Showing 30001 words to 33000 words out of 177131 words

Chapter 11 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

14832

kusa da shi suke.

            A mugun tsora ce, ya fara kokarin shiga wardrob din. Yana daidai sun tawo zasu caka mishi wukar har ya rutsa idanun shi, kawai yaji kamar an tare shi.... Karar da yaji tare da zuɓewa a jikin shi yasa shi bude idanun shi da sauri, ya had'a zufa sosai zama yayi yana kallon cikin kasuwar, sanan ya mike tare da ɗaukar karamar buta ya zaga bayan gidan yayi alola bayan ya kama ruwa, sanan ta dawo ya fara sallah nafilla, yana idarwa ya fito, sakamakon motsin da yaji. A hankali ya zuba ido akan Baba Nasiru.
"Zauna Mamoon" zama yayi yana kallon dattijon.
"Wato kaga rayuwar mun nan! Cike yake da al'ajabi, wasu na farin ciki, wasu na dariya da ban mamaki, wasu kuma masu saka kuka. Karka yarda Allah ya jarabce ka da laluran da bata da magani, karka yarda Allah ya daure maka kaddara da bata da iyaka, duniya cike take da mugaye, kowa da ka gani son kanshi yake, kowa da ka gani son abin duniya yake, kasan dai rijiya mai gaɓɓa dubu, idan ka fada kafin a ciro ka ai kasan ka sheka lahira, toh haka tafiyar ƙaddara take, na farko ba a tanada mata guri, sannan baka shirya mishi lokacin dawowa, sannan tafiya ce da motar da baka da matuki, tafiya ce da ko kana hanya ko baka hanya idan motar ta lalace tafiyar kafa zaka koma.

Kasan yadda tafiyar yake a cikin tsannanin zafin sahara? Toh lallai wannan shine zanen ƙaddara, tafiya a cikin sahara ha zafi, ga babu guzuri, shi babu takalmi da zai rage mak ga zafi sahara, yunwa da ƙishirwa. Sai ya rage maka taki kad'an domin cimma manufar ka da burarrakinka na rayuwa, sai kuma kayi katari da alkalamin ƙaddara, wacce take rubuta fari da baƙi. A lokacin zaka ji duniya tayi maka zafi, kowa ya koma ya zuba maka ido. Allah Sarki sai ka ga lokacin duk inda zaka nufa cike yake da azzalumai.

Duk inda zaka dafa mugaye cike suke da gurin, kowa kokari zai yi domin a sami dama daya tal! Kowa yunkuri yake yaga ya shiga cikin lamarin mutum, amma sai ka tadda zuciya ta kangare sakamakon jin bakon lamari, ƙwaƙwalwar mutum ta gigita. Fansa da rashin adalci ya girmama zukatar mutanen. Miyagun mutane suna karawa juna ilimi suƙa, masoyan asali sun koma a abokan gaba, taurin zuciya da ɗaukar zafin rai, zai zama linzamin farko na jagorancin zuciya, kafiya da rashin makusantan kwarai zai zama janabi na tunkarar mutanen da suke fadi tashi domin kaucewa kusakuran su.

Yaro karka sake lokacin yayi kana me jin haka tabbas zai faru, karka yarda duniya ta baka damar amsar wasikar jaki, Rayuwar da aka gina bayan an saka Allah a cikin shi, bata lalacewa. Duk mutumin da ya dogara ga Allah baya tab'a tab'ewa, idan kaga Abu ya same shi, Ubangiji yayi haka ne domin ta tura mishi wani irin yanayi domin gyara alamarinshi.

Allah ya kawo mu lokaci ne da mutane suka rufe idanun shi da yagar namar wasu, suna taunawa. Allah ya turo mu karnin da bamu da abinda zamu yi domin kaucewa tafarkin mugaye sai Addu'a, ina ma da zaka rike wannan tatsuniyar tawa, da ka kaucewa kuskure mara iyaka. Yaro mutanen da basu san darajar damuwa ba, a duk lokacin da damuwa ta faɗa musu, sun kan dimauta su gigita, Yaro kaga duniyar nan tsoro yake bani, gani dai a cikin ta amma ina shakkar mulkin da duniya take.

Wasu mutanen basu da kirki, kana son aikata abin alkhairi, amma sabida sharrin zuciyar su, haka ,zasu yanyayemak da mugun nufin su, irin su basu barin mutanen kirki zama a kusa da mutum sabida sharrin su ya fi ta bakin maciji, fitinar su ta fi ta fitinar karni, bala'in su tafi ta annoba, kai yaro nasan ba fahimtatta kake ba.....

_Don Allah kuyi hakuri 👏👏👏 wallahi na fita ne kuma fitar gaggawa ce ya kama ni! Kuyi hakuri ban cika muku alkawari ba amma muyi Abu daya mu sauya tsarin Posting ku fada min lokacin da ya dace na muku Posting naga kamar zai fi dad'i ayi da daddare sabida kowa ya gama busy na rana, kunga sai ina baku page me yawa ya kuka ce? Ina jiran ra'ayin ku idan kuma zan cigaba da rana ne shi kenan amma idan na shiga busy ba zan iya Posting ba ina jiran ku nagode sosai_

Hmmmm Wattpad ANYA?🙄🙄 Gaskiya toh wallahi zamu sake lalle domin zan bar Posting iya Whatsp.....🚶🏾‍♀️ Maneji....
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
BOOK ONE
https://www.instagram.com/batool_spices
Fatima Batool enterprise
Yaji
Ginger and garlic
Onion powder
Pepper soup
Curry
Biryani spices
Mixed spices
Indian spices
Arab spices
Chai masala
Baharat blend
Tandoori blend
Thai masala
Garam masala
Provence
Tea spice
Zobo powder
    Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Baool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris

  *Hmm! Kalma ce da take kunshe da ma'anoni bila'adadin! Koda yake bana ce ba! Ba kuma zan fadi ba Amma idan har zan fadi gaskiya ku din masoyan gaskiya ne ba masoyan bogi ba. 🤣😜 Wato masoyan Mata maza, #Team Majnunu! Mukan Yan tawaye ne❤️🙄 Team Malam ANSAR*

Wata Rayuwar..
BABI NA SHA DAYA..

Dariya ce ta so subuce mishi, ya kalli Baba Nasiru, sannan ya ce.
"Ina fahimtar ka, kawai maganar  ce tayi min nauyi sosai. Na gaza gane me kake son ka fahimtar dani"
 
Tashi yayi dakyar ya nufi ban daki yayi alola sannan ya fito yana faɗin.
"Wata rana zaka tuna da haka"
Ya fada tare da nufar masallacin. Shima sallah yayi a cikin dakin, sannan ya zauna yana nazarin, mafarkin shi da. Can ya tuna da halin da yake ciki, iskar bakin shi ya ja, yana kallon hasken da rana da yake hudowa ta  gabar. Ranar yayi wani irin kyau ta bada Wani irin yanayi, a hankali ya fito waje yana kallon yadda garin yake washewa. Shaƙar iska yayi me dad'i da ni'imar safiya.

   Ya lumshe idanun shi, yana kara tabbatar da kanshi, yana cikin nutsuwa.
"Kasan wata ƙaddaran tamkar hudowar rana ce, idan ta shigo bata tab'a barin ka har sai tabbata akan ka."

    Kallon inda hasken ranan yake murmushi yayi sannan tacewa Baba Nasiru.
"Zan koma gida" ya dauki kayan abincin shi ya juya tare da fita a kasuwan, yana isa gidan wanka yayi, Almamoon akwai tsafta ga son kwalliya, dan haka ya gama kome yana kallon Innah, sannan ya shige dakin ya kwanta. Barci me nauyi ya dauke shi.

    ..... Haka rayuwar su, take tafiya cikin ikon Allah da kuma matsin rayuwa, ga jikin Baban shi sai ruruwa yake, Nana cikin wannan yanayin aka yi sata a kasuwa, ai kuwa aka kama Almamoon. Aka rufe halin kunciin ya kuma rub'anyan sama da haka, rayuwar ta kuma ta'zara.

   A wannan gaɓɓar halin da Innar shi take ciki kawai ya isa ya karya maka zuciya, domin wallahi ba karamin matsanancin rashin hali take ciki ba.

Ga ciwon Baban ya matsa mishi, wasa wasa sai da Almamoon ya cika sati biyu, sannan aka sake shi ya dawo ya daku, yayi laushi ko magana baya iya yi. Kwana shi uku yayi bai san inda kanshi yake ba, sai da ta haɗa mishi ganyen Tsamiya da wasu sassake ta dafa mishi yayi wanka, yana sha kafin Allah ya bashi lafiya. Sai dai kuma halin da yake ciki na rashin abinyi ga rashin abinci sai Innar shi ta tafi Bara suke samun abinda zasu ci.

     A hankali kwanaki suke tafiya, watanin suna kara nisa, abin mamaki Almamoon ya cinye zangon karatun shi a gida.

     ----
Burin shi nason zuwa ya duba Almamoon bai samu ba, sakamakon tura shi wani yanki da kayi na aikin zaɓe,yana dawowa kuma yayi ta faman zirga zirgan asibiti da Umman shi, baki daya yaron ya tsaya mishi a ranshi, ya rasa gane wani irin kauna yakewa Dalibin shi, a iya sanin shi. Dai kaunar da yake mishi bai kai yadda yake ji ba a baya, amma rashin dawowar shi makaranta Yasaka shi jin kamar zuciyar shi ce a Damagaram.
  *
Yau ta kama lahadi.

Gyara mishi gashin kanshi dan Ba'are yake, cikin kulawa da nutsuwa. Duk da yaki tsayawa amma kuma haka bai hana shi gyara mishi sumar da yake kanshi buyayya haka nan ba.

         Wayar tafi da gidanka na shine yayi kara. Dauka yayi sannan yace.
"Kaga Bama bukatar mace? Namiji muke bukata don Allah kar ya wuce nan da kwana uku, matukar ya wuce haka da akwai matsala bana son tafiya na bar mara lafiyar ne"

Kome aka gaya mishi sannan tace.
"Alhamdulillahi, ku taimaka min daga fadar shugaban ne kuma albashin akwai kyau Insha Allah babu matsala, Nagode sosai"

      Sannan ya katse kiran, yana jin kamar ya janyo kwana ukun zuwa yau, dan an addabi rayuwar shi da kira, ya dawo bakin aikinshi. Bayan ya gama mishi gyaran gashin kanshi ne ya kuma dawowa kan fuskar shi, a nutse yake gyara mishi fuskar. Shi dai yana zaune sai yadda aka yi dashi, yana gamawa ya kama mishi gyaran farcen shi, har ya gama sannan ya mike ya haɗa mishi ruwan zafin wanka.

   ***
Ofishin shugaban jami'ar, shiru yayi sannan yace mishi.
"Yallabai yaron nan haziki ne, idan aka kore shi ba a mishi adalci ba, don Allah karka yanke hukunci Ni zan tafi garin su na duba bashi, don Allah yallabai ka du..."

Daukar wayar gaban shi yayi ya fara waya, ya jima yana magana kafin ya ajiye. Har ya manta abinda Malam Ansar yake rokon shi nan ya shiga rabtabo bayanin.
"Wai ana niman wanda zai yi jinyar wani na hannun damar shugaban kasa ne, kuma namiji matashi, sun hadani da aiki ina zan samu me wannan yanayin kuma wai basa son mace, don Allah ka taimaka min ka tayani cigiyar."

"Toh yallabai ya batun Almamoon?" Ya fada a marairece,
"Zan duba ka fara duba min yaron idan ma ta kama ma waye ka kawo min   zaka nima akan aikin shi kenan, albashin sa na farko nawa ne, sauran kuma zamu yi ta kashe mu raba"

  "Hmm! Toh zan duba maka. Mun gode da alfarman da kayi mana daura dari biyu a fara jarabawa, dan haka Insha Allah zan tafi har Damagaram ɗin." Ya fada tare da gyada kanshi.

       Mikewa yayi tare da ɗaukar kayan shi ya fita, yana me cewa.
"Insha Allah ba zan koma gida ba dai na nimo inda kake" ya faɗa cikin motar shi, ya bata wuta. Gidan mai ya fara tsayawa ta cika tanki, sannan ya dauki hanya.

---
Karfe shida na yamma yana zaune a kofar gidan su, dake basu da nisa da Makarantar da yayi, yana hango motar kamar ya santa, Amma haka ya kura mata ido, har ta iso gare shi. Mik'ewa daga kan dakalin ya tunkari malam Ansar.
"Barka da zuwa Malam" zuba mishi ido yayi ya kara lalacewa bakin shi ya karu ainun. Fitowa yayi yana kallon shi, sunkuyar da kai yayi yana wasa da hannun shi.
"Baka iya tarba'n baki bane?"
Da sauri yace mishi,
"Kayi hakuri mu shiga daga cikin gidan."

Almamoon yana gaba Malam Ansar yana baya, har cikin gidan. Inda yayi mishi shimfid'a a kusa da inda Malam Sanda yake zaune, yana fama da sauran mikin wutar da ta kona shi.
"Barka da zuwa malam" inji Innar Almamoon tana kawo mishi ruwa, "Yawwa nagode Inna"

  Gaishe gaishe suka yi, kafin dai ya kawo dalilin zuwan shi. Mik'ewa Almamoon yayi Tare da cewa.
"Ni dai bani komawa ko ina, zan zauna da iyayena babu wanda yafi dacewa da kulawa da lafiyar su sama da ni, sannan babu me taimaka sama dani, idan na tafi waye zai kula da lafiyar su? Idan na tafi waye zai nima musu abinda zasu ci? Ba kowani lokaci ake samun abinda ake so ba.

         Koda zaka samu dole sai ka dandani azabar da kowa ke sha, Na gode sosai malam" ya faɗa cikin sanyin murya, duk sai son shi da kaunar shi ya cika mishi zuciya, ya kuma jin yaron ta cancanci yayi rayuwa me kyau da tsada, toh amma shima ga halin da yake ciki, mahaifiyar da duk wata take cinye sama da rabin albashin sa, ga bikin kanen shi biyu da aka saka. Duk sai yaji babu dad'i Meye ma ya kawo shi?

     Kurawa Baban Almamoon yayi ido, kafin yace musu.
"Ku saka baki ya koma makaranta Insha Allah zan nima mishi aikin da zai rike kan shi da kuma baki ɗaya"  dukkan su a lokaci guda suka zuba mishi ido, sabida rashin yarda da ya shiga zukatar su. Ganin irin kallon da ake mishi yasa shi gyara zaman shi sannan ya fara da basu labarin yadda suka yi a ofishin shugaban jami'ar.

"Idan har daga jikin firaminista ake niman shi toh ba makawa ba iya kune kuka huta ba, hatta wasu zasu huta a jikin ku, bawai dan na rena muku bane sai dai ina son yayi rayuwar da zata saka shi farin ciki ne, kar ku damu ni ma kamar dan ku nake, don Allah ku fahimce ni".  Shiru suka yi kafin ya cigaba da cewa.
"Wani sana'a kike anan?"

     Sunkuyar da kanshi yayi tare da labarta mishi ko sati biyu bai yi da fitowa ba daga ofishin yan sanda, sakamakon abinda ya faru. Idanun shi sunyi jajjur,
"Dako fa?" Ya kuma tambayar shi.
A hankali ya saka hannun shi a cikin aljuhun wando shi ya ciro kudi masu kauri, ya ajiye musu.
"Ku dubi girman Allah ku taimaka gobe ya dawo makaranta, ba nazo dan na tilasta ku bane, a'a nazo ne dan na tsayawa dan uwana kanina zan tafi Nagode ga wanna Ku sayi magani"

     Duk da suna cikin damuwa da matsin rayuwa, bai hana su ce Mishi.
"A'a , bawan Allah mun gode Insha Allah zamu turo shi amma ka dauki kudin nan kai Almamoon dauka ka bishi da abinshi mun gode"

    Cikin sanyin jiki ya zuba musu ido kafin yace musu.
"Baku yarda dani ba kenan?" Yadda yayi maganar yasa Malam Umaru yace mishi.
"Allah ya kara budi mun gode sosai, Allah ya tsare hanya Ubangiji ya jibanci alamarunka"

Cikin wani irin jin dadi yace mishi.
"Amin Ya Allah Nagode sosai baba Allah ya baka lafiya, Toh sai an jimanku Almamoon sai na ganka kenan" mik'ewa yayi suka fita. Mika mishi hannu yayi, amma fir ya coge, sai ma yayi kamar bai da lafiya.  Shiru suka yi dukkan su.

    ...
Bayan fitar su, a kidime Innar Almamoon ta kalli Malam,
"Malam!" Ta kira sunan shi a sanyayye,
"Kabo, bana son damuwa akan Almamoon. Ba wai dan ina cikin tsannanin rayuwa bane, sai dai ba zan ji dadin yaron ya kare rayuwar shi anan ba, kamata yayi ya tafi koda babu aikin da zai yi a jikin masu kuɗin."

"Malam ba haka bane, na hango tashin hankali a kwayar idanun malamin, na hango kaunar Almamoon a cikin idanun shi."

    "A'a ki kyautata zaton ba wai ki munanan zato ba, ban ji dadin abinda kike tunanin ba."  Tana son yin magana amma sabida yadda malam yaki amsar uzurin ta, yasa tayi shiru.

....
"Almamoon!" Kasa d'ago kai yayi dan yasan yana nan yana kare mishi kallo,
"Almamoon dama irin wannan rayuwar ne ya hanaka zakewa a ko ina? Me yasa baka gaya min ba tun farkon zuwanka makaranta a nima maka aikin yi yadda zaka rike kanka da iyayen ka? Me yasa baka tab'a gaya min ba?" Ya tambaye shi cikin wani irin yanayi. Tar ya kalle shi kafin yace mishi.
"Bana niman taimako a gurin kowa sai Allah, bana son wanin da ba Allah ba ya goranta min, sannan idan daga haduwar mu nace maka ina son ka nima min aiki ya zaka ji? Dan haka ya yankewa kaina damuwar Kowa sai na iyayena, yanzun ma zan yi shawarwari dasu idan suka amince na dawo shi kenan, idan basu amince ba kayi hakuri. Na iya talaucina" ya faɗa kai tsaye ba zaka tab'a tsammanin zai iya fadar haka ba, domin babu shakka ko wani abu a ranshi sai ma tsantsar gaskiya wanda daga kin shi sai b'ata.

     Shafa kan shi yayi tare da hura iskar bakin shi yace mishi.
"Ba zan yi kasa a gwiwa ba, idan har baka zo ba gobe jibi Insha Allah zan zo" daga haka ya juya tare da shiga motar shi. Har ya bar Unguwar, kallon motar Almamoon yake.
"Hm" ta faɗa tare da shiga cikin gidan. Yana shiga ya lura da Innar shi fushi take dashi.
"Inna" ya kira sunanta,
"Wato baka jin maganar mu ko? Me yasa ba zaka gane yanayin ka da na sauran mutane bane? Sai da muka baka shawara kan babu ruwanka da mutane amma kayi kunnen uwar shegu damu, Allah ya baka sa'a tunda ka jajjubo shi."

         Kamar wanda aka dasa, haka yake tsaye bai tab'a ganin irin haka ko ji ba, sai gashi lokaci guda kome ya sauya.
"Kai Almamoon zoka dauki kudin nan kasayo sabulu ka wanke kayanka gobe ka koma makaranta ko baka yi aiki ba, ai bamu ke daukar dawainiyar ka ba, tallafi ka samu, ina me rokonka da ka kame kanka. Insha Allah babu abinda zai faru sai Alkhairi babu ruwanka da kowa, don Allah ka rufa mana asiri. Ka ji"

"Baba ni ba zan koma ba" ya faɗa kan shi a sunkuye, shiru ne ya ratsa tsakanin su, kafin Malam Umaru ya sake wata magana kamar saukar aradu.
"Aminatu kenan, ba sai kin gwada min karfin ikon ki akan Jinin Sama'ila ba" ya fadi haka tare da mik'ewa, ba ita ba hatta Almamoon sai da ya mike tsaye.
"Malam!!!" Ta kira suna shi jikinta na rawa.
"Ayya Ayya Ayya Malam, Ayya Malam me yasa? Malam alƙawari bai ce haka ba, Malam me yasa zaka nemi kifar min da miyar da na jima ina wahalar had'a shi? Malam me yasa zaka kunce min zani lokacin da ban shirya kuncewa ba, Ayya Malam Ayya Ka yi min adalci kuwa? Malam me yasa baka Cigaba da YAKANA ba? Malam karka tulamin kasa a idanu mana, karka sare min gwiwa ta mana, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ubangiji."

  Shi kanshi bai zata maganar zata iya fitowa a bakin shi ba, kallon su Almamoon yaƙe, kafin yace.
"Waye Sama'ila da nake amfani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login