cikin idanun shi.   Suna sauka a saman fuskar ta.

"Ki tashi haka, idan kina cigaba da kwanciya Allah kaɗai san rayuwar da da zasu kwanta, sabida ke? Don Allah ki tashi. Iya haka ma horon ya isa haka, karki cigaba da gana min azaba."

   Haka yayi ta surutu, kai kusan kullum aikin shi kenan, idan yana kula da ita, baki daya  ya koma bai da wani abu me muhimmancin sama da ita, kamar yadda ta badda rayuwarta domin shi haka shima ya ajiye kome, aikin shi da FBI ya ajiye baki daya. Ya zauna a jikin matar shi.

    Mahaifin shi da yan uwan shi sun zo, sun duba su sai da suka Mishi sati domin baki daya bayi da nutsuwa kuma yaki wani ya zauna a jikinta sai shi kawai. Bayan tafiyar su da wata hudu likitan yazo amma bai fara duba su ba, ya fara da mutanen da suke jiran shi.

     Sai da suka dauki wata biyu cur, kafin aka shiga aikin farko na bayanta, cikin niman yardan Ubangiji, ana saura sati za a shiga aikin da ita, Mohan ya tura kudi mai mugun yawa aka rabawa mabukata, tare da niman Allah ya amshi bakunar su, yasa ayi aikin cikin nasara, makarantun allo kuwa haka akayi ta kai musu sadaka.

    Gidan marayu haka aka kai musu motar abinci har gidan, tare da tawwasalin Allah ya kare su ya kuma basu lafiya, musamman Maimunari.

         Haka aka yi ta rabon nan har aka ya kira yace an shiga da ita aiki.

          Awa goma sha daya aka dauka kafin aka fito da ita, tana kwance rub da ciki. Mikawa Mohan hannu yayi sannan yace mishi.
"Zan tafi, nan da wata uku zan dawo a duba na kanta, Allah ya bata lafiya, kai kuma ya baka hakurin jinya, amma zaka yi hakuri domin ba zata farka yanzun ba, sai anyi na kan Tukun.  Shine me muhimmancin.  Shi idan ana aikin ma zata fara kokarin farkawa, na fara na bayan ne dan shine Rayuwarta."

    Cikin karaya yace.
"Toh Dr kana cewa zaka tafi sai bayan wata uku, ka duba ta bar yarinyar mu yar wata goma sha daya, dole yasa aka cire ta a nonon, Dr ka tab'a zuciyata ji nake kamar ba zan kai wata ukun  nan ba, please ka duba al'amarin, mata ta ce. Ko zaman wata daya bamu cikin soyayyar juna ba"

Ya shiga bashi labarin halin da suka tsinci kansu, take jikin likitan yayi mugun sanyi, ya rike hannun Mohan, tare da cewa.
"Nayiwa Yarka alqawarin ba zan wuce kwana talatin ba zan dawo na mata aikin karshe ka yarda dani akwai ayyukan masu muhimmanci ne suna jirana, zan mata aiki da Yardan Allahn ku, kuma zata farka da izinin shi, ka yarda da Ubangijinku.  Kuma ka nime ya bata lafiya."

      Duk da ba musulmi bane amma yayi Imani da Allah kuma ya yarda shi ne mai badawa. Bayan tafiyar shi Mohan ya kira gida ya gaya musu, yadda suka yi. Sannan ya kuma ware wasu kudin yace kai gidan marayu, domin yana sauraron wani wa'azain Kabir Gombe akan marayu, dan haka ya ce.
"Abbu don Allah a kai gidan Marayu, suna da bukatar shi, a kula da su da matsalar su. Idan bai kai ba Abbu a kirani zan turo, ko ka tambayi Khalil akwai katin bankina na kasuwanci. Duk wani abu idan ana bukata a gaya min INSHA Allah zan turo."

    Alhamdulillahi a cikin wata biyu Allah da ikon shi aka kuma shiga da Ita aiki na biyu, cikin nasara ana aikin ta fara motsi wannan ba karamin dad'i ya saka su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login