Showing 138001 words to 141000 words out of 177131 words

Chapter 47 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

14795

abinda Innah ta gaya min da ban rasa kome na daraja ta ba.(zaku ji bayani nan gaba Insha Allah) domin baki daya abinda aka tura mishi aka gaya mishi a kaina ne a kasan ranshi, dan haka cikin salon kidima da yaji yadda gurin take da dumi bai san lokacin da ya buga iska.(😏🤣🚶🙆🏽‍♀️ Ya isa haka ku hango yadda Mohan ya gigice mana sai nayi fashin bakin har haka!)

    Na sha bakar azaba a hannun shi nayi kuka na roke shi, na gantsara mishi cizo amma mugun dai da ya mai dani cikakkiyar mace, hankalin shi ya kwanta, ta tattara min gashin kaina ya rasa me zai min ma yaji dad'i.

     Haka ya haska wutar gefen gadon, ya kalle ni yadda nayi laushi.
"Allah yayi miki albarka, kamar yadda kika faranta min Allah ya faranta miki." Tashi yayi ya shiga ban daki.
Kasa kasa nace mishi.
"Amin mugu!"
Dariya na bashi yace min.
"Bari na hada mana ruwa sai na kuma ko sau daya ne!"
Jan bargon nayi, kawai naji an fisgo shi, da sauri na rike tare da sake kuka zan mishi mita.
"Tashi Shegiya bakar munafuka, gurbatacciya! Kin shigo min tsabtataccen Zuri'ata, wanda bamu hada iri da shegu ba, tashi."

"Ammyn karki wulakanta ni a shimfid'ar d'anki, don Allah ki rufa min asiri na suturtta jikina!"
"Tashi dan Ubanki da ya dauke uwarki ranar aurenta yayi cikin ki aka haifi Shegiya irinki, yar zina. Kazamtar da tafi kowanne muni, ayi zina da matar aure. Aka haifi Shegiya irin ki! Tashi."

Kura mata ido nayi kome na kaina ya tsaya, a hankali na fisge Zanin gadon daidai fitowar shi daga shi dai towel, ganin uwar shi a tsaye ya sashi komawa cikin ban dakin da sauri ya dauko rigar wanka ya saka. Sannan ya fito.
"Ammyn lafiya?"

Kifa mishi mari tayi.
"Sake ta dan Ubanka. Shegiya ce mara asali kije ki tambayi Innarki da mijinta ke ba yar su bane maza sake ta kafin na tsine maka ka shiga duniya."

Yaki magana yana kallona ina kallon shi. Ni kam zunzurutun na shiga kidima bansan me suke fada ba.

"Sake ta nace ko na tsine maka!"
Yaki ko guzau.
*Kar Allah ya nuna min ranar da ba zan iya amfanarki ki da kome ba sai ido* wani irin hawaye ne yake zuba daga idanun shi, Ni kam kukan ya tsaya min bana jin kome, a hankali ya dauki kayana yana mika min nasa hannuna amsa. Rufe shi da duka tayi, tana faɗin.
"Zaka sake ta ko sai na maka baki"
"Kiyi hakuri zai sake ki Ammyn! Insha Allah zai sake ni,  ba zan kuma dawowa cikin duniyar ku ba! Mohammed kayi abinda tace kaji"

    A hankali ya fita daga dakin na dauki kayana na shiga ban daki na saka, sannan na fito ina kallon shi. Mika min tai.
"Maza Allah ya raka taki gona abinda aka so a lalata mana siyasar mijina."
"Ammyn karfe ɗaya ne fa;"
"Ba zata kwana ba dan Ubanka, wallahi ka jima baka mutu ba" haka na fito ina jan kafa yana bin bayana, a daren na fita daga gidan shugaban kasar Nijer. Zuciyata tayi sanyi Abu daya zuwa biyu nake son ji.. wacece ni?....
Allura ta tono garma.....
*Intermission! Yanzun muka shiga tsakiyar labarin.... Da alamu na fara shinshimo karshe..... Amma haka ba zai samu ba sai na ga ruwan kaunarku da voting 🤣🙆🏽‍♀️🚶🏌️ rashin daraja*
#Mai_Dambu...
[8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1113774799?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=wttFXwlCWTsu7Xd9brt9PkpuxFS1NA%2FyyAvcpakR2j0eLdqgraAaqKDIsHkdoAh9cMAZ0F3vUQbYnQqanCDd%2B8Ah01MAW4cg9qyzlshahFd%2FF%2Fce11kN%2Fe9K0RRl58%2BM
🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA HAMSIN DA BIYAR.

"WALLAHI ka kuma taku daya sai na la'anance ka!" Ta fada da karfi, wani irin sanyi ne ya shiga jikin shi, ya kalle ta a hankali sannan yace mata.
"Anya ke kika haife Ni? Anya ke kika dauki nauyin cikina? Lallai Ammyn Kinyi abinda kike so ni kuma zan miki yadda kike so! Ba dai Maimunari kika cire a rayuwa ta ba? Alhamdulillahi na hakura da ita koda itace rayuwata Allah ya bata wanda ya fini."

   "Wallahi naji wannan maganar a kunnen Yallabai sai na tsine maka wanda bai san ciwon kan shi ba, yarinyar da aka haife bata hanyar aure ba."

"Bani da lokacin da zan yi magana akan wannan Ammyn wallahi ba zan yi magana akan shi ba, amma Allah zai bi min hakina mata ta ina sonta kina rabani da ita, ina kaunar ta kika rabani da ita Allah yana nan"

    A hankali ya juya zuwa cin gidan shi, ita kuma ya juya zata shiga cikin gida, ganin wani dogon abu tayi wanda bata hango karshen shi balle farkon shi yana tawowa da mugun gudu, aikuwa ta arta a guje, tana shiga falonta ta yanki jiki ta fadi saboda giftwar shi a falon. Ihu ta saka tare da firgita sosai.ihu take tana kiran mutane.

Kafin kace me haka gidan ya cika da jama'a,dole aka rufeta da Addu'a, kafin ta samu barci. me wahalarwa.
**
A hankali nake tafiya motar sojojin shi suna bin bayana, a hankali na tsaya a jikin wani mota, na jingina ina sauke ajiyar zuciya, saboda na gaji sosai. Wayata na cire a jakata da ya mika min kafin na fito. A hargitse nake dan haka koda ba kira Number Abie naji a kashe kiran Ansar nayi.

"Kana ina?"
"Toh ina masaukina ne! Lafiya a tsohon daren nan?"
"Kazo ka kai ni Damagaram."
"Ina Mohan"
"Zaka zo ko ba cigaba da tafiya?"
"A'a gani nan zuwa"
.ina tsaye a gurin, bayan wasu mintina sai gashi nan ya iso. Da sauri ya bude min kofar, na na ja kafana a hankali, domin zuwa yanzun dan tafiyar da nayi tare da motsa gurin da bai samu kulawa na tasa ina jin nauyin har kirjina.
Ina shiga motar kwanciya nayi, ya shiga mazaunin Driven,  "ba zan kai ki asibiti ba kuwa naga kina bukatar taimakon?"

"Bana bukata Damagaram kawai zaka kai ni."

*
Abuja.

Karfe goma suka gama taron su na majalisar Alkalai ta yankin west africa. Dan haka yana gama abinda zayi ya ga lallai zai iya samun daurin auren tunda ba mamaki tunda yafi tsammanin da tsammanin ranar ne kuma zai iya kasancewa da azhar ne.

    Dan haka akwai liyafar da aka shirya musu, amma baki daya ya kasa fahimtar kome, karshe gaya musu yayi zai kome gida akwai daurin auren da zai halarta.
Haka yayi musu sallama ya bar garin Abuja.

         ... Yana isowa bai tsaya ba, sai gidan shi ya sauya kayan shi. Sannan ya dauki katin auren da bai duba ba sai yau.

Maimunari Isma'il Wodaadabe. Abinda idanun shi ya hango mishi kenan, kan shi yayi wani irin dumm, maganar mutane ne ya shiga dawo mishi. Tare a tunawa da yadda suka yi ta cewa yar shi ce.

       Wani irin jiri ne ya dauke shi, ya zauna dabas, tare da dafe goshinsa. A hankali yaji kwalla na zuba mishi,.Yar shi ce ya zauna da ita tsawon watanni bai sani ba,.ko dai ba shi Isma'il Wodaadabe bane, mik'ewa yayi ya haɗa kayan shi. Ya fita tare da nufar airport, sai kusan karfe biyar ya samu jirgin damagaram.  Dake daurin auren a babban Masallacin Damagaram ne.

  Shi yasa yana isa gidan bai zame mishi boyayyen gida ba, tun daga nesa ya hango Aminin shi Sanda. Kwalla ce ta cika mishi ido,ana isa kofar gidan mai taxi din ya tsaya, biyan kudin yayi sannan ya fito ya dauki kayan shi. Ya nufe shi, zama yayi a gefen shi suka gaisa. Kafin ya saka hannu a aljuhun shi ya dauko sarewa. Ya fara busawa. Hawaye na zuba mishi. Juyawa Baba yayi.
"Sama'ila!"
Bai mishi magana ba, ya cigaba da busawa hawaye na zuba sosai, daga cikin gidan Innah taji sautin sarewan ta fito da gudu, a hankali ta isa kusa dashi, ta zauna tare da daura kan ta a kafad'ar shi. Yana busa sarewar yana kuka.
"Ina ka shiga shekara Ashirin! Ina ka tafi ka barmu, Maimunari ta girma yau ake aurenta sun tafi da ita"

     Cire sarewar yayi tare da kallon ta.
"Ki yafe min!"
"Baka min kome ba."

A hankali Abokin shi kuma wanda yake ji kamar dan uwan shi ya dauki kayan.
"Sanda na Barka da nauyi"
"Babu kome!" Cikin gidan suka shiga har falon Baba, anan aka shiga kuka kuma, kafin aka nutsu.
Ya fara magana a hankali.
"Bayan na bar ruga, ba zan iya fada muku abinda nake ji ba, amma wallahi ƙaddara jaririn shi ya sa na aikata haka, dan haka ina fita ban tsaya ba na kad'a shanun mu na tafi dashi. Tafiya sosai nayi har na isa Maradi, daga nan na fita daga yankin Nijar na nufi Nijeriya, tafiyar kwana da kwanaki ya kai ni Sokoto.

      A hankali na nufi kasuwar dabobbin na sayar da su har da naki, nayi fatan Ubangiji ya albarkace shi, sannan na shiga niman sana'ar a zata rike ni, a hankali na sauka a wani gidan gwauraye, na fara fita ina zaga garin. A dan gaba da gidan da na sauka akwai wani attajiri, sai dai kuma daga shi har yaran shi an musu bakin asiri, kullum zaka samu ya zauna yana ta gyangyadi yaran ma basu da abinyi sai yawo da shashancin. Dan haka na same shi muka gaisa ranar mun fito masalaci.

      "Alhaji Ni kuwa naga wani abu a tare da kai da zaka bani dama da na gwada maka shi"

  "Yaro xan tafi kasuwa ne, idan na dawo xan maka magana" yana fadar haka ya nufi kofar gidan shi ya zauna daga nan dai barci, ina gurin shi har aka kira sallah ya tashi zai tafi nace Mishi.
"Alhaji bana bukatar sisinka kawai ka amince min na taimaka maka, da abinda Allah ya wuwace min."
"Toh yaro muje"
Bayan mun yi sallah na saka ya sayi kayan aikin da kudin shi dan kar yace zan damfare shi, sannan na hada mishi kome nace ya tafi xan yi daukar Alqur'ani.  Haka na kwana akan ruwan addu'o'in nan, washi gari da asuba kafin ya yi magana da kowa ya isa kofar gidan, yana bude kofa na mika mishi zai magana na rufe mishi bakin shi alamar yayi shiru, yana sha ya nufi masalaci, muka yi sallah.

      Bayan mun fito zai magana nace.
"Kayi hakuri! Karka yi magana da kowa, ka dauki kayan ka ka nufi kasuwa Allah yayi mana tsari da muguyen mutane."

Haka kuwa ya faru, ya tafi kasuwar. Sai gashi babban abokin shi yana ganin shi yakira sunan shi waye? Meye ya dawo dakai kasuwa? Kai da aka maka iyaka da kasuwa. Sunan kasuwa ma barci zai saka. Yaran ka da suke kula da shagon ka suma haka. Dariya ya fara yana faɗin ai nasan za a rina. Hauka tuburan abokin yayi. Bayan kwanaki nayi mishi na yaran shi, suka sami lafiya suka koma kasuwa. Yayi yayi dani na auri yar shi. Hajara amma naki, sabida zuciyata tana gurin Zainab. A haka na zauna a gidan shi. Har na fara karantarwa.

Kafin na shiga yaki da jahilci, Allah cikin ikon shi na samu shekara hudu, kafin na dawo Nijar nayi diploma a harshen Faransa, sannan na shiga jami'a inda na karancin Shari'a, shekarau ashirin din nan ban yi shi karon iska ba, nayi karatu har kasar Saudiyya, kafin na hadu da Primer minister, ya bani babban alkalin Alkalai na kasar Baki daya, har zuwa wannan lokacin zuciyata tana gurinta."

Kuka suke suna bashi labarin yadda suka sha wuya kafin suka daura da rayuwar Maimunari. Murmushi yayi sannan yace musu.
"Na kasa amincewa ni na haifi wannan doguwar yarinyar, sai yanzun nake kara hango yanayin ta, yanayin mahaifiyarta. Ashe jini na ne, shi yasa da akayi ta jifarta sai da na koma baya, domin kare yarinya na, ko kuka bana son tayi sosa min rai yaƙe, gashi Allah ya bata yaron da zai iya bada rayuwar shi domin ita."

"Amma har yau bata san kome akanta ba Hammah Sama'ila ina tsoron kar ta sani ta birkice mana"
"Insha Allah Ubangiji zai yayyafa mata ruwa, me yasa kika boye mata al'amari haka? Ko yayya ne ai da kin gaya mata, gaskiya ban ji dadi ba. Koda nace idan ta kasance mace a boye min ita sabida tsoron kar a wulakanta min ita ne, sai ki gaya mata cikin lumana yadda zata gane wacece ita."

"Toh ya zanyi mata, bana son ta rasa farin cikin tane." Ajiyar zuciya ya sauke kafin suka shiga hiran da tafi wancan har magarib ta cimma su, suka tafi masalaci.

Kusan raba dare suka yi suna hira, da asuba suka nufi masalaci.
...
Wani irin azazzaben gudu Ansar yake, karfe shida na safe mun iso garin Damagaram.

   A kofar gidan ya tsaya, a hankali na tashi tare da rintsa idanuna, kafin na mike na bude kofar a hankali, na sako kafana. Wani kwarin gwiwa nake ji, na dauki jakata, ban mishi magana ba, na shiga cikin gidan ina dingishi. Jini na sauka a kafaffuna.

       Ina shiga na sami Innah tana abin karyawa sake wukar hannunta yayi tare da mik'ewa.
"Lafiya!" A sannun na isa gurin wukar na cire mayafin jikina  na dauki wukar ina wasa da shi.

"Wacece Ni?" Na tambaye ta.
"Ina tambayar ki wacece ni?"
"Ke yar dan uwana ne, kuma yana nan yazo kin san shi ma ai ba bako bane!" Ganin zata b'ata min lokaci na ja wukar da karfi akan wuyar hannuna. Aikuwa jini yace gani nan..

"Ki gaya min ni Shegiya ce?" Na daka mata tsawa,
"Maimunari Abie!" Da sauri na juya sai yanzun na yarda da cewa da ake muna kama dashi, takowa yake cikin tsawa nace.
"Karka yarda ka zo kusa dani! Ko na yanke wuyata"

"Don Allah Hammah karka je." Inji Inna tana kuka.
"Kiyi hakuri, gaskiya ce abinda kike tambaya kiyi hakuri ƙaddara ce ga fada miki" da gudu ba shiga dakin tare da yanke gefen wuyana, sannan na rufe kofar na fadi a gurin. Gwara na mutu, gwara na mutu kawai da abinda suka ja min.

Buga kofar suke ina kwance, jini na malala, a hannuna da wuyata zai kasana da gurin ya kumbura sosai. 

A kofar gidan kuwa bayan na shigo masalaci Ansar ya wuce yana shigowa, ya samu ana ta kokarin na bude, yana zuwa ya tokare kofar,  cikin azama Abie ya shigo, daukata yayi suka nufi asibitin da ni, sai dai abin takaici ganin irin jinin da nake zubdwa suka ki amsata, dole aka nufi Maradi dani, tare da fatan Allah ya ceci rayuwata.  Dake a motar asibiti ne Abie ya gama kome. kallon Ansar yayi.

"Kar ka kuskura ka biyo mu! Domin idan na tashi zan maka abinda zai dame ne, ka rabu da ita."

"Dattijo ka isa ka rabani da ita ce? Kamar yadda ka raba uwarta da mijinta shine na gwada maka ba zaka iya kome..."

Kasa magana yayi tare da kakari,
"Ka tambayi Ubanka Wa'adi Ansar, waye Sama'ila Wodaadabe Bororo idan ya baka amsa ina jiranka kafin nan ya fara taimaka maka lallai kun tab'a mai tsada, idan tsafi kuke ji ko maita, hmm Ni Alqur'an nayiwa fahimtar zahiri, ka tambaye bashi waye ni"
Abie ya ture shi ya fadi sannan suka bar shi gurin, dole idan ya kai ta asibitin ya dawo domin baya da kura,

Sun yi tafiya sosai dan ma an saka mata ruwa da allurai, hannun shi yana cikin nata, jikinta yayi dumi, a hankali yake jin kwalla yana zuba mata, duk abinda ka shuka shi aka girba. Yau ya tab'a ba, an tab'a mishi ita.

        Allah cikin ikon shi suka isa da ita akan lokaci, Ta gama gajiya domin yau mutane uku tayiwa aiki, ban da amsar haihuwar da tayi.
"Dr an kawo mara lafiya daga Damagaram."

"Toh na gaji wallahi. Ku duba wasu likitocin mana"

   Shigo da ita da aka yi dan su Inna ma sun iso, an tafiya da ita hannunta me jinin yana zuba.
Daga nesa ta hango fuskarta,  a hankali ta iso gare su.
"Ikon Allah meye ya faru? Wannan case din dole a hada da yan san..."

"Zainab!"
"Kai! Fita min  a cikin asibitina,  maza ka fita." Ta fada da karfi.
"Idan kin gama haukarki, ga ta nan abinda kika tafi kika bari, Ruwanki rayuwarta ta rayu ruwanki ne ki watsar da ita waje."
Ya fadi haka tare da nufar hanyar waje, dauke idanun ta tayi akan shi jikinta yana rawa, da sauri ya kira sauran abokan aikinta aka shiga da ita dakin tiyata, tana kuka ta rasa me zata yi. Ashe tun ranar da aka kawota da abinda aka mata take jinta, har jiya da taga daurin aurenta a Tv, haka kawai taji nutsuwa ya shige ta.

     Kuka take tana cewa.
"Don Allah ku taimaka min ta rayu, don Allah ku taimaka min karta mutu."

   Jinin da ta gani a Kafarta yasata sake salati.
"Ku duba min kasanta"
Kai kasa hakuri tayi, tace musu.
"Karku tab'a gurin zan dubata, domin akwai aikin da mika mata na angurya."

Haka suka gama, ta kifa kai a jikin gadon tana kuka, sai da tayi ya isheta sannan ta ware kafar ta fara dubata bakinta yana ambaton Allah. Tsoro take ji kar wani ne ya lalata goben yarta da mijinta kamar yadda Ubanta yayi mata. Lumshe idanun tayi lokacin da taga yadda gurin ya kumbura, a hankali ya duba taga babu karuwa, sai rashin kulawa da bai samu ba,

       A hankali ta mike bayan ta gama bata kulawa, sannan tafi to.
Bata ce musu kome ba ta bar asibitin, sai yau mutuwar mijinta ya tab'ata sama da koyaushe, tayi kuka har Yumnah da Beenah suka samu sukan su.
**
Karfe bakwai na dare ya shiga cikin gidan. bai kula kowa ba yana shiga ya tokari keken guragun da Wa'adi Ansar yake, tare da cewa.
"Meye nufin ku! Yar guda daya tal zaku tab'a min ita?" Ya kuma wurgi da keken, tare da shake wuyar Wa'adi Ansar.
"Wallahi dukkan mu Bororo ne, idan ka sake d'anka ya kuma rab'an Inuwar ta, sai nayi ajalin shi.....
#Mai_Dambu.
[8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1113775660?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA HAMSIN DA SHIDA.
___________________________________
Hlo
```Assalamu alaikum sisters,hp everyone is fn🙏
Nazo muku da labarin wani sabulune maiban mamaki🥺wato *mg's herbal whitening black soap*🧖🏻‍♀️ yan'uwa inamasu bukatar sugyara jikinsu fatarsu tayi kyau tazama Babu kuraje,tabo dama dukwani matsalan fata toh Yan uwa kuyi kokari kujaraba mg's Babu tantama zaisharemuku hawaye insha Allah duk wnd tayi using mg's koda roba dayane sai fatarta tagoge tabanbanta Dana saura,Ina maisan yaga fatarshi tayi smooth tana kyalli toh kujaraba mg's domin fatarku zata dinga haskawa tana walkiya da daukar Ido kmn kunsha supplement domin anyishine da ingantattun natural abubuwa masu gyarajiki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login