Showing 54001 words to 57000 words out of 145203 words
shiga na ɗau hoto. Ni ba abin da na yi"
Wani a gefe ya ce " Miss Salihu binciken mu ya nuna kin haɗa hannu da Kamfanin VESTAC domin ki lalata sunan kamfanin nan ta hanyar sace takardun zane da kuma faffasa modelling ɗin da aka haɗa"
"Ni ban san su waye VESTAC ba, jiya su ka turomin kuɗi batareda na taɓa sanin su ba"
"Ƙarya ki ke Miss Salihu, kin je bid ɗin da aka yi a Lagos tareda Mr Najeeb kuma kamfani VESTAC na ɗaya daga cikin wanda su ka je wannan bid ɗin, su na neman a basu wannan project"
" Allah ya isa na"
"Miss Salihu ga details na account ɗin ki, miliyan biyu sun shigo mi ki jiya daga Kamfanin VESTAC, mi za ki ce gameda haka? " wani acikin su ya kuma faɗi.
"Ni kam kun sani a gaba da tambaya kamar wanda na kai ziyara ƙabari. Ni ban san VESTAC ba balle na san dalilin da za su turomin kuɗi"
Wani daga cikin su ya ɗau waya yai kira ya ce " ku ce ya shigo"
Wani tsoho ne ya shigo, masinja ne a kamfanin tun farko-farkon buɗeshi, da ke a first floor ya ke aiki Farida ba za ta ce ta san shi ba sai dai kaman ta taɓa ganin sa.
Ce wa aka yi ya shigo yai bayani.
Ya zo ya tsaya gefen Farida saboda kujera ɗaya ne a wajen ya ce " Ranka shi daɗe. Sakatariyar Oga Najeeb ta zo ta sameni akan an ba ta aiki amma ba ta san ya za ta aiwatar ba dan za a iya ganeta. Ta sanar da ni kamfanin Vekta"
"VESTAC" wani aciki ya gyara ma sa.
"Yawwa kamfani VESTAC sun ce ta lalata aikin da aka yi ta kuma sace takardun zane saboda ba sa so kamfanin nan ta samu wannan aiki. Sun ce za su ba ta miliyan biyu. Ni kuma ta min alkawarin za ta bani dubu ɗari biyar aciki idan na yi wannan aiki"
"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun. Tsohon banza ka ji tsoron Allah. Ni yaushe ma na taɓa magana da kai"
"Na rantse da Allah, kai na rantse da mutuwata ita ta sani na je na ɓata abun nan na kuma sace takardun zanen, ba na baku takardun ba ɗazu"
Malam Muntari irin tsofin Najadun nan ne, wanda sun yi ƙuruciyar bariki tsufan su kuma ya zo ya zama a lalace.
"Malam Muntari munji bayanin ka za ka iya tafiya"
Sai da ya fita wani da ke gafen Najeeb ya ce " Miss Salihu kin dai ji abinda ya ce, mi za ki ce gameda abinda ya faɗa domin ki kare kan ki"
Ajiyar zuciya Farida ta yi sannan ta ce " ni ba abinda zan ce, tunda tsoho kamar wannan bai ji tsoron Allah ya faɗi gaskiya ba ai ba abinda zan ce. Allah ne shaida ta, ni ban san VESTAC ba, wannan tsohon kuma ban taɓa magana da shi ba"
"To Miss Salihu ki ɗan bamu Minti biyar"
Har ta zauna a lobby ɗin wajen ba ta daina maimaita kalmar Hasbunallahu wa ni'imal wakil ba.
Minti shabiyu ta yi a wajen sannan a ka kirata.
Tana zama wanda ke gafen Najeeb ya ce " Miss Salihu mun sameki da laifin ɓata sunan kamfani. Daga yau kin bar aiki a Najeeb Constructions sannan kamfanin nan tana bin ki taran miliyan biyu da rabi za ki biya cikin kwana talatin, idan ba ki amince da wannan hukunci ba ko kuma ki ka ƙi biyan wannan kuɗi to za mu shigar da ke ƙara kotu"
Kallon Sir Najeeb ta ke idon ta ya ciko da hawaye. Shima ɗin kallon ta ya ke amma wannan karan ita kan ta ba ta san kallon tausayi ya ke ma ta ba ko kallon madallah.
"Sir ka na da abin cewa?" Wanda yai maganar ɗa zu ya tambayi Najeeb...
*Allah ya kaimu daren yau da rai da lafiya sai ku ji mi Sir Najeeb zai ce*
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0️⃣2️⃣1️⃣
"She stays" abinda ya faɗa kenan.
"Sir amma..."
"Za ta biya taran kamfani but she stays"
Daga haka ya tashi ya fita. Tana zaune a wajen ta kasa tashi, ji ta ke kamar an kafe ƙafafuwan ta a wajen. Tana ji su na wasu maganganu a kanta da Sir Najeeb amma kuma ba wannan ne damuwar ta ba. Ita da ta ke shirin aure ina za ta samu 2.5M, 'yan kuɗaɗen ta duk ta yi amfani da su wajen siye-siyen abubuwan biki. Ummi da Baffa Musa da wanne za su ji, da siya ma ta kayan ɗaki ko da biyan miliyan biyu da rabi.
Har su ka gama fita ba ta tashi a wajen ba sai da Yakubu ya zo.
"Farida wani hukunci su ka yanke?"
Maimakon ta bashi amsa sai ta ce "Yakubu kai ma ka yadda ni na yi abun nan?"
"Na san duk tsiyar ki iya maganar baki ta tsaya, wannan ba halin ki bane"
"Yakubu 2.5M ina zan samu?"
"Malam Muntari ɗan giya ne, zai yiwu an biyashi dan yai miki wannan sharrin ne, amma Allah ya fisu koma waye ne"
"Ni kam aikin nan nawa ake bani da mutane su ka sa mun ido a kanshi haka?"
"Akwai Allah Farida, tashi mu tafi"
Office ɗin sa ya kaita ta zauna yana daɗa ba ta baki, sai da ya ga ta samu nitsuwa kafin ya rakata zuwa office ɗin ta.
Ta zauna ne amma kaman a ƙaya ta ke, ko da ta cigaba da aiki anan, hankalinta ba zai kwanta ba domin kowa da wannan abun za a dinga ganin ta.
Tana cikin wannan tunanin Anas ya shigo.
" 'yar uwa dan Allah ki yi haƙuri, wallahi ban yadda ke ki ka yi abin nan ba. Zan cigaba da bincike har sai na gano gaskiya"
"Ba komai Yaya na. Allah shi ne shaidata"
"Kin yi magana da Najeeb ne?"
"A'a"
"Barin sameshi"
Anas na shiga office ɗin ta yi ajiyar zuciya sannan ta jawo wayan ta ta fara dube-duben hotuna. Sai da ta kai kan hotunan modelling ɗin nan sannan ta tsaya. Hoto kawai ta je ɗauka ga shi ya zame ma ta jaraba. Tana kallon hoton ba ta san lokacin da hawaye ya fara zubo ma ta ba, hawayen da ba ta yi ɗazu ba shi ta ke yi yanzu...
"Na ji hukunci da aka yanke, amma Najeeb kai ka san Farida ba za ta iya samun 2.5M cikin 30 days ba"
Yai ajiyar zuciya ya ce "zan biya ma ta"
"No need"
"Ban gane ba?"
Najeeb yai dariya wanda ya fi kama da dariyar yaƙe.
"Ni ta yiwa laifi, so only i gets to punish her. Wannan duk formalities ne na Kamfani and i've cleared it up"
"Wait, ka biya ma ta 2.5M ɗin?"
"Ina da abinyi Anas, so get out"
"Najeeb are you inlove with her?" Tambayar da ta sa Najeeb ya tashi tsaye lokaci guda, cikin fushi ya ce "how dare you say that to me"
"Dude, abin ne da mamaki. Tunda Farida ta zo kamfanin nan ka chanja, when it comes to her ba ka iya taɓuka komai. What could that be if not love"
"Get out, get the hell out of here"
Anas dai ya fita ne amma zuciyar sa ta gama amincewa da Najeeb na son Farida. Its so obvious all this while bai gane ba...
"Wai wani irin magani ki ka yiwa Najeeb ne? Duk abinda ki ka yi sai ya shanye. Gaya min wani malamin ki ka riƙe?"
Takaici ma ya sa Farida ba ta tanka ma ta ba.
"Farida da ke na ke magana"
Wannan karan ba za ta ɗauki cin fuska daga wajen Khalidah ba.
"A wajen uwar ki na ke karɓan magani. Ki fita min a office kafin ki ga rashin mutunci"
"Its not over yet Farida" ta snapping a dai dai fiskarta sannan ta fita.
"Kai ya Allah daga wannan sai wannan. Ni da na san wannan cin fuskan zan fiskan ta a wannan kamfani da tun farko da Sir Najeeb ya koreni na tattara koli na na tafi"
Ba ta idda zancen zuci ba wayar ta ta fara ƙara.
Tana ɗauka ya ce " to my office"
Saɓanin ɗazu da ta ganshi a wancan hall ɗin yanzu fiskar sa ta sauya akwai ɗan fara'a a tattare da shi.
"Ki fixing meeting da team Alpha anjima"
"Sir Najeeb ba abinda za ka gayamin, ba za ka tambayeni gameda gaskiyar lamari ba"
"Miss Salihu, ba yau na fara gaya mi ki ba. Our relationship is strictly professional, anyi investigation kuma an sameki da laifi, kuma an hukunta ki. What else do you want me to say?"
"Sir Najeeb ko da na cigaba da aiki anan, daraja na ta zube, mutunci na ya zube"
"Wanni daraja ki ke da shi dama? You are just a secretary, my secretary"
"Shikenan tunda abinda ka ce kenan. Amma duk min daren daɗewa gaskiya za ta fito kuma da kai da sauran ma'aikatan na ka duk sai kun ji kunya"
................
Wata ɗaya kenan da ya wuce. Aiki a Najeeb constructions ya zamewa Farida sabuwa, zuwa kawai ta ke amma ba ta jin aikin a ranta. Ko da Anas ya ce ma ta Sir Najeeb ya biya ma ta kuɗin ba ta ma sa godiya ba. Ta so ajiye aikin amma sai ta yi tunanin idan ta bari to wanda basu yarda akwai hannunta a abinda ya faru ba ma za su yarda, shiyasa ta cigaba da zuwa. Dama niyyarta da zaran saura wata ɗaya auren ta za ta je ta rubuta takardar barin aiki.
Sir Najeeb bai chanja ma ta ba, yadda ya ke da ɗin haka ya ke, wani lokaci yai ihu yai faɗa wani lokaci kuma yai magana a hankali. Saɓanin da da ta ke maida ma sa magana yanzu kam ko mi zai ce ba ta kulashi.
Ta koma ba ruwan ta da kowa aikinta kawai. Ko sallah a office ɗin ta ta ke, balle wajen cin abinci kam ta dena zuwa...
"Sir ga resignation letter ɗi na" ta faɗi lokacin da ta ajiye ma sa takardar a gaban sa.
"Ok" iya abinda ya faɗa kenan ko ɗagowa bai yi ba balle ya kalli idon ta.
Ta yi mamaki dan Najeeb ɗin da ta sani da ba zai yi shiru ba.
"Allah ya sada mu da alkhairi Sir Najeeb. Na gode da taimako da kulawar ka"
Cikin zuciyar sa ya amsa da amin.
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0️⃣2️⃣2️⃣
Waɗanda ta ke mutunci da su kawai ta je ta yiwa sallama. Lokacin tashi yai ta haɗa yanata-yanata ta tattara office ɗin,ta ɗauko office laptop da Najeeb ya ba ta dawo ma sa da shi.
"Sir Najeeb zan tafi, ka yafeni dan Allah, na san a zaman da mu ka yi na yi laifuffuka dayawa amma ka yi haƙuri. Allah ya yafemu gaba ɗaya"
Shiru ne ya ratsa office ɗin na lokaci mai tsawo. Tun tana ganin Sir Najeeb zai buɗe baki yai magana har ta cire rai ta fita daga office ɗin.
Sai da ta fita daga office ɗin sannan ya ɗago idon sa ya ce " i'm not done with you yet Miss Salihu"....
Office ɗin Anas ta je dan ta ma sa sallamar ƙarshe.
"Yanzu ƙanwata shikenan kin bar aiki da mu?"
"Yaya na ai ana tare ko da bana aiki anan"
"Gaskiya ban ji daɗi ba, yanzu idan ki ka tafi wa za mu samo ya replacing ɗin ki. Ke ce the second longest surviving secretary a wajen Najeeb"
"Ya Anas kenan, ai da ƙyar mu ka sha mu ɗin ma"
" ba wani, da ƙyar dai Najeeb ya sha a wajen ki"
Dariya ta yi sannan ta ce " ya Amaryar ta mu?"
"Tana nan sai rigima"
"Ta kaini rigima"
Anas ya zaro ido yana dariya "ai Farida idan ta kai ki rigima bulaguro zan yi a garin. Irin ki ai sai su Najeeb"
"Hmm Ya Anas kenan. Nikam ina abokin adawar ka? Ko ya janye ne?"
"Ai tunda Daddy ya sa min stamp na yaƙice shi. Ga shi dama gimbiyar wannan ɗan baƙin kaɗai ta ke gani"
"Allah ya kaimu lokacin biki Yaya na"
"Amin ƙanwata, kar a manta da IV ɗin mu fa"
"Ai kune ƙarɓan fari".....
...................
Shirye-shiryen biki ake ba kama hannun yaro saura sati uku aure aka kawo lefen Farida kuma gaskiya Rayyan ya yi ƙoƙari sosai.
Farida ta duƙufa da gyaran jiki da shirye-shiryen yadda biki zai kasance.
Yau ana saura kwana goma sha takwas aure, Baffa Musa ya kirata.
"Wani shirme na ke ji za ki yi ranan Alhamis?"
"Baffa friends day za ayi ranan Alhamis tunda ka hana ayi kamu"
"Enemies day za ki yi ba friends day ba. Yanzu ke Farida ba za ki yiwa kan ki faɗa ba. Ayi miki walima salamun alaikum a kaiki ɗakin ki hankali kwance, sai kin bijiro da wani shirme"
"Baffa a cikin gidan nan fa za'ayi kuma iya mata ne ka san inada jama'a"
"Ungo na ki ke da jama'an na ki"
"Mun gode Baffa"
Taɓe baki yai kawai yana bin ta da kallo. Bakin tan nan yana fata ya zaunar da ita lafiya a gidan ta, ba ya kawo fitina ba.
"Baffa ina ka amince?"
"Ya na iya uwata. Allah ya kaimu lokacin ya kuma kaɗe fitina"
"Baffa thank you" ta faɗa tana tashi da sauri...
................
Duk yadda ta ke ji gameda auren sai da auren ya zama saura sati ɗaya sai jikinta yai sanyi. Haka kawai sai tsoro ya shigeta gani ta ke kamar za a kuma wani chakwakiyar kamar yadda aka yi lokacin Lukman. Ummi ta zo amma su Nanna sai Alhamis za su shigo. Ranan talata da safe ta wuce Najeeb constructions. Ta fara biya wa office ɗin Sister Munibat ta ba ta katin gayyata tareda cewa idan ba ta zo ba to sun ɓata.
"Sister Aisha kenan, ai indai ina da rai da lafiya to bikin ki da mu za ayi"
Farida ta ɗan harareta " kaman da gaske, kin sayi ashobe na kuwa?"
Sister Munibat ta fara sosa kai.
" hmmm ai dama na sani, Dan Allah ki daure ki zo"
"Insha Allah sister Aisha zan zo"
Daga wajen Sister Munibat ta wuce wajen Anas. Ta jima a wajen sa, inda ya ke ba ta labarin sakataren da aka ɗauka bayan ta tafi.
"Farida kwanan sa huɗu ya ajiye aiki, wai ba zai iya ba"
"Ai Sir Najeeb idan ba jan wuya ba ba mai iyawa da shi"
"Jan wuya kamar ki ba"
"I'in ai mun sha fama da shi"......
Lokacin da ta shiga office ɗin sa yana jikin shelf ya na neman wasu files. Ta tsaya tana kallon yadda ya ke ta dibi-dibi a wajen. Da ta na nan yanzu da ita ke wannan aiki.
"Sir Najeeb mai ka ke nema?" Muryan da bai yi zatan jin sa ba ya ji a ta bayan sa. Bai san lokacin da ya sake file ɗin ya faɗo ba. Tsayawa yai yana kallonta, ta wani yi haske tana sheƙi, ga wani ƙanshi mai daɗi da jikinta ke fitarwa.
Tsugunnawa ta yi ta ɗauka file ɗin sannan ta miƙa ma sa. "Ga shi na ma ka aikin ƙarshe"
Bai amsa file ɗin ba sai ma juyawa da yai ya je ya zauna a kujerar sa.
"Iko sai Lillahi, daga ganin Sarkin Fawa sai miya ta yi zaƙi. Sir Najeeb ba fa aiki na zo ba da za ka min jan ajin da ka saba"
"Oh really"
"Gashi, dama IV na kawo ma ka" ta yi saurin ajiye file ɗin tareda ciro IV ta ajiye ma sa.
"Dan Allah a daure a zo. Duk da ma dai i'm just a secretary"
Ta ɗan yi dariya ta ce " was just a secretary"
"Congratulations Miss Salihu"
"Thank you Sir Najeeb"
Ya ɗan kurɓi coffee da ke gaban sa sannan ya ci gaba da latsa laptop.
"Sir Najeeb ina da magana. Dan Allah ka ɗan rage halin kan nan. Ka ga ba kowa bane zai iya jurewa. Ni ma da ƙyar na sha a wajen ka. Allah, watarana idan na koma gida daga office har ƙaramin zazzaɓi na ke saboda stress da zafin kai. Kai ba a maka gwanin ta sannan..."
"Out"
"Ka ga irin halin na ka ko"
"Miss Salihu get out"
Ta yi shiru tana kallon sa sai da ta ga zai sake ɗaukan mug ɗin coffee ɗin sannan ta yi wuff ta ɗauke.
Ta kai baki da nufin ta kurɓe duka lokaci guda sai ta ji shi da zafi sosai. Ta ɗan kurɓi kaɗan ta sake kurɓa sannan ta ajiye ma sa.
Dariya ta yi saboda yadda ta ga ya zaro ido.
"Sir Najeeb tsokalar ƙarshe ne fa. Na tafi"
Harta juya sai kuma ta juyo ta ce "Sir Najeeb a yafe mu"...
Sai da ta rufe ƙofa ya ce "devil in a dress" ya jawo wani dogon envelop ya buɗe, hotuna ne guda uku a ciki " happy never marriage Miss Salihu" ya faɗa a fili.
(🙄Sir Najeeb ya dai?)
.......................
Farida na komawa gida ta tarar da Maijiddah ta zo.
"Kai-kai Jiddah mi ki ke ci haka? Kin ganki kuwa"
"Kai Anty Farida"
"Zo zo mu shiga ɗaki ki gaya min sirrin"
Sai da su ka zauna ta ce " Jidddah ciki gareki, wannan ƙiban da walakin"
Maijiddah ta rufe ido tana murmushi.
"Masha Allah, Allah ya raba lafiya. Ina kishiyar ki? Har yanzu tana Abuja?"
"E, amma yanzu sau biyu ta ke zuwa a wata"
" 'yar kusun'wa, za ta ma ajiye aikin ta dawo gidan ta, ko kuma ta ji ta a silencer dan mune ma su gidan yanzu"
"Na gode Anty. Kayan da ki ka bani sun min rana"
"Zauna a wajen, ai mazan yanzu sai da shigar bariki. Nima na je Jos na kwaso nawa suna nan jingim"....
Biki na matsowa jikin Farida na ƙara sanyi kullun ta yi bacci sai ta yi mafarkin an fasa aurenta. Abin ya dameta ta gayawa Ummi, Ummi ta ce ta dinga addu'a. Itama ɗin Ummin Allah-Allah ta ke ayi bikin lafiya ba tareda wata matsala ba.
Ranan Alhamis aka je aka yiwa Farida jere a gidan Rayyan. Rayyan ya gina 3-bedroom flat mai kyau. Baffa yai ƙoƙari dan ya kashe kuɗi sosai wajen sayen ma ta kaya, 'yan uwan Ummi ma sun yi ƙoƙari gaskiya...
........... ..........
Ya na zuwa ƙofar gidan ya sa yaro ya kira ma sa maigidan. Da yaron ya fito ya ce yana zuwa...
Musabaha su ka yi da dattijon sannan su ka gaisa.
"Yi haƙuri ban ganeka ba"
Ya miƙa masa envelop sannan ya ce " ɗan ka zai yi aure ranan Asabat ɗin nan ko?"
"Insha Allahu"
"Matar da zai aura ba matar aure ba ce"
"Ban gane ba"
"Ka dubi cikin envelop ɗin nan za ka ga zahiri" daga haka ya juya ya tafi.
.....................
Anyi friends day lafiya kuma ba laifi ƙawayen ta na Jos sun zozzo, anci an sha kuma an girgije.
Ƙarfe