Showing 126001 words to 129000 words out of 145203 words
yana fidda numfashi da sauri-sauri. Idon ta ke sa shi samun nitsuwa, idon ta ke sa ya ji sanyi a ransa. Amma yanzu da ta ma sa tsirara sai ya ke jin wani ƙunci da baƙin ciki, kan sa ne ya hau sarawa ya dafe goshin sa yana jin kan kaman zai tsage biyu.
"Sweetheart mi ya faru? What's wrong? Are you sick?" Naomi ta faɗa tana ƙoƙarin riƙe shi. Gaba ɗaya rikicewa yai yana jin kamar idan ya sake goshin sa kan shi fashewa zai yi.
Ganin yadda ya ke yi ya sa Naomi ta tsorata, ta shiga maida kayan ta...
...............
Tun kan su isa asibiti Abdullahi dreba ya turawa Farida text akan Najeeb ba lafiya su na hanyar asibiti.
Ta fito daga wanka kenan ta ji ƙaran shigowar saƙo. Da sauri ta je ta ɗau wayar saboda tunanin ta Najeeb ne ya ma ta reply ɗin texts ɗin da ta tura ma sa ɗazu.
Tana ganin Abdullahi hankalinta ya tashi. Ta buɗe saƙon da sauri.
*Oga ba lafiya muna hanyar asibiti*
Innalillahi ta faɗa tana kiran numbar Abdullahi...
Su na zuwa asibitin aka shiga da shi emergency saboda kafin su isa asibitin ya riga ya suma.
Naomi jikinta ɓari ya ke yi. Tsoro biyu ne a ranta, na farko kar asirin da ta ma sa ya zama ya karye na biyu kuma kar Najeeb ya mutu domin za ta shiga hali na ƙunci ga zargin ta da mutane za su yi...
A birkice Farida ta shigo asibitin. Ganin Abdullahi da Naomi su na tsaye cirko-cirko ya sa zuciyar ta ya karaya.
"Malam Abdullahi mi ya samu miji na? Ina ya ke?"
"Hajiya dan Allah ki kwantar da hankalin ki. Insha Allahu ba abinda zai sami Oga"
"Ina ya ke?" Ta faɗa da ƙarfi.
Kafin Abdullahi yai magana aka buɗe ƙofan ɗakin da ya ke. Da sauri ta ƙarasa gaban likita tana tambayar lafiyar Najeeb.
"Hajiya yana bacci yanzu. Sai dai dan Allah ku dinga kiyaye ɓacin ransa, yanzu haka jinin sa ne ya hau sosai"
"Can i see him?" Ta faɗa da raunatacciyar murya.
Likita ya ce e amma ta bari za a chanja ma sa ɗaki yanzu.
Su na tsaye aka fito da shi akan gadon marasa lafiya, aka turashi zuwa ɗakin da aka ba shi.
Farida da Abdullahi su ka bi nurses ɗin har ɗakin da aka maida shi, yayinda Naomi ta juya da baya ta tafi. Ta ji kaf abinda likita ya ce, amma zuciyarta ta rasa gane ko mi ya sa ran Najeeb ya ɓaci har ta kai ga haka. Normal su ka je hotel ɗin, infact da murmushi a fiskar sa lokacin da su ka shiga ɗakin. Tana cikin keke tana tariyo duk abinda ya faru tun safiyar yau. Ba wani abinda zai ɓata ma sa rai sai dai.... karaf ta tuna dai-dai lokacin da Najeeb ya fara chanja fuska. Tabbas tsiraicin ta da ya gani ne. Idan har saboda ba su yi aure ba ne ya ke jin ba zai iya kusantar ta ba to tabbas za ta gaya mi shi su yi aure nan ba da jimawa ba...
Awa uku kafin Najeeb ya tashi, lokacin duk 'yan gidan su sun zo har da Sabreen. Kowa tambayar abinda ya faru ya ke amma Farida ba ta da bakin magana tunda itama ba ta sani ba. Tunaninta ko saboda ita ne ya shiga wannan hali. "My Champ laifin mi na ma ka ne?" Ta faɗa a zuciyarta.
Daddy ya tambayi Abdullahi ko daga ina su ke. Ya san matuƙar ya faɗi gaskiya to iyayen Najeeb za su shiga tashin hankali musamman ma Farida da ciki gareta.
Ya chanja maganar da cewa sun je wani site ne yai magana da ma'aikatan da ke wajen to da su na dawowa shi ne ya fara riƙe kan sa yana nishi sama-sama.
Daddy ya ce " Allah shi kyauta, amma daga yanzu duk wannan aikin fita supervision ɗin ya isa haka. Anas ko wani daban zai dinga zuwa"
Lokacin da ya farfaɗo garau ya ke jin sa sai dai rashin ganin Naomi a wajen ya sa ya ji ba daɗi. Yana son tambaya amma Mom da Farida sun ƙi bashi dama kowa nan da nan ya ke da shi. Ya haƙura ya zuba mu su ido.
Chan dare aka sallamesu saboda ya ce ba zai kwana ba, shi lafiyarsa lau...
Su na cikin mota amma ba wanda yai wa ɗan uwansa magana. Farida ta kamo hannun sa ta kai kan cikin ta tana faɗin "baby ya missing ɗin ka sosai"
Zare hannunsa da yai daga kan cikinta ya sa ta zaro ido. Tana binsa da kallon mamaki, juyar da kan sa yai yana kallon titi.
Hawayen baƙin ciki su ka fara zubo ma ta.
"Wai mi ke faruwa ne?" Ko lokacin da bai gane ta ba a asibiti farkon farfaɗowan sa ai ba ya ma ta wannan walaƙanci balle yanzu da su ke tsaka da soyayya. Wai har cikin da ke jikinta ma bai damu da shi ba.
Ba ta kuma yunƙurin yin wani abu ba har su ka isa gida. Ido kawai ta ke binsa da shi duk abubuwan da ya ke yi.
Tana ganin ya zauna a bakin gado yana shirin kwanciya ta zo gaban sa. Tsugunnawa ta yi ta riƙe gwiwowin sa duka biyu.
"Na roƙe ka da girman Allah Ubangiji Mai Rahama. Ka yafe min mijina, na yadda na yi ma ka laifi a rashin sani amma ka yafe min. Horon rashin magana da halin ko in kula ya min tsauri. Mijina abin so na, abin muradi na. Kai kaɗai ka mallake zuciyar Aisha Farida. Ba ni da tamkar ka kuma ba zan taɓa samun tamkar ka ba, ka yi haƙuri dan Allah ka gaya min mi na maka ka kuma yafe min. Idan ka cigaba da haka ciwon zuciya zai kasheni...." kuka ya kufce ma ta.
Duban ta ya ke yadda ta ke ta sheshsheƙar kuka, maimakon ya ji tausayin ta sai ma ran sa ya ɓaci.
Da kakkausar murya ya ce " you liar, ba ki da wani bayan ni? Oh really! Shi ne daga fita na ki ka kira tsohon saurayin ki ya ɗebe mi ki kewa kafin na dawo ko?"
Shiru ta yi tana rarraba ido dan ba ta gane maganar sa ba.
"Tsohon saurayina kuma? My Champ...."
"Oh please! Ba na son jin komai ki je ki yi duk abinda ki ke so"
"Wai Lukman ka ke magana? Haba My Champ, haba. Tsakanina da Lukman ya zama tarihi"
Miƙewa yai ya ɗau pillow zai fita ta riƙe ƙafar sa.
"Dan Allah ka tsaya na ma ka bayani. Wallahi ba abinda ka ke tunani ba ne"
Turata gefe yai ya fice abinsa.
Farida ta fashe da wani sabon kukan. Ba abin da ya fi damunta irin wai duk hukuncin nan akan zargi ne. Ta ya zai zargeta, wani irin so za ta nuna ma sa ta tabbatar babu wani namiji a rayuwarta da ya wuce shi. Tafi minti talatin tana kuka kafin ta tashi ta shige banɗaki ta ɗauro alwala.
Bayan ta yi sallah ta zauna a sallayar tana kuka tana gayawa Allah buƙatunta. Ta jima tana addu'a kafin ta naɗe sallayar ta je ta kwanta. Ba abinda ke ranta irin cin uban Naomi da za ta yi gobe, tunda ita ce 'yar burauban da ta haɗa ta da mijinta, ta ma ta ƙaryan mijinta bai zo ba ranan. Ashe ya zo har ya ganta da Lukman.
Ta jima tana saƙa da warwara kafin bacci yai gaba da ita.
.........................
Washegari tun da sassafe ta kira Sabreen akan dan Allah ta shirya za ta mata wani taimako. Sabreen ta amsa da ba matsala.
Karyawan kirki Farida ba ta iya yi ba. Zuciyarta ke tafarfasa yana zafi. Ba ta san sadda ma Najeeb ya fita ba tana tsammanin ƙila lokacin da ta koma na ta ɗakin ne...
Kamar jiya ma dai Najeeb cewa yai ya kai shi gidan su Naomi. Jin haka ya sa Abdullahi ɗaura aniyar dole ya sanar da Farida, domin gaskiya akwai lauje cikin naɗi a wannan al'amarin.
Naomi ta yi farin cikin ganin Najeeb garau ba kamar jiya da ya ke rai a hannun Allah ba. A cikin motan hannunsu sarƙe cikin na juna har su ka isa kamfani...
Suna isowa sai ga Anas shima motar sa ta yi parking. Da sauri ya fito ganin Najeeb da Naomi sun fito mota ɗaya.
"Najeeb... Najeeb" Anas ya kira shi da ƙarfi da ke sun riga shi fitowa a mota.
Najeeb ya juyo ya kalli Anas. Kallon tuhuma Anas ke wa Najeeb ɗin har ya iso.
"Good morning Sir" Naomi ta gaishe da Anas tana murmushi.
Ko amsawa bai yi ba ya ce ta basu waje. Naomi ta yi gaba tana tafiya tana yauƙi.
Anas ya kalli Najeeb ya ce "mi ke faruwa Najeeb? Mi ya sa za ku taho tare kai da sakatariyar ka? Ina Farida?"
" Dude ka ci sa'ido. Ina Baby? Fatan ka na kula min da ita sosai"
"I'm serious Najeeb. Mi ke faruwa?"
Najeeb ya ɗan buga kafaɗar sa ya ce " kar ka cika ni da surutu we have board meeting today"
Girgiza kai Najeeb ya fara yi yana neman yaƙi da abinda zuciyar sa ke raya ma sa. Najeeb ba zai taɓa haka ba, ba halin sa ba ne, No.
Ya jima tsaye kafin ya bi bayan Najeeb wanda tuni ya shige ciki...
Ƙarfe tara da rabi Farida da Sabreen su ka iso Kamfani. Tun a mota Sabreen ke tambayar Farida me ke faruwa amma ta ka sa gaya ma ta. Cewa kawai ta yi za ta ba da wani shaida ne.
Farida kam cikin zuciyar ta ayyana yadda za ta yi ƙuli-ƙulin Kubra da Naomi ta ke yi...
Kai tsaye sama su ka wuce. Sabreen na ta cewa ta yi a hankali saboda condition ɗin ta.
Su na isa office ɗin kuwa Naomi na fitowa daga office ɗin Najeeb.
Belt ɗin Najeeb da ta sa a jaka ta ciro, ta yi kan Naomi da sauri. Naomi ba ta ankara ba ta ji saukar belt a bayan ta. Dama ta gan su, ta kau da kai ne kawai, saboda yanzu ta gama convincing Najeeb akan ya aureta kuma ya ma ta alƙawarin zai auretan. Tunda za ta zama matar Najeeb mi zai sa ta wani tsaya ba wa Farida girma...
Farida ta sake warɓa ma ta belt ɗin tana masifa "shegiya mai kaman Aladu, ke ce sheɗaniyar da ki ka haɗa ni da miji na ko"
A na huɗu da ta kai ma ta dukan ne Naomi ta riƙe belt ɗin tana huci.
" 'yar iska ramawa za ki yi? Bismillah, rama" ta jawo gashin Naomi ta falla mata mari. Naomi ta challa ƙara tana kiran sweetheart.
"Kan Uban chan, mijina ne sweetheart ɗin ki" ta sake yowa kan ta. Naomi ta shige office ɗin Najeeb da gudu.
"Ayshah take it easy" abinda Sabreen ke ta faɗa kenan.
Farida ta cire gyalenta ta miƙawa Sabreen ta ce " yau yarinyar nan za ta san da wa ta ke ja, sai na chanja ma ta kamannin ta"...
Numfashin ta sai da ya kusa ɗaukewa saboda abin da idon ta ya ci karo da shi. Najeeb ne tsaye gaban Naomi yana goge ma ta hawaye da hankerchief ɗin sa.
"My Champ" kawai ta iya faɗa bakin ta na rawa.
Ya kalleta da idon sa da su ka rikiɗa su ka koma ja....
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0️⃣5️⃣3️⃣
"Mi ya sa ki ka dake ta"
Najeeb ya faɗa da ƙarfi.
Mamaki, tsoro, kishi, baƙin ciki su suka haɗu su ka hana Farida Magana.
"Sorry, sorry dear" ya faɗi yana bubbuga bayan Naomi.
Sabreen ma dai mamakin ne ya cikata. Da ƙyar ta iya cewa " Noory what's this?, what's happening here?"
"This should be the last time da za ku taɓa min ita, she's very special to me, duk abinda ya taɓani ya taɓa ta"
Maganar da yai ya sa hawayen da Farida ke tarewa su ka fara zubowa.
"Najeeb akan wannan Kafirar ka ke min walaƙanci tun shekaranjiya? Akan wannan fasiƙar?"
"Please ku bar min office ba na son hayaniya" ya faɗa tareda kwanto da kan Naomi jikin sa.
"Noory what's wrong with you?" Sabreen ta faɗa ganin yadda Najeeb ya bada hankalin sa kwacokam a wajen Naomi.
Zuciyar Farida kaman za ta bulluƙo tsabar yadda ta ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi. A hankali ta tako gaban su tana kallon cikin idon Najeeb.
Naomi ta sake narkewa jikin Najeeb tana kukan munafurci.
"Wallahi yau ka ce kana son Sabreen za ka dawo da ita rayuwar ka. Zan yi kuka, zan ji baƙin ciki, amma daga baya zan rarrashi kai na na amince ma ka. Amma wannan?"
Ta faɗa tana nuna Naomi.
"Ba zan taɓa amincewa ba har abada"
"Fine, dama ba amincewar ki na ke nema ba. Infact we are getting married soon"
Ta buɗe baki za ta yi magana amma sai hawaye. Ta juya da sauri ta fita, Sabreen ta bi bayan ta da gudu...
Ganin halin da ta ke ciki ya sa dole Sabreen ta raka ta gida. Kuka ta ke cikin motar kaman ranta zai fita. Da ƙyar Sabreen ta dinga rarrashin ta saboda abin cikin ta...
Kwanciya Farida ta ce za ta yi hakan ya sa Sabreen ta ma ta sallama tareda cewa za ta gayawa Mom abinda ya faru dan abin ya ɗaure ma ta kai...
Sabreen na tafiya Farida ta shiga haɗa kayan ta.
...........................
"Wato dai ba za ki gaya min mi ya dawo da ke gida ba ko"
Farida ta juyar da kai ta cigaba da hawaye.
"Ki tashi ki koma gidan ki kafin Baban ku ya dawo"
"Ummi kafira ce fa, wai kafira zai aura. Akan ta ba irin walaƙancin da bai min ba. Ni na haƙura, ya je ya auretan zai gani ai"
"Najeeb ɗin?"
"Ummi cikin ido na fa ya kalla ya ke faɗa min wai zai aureta. Ko na amince ko ban amince ba babu ruwan sa aurenta zai yi" ta fashe da kuka.
Ummi ba ta yi ƙoƙarin hanata kukan ba sai ma nazarin maganganun Faridan da ta fara yi wanda ta ke ganin ba lafiya ba. A yadda ta karanci Najeeb yana tsananin son Farida ba zai taɓa ma ta walaƙanci haka kawai ba musamman yadda ta ke da cikin nan.
Rarrashin Faridan ta shiga yi saboda cikin jikin ta...
Sabreen na zuwa ta sanar da Mom abinda ya faru. Mom ta ka sa gaskata hakan, ta ɗau waya ta shiga kiran Najeeb amma bai ɗauka ba. Mom ta ce ba ta ga ta zama ba dole su je har kamfanin ta ji bahasin wannan sabon salo na shi...
Da su ka je ba su same shi ba. Shi da Naomi sun fita. Mom ta je office ɗin Anas shima baya nan ya fita. Haka su ka dawo gida tana jira Daddy ya dawo ta sanar da shi komai...
Farida kashe wayarta ta yi lokacin da ta ga Anas ya dameta da kira. Bayan ta yi sallar Azahar ta samu ta kwanta saboda baccin da ba ta samu ta yi jiya ba.
Anas kuwa ya ga lokacin da Najeeb da Naomi su ka fita. Yana kiran Najeeb amma ya ƙi kula shi. Farida ya shiga kira amma ba ta ɗauka ba, ƙarshe ma aka kashe wayar. Hakan ya sa ya je ya shiga mota ya wuce gidan su. Da ya isa gidan Tasallah ke gaya ma sa Farida ta tafi gidan su kuma yanayin kayan da ta ɗauka kaman yaji ta yi.
Hankalin Anas ya kuma tashi yana tunanin mi ke faruwa tsakanin wannan masoya.
Gidan su Farida ya wuce direct. Da ya isa ya aika yaro akan ya kira ma sa Farida inji Anas. Yaron da ya shiga ya samu Ummi ya gaya ma ta. Ummi ta aiki Zainab ƙanwar Maijiddah akan ta cewa Anas Farida ba ta jima da bacci ba. Za ta kirashi idan ta tashi.
Anas dai ya tafi ne amma ya so ya ga Farida ya tambayi mi ke faruwa. Yana hanya saƙon Mom ya shigo akan idan ya tashi a waken aiki ya zo gida...
........................
Bayan la'asar ta farka. Kuma Alhamdulillah zuciyarta yai sanyi.
Sai da Ummi ta tabbatar ta ci abinci sosai sannan ta shiga ma ta nasiha tareda faɗa ma ta illar baro gidan ta da ta yi.
"Ummi to na koma na ma sa mine? Bayan ya samu 'yar ma su fitsari a tsaye yace yana so"
"Farida kenan, har yanzu da sauran ki. Wa ya gaya miki zaman aure zaman jin daɗi ne na dindindin. Ki koma gidan ki ki cigaba da yiwa mijin ki addu'a har Allah ya warware mu ku matsalar da ku ke ciki. Ni ina tunanin ba haka yarinyar nan ta bar shi ba. Amma addu'a ya fi ƙarfin ko wani sharri dan haka shi za ki riƙe"
Maganganun Ummi ya sa jikin Farida yai sanyi. Sai yanzu ne zuciyar ta ya fara wannan tunanin. Ƙila Naomi ta yiwa Najeeb wani abu ne...
Cikin ruwan zamzam da su ka zo da shi daga saudiyya Ummi ta ɗauko ta kawo ma ta. Sai a lokacin Faridan ma ta tuna su ma na su da su ka zo da shi bai ƙare ba. Ta amsa tana yiwa Ummi godiya.
"Kar ki saka damuwa a ranki dan Allah, ki riƙa tashi da dare kina yiwa mijin ki addu'a, sannan wannan ruwan zamzam ɗin ki dinga haɗa ma sa a ruwan shan sa, abinci dama shayin da zai sha. Ki riƙa tofe makwancin sa da kuma inda ya saba zama da Suratul Falaƙi da Naasi saboda suna maganin asiri da sheɗanu"...
Ƙarfe bakwai saura ta isa gida. Kunna wayarta da ta yi ta ci karo da saƙonni. Biyu daga Anas sai ɗaya daga Mom sai ɗaya daga Lukman inda ya ke ma ta godiya domin Sabreen ta amince da shi. Na ƙarshen ne ta ga Abdullahi dreba inda ya ke cewa "Hajiya dan Allah akwai maganar da na ke son gaya mi ki gameda Oga".
Ta turawa Lukman saƙon taya murna kafin ta kira Abdullahi. Da ke yana tareda Najeeb a mota sai bai ɗauka ba. Da aka sake kira sai ya ɗauka ya ce " ina tuƙi Hajiya, mun ma kusa isowa gida"
Farida ta sauke ajiyar zuciya lokacin da ta kashe kiran.
Numbar Mom ta kira dan saƙon na ta cewa ta yi ta kira ta dan Allah.
"Ayshah ki na lafiya?"
"Lafiya Mom" ta amsa tana ƙoƙarin saita maganarta.
"Anas ya ce min kin koma gidan ku, dan Allah 'ya ta ki dawo, zan zo gidan na ku gobe"
"Mom na dawo ma, yanzu haka ina gidan"
"Allah ya miki albarka"
Farida ta amsa da amin...
Bai fi minti shabiyar