Showing 105001 words to 108000 words out of 145203 words

Chapter 36 - SAKATARIYA TA COMPLETE

Azizat   

13 Jul 2024

25711

ya ga komai na nan yadda ya ke, ya kalli kayan da ta bari a kan gado riga da skirt na atamfa wanda ta sa da fari kafin ta chanja su.

"Clumsy Aysherh, will she ever change?" ya furta a fili...


Farida kam sai da ta ga bayan taro, domin jama'a sun ma ta chaa kowa yana jinjina ma ta kan namijin ƙoƙarin da ta yi. Tun daga 'yan uwan Najeeb na ɓangaren Daddy da su ka zo daga Gombe zuwa 'yan uwan Mom da su ka zo daga ƙasashe daban-daban. Mom ta nuna ma ta yayun ta biyu maza da kuma cousin ɗin ta mahaifin Sabreen. Farida kam baki har kunne domin kyauta kam ita kan ta ba ta san iyakan abinda ta samu ba...


Ƙur'ani ne a hannun sa yana karatu lokacin da ta shigo ɗakin. Yadda ta ke jin jikinta idan ba ta je ta watsa ruwa ba ba za ta ganema kan ta ba.

"Aysherh"

Ya kira sunan ta.

Ta juyo ta kalleshi har da lumshe ido.

Yatsa kawai ya ɗaga ya nuna ma ta kan gado. Bin yatsar ta yi da kallo har idon ta ya sauka kan kayan ta da ke kan gado.

"Ba na son ƙa..."

"Na sani- na sani. Kawai dai su Ummi da su ka kirani ne ya sa ban ɗage kayan a wajen ba, Mr ba na son ƙazanta" tana faɗa tana tattara kayan.

"Kai fa ka dawo kenan ka yi ta yiwa mutane gadara da ɗaki, bayan ɗakin na mu ne mu biyu"

Bai kulata ba ya cigaba da karatun da ya ke yi...

Bayan ta fito daga wanka ta sa wata ƙaramar riga wanda ko rabin cinyar bai gama rufewa ba. Ƙaton hijabi mai hannu ta sa ta zo ta ɗau sallaya ta tada sallah. Lokacin da ta idar ba ya ɗakin. Ba ta san ya aka yi zuciyar ta ya raya ma ta kaza ya je nemowa ba. Haka kawai ta tashi ta fara duba hammata da gabanta ko ta yi waxing na shi da kyau, ba ta so ya kalleta ya faɗa ma ta kalmar da ke baƙanta ma ta rai ɗin nan "Mrs Jibo ba na son ƙazanta yanzu kuma Aysherh ba na son ƙazanta"
Ta girgiza kai ganin komai na nan tsaf-tsaf ba ta jima da gyara wajen ba.
Ta fesa turaruka a ɗan filingin kayan na ta, sannan ta shafa turarukan jiki.

"Aishatu anya wannan uban turarukan bai yi yawa ba?" Ta tambayi kan ta tana shinshina jikin ta...



Wajen Daddy ya je a chan ɗakin sa, shima dawowan sa kenan daga rakiyan baƙi.

"Dad you called me"

"Ya ƙarfin jiki?"

"Alhamdulillah"

"Son abu biyu ya sa na kiraka. Na farko lokacin da ba ka da lafiya Anas ya turo magabatan sa kuma na bashi Najdah. Mun saka biki ƙarshen shekara lokacin ta ƙare karatun ta. Alhamdulillah along the line sai ka farfaɗo, saboda hankalinmu na kan samuwar sauƙin ka shiyasa mu ka jingine maganan aure a gefe. Amma yanzu tunda ka samu lafiya sosai me ka ke gani mu ɗaga bikin ne ko kuma a bar shi a date ɗin da ɗin?"

"Duk abinda ku ka ga ya dace ni bani da abin cewa"

"Abu na biyu shine maganar mahaifiyar ka. Najeeb dan Allah ka gyara tsakanin ka da mahaifiyar ka. Ta yi kewan ka sosai, na san yanzu ba kaman da bane tunda har kana kiran ta da kalmar uwa. Amma still ka raɓeta ka samu albarka ajikin ta. Uwa fa Uwa ce Najeeb..." haka Daddy ya cigaba da yi ma sa nasiha mai ratsa jiki

Ya jima yana hawaye kafin daga baya ya bawa Daddy haƙuri tareda alƙawarin zai gyara...

Ya so ya samu Mom a wannan dare sai dai kuma bai san waɗanne kalmomi zai yi amfani da su ba, shiyasa ya haƙura har sai ya samu nitsuwa sosai...


Ana murɗa ƙofa ta yi saurin rufe idon ta kamar mai bacci. Tana kwance ne tun ɗazu tana jiran kaza da kuma abinda ake yi bayan kaza sai dai Najeeb bai shigo ɗakin da wuri ba.

Jin bai zauna akan gadon ba ya sa ta ɗan buɗe ido ɗaya ta leƙa shi. Mug ne a hannun sa yana shan tea, ta sake buɗe ɗayan idon ta duba gefe da gefen sa da kyau ko za ta ga leda ko take away ba ta ga komai ba. Tana bin sa da ido har ya ƙarisa shan tea ɗin ya shiga banɗaki yai wanka.

Pyjamas ya sa ma su laushi baƙaƙe kamar yadda ya saba, ya zo ya kwanta gefen ta. Kashe wuta yai ya jawota jikin sa sannan ya fara bacci bayan ta ji bakin sa na motsi alamar addu'a yai. Ta jima tana ta tunani kafin bacci yai gaba da ita ba tareda abin da ta hasaso ya auku ba. Ba maganar kaza ba maganar abubuwa...


*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣4️⃣3️⃣



Washe gari ma baƙi ne su ka yi ta zuwa gaisuwa, tun da safe har yamma. Kafin su samu sarari ma sai da aka yi kwana huɗu da dawowar shi gida...

Da sassafiyar Jummu'a ya shigo ɗakin mahaifiyar sa. Dad bayanan ya tafi wani taro a Minna.
Tana zaune akan sallaya tana jan carbi ya shigo.
Gwiwowin sa ya sa a ƙasa ya ɗaura kan sa a kafaɗar ta.
"Mon ki yafe min dan Allah, for years i treated you..."


"Shhhhhhh" ta dakatar da shi, hawaye ne ke zubowa a idon ta wani na bin wani.

"Son na yafe ma ka. Ba laifinka ba ne kaɗai, har da ni. You were young, you're traumatize, maimakon na ja ka ajikina na nuna ma ka kulawa sai na barka hakanan har abin ya zo ya girma a ranka. I'm sorry son"

Ita hawaye shi hawaye. Uwa da ɗa sun jima rungume da juna kafin daga baya Najeeb ya janye jikin sa ya ce "Mom zan sake yin wani laifin. Ki yafemin kafin lokacin"

"Son minene?"

A hankali ya furta Sabreen...

.............................


Farida ta shiga kitchen tana ƙoƙarin haɗa Alala saboda sha'awarta da ta tashi da shi yau da safe sai ga Najdah ta shigo kitchen ɗin. Da alama shigowa ta yi dan ta ɗauki wani abu, ba gaisuwa balle sannu da aiki. Farida ma ta yi kamar ba ta gan ta ba.

"Adama, Adama, Adama" Najdah ta fara ƙwala kiran sunan baiwar Allah.

"Wai ke wacce irin daƙiƙiya ce. Kin dai ga ba ta kitchen ɗin nan dai ko, sanin kan ki ne sarai tana shayarwa yanzu. Ki dinga kiran ta kamar wata 'yar cikin ki. Matar nan idan ba ta baki shekara goma ba za ta baki takwas amma ki wage baki ki dinga kiran sunan ta kamar wanda ku ka yi wasan ƙasa tare. Adama...Adama"

"Kin ga bana son shishshigi Farida, ban yi da ke ba dan haka kada ki shiga harkata"

"A hakan za'ayi auren, yarinya ba tarbiya ba komai"

"Uban ki da uwar ki ne ba su koya min tarbiyan ba"

Maimakon Farida ta bata amsa sai ta zo ta kama hannun ta.

"Ki sake ni, ki sake ni Farida"

Jan ta ta ke yi Najdah na tirjewa, amma da ta ga uwar bari sai ta haƙura ta bi ta dan taga iya gudun ruwan ta, ta san ƙarshe wajen Mom za ta kai ta.

Ba ɗakin Mom su ka shiga ba sai ɗakin su Faridan.
Yana zaune akan kujera yana ƙoƙarin duba wassu takardu, yana so ya fara fita aiki ranan monday, tunda yanzu ya gane kusan komai gameda ayyukan sa.

Buɗe ƙofar da aka yi ya sa shi juyowa. Yanzu su ka gama daru da Farida kafin ta fita akan wai ta chanja ma sa tsarin da ya jera kayan sa.

Gaban Najeeb su ka tsaya kallon su ya ke yana so ya gano mi ke faruwa.

Farida ta zage hannu ta falle Najdah da mari. Shi kan sa Najeeb sai da ya tsorata da marin nan.

"Matar yayan ki na ke Najdah, ni ba kishiyar ki ba ce. Idan ba za ki bani girma da matsayi da Allah ya bani a kan ki ba. To kuwa ki shirya dan kafin ayi bikin ki sai na gyara miki zama a wannan gida"

Ta juya ta kalli Najeeb ta ce " ka gayawa ƙanwar ka cewa ba na son raini, ko kuma idan na sa ma ta ƙahon zuƙa a gidan nan sai na zuƙeta zuut"
Ta juya ta fita ba tareda ta jira amsar da zai bata ba.


Najdah ta tsugunna a gaban Najeeb riƙe da fiskarta tana kuka.

"Big B she slapped me. Ba yau ta fara ba, she's being doing this for along time now"

Dafa ƙafarsa ta yi ta ce "Big B ka rabu da ita, she's not good for you wallahi ba ta son ka kuɗin ka kawai ta ke so"

Duk surutun Najdah bai ce komai ba kawai kallon ta ya ke. Bai rarrasheta ba dan haka da kanta ta bar kukan ta share hawayen ta.

"I love her Najdah" ya furta a hankali.

Najdah ta ɗan zaro ido dan ta yi mamakin kalaman Najeeb. Ita tunanin ta duk yadda ta dinga gaya ma sa aibun Farida lokacin yana asibiti abin ya shigeshi.

"Why? Big B why her? Akwai mata dayawa da ke son ka wanda su ka fi Farida komai. A hankali za ka ga wadda ta dace da kai"

"Because i love her"

Najdah ta haɗe rai.

"Ina son ki Baby, you're my dearest sister. Na san abinda ki ke so na yi bai wuce na zaɓa tsakanin ki da Aysherh ba. Kar ki nemi hakan a wajena domin za ki sha mamakin wanda zan zaɓa"

"Big B..."

"Na yadda bakya son ta, ba ta kuma burgeki amma ina so ki ba ta girma a matsayin ta na wacce na ke so"

"Big B you're confused, har yanzu ba ka san wacece Farida ba, har yanzu ba ka tuno rashin mutuncin da ta yi ta shuka ma ka ba. The girl is just a gold digger"

Najeeb yai murmushi ya ce " ki na son Anas ko?"

Najdah ta yi shiru.

"Ba kya tunanin yadda ki ka ƙi ɗan uwan ki Mustafah ki ka amince da Anas haka ƙannen Mustafah za su dinga ganin Anas a matsayin wanda ke son yin auren jari"

"Accept this simple truth Baby. I love Aysherh. Bana tunanin kina yiwa Anas rabin son da ta ke mini"

To mi za ta ce ma sa? wani ƙorafi za ta kuma yi?.tunda wanda ta ke tunanin zai ɗau mataki akan Farida ya nuna ma ta yana tsananin son Farida. Gwiwa a sace ta tashi ta fita daga ɗakin...


.............................

Yana ɗaura tie ta shigo ɗakin ɗauke da tray. Ta riga ta shirya tuntuni, fita ta yi ta ƙarɓo mu su breakfast.
Bayan ta ajiye tray ɗin ta ƙaraso gaban shi. He looked so handsome a grey three pieces suit ɗin kamfanin Brioni Vanquish II.

Hannu ta sa tana gyara ma sa tie ɗin.

"You look great My Champ"

"I think the right word is handsome" ya faɗa yana kissing hannun ta.

Murmushi ta yi ta ce"Mu je ka ci abinci"

Tea kawai ya sha sai ya ɗan tsakuri soyayyan dankali. Farida kam bayan toasted bread da ta ci guda biyu sai da ta ci soyayyen ƙwai da potato fries ɗin sosai.

Kallon yadda ta ke cin abincin ya ke yi yana sipping tea. Lokaci guda ƙwaƙwalwar sa ta tuna ma sa ranan da Farida ke cin cucumber a mota, yai murmushi.

"Na sani za ka ce wannan matar ta cika ci ko. Ba na juran yunwa ne ga ulcer da ta haɗumin biyu"

Kalmar ulcer da ta faɗa ya sa shi tunowa da ranan da ta sawa Sabreen yaji a gado har ta yi ƙaryar ulcer. Dariya ya farayi saboda tunowa da yai da abinda ya faru.

Tsayawa ta yi tana kallon yadda ya ke dariya, ya mata kyau sosai...


Driver ne ya ja su dan a asibiti sun hana shi tuƙi, atleast sai ya ɗau lokaci. Ita kuma Farida har yanzu ba ta iya tuƙi ba...

Su na fitowa daga mota ya bi building ɗin kamfanin da kallo, akwai so many memories a wannan waje wassu ya tuna su wassu bai tuna su ba. Tafiya su ke a hankali dukkan su biyun kowa da abinda ya ke saƙawa a zuciyar sa.
Dai-dai sun zo ƙofar shiga ya saka hannunsa cikin na ta. Kallon sa ta yi ya ɗaga ma ta gira...

Suna shigowa aka fara tafi, wajen ya sha decoration na flowers ga ƙatuwar banner da aka rubuta *Welcome back Mr and Mrs Najeeb Jibo*
Mutane dayawa da basu halarci waliman gidan su Najeeb ba su ka zo su na musabaha da Najeeb su na ma sa fatan alkhairi. Unlike Najeeb ɗin da yana amsa musabahar ne fiskar sa shimfiɗe da murmushi hatta ma su ƙananan matsayi kamar masinja ko cleaners sai da su ka gaisa da Najeeb.

Anas ne ya ja su suka je wajen da aka ajiye mu su cake, shi da Madam ɗin sa su ka haɗa hannu su ka yanka. A baki ya sa ma ta itama ta sa mishi a baki.
Sun ɓata kusan awa ɗaya a wajen kafin su ka shiga lifter zuwa third floor.


"Ga Mrs Comfort Masoyi ita ce sabuwar Sakatariyar ka"

Mrs Comfort ta rusuna ta gaishe da Najeeb.

Da Bismillah ta shiga office ɗin. Abin mamaki sai ta ga office ɗin ya chanja ma ta. Rabon da ta shigo office ɗin tun farfaɗowan Najeeb. Sau ɗaya ta zo ta yi meeting da wassu 'yan china da su ke son siyan hannun jari amma ba ta basu dama ba.

Office ɗin ne aka raba biyu an saka glass an raba tsakani.

Ba ta san anyi gyaran nan ba hakanan ba ta san wayayi ba.

Waya ta ɗauko tana ƙoƙarin kiran Anas Najeeb ya karɓi wayan.
"I made the changes" ya faɗa yana kama hannun ta su ka shiga ɗaya ɓangaren da aka raba. Bai ajiyeta ko ina ba sai kan kujera.

"You're good in marketting strategies, abinda ya sa ki ka iya bunƙasa kamfanin nan kenan. Ba zan iya yin aiki ni ɗaya ba, kafin na gane kan zaren aikin sai an ɗau lokaci. But with you beside me komai zai zo da sauƙi"

"My Champ..."

"Shhhhh" ya sa hannu ya rufe ma ta baki.

"We're going to work together now and always"

Faɗawa jikin sa ta yi tana kuka.

Ya fara bubbuga bayan ta yana lallashinta...

Shirye-shiryen bikin Najdah aka fara dan an mayar da date ɗin bakwai ga watan January kusan wata ɗaya da sati ɗaya kenan yanzu. Tun daga ranan da Najeeb yai wa Najdah magana ta dena shiga harkan Farida, magana ba ta haɗasu hakanan ba ta iya ma ta kallon banza kamar da...

Najeeb da Farida tare su ke fita aiki su dawo tare. Kusan komai ma ita ke jagoranta dan har yanzu wassu abubuwan sun sha ma sa kai.
Ana saura sati huɗu aure Mom ta sa aka fara yiwa Farida gyaran jiki tareda Najdah, wata mata ce aka kawo daga Sokoto. Farida dai dan Mom ta takura ne amma da ba abinda za ta yi, shi mutumin da za ayiwa gyaran jikinma domin shi har yanzu bayan kiss ɗin cikin mota ba abinda ya kuma yi. Daga ya rungumeta tsam ajikinsa idan za su kwanta sai wani lokaci ya kissing hannun ta ko goshi. Ita idan ba dan ranan a mota ta ji tudun abun shi ba, da sai ta ce ko ba shi da lafiya ne.

Da ke an ɗau hutun ƙarshen shekara ba sa fita aiki yanzu. Daga gida sai gida, ita Najdah har haushin Mom ta fara ji saboda yadda Mom ke wani ɗari ɗari da Farida, duk abinda aka mata na gyara sai ta ce a yiwa Faridan irin sa...

Saura kwana goma shashida a ɗaura aure sai ga Sabreen. Farida tun washegarin da aka yi walima ba ta sake ganin Sabreen ba. Da ke ba ta gabanta shiyasa ba ta tambayi ina ta je ba. Yadda ta ɗauka ma shine Sabreen ɗin ta bar ƙasar kenan har abada, amma da ya ke ba ta da kunya sai ga ta ta dawo. Ta san dai ba wai dan bikin Najdah ta zo ba, wani neman fitinan ne kawai...

Suna zaune a falo dukkan su, lokacin da ta shigo tareda tawagarta su uku. Biyu larabawa ne suma ɗaya kuma baturiya ce.

Najdah da Farida na zaune ƙafafuwan su na cikin ruwan ɗimi wanda aka cikashi da kayan ƙanshi.
Sabreen ta zo da gudu ta rungumi Mom tana kissing ɗin ta. Sai da ta gama shiriritar ta kafin ta nuna team ɗin da ta kawo. A matsayin ma su taimaka ma ta.

Ta kalli wata dattijuwa aciki wacce za ta kai 50yrs ta ce "this is Sarah, ita ce za ta kula da gyaran jikina" sai ta nuna ɗaya matashiyar wacce ba za ta wuce 25-26yrs ba. "Wannan ita ce Arfa, ita ce za ta dinga min kwalliya" ta nuna baturiyar ta ce "Najdah i brought her specially for you. Sunan ta Jean ita sexologist ce, i know you're a virgin, so she'll help you get rid of the fear and educate you on how to..."

Hahhahaha ta fashe da dariya.

Mom ce ta iya ce mu su sannu da zuwa ta ƙara da cewa " Najdah da Farida ga Sabreen itama ta kusa zama amarya"

Kaman bugun guduma haka Farida ta ji saukan maganan Mom " Sabreen ta kusa zama amarya. Amaryar wa?"

Ka sa zama ta yi a wajen ta cire ƙafafuwan ta acikin ruwan ta sa room slippers ɗin ta da ke gefe ta bar falon ba tareda ta ce komai ba. Ta sani Najeeb baya
nan, tun safe ya fita shi da Daddy. Waya ta ɗauka ta fara kiran sa amma bai ɗauka ba. Abu ɗaya ta sani idan har Sabreen za ta auri wani ba Najeeb ba to ba abinda zai sa ta baro chan ƙasar su ta zo nan ta zauna da niyyar wai ta zo gyaran jiki. Mi ke shirin faruwa?

Ranan har yamma ba ta kuma fitowa ba. Zazzaɓi ne ma ya rufeta. Tana nan haka Najeeb ya shigo ɗakin da sallama.
Ba ta kulashi ba har ya gama abinda zai yi ya zo ya kwanta gefen ta. Ƙanshin jikinta na ratsa duk wani jijiyar jini a jikin sa.

"Mi ya faru na ga ko sannu da zuwa ba ki min ba"

Idonta da su ka yi ja ta ɗago ta kalleshi ta ce "mi Sabreen ta ke yi a gidan nan?"

Ɗan dafe kan sa yai yana danne dariyar da ta taso ma sa.

"Oh sorry" ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce "i'm going to marry Sabreen,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login