Showing 129001 words to 132000 words out of 177131 words

Chapter 44 - Bororoji Compelet COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

14810

sai kayan Auta. Hankalin shi yayi mugun tashi.

Dan haka ya sauke ajiyar zuciya yace mishi.
"Mohan meye ya haɗa ka da ita? Haka kawai bazata dauki kayanta tabar gidan ba"

"Khalil babu lokaci ne, idan na dawo zan gaya maka amma bari na fara ganinta, tun."

    Haka suka kasar wayar, tashin hankalin da yake ciki. Allah Allah yake ya gama abinda ya kawo shi, ya koma. Ranar da ya koma bai b'ata lokaci ba. Ya dauki hanyar.

*
Ina gurin aiki Abie ya kalle ni.
"Uwata ina MG ne bana ganin shi?" Sosa wuyana nai tare da cewa.
"Baya gari ne, amma ina kyautata zaton zai iya dawowa cikin satin nan."

"Allah ya nufa ya dawo dashi lafiya." Ya gaya min,
"Amin Ya Allah" na fada ina aikin, ina halkance dashi kawo min hirar Mohan yake amma fir naki kula shi. Har muka tashi naki yarda muyi maganar Mohan din lokacin da na dawo gida abinci na ci tare da kwanciya, ina nazarin matakin da na daukar kallon zoben hannun nayi a cikin kasa da wata daya kome ya ruguje, haka na tattara kome na zuba a gefe bayan nayi sallah. Sannan na gyara kwanciya na, haka lokacin sallah isha, nayi na gabatar da sallah, ina idarwa na zauna a gurin har nayi sallah shafa'i da witirin,. Ina idarwa na kwanta. Nauyin da nake ji kullum ya ragu min.

   *
Lokacin da ya iso gidan, a gajiye ya shiga Part din shi, yayi wanka sannan ya fito, yana share jikin shi ya gama gajiya ko cikin gidan ba zai samu damar shiga ba, dan haka na kwanta yana son gobe lallai ya hadu da Moonah.

Kusan barcin ranar kasa yayi shi yayi, yana kara nazarin videon din? Ranar da abin ya faru, ina ta shiga ranar da aka kashe Malik? Sannan Meye ya faru a ranar?  Yana niman sanin ba'asi kome, a shagon saloon din Uwani aka yi wancan abin taya aka yi, hakan bai zo mishi tunanin shi ba.

    Ya manta da Uwani baki daya, bari ya fara haduwa da Moonah sai kafin ya fara diran akan Uwani da Hanan. Tashi yayi ya fito waje, sannan ya d'aga kanshi yana kallon sama, yana mai tuna abinda ya faru a tsakanin su. Lokacin suna dubai, wani irin yanayi yaji na damuwa, ya bada akwai abinda aka yiwa Maimunari haka kawai ba zata aikata kome sabida son ranta ba. Dan haka insha Allah gobe zai ji da kome.

   **
Washi gari.

Ina karyawa naga kiran shi baki dauka, ina gamawa na dauki kome nawa na nufi waje, ina fita na sami abin hawa. Sake kirana yayi na dauka.
"Malam ina da abin yi, idan na gama zan kiraka."
Na kashe wayar baki ɗaya.

Ina shiga kotu wanda ya rage mana kwanaki na kammala shi. Ina shiga na same Abie ya shiga  dakin nazari zai shiga wani Shari'a, nima mai da hankali nayi d abinda yake gabana.

Karfe biyu na mike tare da yiwa Abie sallama na tafi. Ina fita na kira shi.

"Ka same ni a inda ka kaini ranar"
"Toh" ya faɗa min a sanyayye, ban damu da jin haka ba, kawai abinda nasani zuciyata, ta gama bani shawarar ta dace. Kuma ina kaunar iyaye na. Dan haka bana jin zan yi nadama ko danasanin abinda na aikata, ko zan aikata bana jin akwai wani kuskuren da zanyi, bana jin zan yi wani cizon yatsa akan abinda na aikata, kawai zuciyata ya bani shawara kuma kamar yadda Mahaifiyar shi ta bukaci na rabu da mata danta ko ta kashe min iyaye na, tabbas zan yi haka. Sai dai ba zan iya cire Mohan a cikin zuciya ta ba, ba zan iya raba ruhina da ruhin Mohan ba, duk abinda zai yi zuciyar mu tana had'e da juna, amma dan ta gane dan ta baya cikin mutanen da idan na rabu dasu zanyi danasani ba. Kawai zan rabu dashi.

   Zan nisanta kaina da shi, zan tafi nayi tafiyar ba zata dashi, ba zan kuma dawowa rayuwar shi ba,  zan nisance shi na tafi kamar yadda bai sanni ba haka nake son na kasance. Ina son nayi tafiyar ƙaddara wanda nasan bai zama dole na waiwaye shi ba, so nake nayi nisar kiwo.

Yadda koda zai ganni sai ya gama shan bakar azaba da bakin ciki, tare da cire tsammanin da gani na zan bayya mishi. Ko kasan ban tsani Mohan ba, asalima shi ya tsane ni ya tsane ni tsana mai matukar zafi da cin rai. Baya bukata na a rayuwar shi , yasa baki daya yaki tsayawa ya fahimce ni.

   Gida na koma tare da watsa ruwa kasancewar ana zafi, ina gamawa na shirya cikin riga da wando na English wear, na saka wata Jacket din da ya taba saya min, rigar cikin fari ne wandon kuma baki ne, sai na daura Jacket din mint color, na daure kaina da mayafi nayi kyau sosai. Sannan na dauki ladies boots shallow shoe, baki tare da gyara fuskana na manna bakin madubi tare da ɗaukar yar karamar pose mai Chain na rataya a ƙafadana. Sannan na nufi waje, na tari abin hawa bayan na fito daga Unguwar.

       Na gaya mishi inda zai kai ni, bai wani ki ba sabida kudin da ya faɗa min zan biya na amince, ina tafiya a hankali maganar Mahaifiyar shi take dawo min bayan ta sallame ni a gurin saloon din zan fita tace Min.
"Dakata!" Tsayawa nayi ta tako har gabana.

*_Nasan waye Mohan! Kuma idan ya nemi sanin dalilin rabuwar mu ki nime amsar da zata tarwatsa mishi tunnain shi ki gaya mishi! Idan kika sake haka bai faru ba. Toh wallhi zan kashe iyayenki! Ina son ki saka shi ya tsane ki tsana mai muni! Matsiyaciya yar talaka jinin tsiya da masifa_*

Iska na ja lokacin da mai taxi din tace min.
"Mun iso yan mata!"
Fitowa nayi na bashi kudin shi sannan na  wuce inda zan shiga gurin, daga nesa na hango shi. A hankali na cigaba da takawa, sannan na isa gare shi.

Zama nayi tare da cewa.
"Barka MAJOR GENERAL MOHAN MAMMAN!"

Cike da Mamaki yake kallona, kafin ya gyara zama yana d'aga hannu, sai gashi a cika mana gaban mu da abinci.
"Bana jin yunwa!"

   Kallon shi nayi sannan na tab'a zoben hannuna. A hankali na mike tare da dawowa gaban shi na zauna a jikin table din, na shiga zare zoben a hankali, fuskana. Na kai kan nashi a hankali na sunkuyar da fuskana sosai, na hada bakin mu guri daya, lumshe idanuna nayi bayan na kalli cikin nashi, sannan na shiga sumbatar shi, baki daya jikin shi ya mutu.

Ya jima yana niman wannan damar amma bai samu ba, ya jima yana dakon wannan al'amarin amma bai ga zuwan shi ba,yau da bai san meye ta shirya mishi ba,ta sumbatar shi nake har nayi nasarar riko hannun shi, na cusa mishi zoben da na cire a hannuna.

Sannan na janye bakina. Ina sauke numfashi, kafin nace mishi .
"Ubangiji ya hada kowa da rabon shi! Kayi hakuri kaje na samu wanda nake so ANSAR. Allah ya baku zaman lafiya da Hanan, na zab'i Ansar abokin tarayya na, domin bai tab'a zargina ba ko ya cusguna min ba. Ina son iyayena kai ma ka tafi kayiwa iyayenka Biyayya fatan Alkhairi"

A hankali na juya tare da barin shi a gurin kamar gumki, ya kasa kome yana rike da zoben..... Breakup

*Zaku yi hakuri domin labarin nan yana da mugun tsawo kuma bana son na yanke wani part na labarin dan haka Insha Allah idan na kai Page 60 to 70 zan tafi hutu sai na gama Kishi INSHA Allah zan cigaba dan haka ku Cigaba da bibiyar labarin Yanzun aka fara idan kuma kuna so na yanke babu damuwa wallahi sai na gutsire shi 🤷🏼‍♀️🙄🤣 Alqur'an babu wani abu dan gaskiya ko hudu nake baku bai zama dole na gama shi da wuri ba bana son nayi shi da gudu bana son na yanke shi dan haka Insha Allah na kusan tafiya break na gaya muku ne dan ku sani kar na tafi a fara nima na🚶🚶🚶🏌️*
#Mai_Dambu
[8/10, 11:13 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1113280247?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=ml%2Bd8%2BtyaNvCS53u6EaYCY0%2BG5P22hSwCFwvGtn%2BKunHRm1zijdp8fID0AwXDh4gnK9vZRZB50KRbcFjAmVYTaXq5PR1XBfOZ44m3%2FgOsffzZwrch908ki14DMntH%2FiK

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA HAMSIN DA BIYU.

Dafe kirjin shi yayi tare da kurawa Zoben idanun, a hankali ya shafa bakin shi. Yana jin alamar maikon bakinta, sake juyawa yayi yaga babu ita babu alamar ta. Yason ya tashi amma ya kasa koda motsi ne, wayar shi ya janyo tare da kiran  Dan Ba'are.

    "Khalil kazo" ya faɗa a wani irin murya, cikin rudrwa ya shiga tambayar shi kana ina ne? Ya gaya mishi inda yake, kafin ya katse kiran, saka zoben yayi a gaba, yana kallon shi. Har Khalil ya iso gurin shi. Bai tab'a sanin yana kaunar Maimunari ba sai yau da ya kasa bude baki ta bada labarin abinda ya faru,sai yau da yana ji yana ganin zuciyar shi tayi wani mugun nauyi. Sai yau da kome nashi ya tsaya cak.

    Yau yake danasani mara amfani.
"Mohan ka kirani kuma ka zubawa zoben idanun meye yake faruwa?"
"Ta rabu dani!" Ya fada a wani irin yanayi, idanun shi sunyi jajjur.
A wani irin kidima Khalil ya ja kujeran ya zauna yana kallon shi.
"Meye kayi mata? Wallahi haka kawai ba zata rabu da kai ba, ka gaya min meye kayiwa Yar mutane. Kafin na ci Ubanka dan iska kasan ba zaka iya hakuri da ita ba ka cutar a zuciyarta? Ka koya mata sonka? Karka manta kana da kane mata meye yasa baka da imani ne? Meye yasa baka tunanin kowa sai kanka? Toh shikenan Alhamdulillahi, Allah ta hada kowa da rabon sa, matsiyaci mara mutunci kawai."

    Tab'a wayar shi yayi tare da cilla mishi videon, dauke kan shi yayi tare da gaya mishi da wani abu daya da yasa shi sanyi sama da farko.
"Mohan! Kasan Allah idan har Ina son Beenah aka kawo min ita, tayi ciki an zubar dashi kai a sa ma taxo min da cikin kaunar da nake mata ba zai tab'a barina na duba cikin ba, fatana ita nake so. Kuma ko a gidan karuwai na ganta zan zauna da ita balle kai da ka dauki yar mutane har Dubai ka shiga da ita kuka kwana daki ɗaya, baka lalata musu ita ba, ta zauna tayi jinyar ka, baka lalata ta ba. Sai yanzun da wani jahili ya turo maka hauka? Tun wuri ka kirata kuyi Magana"

Allah Sarki jikin shi yana rawa ya kira ta, tare da cewa.
"Moonah ki Fahimce mana, kin bar zuciyata cikin tashin hankali! Muna ina sonki dole nayi kishinki!"

"Mohammed Mamman Nasir, ina ga kamar mun wuce wannan yanayin ko? Amma ka tambaye ka! Shin da Ni da Budurcina wanne kake bukata?" Ta watsi mishi tambaya,

  "Munari dukkan ku ina sonku, dake da Budurcin ina sonku" ya faɗa a mugun tsora ce,
"Karya kenan, wallahi sai ka zab'e da ni da Budurcin wanne kake bukata?"
"Ina son dukkan!"
"Toh tunda kana bukatar dukka sai kayi hakuri da Maimunari kake bukata zan iya duba wani abu, amma dake Budurcin kake bukata kaje yana gurin Hanan ni nawa Malik ya rabani dashi kaje na maka tsana irinta k'iyayya da abokan gaba. Mara lissafi kawai. Kuma wallahi ka nime ni sai na illata rayuwarka kaje kaci yar da aka haifa yau ba gobe ba, mara imani da sanin ya kamata, tir da soyayyar da ta had'ani da kai, tir da zama da kai"

   Kashe wayar tai yana kallon Khalil kamar zai yi kuka, mik'ewa yayi tare da zuba hannun shi a aljuhun wandon shi yana faɗin.
"Fatan Alkhairi, idan ka sami damar kashe wutar da kishinka ya kunna ina nan ina jiranka, amma tsakanin ka da Allah, ba iya shi bane matsalar da zata iya hakuri meye ya faru?" Domin dai ba zai iya barin Mohan cikin takaici ba yayi tafiyar shi.

   "Muje shagon saloon din Uwani."

   Taimka mishi yayi suka fita bayan ya kai shi motar ya dawo ya biyan kudin abincin da suka saya, sannan ya tafi ya ja shi a motar shi, Mohan Mohan kuma ya kira driven Khausar mai suna Haliru yazo ya kai motar gidanta.

   .. Cikin bakin ciki ya ke sauraronta.
"Wallahi ban tab'a ganin mutane marasa imani irin Hajiya ba, kayi hakuri sunan ita ta haife ka, amma bata damu da abinda ke so ba, sannan ita Hanan din mahaifiyar ta, fadi tashi take sabida ita. Wai Hajiya Latifah ita kuma kashe D'anta take.. nan suka kira yarinyar bayan sun gama bincike akanta sannan suka saka aka dauko hoton iyayen ta, ta rabu da kai ko su kashe ta, haba iyaye ba abin wasa bane, ko kai ne autan maza wallahi na gama zama da kai sannan tayi mata gargadi akan karta bari ka sani ai yarinyar ta bani tausayi."

         "Mun gode sosai Uwani" inji Khalil, sai yanzun ya fahimci dalilin da abin yayiwa Munari yawa, ga na Mohan yana zargin ta ga Mahaifiyar shi da Kanwar ta suna kawo mata farmaki.
"Dole ko nice na rabu da kai, dole na nisanta kai na da kai, wallahi maimuna Yar halak ce, ta nuna maka ita bata da sama da Iyayenta kai kuma sauran naka ka tsaya kayiwa naka iyayen biyayya."

   Daga haka ya kawo shi gida, sannan ya kalle shi.
"Masu iya magana da larabci sunce Alhubbu fihi mararatin, so yana tare da bakin ciki da farin ciki, dan haka kayi hakuri zanen ƙaddarar ku ce, Allah ya baka hakuri rashin da kayi Ubangiji ya tabbatar maka da Hanan a matar ka ita kuwa Maimunari, Ubangiji ya bata wanda zai aure ta babu Budurcin ya zauna ta da ita haka!"

  Wani irin sanyi jikin shi yayi, a hankali yake d'aga kafa, sannan ya shiga falon ya samu duk suna cin Abinci, kallon Mahaifiyar shi yayi sannan ya tafi inda take ya ajiye mata zoben da Maimunari ta ta dawo mishi da shi, sannan yace mata.
"Ita Mahaifiyar Hanan sabida farin cikin Yarta take wannan hidimar, ke kuma sabida ki lalata min farin cikin na kike kome ko?  Toh Alhamdulillahi, Maimunari ta fasa aurena, kuma na rantse da Ubangiji Rahama. Kuka hada ni da Hanan sai dai wata ba ita ba, dan zan kashe ta"
Ya fada tare da nufar hanyar part din shi, hango Mahnoor yayi da Hindu.

     Tausayi yaran suke bashi, tun daga lokacin da ya fahimci Hajiya Safiya ita ke mishi wani abu, haka ma Primer minister ya fahimci haka, shine ya kore ta a gidan yanzun haka bin abokan shi take tare da yan uwansa, akan a dawo da ita sharrin Oga shaidan ne.

   Ya tattara ta ya watsa gefe can, yanzun yaran an saka musu kahon zuga a cikin gidan musamman ma Hajiya Lateefah, shi yasa idan yana gidan suke zama a part din shi, yana son kanen shi.  Kuma abinda yasa yake burin Auren Maimunari domin ya tattara Yaran su koma gaban shi. Kama hannun su yayi suka shiga part shi. Abincin gwangwani ya basu. Sannan ya koma uwar dakin shi ya kwanta, kamar wanda aka mintsina. Ya mike tare da surar key motar shi ta fita da sauri, gidansu Hanan ya nufa, tun a cikin motar ya zare belt din shi na aikin soja, yana shiga cikin gidan, ya same ta da Kawayen ta suna maimaita abinda suka yiwa Maimunari, tare da kiran mahaifiyar shi jaka.

Wato da bawan Allah nan ya zage yayi ta dukar su, yayi ta kwallon dasu sai da yayi musu kaca kaca, sannan ya nutsu ya juya yana nuna su da dan yatsa.
" Ki saka a ranki wannan wasan ba ayi kome ba, domin sai na miki wanda yafi haka." Sannan ta fita ya bar su a gidan domin Hajiya Karime tayi tafiya.

----
"Ban gane abinda Mohan ya faɗa ba! Kina nufin kin sami yarinyar ne domin ta fasa auren shi?" Inji Primer minister,
"A'a wallahi sharrin yarinyar ce kawai."
"Ammyn sharrin Munari kika ce? Bayan barazanar zaki kashe iyayenta meye na tsare miki da zafi ne haka?" Ya fada a mugun raunane.

    Dakatar dashi Primer minister yayi yana kallon shi, kafin tace mata.
"Ina jinki ko na kira a kawo min Hanan da Karime ne? Na saka a kira Uwani ne?"

"A'a Alhaji nayi domin yarinyar bata dace da Mohan ba, kuma ai yar matsiyata ce. Babu karya a cikin shi, waye ke daukar nauyin su banda shi." Yadda take maganar da kwarin gwiwar ta, san zata aikata dan haka ya kalli Mohan.
"Ka rabu da Maimunari, ka zauna da wanda Uwarka zata baka, Ni kuma zan yiwa Maimunari mijin ban mamaki." A firgice ya mike tare da dafe kirjin shi, sai zuɓewa yayi a kasa.

  Duk soyayyar da yake yiwa Mohan, amma yau yaji aranshi bari yabar shi da uwar shi taji yadda ake rayuwa, dan haka ya tsallake su tana ihu a taimaka mata, ya kuma buga kashedin kar a tab'a mishi motocin gidan shi, Mohan din ya mutu yana da wasu Yaran.

   Ihu da niman taimaka ta gigice, dan haka ta shiga kiran yan uwanta, tana cikin wannan yanayin Hajiyar Hanan ta zo da nata tijarar, ta kuma yi alkawarin sai ta illata Munari da Mohan. Karshe Hajiya Nuratu ta kira Mahaifiyar Khalil, ta gaya mata abinda yake faruwa. Dole ita da mijinta da Khalil suka zo gidan aka kai Mohan Asibiti.  Abin tausayi kuka take tana faɗin.
"Don Allah ku taimaka min Yarona ya dawo daidai na amince ya auri Yarinyar indai itace rayuwar shi."

    Dr Khausar da tasan matsalar yayanta kallon mahaifiyar su tayi sannan tace mata.
"Ammyn dama farin cikin shi kika watsar shine har zuciyar shi take niman bugawa? Toh Alhamdulillahi. Ki duba d'anki wallahi ba zan duba shi karshe ki kuma wurga shi cikin tashin hankalin da yafi wannan ba. Kunga ku bar mata D'anta ta kula da lafiyar shi."
  Cak likitocin suka fito, tare da juyawa zasu tafi.
"Zuɓewa tayi akan gwiwar ta, na amince na Yarda, Ku duba shi don Allah wallahi da kaina zan tafi niman auren shi da ita don Allah ku rufa min asiri, na tuba nabi Allah da Manzon Allah. Ku duba min shi."

   "Dr Khausar! Don Allah!" Khalil da Mahaifiyar shi suka masu magana.

    Dakyar aka samu suka amince, tare da shiga cikin dakin, suka fara aikin su. Har kusan asuba suna tsaye kafin suka fito, zama Khausar tayi tare da fashewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login