Showing 165001 words to 168000 words out of 177131 words

Chapter 56 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

14822

ba, cikin ruwan sanyi ya min shegen duka babu bulala babu sanda, domin sai da ya sani na zubda duk wani abinda yake raina, na makalewa Hammah na, sai da ya gama zungure ni da raruke ni, sannan ya dauke a jiyar zuciya. Kafin ya kara matse ni a jikin shi ina kuka tare da bashi hakuri.

Haka muka wuni a hotel din,. muna makale da juna, sai dare na kunna wayata, sakon Ansar ne ya shigo min, ina kallon Hammah Mohan ya duba wayar duk zantuttikar batsa ce, dan haka ya zuba min ido, ranshi ya b'aci.
"Kinsan zan iya kwana akanki ina abu daya ba tare da ba nemi wata mace ba? Meye gayen nan take gaya miki ne? Wallahi"

Amsar wayar yayi tare da fita ta rufe ni,.ya tura mishi sako tare da amfani da wayar shi yayi tracking wayar shi.

Yana samun inda yake, yana zuwa ya shiga har club ɗin.ya fito da shi, ya shiga cin Ubanshi, wani irin Jahilin duka yayi mishi tare da kai kafar shi zai daki gaban shi ya tare yana ihu.
"Ka ji tsoro? Toh na sake na kuma ganin ka a jikin inuwar mata na, sai na kashe maka wannan abin da yake niman kai mata hari, nasan kai ne silar duk wani abu da yake faruwa damu, amma na baka damar ka rayu lafiyar ka, idan ka gadama ka rabu da ita idan ba ka gadama ba, ka cigaba da bibiyar ta,"

Kai Mishi duka yayi akan cinyar shi sai da yayi tambul....
Hankalin ku ya kwanta...
#Mai_Dambu
[8/17, 2:03 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: https://www.wattpad.com/1116738787?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=3wmUfmF%2FKYCEUTT0Or4R8x%2FOHTGp%2Fn%2Fkrfhn%2FB7lHTkzUJhRD5F2rD16co%2BtrR6HblYEBsLqwfg5mD1Uk%2Fkoc73uYq2Ve9MHX7%2F%2BaImoP0o9HmoKgFJY3ZJx0ImK6wgX

HAKKIN MALLAKATA
#Tue-Aug-2021

BOROROJI

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA SITTIN DA TAKWAS.

"Wallahi ka sake na kuma samunka kai ba kai ba wani me kama da kai na kuma gani a kusa mata ta, sai na kashe ka." Ya daki kafar shi sai da ya karya. Sannan ya kuma cukumar wuyar shi yana haki.

"Wallahi billahi azim, idan na ganka zan b'atar da kai nayi alkawari da rabbil ka'aba!" Ya gwara kanshi da motar da yake gurin, zuɓewa Ansar yayi. Ya dan durkusa.
"Ka ci albarkacin zuri'armu daya da sai na yanke maka wadancan abu" sannan ya mike ya bar shi a kwance, cikin bakin ciki ya isa hotel din ina zaune a tsakiyar gadon ya shigo, murmushi ya sake min sannan ya shiga ban daki yayi wanka sannan ya fito sauka nayi a gadon na nufi gare shi na taimaka mishi ya gyara jikin shi ina kallon shi.

   Zare towel din yayi tare da kashe wutan Dakin, rufe fuskana nayi tare da juya mishi baya,  ina jin sojar shi tana gogan bayana.

   Juyar dani yayi ina kallon shi, a hankali ya dauke ni muka zube a gadon, "Hamma Mohan!"
"Na'am"
Ya amsa.yana kallona.
"Kayi hakuri, naso na maka bayanin yadda Malik yayi yunkurin min fyade." Shafa kaina yayi. alamar yana saurarona.  A hankali na fara bashi labarin abinda ya faru, shiru yayi bayan ya zurfaffa tunanin shi, take ya hasko wasu abubuwan masu muhimmancin.

Na farko da Mal'ik yana raye tabbas shi zai kare Maimunari dab haka Mohan ya kashe shi.

Na biyu y kashe shi ne,.domin kar ya zama shaida akan shi ya saka shi kawo mishi Maimuna, sannan ya kuma ɗauki hoton su da video din su ne dan ya jefa zargi a zuciyar Mohan.

    Murmushi yayi sannan ya shafa fuskar matar shi, kafin yace mata.
"Me yasa kike jin haushina?"
Zubur na mike tare da kallon shi ina faɗin yawwa.
"Kasan me?"
"Ina zan san me tunda ni ba akuya bane"
Tura mishi baki nayi tare da cewa.
"Toh na fasa gaya maka ma"
"Ya hakuri. Yan mata mai nono" buge hannun shi nayi yana wasa da kirjin.
"Dama abinda ya dame ni, ka kawo ni nan bayan ka sake ni, sannan kana ta."

Juyar dani yayi saman shi yana wasa da fuskana.
"Ki koma ki duba takardan dana baki. Amma Ni Muhammad ban isa na sake matar da na sha wahalar samota Dakyar ba, Wallhi ban tab'a sakawa zan rabu dake ba, haka zalika bana jin ma shirya rabuwa dake, amma zan miki cin altsine uwar mai karya"

Daga nan ya labarin ya sauya mana, wani fincike rigar jikina yayi tare da makalewa yana tsotse abincin yar shi, har da cewa.
"Wallahi Widad yar albarka ce,kiga babu ruwan ta da nono.ta bar Papa yana shan dad'i. Yarinya na, zan baki mamaki,"

Rike kanshi nayi ina wani lumshe idanuna, tare da gyada mishi kai. Wato Hammah Mohan karshe ne, domin baki daya ya gigita duniya ta, ya gigita min rayuwa sai da ya mantar dani kome, ya kuma dasa min kaunar shi a raina, sama da koyaushe. Kamar yadda ya fada wallahi yayi min cin altsine uwar me karya, domin sai da na kasa magana, sannan ya dauke ni zuwa ban daki. Muka yi wanka tare muka matse junan yau nice a jikin Mohan, kara rungumar shi nayi ina sauke ajiyar zuciya.

   Bayan mun fito daga ban ɗakin,  ina tsaye a gaban madubi ina gyara rigar jikina, tawowa yayi ta rungumo ni.
"Maimunari! Kin san me?"
"Taya zan san me tunda ni ba akuya bace"

   Shafa bayana yayi yana goga min yallabai din shi.
"Ina Kaunarki, kuma ban gaji ba kullum Ban ki ina tare dake ba, don Allah ki kama kanki, ki tayani rike kanki, ga Amanata nan na baki, kinji Matar arziki yar Albarka wacce haihuwarta ya zama ƙarshen kukan al'umma. Ummul khairi aka fara, Allah ya nufa akanki za a rufe dan haka ina kara niman alfarma a tayani boye wannan manhajar"

       Rungume shi nayi ina faɗin .
"Insha Allah mijina" daukata yayi muka koma gado, ya kama hannu ya daura akan abin shi, murmushi nayi tare da wasa da ita yana bani labarin nasabar mu,nasha kuka sosai tare da haukace mishi. Bayan na tuka shi zuwa kofar Damagaram, kai daren ranar tamu ce dan zan iya cewa amarci muka murza son ran mu.

     Washi gari bayan nayi sallah, dakyar nayi azkar, sannan na kuma bin lafiyar gado. Yar shi ya wanke tare da saka mata nonon da ya goge ina jin su, dan barci yayi gaba dani. A hankali ta gama sha ya daurata a kafad'ar shi har tayi gatsa, kafin ya Cigaba da kula da ita har barci ya dauke ta, wanka ya shiga ya zo ya shirya.

"Nasan kina jina bari na je na dawo"
Da hannu na nuna mishi alamar ya dawo lafiya, shima mutum ne da yasan hakkin abokin zaman shi domin idan wani namiji ne haka zai ta uzura min sai na farka. Amma shi kan babu ruwan shi. Barci nayi sosai har da mafarkin Innah muna hira.

       Ban tashi ba sai da ya dawo ya zauna tare da shafa cikina.
"Widad watan ta hudu babu wasu kwanaki me zai hana na ajiye Abie da Abbu da Abba."

Da sauri na farka tare da watsa mishi harara, na dira a gadon na nufi ban daki na zubda yawun bakina sannan na fito na fara bubbuga kafa na a ƙasa, ina kukan tare da cewa.
"Haka kawai ko tinkiya bata cika haihuwar uku ba, tsannanin ta biyu, Wallahi sai nagawa  Abie domin yayi min alƙawarin bani kuma haihu sai ba bukata da kaina."

    "Toh wallahi uku zaki haifa min Insha Allah" ya fada tare da cire rigar shi bayan ya kira a kawo mana abincin, brush na koma nayi sannan na fito.
Zama nayi a jikin shi na ci abincin har na koshi sannan muka shiga wanka tare, muka fito. Shiryawa yayi tare da hada min kayana.

"Zan koma inda nake aiki ana nima na, ban san lokacin da zan dauka kafin nazo ba, tayu idan na tafi sai kin kammala karatun ki, zan zo amma a kula min da Widad don Allah karki kuma sauraron Hisham don Allah. Idan kin yarda nike auren karki kuma kula shi." Ya fada yana sumbatar goshina.

"Insha Allah tunda kace baka so wacece ni da zan kula shi. Dan haka ka kwantar da hankalin ka"

Haka ya taimaka min muka shirya sannan muka fito bayan ya had'a kome na shi, har gida ya kawo ni, ganin Innah nayi na fasa ihu tare da direwa a kanta ina murna, sai dariya take. Mommy da Abie kam sai kallon juna suke, zama Mohan yayi suka gaida har da Baba.

"Shugaban masu hankali babu gaisuwa ne"
Tura baki nayi tare da cewa.
"Hammah na kaji Abie ko?"
"Abie babu ruwanka da mu" ya fada yana murmushi,
"Innahta yaushe kuka zo"
"Da safen nan mijinki ya dauko mu!"
Juyawa nayi ina kallon shi tare da sake murmushin jin dadi, kwala mishi pillow nayi ba cigaba da cewa.
"Shine ba ka gaya min ba na tashi mu tafi tare."

   "Toh ai babu damuwa yanzun ma bata b'aci ba, toh ni kam zan bar gari domin ana ta kirana a gurin aikina."

   Haka ya mike na tashi nima kamar zan yi kuka, ba fito zan raka shi, har gun taxi din na rako shi.
"Hammah Mohan! Sai yaushe ka koya min yadda zan dinga tunawa da kai don Allah karka jima sauran wata bakwai karka wuce wannan lokacin, don Allah kazo kaji"
Rungume ni yayi  sannan yace min.
"Insha Allah zan zo ki kama kanki, karki manta da azumin Alhamis da Litinin. Ina tare dake Allah yana tare da mu"

Shafa bayana yayi sannan ya shiga mota, ina d'aga mishi. Haka na koma cikin gidan, muka baza hira, kafin na koma dakina na gyara sannan nayi wanka na kuma yi sallah kafin na bi lafiyar gado, haka na wuni ina barci sai biyar na tashi na ci abinci na bawa Widad nono, kafin ba sake gyara jikina na fito, Innah ta saka Ni a gaba na maganin gyaran jiki.

        Tun daga ranar bani da lokacin kowa sai na karatu da kuma shi kanshi mijin nawa Muna waya,  kamar zamu cinye juna ta waya.

        ***
Bayan wata bakwai na kammala karatuna har da su Beenah da tazo da cikinta dan wata shida. Da shi kan shi dan Ba'are,  ban ga Mohan ba, kiran layin shi nayi yaki shiga takaici kamar nayi ta ihu.

     Zuwan Hisham ya sani tafiya gurin shi, yana tayani murna tare da cewa.
"Ban ga Mohan ba, yau babban rana ce amma kamar bai damu dake ba? Da yar shi ce da zaki ganshi jikin shi yana rawa" a hankali maganar shi ya fara tab'a zuciyata, ya shiga gaya min wasu abubuwan da nuna min yadda Khalil ya damu da matar shi.

"Ki duba ki gani mana, duk nan babu wanda bai zo ba sai shi, ke kin kare kanki,kin kama kanki amma shi.yana can yana cin amanar ki. Hmmm."

Wani irin duka aka kai mishi sai da ya fadi kasa, yana rungume da Widad. Shiga tsakanin su yayi ina kallon Mohan.
"Meye a cikin maganar shi? Meye  laifin shi? Da ka damu dani ba zaka ki zuwa akan lokaci ba, ka samu matan da suka fini."
Mikawa Khalil Yarinyar yayi tare da kai mishi duka.
"Na gaya maka ka rabu min da matana amma kaki ji, nace ka fita hanyar Maimunari ka ki ji, bari na koya maka yadda ake gudanar da sha'anin rayuwa."

"Munnah kina ganin zai kashe ni, karki bari ya ya illatani"

Saka karfina baki daya nayi tare da ture shi.
"Dalla kyale shi, akan ka aka fara kishi? Ka kyale shi mana, haka kawai zaka saka shi a gaba sai kace bawan ka. Karka kuma dukan shi. Idan ba haka ba zan baka mamaki"

        Haka ya mike tare da barin gurin, yana dingishi.
"Ina sonki shi yasa na kyale shi, amma wallahi sai na illata shi."

"Bana son ganinka, ka koma inda ka fito matukar haka ba zai samar min da kwanciyar hankali ba."

  Haka na gaya mishi tare da barin gurin ina kuka. Shi da Khalil suka kawo mu gida dan su Abie sun rigamu dawowa. Tunda na shige dakina, khalil ya shigo dakin yana kallona, sannan ya zauna tare da bani labarin duk abinda ya faru.

***
"Ban damu ba, kome zai faru ya faru, amma ina son a kashe min shi, a kashe min shi bana son ganin shi da ita,"
"Amma ita yarinyar fa?"
"Idan ta kama da ita a kashe ta kowa ya rasa shima ya mutu."

"Lallai baka cika mugu ba, ai muguntar da zaka mishi kenan ka kashe ta ya rasa ka rasa,"

Kallon shi yayi tare da cewa.
"Ka kawo shawara, kuma Insha Allah haka zai. A'a a kashe shi kawai ina sonta a raye, ina son Ubanta yaga yadda zan aure yar shi kuma na kwanta da ita a cikin gidan shi. Dan haka daga yanzun har zuwa gobe ku kashe min dan Iska."

      "Toh amma kasan Unguwar akwai tsaro, idan muka tashi kashe shi ya zamu yi?"

"Ku rufe bakin bindigar da salansa"
"Toh an gama"

Haka suka ci-gaba da bayanin yadda zasu kashe Mohan, a waje kuwa wata yar makaranta ce, taji su dan haka ta fita tare da niman Number Maimoon.

   Bata samu ba kamar zata yi kuka dan haka ta kai report ga yan sanda, su kuma suka tuntube Maimoon.
#Mai_Dambu.
[8/17, 2:03 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: HAKKIN MALLAKATA
#sun-Aug-2021

BOROROJI

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA SITTTIN DA TARA.

"Kina Fahimta! Ansar ba kaunar ki yake ba, mutumin yake kaunarki ba zai tab'a lalata miki rayuwa da farincikin ba. Bawai ina gaya miki haka a matsayin Aminin Mohan bane, a'a ina gaya miki haka ne a matsayina na dan uwanki, kuma abokin shawaran mijinki..

     Wallahi bai aiko ni domin na gaya miki, amma ita wannan ta sani, komi kashin damuwa idan ya gani a tare dake kamar zai zauce haka yake ji, ki duba takardan sakin da ya baki,wallahi bai tab'a kawowa zai sake ki ba."

Da sauri na shiga watsi da kayan na fito da takardan a kasar a kwatina.
Hannuna yana rawa, jikina sai bari yake na warware takardan.
*Ina son mata ta! Ba zan tab'a sake ta ba har abada*

Wani irin kuka na sake tare da kallon wayata da take kara, da sauri na dauka.
"Kece Mrs Mohan?"
"Eh nice!" Na fada ina toshe bakina.
"Toh ki kula domin shi bamu same shi ba, amma ana bibiyar rayuwar shi da ke, an saka a kashe shi. Dan haka duk inda yake kice mishi ya kula da rayuwar shi"

  Sake wayar nayi tare da jan mayafina na rufe kaina, sannan na fita ban iya kula su ba, duk tambayar da suke min. Bani da hankalin da zan basu labarin abinda yake faruwa.

Dan haka ina fita na hango shi yana tsayawa a bakin kofar shiga gidan mu, da sauri na isa inda zai bude kofar, ba bude tare da cewa.
"Basu maka kome ba? Fito kaji." Bai fahimci me nake nufi ba yana fitowa kuwa suka fara harbi,kwantar dani yayi tare da janyo wata jaka, ya ciro bindigar shi, ya shiga bin su yana harbin su. Sun samu sun gudu dan haka ya fito  tare da d'ago ni, hango wani mutum nayi. Yana tasowa ta bayan Mohan, a hankali na juya tare da Mai dashi daidai kofar gidan, sai ji nayi kaifin abu ya huda bayana har ya fito ta cikina.
"Hammah Mohan! Na gaya maka rayuwata fansa ce koda ni ba zan more ta ba? Na tab'a gaya maka ina raye ne domin kai? Hammah na, tun kana cikin laluran hauka nake tare da kai, wallahi billahi azim ina sonka da dukka rayuwata..." Na tafi zan fad'i yayi maza ya tare ni, shi kanshi mutumin da fuskar shi take rufe wani irin ihu ya kwala tare da cire abun fuskar shi.
"Hisham!" Na kira sunan shi. Ina jikin Hamma Mohan. Sai gyara mata kwanciya yayi a kirjin shi kamar baya gurin.

"Na gaya maka cewa, ni Mohan nake so!" Na fada a sanyayye.
"Ni shi nake so! Ina son shi baki daya da rayuwata, ko babu kome an kawo karshen rikicin ko? Ni matar Mohan ce, Ina son mijina sosai." Na fada ina share kwalla da ta zubo min.  Daidai zuwan motar yan sanda.
"Hammah na, karka mishi kome kabar shi da ciwon da ya jiwa ranshi ya ishe shi har karshen rayuwar shi."

  "Mohan a kaita asibiti mana"
"Ko an kaini bai zama dole nayi nisan kwana ba"
"Karki damu zaki rayu Wallhi" ya fada da mugun karfi ya nufin inda aka saka motar asibiti yana rungume dani.

Bayan tafiyar su, da kanshi yayiwa Yan sanda bayanin shi ya turo ayi kisan, dan haka suka makala mishi ankwa, suka nufi dashi Ofishin su.

     Hankalin Mommy yayi mugun tashi, dan haka suka nufi Asibitin  tunda suka iso suka sami Mohan, ya kasa tsaye  ya kasa zaune, sintiri yaƙe, ya shiga Nan ya fita nan hankalin shi a mugun tashe.

  Allah Sarki baby Widad tana kwance a jikin Abie hannun ta daya a bakinta tana ajiyar zuciya.
Bayan awa biyar likitocin suka fito. Tare da nufar inda Mohan yake.
"Mun yi kokarin mata aiki, amma gaskiya bamu san yadda zamu gaya maka ba, Matarka koda ta rayu bai zama dole ta mori kafaffunta ba, sabida wukar ta tsinka mata jijjiyar lakanta (spinal Code) abin da muka Fahimta a jikin wukar guba a jikin shi, shi kuma ya tab'a mata ƙwaƙwalwar ta, wanda ya tsayar da aikin zuciyarta. Gaskiya muna baku hakuri domin bai zama dole ta rayu ba."

"A'a likita! Wallahi zata rayu. Ina jin haka uwar Ƴaƴana  zata rayu, wallahi bana jin mutuwa zata zo mata a wannan lokacin, kaga gaya min ina ne zan kaita a mata jinya, gaya min inda zan kaita. Don Allah kaga wancan Yarinyar watanta goma sha daya. Don Allah na hada ku da Allah ku gaya min ina zan kaita. Bani da amfani matukar ita bata numfashi, rayuwata mallakar ta ce . Don Allah ku gaya min"

Ka fada a rikice, abin gwanin ban tausayi, su kansu likitocin share kwalla suke, a hankali suka juya tare da barin gurin. Mommy ta tawo tare da rike shi, ta zaunar dashi.  Sannan ta zauna itama tana faɗin.

"A lokacin da na haifi Maimunari, ban tab'a jin ko ganin wani zai kaunace ta ba, musamman ta hanyar da na haife ta, naso da a gidan aure na haife ta, sai na kasa amsar ƙaddara a kanta.  Nayi ta tafiyar ƙaddara. Mohan ban zata ba yau Maimunari zata fada wannan yanayin ba, domin nafi zargin SOYAYYA ba zai tab'a wasa da rayuwarta sai gashi an samu kishi a tsakanin zubda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login