Showing 30001 words to 33000 words out of 145203 words
a wannan ɓangare sai ta dake, ta kalli Sister Munibat ta ce " cewa na yi Sister Munibat ta ce ke 'yar ƙwaya ce"
"Astagfurullah" Sister Munibat ta faɗi da sauri tana yin wiki-wiki da ido tana ƙara cigaba da istigfari a zuciyarta.
Farida ta ce " to kin ji mi tace?"
Kafin sister Munibat ta yi wani magana Halima ta amsa da cewa " za ki ce ba ki faɗi haka ba, ranan a masallaci. Idan kin manta ni ban manta ba"
Ta ƙarasa maganar tana matsowa kusa da ita kamar za ta maketa.
Jikin sister Munibat ya fara ɓari musamman da ta tuno abinda ya faru.
"Kin gani ai ta ka sa magana saboda ta san gaskiya ne, munafuka, kina jikinta kina zaginta"
Farida ta kalli sister Munibat ta ce " ki faɗa min gaskiya. Kin faɗi haka ko baki faɗi haka ba?"
Sister Munibat ta buɗe baki za ta yi magana sai hawaye.
"Shikenan! Kukan munafurci. Dama yare, yare ai sai a hankali, dukkan su munafukai ne"
"Yi min shiru" Farida ta daka ma ta tsawa. Ta kalli sister Munibat ta ce " kin bani mamaki. Ina ɗaukan ki da daraja ina mugun mutuntaki. I consider you an older sister"
Ta juya ta fita saboda ba ta da ƙarfin yin masifa.
.......
Ƙarfe bakwai na yamma sai ga sister Munibat a gidan su Farida. Duk hayaniyar da ake na lissafe-lissafe a tsakar gidan, Farida ba ta ciki. Ƙarshen sati aka ce za a kawo lefen Maijiddah.
Tana chan kwance ta gama murƙususu akan gado saboda ciwon ciki. Maijiddah na gefe tana yiwa wata ƙaramar ƙanwarsu kitso.
"Anty Farida ga ƙawarki ta zo" Sadiq ya faɗa lokacin da ya faɗo ɗakin da gudu
Da ƙyar Farida ta ɗaga kai lokacin da sister Munibat ɗin ta shigo ɗakin su.
Sai da su ka gaisa da Maijiddah sannan ta zauna a gefen gado ta fiddo da ƙur'ani izub sittin ta ce " Sister Aisha na riga na yi alwala kafin na taho. Zan rantse mi ki akan abinda ya faru ranan da sister Halima ta ke faɗi"
Farida ta ɗan tashi jingine ta ce " bai kai har ga haka ba 'yar uwa. Ke dai ki gyara halin ki, zato zunubi ne ko da da gaskiya a cikinta. Sannan ki sani saka dogon hijabi ba shine ke nuna taƙawa ba"
"Na rantse da Allah sister Aisha ba abinda na faɗa ba kenan. Ranan da ba ki zo ba farko-farkon fara aikin ki, inaga lokacin bikin gidan kun nan ne. Ana taɗi shine aka kawo maganarki, cikin maida zance sai na ce *' sister Aisha kam wani lokaci idan ta yi wani abu kamar 'yar ƙwaya'*. Na rantse da Rabbil Arshi iya abin da na ce kenan"
Ta ja numfashi ta ce "dan Allah ki yafe ni sister Aisha"
"Ba komai, ya wuce. Sai ki kiyaye gaba, ki dinga taka tsantsan da mutane, dan abu ɗaya za ka ce ace ka faɗi goma. Ita kuma Halima Baballe gobe sai na ci ubanta tunda haɗi ta ke son yi tsakanin mu"
"Kin yafe min?" Ta tambaya kamar za ta yi kuka
"Wallahi na yafe mi ki, nima ki yafe ni" Farida ta faɗa tana ƙara kwanciya akan gado...
............................
Washe gari ko office ba ta shiga ba ta biya office ɗin su Halima ta je ta ma ta wankin babban bargo, a yadda ta tsara ma ko rabi ba ta ma ta ba saboda har lokacin ba ta warke be. Sai da ta gama silleta sannan ta wuce office ɗin ta. Tana zuwa ta samu Sir Najeeb ya zo sai dai ko da ta shiga bai ma ta magana ba kan latti da ta yi ba. Ta lura tun jiya da ya zo ya ke wani shiru-shiru kamar akwai abinda ke damun sa. Sai dai ta ja bakinta dan kar ya sauke matsalar sa akan ta.
Yau Jumu'ah kuma yau ne za a kawo lefen Maijiddah da yamma. Da ke ranan Jumu'ah ana tashi ƙarfe uku ne maimakon huɗu da aka saba shiyasa ta ke ganin za ayi komai da ita.
Da murnan ta ta shigo kamfanin, yanzu kam ba kasafai su ke zuwa tareda Yakubu ba.
Tun daga shigowarta ake ma ta wani kallo ana ƙus-ƙus sai dai ba abinda ya dameta tunda ba akan kowa ta ke ba. Lifter ta shiga ya kaita hawa na uku.
Abin mamaki sai ta ga Anas da Yakubu suna magana a office ɗin ta, ga Khalidah a gefe tana yamutse-yamutsen fiska.
"Sannun ku dai. Lafiya na ga wajen ya ɗau hayaƙi, Ya Anas me ke faruwa?"
Kallon tsana ya ma ta ya ce " na ɗauke ki a matsayin ƙanwata ashe kallon da ki ke min kenan?. Farida ashe za ki iya jefanmu da wannan mummunan ƙazafi. A dalilin me?
You know what? kafin ma Najeeb ya koreki ni na koreki, ba ma buƙatar mai hali irin na ki a wannan kamfani" ya shige office ɗin Sir Najeeb cikin fushi.
Mamaki, fargaba da tsoro ya cikata. Cikin rashin fahimtar kalaman Anas ta ce " Yakubu mi ya faru? Mi na yi?".....
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Free page*
0️⃣1️⃣2️⃣
"Asirin ki ya tonu, Munafuka 'yar matsiyata. Yau dai dole ki bar aiki anan tunda an koreki" Khalidah ta faɗa tana murmushi.
"Yakubu mi ya ke faruwa ne, mi na yi da har Ya Anas ke faɗin maganganu marasa daɗin ji haka?"
Anas ya miƙa ma ta wayar sa ya ce "ki kunna ki saurara"
Ta amsa wayar ta kunna recording ɗin ta fara ji.
Muryar mace ce ke magana tana faɗin
*"kinga Oga Najeeb ɗin nan, babban ɗan luwaɗi ne. Kin san a ƙasar waje ya taso, so ya jima da zama gay, shi ya sa ma ya ƙi aure har yanzu. Ance fa ya kusa kaiwa 40yrs amma ba aure. Hmmm wani abin al'ajabi da na gano shi ne.... Amma kar ki faɗawa kowa fa, Halima. Oga Najeeb da Anas su na neman junan su, a yadda na jiyo ma, wai sun yi aure a sirrance. A office su ke haɗuwa su ci amarcin su. Ni Farida da ki ke ganin nan na taɓa kallon su sunayi da ido na. Bakiga yadda Anas ke zama boyi-boyi ba a gaban Najeeb , ai saboda shi ne matar Najeeb kuma mijin. Shi Anas fa ba wai son shi ya ke ba kawai kuɗinsa ya sa ya amince. Kin san Anas ɗan maigadin gidan su Najeeb ne"*
"Innalillahi. Yakubu ba muryata ba ne wannan. Wallahi ba murya ta ba ce"
Farida ta faɗa kaman za ta yi kuka.
"Ki ji ƙarya. Lokacin da ki ke hiran da Halima Baballe duk ta yi recording komai dan ma kar ace ƙarya ta mi ki. Kuma kin ji da kunnen ki"
Farida ba ta ce komai ba ta fita daga office ɗin da sauri.
.........
Lokacin da Anas ya shiga office ɗin Najeeb kuwa samun shi yai tsaye jikin window.
"Abokina ka yi haƙuri dan Allah, ban taɓa sanin Farida za ta iya faɗin maganganu haka ba. I'm so dissappointed in her. Kar ka damu, dana koma office ɗina zan typing takardar korarta"
"No need" Najeeb ya faɗi a hankali
"Ban gane ba? Kana nufin ba za a koreta ba kenan?"
Najeeb ya juyo ya kalleshi ya ce " ba muryarta ba ne. Its a trick"
"How?"
" ba muryarta ba ne, ba kuma yadda ta ke magana ba kenan."
Anas yai shiru saboda kansa ya ɗaure. Najeeb ya sake playing ma sa recording ɗin wanda Khalidah ta tura ma sa da sassafiyar yau tun ma kafin ya zo office.
Sai da ya gama ji Najeeb ya ce "barin ba ka satar amsa. Miss Salihu ba ta kirana da *Oga Najeeb*"
"Shit. Kuma fa haka ne" Anas ya faɗi ya na buga goshin sa da taffin hannun sa.
"Kafin Miss Salihu ta fara aiki anan, i know her voice"
"Wallahi na tafka shirme Najeeb. Barin je na bata haƙuri"
..............
Farida na isa office ɗin su Halima ta samu tana tsaye da wasu tana mu su bayani kan recording ɗin da su ka ji. Farida na zuwa ta yaficota ta wanke ta da mari, kafin ta ankara ta ƙara ma ta na biyu. Kafin ka ce me sun kaure da kokawa...
Ruwan cikin Halima Farida ta zauna tana kirɓanta. Halima na ihu. Da ƙyar mazan da ke wajen su ka janye Farida da ga kan Haliman.
"Ku sake ni na ci uban shegiya annamimiya. Ku sake ni na watsar ma ta da haƙora shegiya Munafuka"
Halima ta samu ta tashi tana rufe hancinta wanda ke fidda jini jikinta na rawa.
Kici-kici ta ke tana ƙoƙarin ƙwacewa. Ana ba ta haƙuri amma ina sai masifa ta ke.
"Ku bar ni na nuna ma ta banbancin da ke tsakanin mu"
Tana ƙwacewa ta yi kan Halima da gudu. Ta ɗaga hannu za ta kai ma ta duka aka riƙe hannun. Ta fara ƙoƙarin yakice hannunta amma ta kasa saboda riƙon da aka ma ta. Ta yi ta yi still ta ka sa dan haka ta juyo
"Ka sake ni na dak......" ta tsaya lokacin da ta ga Sir Najeeb ne riƙe da hannunta. Sake hannun yai ya ce " Miss Salihu to my office"
Ta juyo ta kalli Halima ta ce " wallahi ba ta tsaya anan ba. Sai na je har gida na ci ubanki, shegiya dama halin munafurcin da ya hanaki zaman gidan miji kenan"
Yakubu ya ɗauko ma ta gyelen ta da ke yashe a ƙasa ya miƙa ma ta. Wafcewa ta yi da ƙarfi tace " kai kuma zamu haɗu a gida"
Wucewa ta yi ta bar wajen tana cigaba da zage-zage....
Kai tsaye office ɗin Sir Najeeb ta wuce ranta cike da masifa. Ta san ba makawa takardar kora zai ba ta sai dai wannan karan za ta karɓa za ta bar Najeeb constructions amma sai ta wanke sunan ta.
Kaman ba abinda ya faru haka ta ganshi yana zaune yana duba wa su takardu.
"Sir Najeeb, na san ka ji abinda aka ce na faɗa amma ka sani ba muryata ba ce wallahi, ba ni ba ne"
Ɗagowa yai ya kalleta ya ce " Miss Salihu, let it be the last time da za ki maida Kamfanina wajen faɗa"
"Sir Najeeb, wallahi a liƙa min sharri kam ba zan zauna haka ba. Kowaye sai na ci kutumar uban sa, hakan ma sai hukuma ta shiga tsakani. Haka kawai dan an sanni da yawar surutu sai a kwaikwayi muryata a faɗi abin da ban faɗa ba"
Kafe ta da ido yai yana gani tana banbami kaman za ta ci babu.
Miƙa ma ta file yai ya ce " take this file to Anas, kuma ki sanar da Admin na HR inada zama da su anjima"
Mamaki ya kamata. Ta haɗiye miyau ta ce " ba korata za ka yi ba?"
"Ki na so na kore ki ne?"
Ta yi saurin girgiza kai ta ce " ba ka ji recording ɗin nan ba ne"
" muryan ki ne?"
" wallahi ba ni bane" ta faɗa da sauri
"Good. Then get back to work"
Ta ɗau file ɗin ta ce " wani lokaci idan ka yi abu kaman Salihin mutum, Sir Najeeb"
"Miss Salihu!"
Ai da sauri ta bar gaban shi tana dariya.
...........
Zuwa ta yi ta ajiye file ɗin a table ɗin Anas ta juya za ta tafi saboda ba ta son ko haɗa ido da shi.
"Aisha dan Allah ki tsaya"
Ai dama jira ta ke yai magana ta fara masifa " Ya Anas dama zumuncin kenan, idan na yi laifi a tureni gefe kamar wata kayan wanki balle ma banyi laifi ba. Iya zama na da ku yau wata ɗaya da sati uku amma har ka ji a zuciyarka zan iya maka ƙazafi, ai ba zama mai kyau ake ba kenan..."
"Dan Allah ƙanwata ki yi haƙuri. I was blind by anger, maganganun sun girgizani sosai to the extend na ka sa ma tsayawa na lura cewa ba muryan ki bane. Im really sorry ƙanwata"
"Ba wani, kai dai tabarmar kunya kawai ka ke son naɗewa da hauka. Ni ka ma barni na faɗi abinda ke raina dan abinda zai sa na huce kenan"
"To faɗa ina jin ki"
Yadda yai maganar sai ta ɗan ji kunyar sa.
"Shikenan Ya Anas na haƙura amma tsakani da Allah na ji haushin abinda ka yi min"
"Dan Allah ki yi haƙuri my ƙanwa"...
Farida na komawa office ɗin ta ta ji saƙo ya shigo wayarta tana buɗewa ta ga numbar NJ, ta yi tsaki sannan ta buɗe saƙon
*bai kamata ki watsar da kan ki ta hanyar yin dambe da wacce ba ta kai ki daraja ba Aysherh, kin fi ƙarfin haka. Ko kin manta ke matar aure ce ..... N J*
"Mtsww, wannan NJ ɗin ma wallahi sai na binciko shi a wannan kamfani, mutum sai shegen na ci, kai ba za ka kira ba idan kuma an kira ba zai shiga ba" ... ta ajiye wayar ta cigaba da aikin da ta ke.
..............
Turo ƙofar aka yi da ƙarfi. Najeeb ya ɗago ido da sauri don ganin wannan mai karambanin. Farida ma da ke jera wasu files a shelf ɗin Najeeb ta juyo da sauri.
"Najeeb wanni walaƙancin ne wannan? Ga wacce ta ma ka sharri amma ba ka ɗau mataki a kanta ba sai Halima. Ka manta Wannan Jakar har dukan Halima ta yi. You're supposed to sack her"
" ina ganin ba ki shiga office ɗin ki ba har yanzu. Go back to your office akwai saƙo da na sa aka ajiye mi ki"
"Najeeb i'm serious bai kamata ka kori Halima ba she didnt deserve it"
Ko kallonta bai yi ba ya ce " ki je office ɗin ki ki duba saƙona"
Ta juya a fusace ta bar office ɗin.
Farida ta fara dariya dan ta san saƙon, tunda ita ya ce ta typing suspension later ɗin Khalidan.
Ganin dariyan na ta ya ƙi ƙarewa ya sa ya daka ma ta tsawa.
"Miss Salihu!"
"Sorry Sir" ta faɗi tana ƙoƙarin gimtse dariyan...
Ta gama abinda ta ke amma ta fake dan tana son ganin reaction ɗin Khalidah idan ta dawo.
Ai kuwa sai ga Khalidan ta zo a rikice.
Ta cilla wa Najeeb takardar hannunta tana faɗin " Najeeb explain this"
" ba ki iya karatu ba ne ko me?"
"Najeeb one month suspension a kan me?"
Shiru yai bai kulata ba.
"Najeeb a wani dalilin za ka min haka"
Still Najeeb bai yi magana
"Najeeb magana fa na ke. I'm calling my Dad right now"
Tana ƙoƙarin kiran mahaifin na ta ta ji Najeeb yana magana.
"Alhaji Tukur na bawa 'yar ka Khalidah Siraj Tukur suspension na wata ɗaya, ko kana da ja akai?"
Saboda wayar a handsfree ta ke sai kawai Khalidah ta ji Babanta yana cewa "ba ni da ja My Engineer. Komai ka yi dai-dai ne"
Najeeb ya sa hannu ya katse kiran ko ɗagowa bai yi ba balle ya ga yadda Khalidah ta taƙune fiska.
"Shikechar inji wani almajirin mu. Asha hutun wata ɗaya lafiya ko, dama ance idan za ka gina ramin mugunta ka gina dai-dai kai" ta ƙarasa maganar tana dariya
Khalidah ta zo gaban Farida ta nunata da yatsa ta ce " sai na ga ƙarshen ki Farida, you'll see"
"Allah raka taki gona Anty Big"
Tsaki Khalidah ta ja sannan ta fice a office ɗin.
Tana cikin dariya Najeeb ya daka ma ta tsawa.
"Get out"
Simi-simi ta fita a office ɗin sa.
..............
An kawo lefen Maijiddah kuma ba ƙarya AbdulWahab ya kashe kuɗi wajen haɗa kayan nan. A wajen ƙarɓan kaya ma Farida ta ka sa ta tsare dan ganin komai ya tafi dai-dai.
Anty Hanne ƙiri-ƙiri ta nuna kishinta a fili saboda kayan da akaiwa Maijiddah ko rabinsa ba aiwa 'ya'yanta da aka aurar ba.
Baaba Sabuwa kam farin ciki fal ranta.
Ranan sunday da dare AbdulWahab ya zo yiwa Maijiddah sallama da ke ya zo weekend.
Farida ce ta tsarawa Maijiddan kwalliya ta kuma zaɓa ma ta kayan da za ta sa.
Falon Baffa Musa aka saukeshi. Wannan zuwan sa gidan kenan na biyu tun haɗuwar su.
Tareda Farida su ka zo bayan sun gaisa da shi sannan ta fita ta basu waje.
"Ina yini" ta faɗa a hankali dan ita har yanzu ta kasa sake jiki da shi.
"Lafiya gimbiya ta"...
Hiran na su yawanci shi ya ke maganar dan Maijiddah kam kunya ta hanata sakewa.
Ya ɗan taɓa abinda aka kawo ma sa sannan ya tashi akan zai tafi.
"Allah ya tsare hanya, ya kai ka gida lafiya. Ka gaida su Baby da Alizah"
"Amin tawan. Shikenan gimbiya ba wani ɗan abu da za ki bani"
"Abban Alizah mi ka ke so"
Ɗan matsowa yai kusa da ita ya riƙe hannunta ɗaya yana ɗan murzawa. Ya sa hannu ya saukar da gyalen da ta yane kan ta da shi sannan ya tufke ɗankwalin,
warware gashin da ta tufke yai sannan ya fara shafa gashin wanda ya zubo har tsakiyar bayanta ƙanshin man da ta shafa wanda ke fitar da ƙanshin mint leaf kaman kuma lemon grass. Ya kai hancinsa yana shaƙar ƙanshin.
Hannunta da ke trembling cikin na sa da kuma yadda bugun ƙirjinta ya ƙaro saboda closeness na su ya sa ya saita kan sa yai gyaran murya bayan ya miƙe tsaye sannan ya ce " Allah ya kaimu kwana ashirin da tara gimbiyata"....
....................
Yakubu ta sa ya ciro ma ta kuɗi bayan ta ga cikakken alert ɗin ta wannan karan Sir Najeeb bai cire komai ba.
Karfe goma saura kwata ta shiga falon Baffa dan bai jima da dawowa ba, sai da ta ba shi lokaci kafin nan ya ci abinci.
Ɗan gefe da shi ta zauna suna gaisawa.
"Baffana na kai na. Allah ya ja zamaninka ya ƙara ma ka lafiya amin"
"Amin 'yar Baffa"
Hannu biyu ta sa ta miƙa ma sa kuɗi. "Baffa a sa mana albarka"
" wannan bai yi yawa ba Farida"
"Baffa na so ya fi haka ma sai dai ka san mu mata sai a hankali, kuɗin na wa na sayo gwanjo da su kuma ban gama haɗa kan kuɗin ba"
"Allah ya miki albarka Farida" ta amsa da amin.
"Dubu hamsin yai yawa Farida, ba dai duka albashin na ki ki ka kawo ba?" Baffa ya faɗa lokacin da ya gama irga kuɗin.
"A'a Baffa"
Shiru ne ya biyo baya na minti biyu kafin ta ce " Baffa dama na ce tunda wannan shekaran ka yi bikin su Salima ga na Jiddah nan da wata ɗaya mi zai hana nawan a barshi wata shekaran kaga kafin nan ka tara wani abu"
" A'a Farida, idan na yi haka na ci amanar mahaifin ki. Duk cikin 'ya'ya na ba wadda ta wuce shekara ashirin na aurar da ita, Maijiddah ce ma har ta kai ishirin ɗin. Idan ba ƙaddara