Showing 75001 words to 78000 words out of 177131 words

Chapter 26 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

14797

yayi min tsari da wannan kazamtar." Ta fada tare da toshe bakinta.  Cikin wani irin tsana da kyamar su tace.
"Ku tashi ku bar min gidan mu na tsane ka dama ba son ka nake ba, aka sani dole kuje bana son ganinku." A hankali na mike ina kallonta a raina kuwa dad'i naji tare da kallon yadda take matsar kwallan.

          Mikewa yayi sannan yace mata.
"Lover na ne, yayi miki" kamar wacce zata yi amai ta fara yunkurin amai haka muka bar gurin ya saka hannun shi daya a aljuhun wandon shi, hannu daya riƙe da waya yana niman dan Ba'are.

"Kai Man har ka gama abinda ya kawo ka?"
"Kasan sarauniyar kyau ce da zan zauna kallonta mun gama kome saura kai da Ammin ku ji da sauarn." Ya fada tare da kashe wayar yana kallon yadda na takura a gefe guda, sai harde hannuna nake baki daya na gama kosawa na koma gida.

    Takowa yayi har gaba na, tare da d'ago kaina.
"Meke damunka?"
"Babu"
"Ka tabbatar?"
"Eh" na fada tare da gyada mishi kai kwalla na zuba min. Fuskar shi ya kai kamar zai sumbaci bakina, nayi baya da kaina.
"Toh meye matsalarka?" Ya tambaye ni a gajiye da abinda nake mishi.
"Don Allah ka mai dani gida na gaji Ni ba makaranta ba ni ba gida b..."

"Baka son zama dani ne?" Cikin wani irin sarewa na zuba mishi idanuna da suka yi jajjur.
"Ba haka nake nufi ba"
"Toh nace ba zan kai ka gida bane? Ko so kake mutane suce na maka wani abu! Kayi min shi kafin raina ya b'aci." Yana rufe baki sai ga Dan Ba'are ya iso a masifance ya bude motar ya shiga,.nima na  shiga.

    Tunda na shiga na had'a kai na da gwiwa ta, sai kuka nake.
"Meye ya same shi?" Inji dan Ba'are,ya tambaya kamar zai tsaya. Banza Mohan yayi mishi kamar baya cikin motar.

  Katse kukan nayi tare da cewa.
"Hammah Khalil zaka mai dani Maradi ko?" Na tambaye shi ina kara sake kuka,
"Eh zan mai da ka." Ya fada min yana kallona ta cikin madubi. Duk da idanun shi a lumshe yake bai hana shi dakawa dan Ba'are tsawa ba.
"Dalla can ka kalli hanya karka ja min magana, ya faɗa tare da gyara zaman shi jikin kujeran. Tare da lumshe idanun shi.

   Haka yayi ta masifa shi daya tare da fadin.
"Wallahi na rantse da Allah idan baka min shiru na sai na ga wanda zai kai ka Maradi" had'iye kukan da nayi kenan ban kuma ko tari ba har muka isa gidan.

     Muna shiga ana kawo mana abuncin daga ɓangaren Hajiya Sahiya. Ina karb'a kitchen na kai na juye abincin. Sannan na fito tare da nufar dakina na hada kayana.

      Kwalla ne ya shiga zuba min, ina had'a kayan. Har na kusan gamawa na ji motsin mutum a bayana, a hankali na mike ban juya ba. Wani irin fitar numfashi na ja, tare da sake kayan hannuna. Kwalla na kara zuba min. Hannun shi dukka biyu da ya sakalo su akan cikina, na kalla. Kwallar da suke zuba ne suka kara yawan fita tare da zuba akan hannun shi, juyar dani yayi yana mai daura kaina kan kirjin shi. Ina jin yadda zuciyar shi take bugawa very faster.

        Kanshi yana saman kaina, a hankali ya shafa bayana.
"Karka zama stupid, ka mai da hankali akan abinda ya kawo ka niman Insha Allah Wata sati zan shigo duba ka.". Gyada kai nayi sannan na janye jikina, amsar kayan yayi tare da fitar dashi, ina bin bayan shi. Yana fitowa falon ta mika min wayata da jakar Laptop, sai ta card din bankin shi. Kallon shi nayi domin kuwa idan na tafi da wannan kayan gida mai hana Innah ta min Yankan rago Allah da ya halicce mu ne, na bude baki zan yi magana ya daura min yatsar hannun shi a bakina.

   "Na tsani musu" ya sanin katin a cikin hannuna. Sannan ya nufi Hammah Khalil, ya cakume wuyar rigar shi cikin fushi yana faɗin.
"Dan Ubanka idan kayi mishi magana sai na karya maka muƙaminka, Allah ya tsare hanya."

        "Sake ni don Allah idan baka yarda ni ba, kazo muje." Ya fada mishi cikin jin haushi.

    Haka ya sake shi tare da shigewa dakin shi bai kuma fitowa na har muka bar gidan. Yana kallon motar ta dakin. Bai san wani irin mugun kaunar Yaron yake ba? Bai san lokacin da kaunar yaron ya mishi kamun kazar kuku ba.

     Abinda ya sani kawai yaron yana burge shi, toh bayan nan sai ya fahimci ko tab'a Yaron aka yi sai yaji kamar zuciyar shi aka tab'a. A cikin haka ya fahimci baya son yaga yaron yana mu'amala da kowa shi, yayi imanin yadda ya koyawa yaron yadda zai iya hakuri dashi.

   Ya koyawa yaron wani mugun sabon shi, wanda idan ba shi ba ba zai tab'a hira da kowa me tsayi ba sai shi, ya sakewa yaron zuciyar shi yadda ba zai iya jin dadin Kowa ba sai shi.

      ... Wani irin numfashi yake saukewa kamar wanda yayi aikin wahala, lumshe idanun shi yayi tare da bude su akan hoton shi da Almamoon da yake manne jikin wallpaper na Laptop din shi.
            Shafa hoton yayi tare da jin wani irin kewar Yaron, kamar yace mishi ya dawo amma babu halin haka. Dan haka ya kwanta yana kallon hoton.
.---.
Tunda muka bar gidan na kame kaina, haka muka yi ta tafiya da tsakiyar sojojin da suke bin bayan Dan Ba'are.

    Kallona yayi yaga ina ƙoƙarin share kwalla.
"Baka son rabuwa da Mohan ne?"
Gyada mishi kai nayi, tare da kallon gefen hanya. daga haka bai kuma min magana ba, har Allah ya kai mu Maradi, wani Unguwa da take kusa da makarantar mu ya kai ni daidai kofar wani gida, horn yayi aka bude kofar gidan, a hankali ya tura hancin motar zuwa cikin gidan. Sannan ya tsaya tare da budewa ya fito, sojojin suka tsaya a kofar gidan.

     Daukar jakar Laptop din nayi sannan na fito, cikin gidan nake bi da kallo har muka shiga asalin cikin gidan, ko ina gwanin ban sha'awa. Sannan ya kalle ni.
"Gashi nan inji Mohan, idan ya dawo zaka koma gidan da yake jecader wannan kuma ya saya maka ne dan yaji kace kana son sayawa iyayen ka. Wancan motar da muka zo dashi kuma na kane, ka shiga cikin gidan zaka ga kome ya saka maka. Fatana kayi karatu karka b'oyewa abokan banza dan Mohan bai da saurin fada amma idan zai yi wallahil sai ka sha mamaki, Ni zan tafi."

  Gyada mishi kai nayi domin kamar wanda aka rufewa baki haka na kasa magana, ina ganin ya fita wayata ta fara kara, kallon Number nayi, ina niman sanin Number waye? A hankali naja shi zuwa kan koren na saka a kunne na.

    Wani irin huci ya sake min. A hankali na zube akan sofar da take falon, ina me kumshe idanuna. Wata irin kasala da gajiya nake ji.
"Kun isa lafiya?" Sai da naja numfashi sannan na iya bashi amsa a hankali.
"Alhamdulillahi!"
"Kayi sallah ka ci abincin yanzun za a kawo maka, sannan akwai sojojin da zasu na gadin kofar gidan, akwai wanda zai na zuwa aka hidima kama daga shara da wasu abubuwan, sabida karatunka. And second And the last karka ji kar na gani wani abu ya shiga tsakanin ku da Ansar idan kuma kana son ganin gawar shi bismillah."
"Don Allah bana son kana fadar haka, zan kiyayye amma karka kara furta kalmomi marasa dad'i akan ka."
Na fada ina lashe bakina, kashe wayar yayi.
Tashi nayi nayi wanka tare da gabatar da sallah da take kaina da wanda zata zo, ina idarwa ana kawo min abincin. Bude kofar nayi naga Hamma Malik.

    Murmushi muka yiwa juna, sannan nace mishi.
"Kwana biyu?"
"Yaron Oga ai kayi wuyan gani ya jikinka?"
"Da sauki, shigo mana"
Girgiza min kai yayi sannan yace min.
"Ina nan Oga ya bani umarni daga haka laifi ne"

"Toh" na fada, ina kallon shi bayan ya ajiye min abincin yayi tafiyar shi.
     A hankali na dauka na shiga cikin gidan, ina mamakin Hammah Mohan. Ya hanani mu'amalar kowa toh me yake nufi? Toh ba mamaki ko dan saboda Matsalata ce.
   ***
Washi gari.

Da wuri na shiga makarantar, tare da nufar hanyar Office din shugaban makarantar, muka yi magana dashi ya tabbatar min Bani da matsala daga sama an yi min kome kawai na maida hankali nayi karatu kawai.

     Sati biyu
Tunda na dawo babu labarin malam Ansar, bawai baya makarantar bane yana nan kawai sabgar gaban shi ta ishe shi, kuma Bama haduwa, haka yasa min nutsuwa gashi sojoji ke rakoni makarantar, yau da wuri na fito sabida muna da test. Ban damu na bi mota ba, kawai ina son tafiyar kafa, ina rataye da jakar makaranta,  dan haka na mai da hankali na sosai a tafiyar da nake har na kusan shiga makarantar, na juya baya naga sojojin Hammah suna bina, cikin jin haushi na harare su. Kafin na ciro wayar dake aljuhun jakar na fara kiran shi.
"Ya dai abokina?"
"Hammah kacewa mutanenka su daina bina, sun hana Ni shakar iska me dad'i kowa gudu na yake, don Allah kace..."

Ji nayi kamar an d'agani sama anyi gefe dani motar ta shiga cikin makarantar da mugun gudu, baki daya na zata motar ce tayi watsi dani, sai dai har yau hancina bai daina banbanta kamshin sa dana kowa ba, D'ago kai nayi ina kallon Ansar Yusuf.

"Ka nutsu ka daina waya akan hanya, rayuwar ka tana da amfani." Ya fada yana kallon yadda na razana.
Da gudu sojojin suka iso suna mishi godiya. Ni kam na kasa magana sai kallon Malam Ansar nake, ya kara kyau da girma. A hankali yayi tafiyar shi tare da barina a tsaye.

      Sai lokacin na tuna da wayata da take ya she, dauka nayi ina ganin yadda take magana. Sakawa nayi a kunne na. Hucin shi naji alamar ran shi yana b'ace.
"Meye ya faru da kai naji muryan Ansar Yusuf."
"Hamm"
"Kayi min shiru" ya buga min tsawa har yana dukar wani abu, kashe wayar nayi, can ga daya daga cikin sojojin yana mishi bayani, ban ce kome ba na nufi makarantar.

     Bayan an fito test naga motar da ta bangaje,. Ina zuwa gudun na duba wani dutse na dauka ina juyawa kafin mutanen gurin su fahimci ma'anar abinda zan yi na fasa gaban motar, tare da kallon yadda kowa ya razana. Sannan na daki kofar motar da kafana.

    Nayi tafiyata, ina jin duk wanda ya isa ya tare ni. Fitowa suka yi da Kawayen ta, dukkan su yarane bana zasu fara jami'a. Tana zuwa taga motar da Appa ya saya mata ko wata biyu ba ayi ba.
"Waye ya min wannan barnin." Darewa suka yi tare da nuna musu Almamoon yana tafiya a nutse, da gudu ta kwasa tare da shan gaban shi.
"Uban waye ya ce ka fasa min motana"
"Ubanki ne!" Na bata amsa a nutse,
"Kai dan gidan Uban waye a makarantar nan?"
"Dan gidan Ubanki"
D'aga hannu tayi na rike mata shi. Ina murmushi.
"Yarinyar karya kika yi, ba'a tab'a ba mace ta mari Mamoon karya ne"
Karan da waya ta tayi a karo na biyu na duba, Number Hammah ce.
"Hammah"
"Me yasa ka fasa motar?"
"Na koya mata yadda ake tuki ne?" Na fada mishi.
"Baka jin magana ko? Akan me yasa?"
"Hamma yadda tayi tukun saura kanta ta kashe ni, sabida rashin sanin hakkokin dan Adam?" Na tambaye shi ina kallon yadda take kallona,
"Benazir zo mu tafi zamu hadu kuma dole ya biya kudin motar dan shima kamar Uban shi kwaro ne"

Kashe wayar yayi bayan ya gama masifar shi, itama kuma yarinyar tayi tafiyar ta, bayan ta gama huci.

         Oho ban san ya aka kare ba, sai dai washi gari bayan malam Ansar ya gama darasi ya tura naje.

  Bayan na shiga ya kalle ni sannan ya ce min.
"Zauna"
Babu musu na zauna, sai da ya gama abinda yake sannan yace min.
"Kayi hakuri da abinda ya faru, sharrin shaidan ne insha Allah ba zai kuma faruwa ba, amma ina son niman wata alfarma daya ?"

   Duk sai naji ya cika min idanuna. Sunkuyar da kai nayi.
"Ina jinka"
"Zamu iya zama abokai" da sauri na d'ago kai.
"Don Allah, nasan ba zaka tab'a sauyawa ba, kuma babu wani abinda zai bayyana bayan kasancewar ka namiji, so ina son mu zama abokai na har abada."

         Kallon shi nake ina mamakin yadda ya sauya baki daya, yayi laushi. Murmushi nayi tare da mika mishi hannu, muna gaisa.

         Tun daga lokacin muka dinke tsakanin mu akwai kyakkyawar fahimta, da kanshi ya kawo min Baba Mari ta zauna dani, karatu yayi zafi dan haka koda muka fara jarabawa babu wani lokaci, Alhamdulillahi kuma kamar ina nan akayi darussan baya.

    Benazir kuwa ban san ya akayi ba sai dai naga ta gyara motar ta, bayan tayi mako biyu bata zuwa dashi, ranar da tazo ita da kawayenta. Suka tako har gabana zasu min Iskanci na dauki wani dutsen.
"Kuna cewa tak zan rushe wancan sabon glass din"' na fada ina kallon su. Babu wacce tayi magana.
"Matsalar ku baku da tarbiyya ni kuma na tsani renin.

Na fada ina kallon su, mik'ewa nayi na bar su, a gurin ban san me yasa nake iya dauke kai a tsiyar da Benazir take min ba, dan ko tayi min bana kulata.

   Muna gama jarabawa, ban gayawa kowa ba, kawai na nufi Damagaram tare da jin kamar karna je, sabida tsoron Innah.

Da yamma likis na isa gidan, ana gama sauke min kayana, na shiga cikin gidan gabana yana faduwa.
Baba na samu a tsakar gida, Inna tana daki.
"Almamoon" Baba ya kira sunana a hankali, da sauri Innah tafito tana bina da wani sassanyar kallo, sunkuyar da kai nayi. Tare da isa cikin gidan. Ban yi aune ba sai ji nayi an kife ni da mari, sai da bs zube.
"Haba Aminatu murna zamu yi Allah ya dawo dashi lafiya, ba duka ba." Cikin kuka ta sake rufe ni da duka.
"Malam kafi kowa sanin har hawan jini aka ce ina dashi sabida wannan Yaron, kafana shida A cikin Maradi ina niman shi, makarantar su ma since basu  gan shi ba, maza mike min ka shiga daki ka kuma cire kayan ka gani nan shigowa."
" A'a Aminatu karki zarge shi mana kiyi hakuri zai gaya miki inda ya shiga."

"WALLAHI har gwajin juna biyu sai na mishi dan abin kunyar shekaru shatakwas ma ban gama fita ba a cikin shi balle ya ajiye min dan daka kuka......
🤣🤔 Ra uba inji Hamzan zaranda ana wata ga wata.... Mohan ko ka afkawa mata maza ne, ga rubutu ya dauko tafiya ni kuma wani babban uzuri yana taso min ya damu yi kenan...... Kuyi hakuri da rashin editing...
#Mai_Dambu...
[7/29, 10:27 AM] Hafsatu Hafs: https://www.wattpad.com/1106761947?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=96bc8j7ajP40xeHpU1lx3Iq9KNgJDweWbOsQ2t4marCDkKriXYt89TwgT%2BmS3tOH%2FA0PvkmbeXh9jXQ8GnCAYeKrGW2Uqpce1Fx0xCDcXJXOV%2BHIdFegRFE9fS%2FUP7i8
🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

*Wannan shafin gaisuwar kune Mutanen Jikar kulu 💞💓😍 da Masoyan BOROROJI Novel tare da Masoyan MOHMOON da MOONSAR*
TeamOneLove❤️😘

BABI NA ASHIRIN DA TARA.

A wani firgice na kalli Innah, jikina yana rawa, ta daka min tsawa.
"Ina kuka je?"
Dakyar na sami bakin magana na gaya musu abinda ya faru. Cike da mamaki take kallona yau dan da ta rena shine har da bin wani namiji wata ƙasa. Zama tayi tana nazarin ta ina ta gaza a tarbiyyar da tayiwa Mamoon. Cikin kuka ta nuna kanta.
"Ta ina ma Gaza?  Meye nayi maka da zaka zabi bin namiji? Mamoon wata biyu bana barci cikin sa'ida kullum mafarkin mahai...." Rufe mata baki baba yayi tare da mika mata ruwa.

"Kisha" karba tayi tare da sake wata irin kuka.
"Gaya min meye yayi maka? Ko kuma na saka wuka nayi maka yankan rago"

  "WALLAHI bai min kome ba na rantse da Allah, ki duba jikina." Na fada mata, wani irin kuka take sannan ta riko hannuna da yake b'ari, ta rungume ni.
"Daga yau ba zaka kuma komawa bokon ba, ina tsoron sanadin boko karka bijiro min da tashin hankalin da zai hanani sukuni"

       "A'a ki bar shi yayi karatun."
"A'a malam, tsoro nake ji ina son shi kamar yadda nake son dan uwana." Ta fada tare da kallon shi bayan ta rungume kan Mamoon a kirjinta.

Cikin hikima take bugun cikin Almamoon, wanda tsoro ya sashi ya fadi gaskiya ba tare da yasan dabaranta ba.
"Kuka kwana daki ɗaya? Ban san iya abinda yayi maka ba Almamoon anya kayi mana adalci."

   "Innah kiyi hakuri" na fada a tsora ce, sai da ta gama jin abinda muka aikata, sannan ta kama kunne na ta buga min katon kashedi tare da cewa.
"Ka gama zama a wani gurin, sannan kudin da ya baka da kayan shi zaka mai da mishi kwadayayyen banza irin haka ake cutar da ku saboda mugun kwaɗayin ku, baku zama inda Allah ya ajiye ku, burin ku kawai kuyi ta bin masu kudi suna baku abin hannun su, ana amfani da ku. Waye ya sani ko ya gama abinda ya gadama da kai malam bani guri na duba shi"

       Duk yadda Baba yaso ta hakura Innah fir taki, sai da ya fita ta jika wani saiwa, ta mika min masha, sannan ta sani na cire kayana, ta kwantar dani ta duba lafiyar jikina, sosai wani irin ajiyar zuciya take saukewa bayan ya sani na juya baya ta duba mazaunaina, sujada tayi tare da mika min kayana bayan ta mike.

"Kana barin ana tab'a maka kirjin ka ne?" A tsora ce na lalle kirjin.
"A'a kawai na sayi wanc.." na bude jakar na ciro mata bra ɗina, kifa min mari tayi. Tare da cewa.
"Ina yadin da na baka?"jikina yana rawa na dauko tare da mika mata, ganin ma na daina amfani dashi yasa ranta yayi mugun b'aci.

"Waye na shi da ys canza maka duniyar ka? Nasan ba Ansar bane, waye shi da idanun ka suke nuna min kana bukatar shi anan?" Ta fada cikin kuka, anan ne kuma na kasa mata magana, duk yadda taso na gaya mata waye ne shi naki.

      Ta dake ni a ranar kamar bata kaunata, tayi juyin duniyar nan na gaya mata waye haka, naki naki karshe ma kin magana nayi  sai kuka domin idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login