Showing 84001 words to 87000 words out of 145203 words

Chapter 29 - SAKATARIYA TA COMPLETE

Azizat   

13 Jul 2024

25694

bada dama a kawo shawara. A wajen kashi saba'in sun ba da shawaran a sayar da 40% ɗin sauran kashi talatin ɗin kuma su ka bada shawaran a kan kada a siyar a bari su janye 11% ɗin su. Duk da kuwa kamfanin za ta shiga wani yanayi amma idan aka jure aka kuma bi matakai masu tsauri za a farfaɗo daga faɗuwan da kamfani za ta yi. Cikin wanda su ka ba da shawaran a bari su cire hannun jari har da Anas. Bayan Mrs Najeeb Jibo ta gama sauraron su sannan ta ce
"11+40?"
Kallon kallon aka farayi dan ba a gane me ta ke nufi ba. Ganin ba ta kuma cewa komai ba ya sa wani ya ce "its 51"

"Exactly 51" ta faɗa tana buga table.

"Taya 51% zai kasance shares ɗin wassu turawa, mun amince mu sallama mu su kamfani kenan?. Ta ya za mu bar wa wassu turawa kaso mafi tsoka cikin wannan kamfani, bayan shekaru bakwai kenan ku na yiwa wannan kamfani hidima ace kun kasa riƙeta har sai wassu baƙin haure sun zo sun mu ku jagoranci. Miji na baya nan hakan bai sa komai zai tsaya ba, dukkan mu mu na da hakki akan wannan kamfani. Maganar ma a saida mu su shares ba ta taso ba. We will fight, we will fight with everything we've got. Tsoro ba na mu ba ne, the moment mu ka sa tsoro to mun faɗi, we will all fight this together"

Gaba ɗaya wajen aka sa tafi.

Anas yai murmushi tareda ma ta thumbs up...

A hankali ta buɗe ƙofar office ɗin, office ɗin na nan yadda ta san shi. Ba wani chanji illa kawai mai office ɗin da baya nan. Ta ƙurawa kujeran sa ido tana ganin kaman Najeeb na zaune a wajen sai dai wannan karan maimakon yadda fiskan sa ke tsume koyaushe to yanzu murmushi ya ke ma ta.

"Sir Najeeb" ta faɗa a hankali.

"Aysherh" ta ga ya faɗa ma ta yana ma ta thumbs up.

"Farida" muryan Anas ya dawo da ita daga tunanin da ta ke.


Ta juyo tana kallon sa.
"Gaskiya kin yi ƙoƙari, sai dai da sauran aiki saboda jibi za su zo kuma ba mu shirya komai a kai ba"

"Ya Anas su zo ma na, su ɗin mala'ikun mutuwa ne da za mu ji tsoronsu?"

Anas ya girgiza kai.

"Wancan Mr Ogonnan ka sa a rubuta ma sa suspension na sati biyu. Ba ma son ɓata gari irin sa"

"Amma Farida ba kya ganin this is extreme".

Farida ta zauna akan kujera tana mai faɗin Bismillah a zuciyar ta.

"Lokacin da na ce ba zan karɓi aikin nan ba mi ka ce min?"

Anas yai ajiyar zuciya sannan ya ce "Shikenan Farida, zan yi yadda ki ka ce"

" na gode Yaya na" fita yai daga office ɗin yana mai fatan zuwan Farida zai yi gyara ne ba lalata lamura ba.


Ta san dole za a samu matsala dama, shi ya sa tun farko ta ce ma sa ba za ta yi ba, saboda za su samu matsala da shi. Za ta iya bada umurnin da bai ma sa ba yai magana. A lokacin ya ma ta alkawarin duk abinda ta ce zai bi matuƙar bawai a harkan zane-zane ba ne tunda ba ta da masaniya a kan wannan harka.

Tana juyi a kan kujeran tana tuna hiran su da Daddy shekaranjiya.

" 'ya ta, Anas ya faɗa min ba za ki kula da kamfanin Najeeb ba, mi ya sa?"

Ta sunkunyar da kai ta ce "Daddy, aikin ya min girma kuma ban da ilimi a wannan harka"

Murmushi yai ya ce " Kamar ba Aisha Mai Gwanjo ba"

Farida ta yi saurin ɗago ido ta kalle shi cike da mamaki

Ya cigaba "Aisha mai turare, Aisha mai takalma, Aisha mai jakukkuna, Aisha mai zoɓo roto one in town.... and the list goes on. Aisha Baffan ki ya gaya min yadda tun ki na yarinya ki ka fara siye da sayarwa. Ko ba ke ba ce kina shekara tara ki ka saro goruba da taura ki ka zo da shi hutu kano, Baffan ki ya hanaki sayar wa ki ka ce ai ba za ki yi asara ba sai dai ya siye ya biya ki kuɗin hajar ki"

Farida ta sunkuyar da kai tana ƙoƙarin rufe fiskar ta da gyale saboda kunya.

"Lokacin da Najdah ke shekara tara ba abinda ta sani sai sakalci. "Lets go for ice cream Dad" ko "are we going to Disney this summer?" " Dad i want a pink teddy not brown" yai murmushin yaƙe sannan ya cigaba.
"Allah ya ba ki baiwa Aisha ki gode ma sa bisa wannan ni'ima. Ba zan takura mi ki ba amma ni akaran kai na ina so ki jagoranci kamfanin Najeeb, Allah kuma zai taimake ki a kan hakan"...

"Allah ka taimake ni bisa wannan jagoranci, ka bani ikon sauke nauyin da ya rataya a kai na, ka ba ni ikon yin gaskiya da adalci, Amin" abinda ta faɗa kenan kafin ta fara buɗe tarin files da ke gabanta.

.............................


Ƙarfe biyar da rabi ta isa asibitin, bayan an tashi sai da ta tsaya su ka tattauna da Anas kafin ta taho.
Tana shigowa ta samu Najma da Najdah a ɗakin.

"Sannun Anty, barka da yammaci" ta faɗa tana ajiye jakarta a kan ƙaramin fridge da ke ɗakin.

" an samu abinda ake so ko? Shi ne yanzu ba za a iya zama da shi ba" Najma ta faɗa tana mata wani kallo.

"Big sis ai dama kukan munafurci ne, neman attention ta ke yi kuma ta samu shine ta guje shi. I cant believe wai Daddy ne ya ce ta zama CEO ko mi ta sani oho"
Ta rasa cikin yayar Najeeb da ƙanwar sa wanne cikin su ta fi tsanarta. Mom da Daddy du ka sun karɓeta hannu bibbiyu kuma ba su da girman kai amma Najma da Najdah kam sai a hankali, ƙiri-ƙiri su ka nuna ma ta ba sa yinta, ba kamar Najdan ma.


Farida ba ta ce ƙala ba, ta ƙarasa bakin gadon da Najeeb ya ke kwance kamar mai bacci. Ta manna ma sa kiss a goshin sa ta ce " My Champ, ka ga na jima ko? Aiki ne ya min yawa. Ka san sai yanzu na gane ba ƙaramin wahala ka ke sha ba a office ɗin nan. Da ni kullum gani na ke kana zaune kan kujera mai laushi ga AC ba ka da wata matsala, ashe abin ba sauƙi. Yau har irin zamanka na yi dan kawai na ba su tsoro, na nuna mu su cewa kana tareda ni. Kuma Wallahi sun tsorata. Ka san yanzu kai ni ne, ni ma kuma kai ne"

Najdah ta ja doguwar tsaki Najma kam ido da baki ta sake tana kallon ta. Ba su sha mamaki ba ma sai da ta ce "dan Allah tunda kun riga kun gaisa da shi ku bamu ware, miji da mata su na son keɓewa da junan su"

"Heeeee wonders shall never end, shegiya ke a suwa ki koremu a wajen ɗan uwan mu"

"Ni ɗin ce dai matar Najeeb"

Najdah ta kalli Najma ta ce " Big sis ki ji abinda ta ke faɗa fa, wai mu fita a ɗakin Big B"

Najma ta tashi ta ɗau jakar ta ta ce " ba laifin ta ba ne Najdah. Laifin Daddy ne da ya je ya kakaɓo wata 'yar ƙauye ya haɗata da Najeeb, har ta ke ganin matsayin ta yana dai-dai da namu"

Har su ka fita ko kallon su ba ta yi ba. Ba ta da lokacin su, idan fitina su ke nema su jira Najeeb ya warke su ga ikon Allah.
Ta zauna ta sa kanta a gefen sa ta na shafa hannun sa. Bai jima ba bacci ya ɗauketa a haka...


Da dare su Daddy su ka zo anan Mom ke ma ta sallama akan jibi za ta wuce za ta je Umurah ta yi wa Najeeb addu'a. Farida ta yi farin ciki da hakan tareda addu'an Allah ya kai ta lafiya ya dawo da ita lafiya.
Fitan su ke da wuya tana zaune ta zubawa Najeeb ido, ta kai hannu za ta kama hannun sa sai ta ga ya motsa yatsun sa biyu. Wani ihu ta ƙwalla tana kiran sunan Daddy.

"My champ da gaske kai ka motsa yatsun ka? Da gaske yatsun ka ne su ka motsa?"

Ganin ba wani reaction da ya sake yi ya sa ta fita da gudu tana kiran su Daddy.

Sun yi nisa da ɗakin dan sun kusa fita a asibitin kafin ta taro su.

"Daddy ku tsaya Sir Najeeb ya motsa yatsun sa yanzu" ta faɗa tana haki.

Daddy da Mom ɗin kowa sauri ya ke ya je ya ga shalelen ɗan na su.

Koda su ka zo ɗakin Najeeb yana nan dai yanda ya ke.
Kallon da Daddy ya ma ta ne ya sa ta san ba su yarda da maganarta ba

"Allah Wallahi Daddy ya motsa yatsun sa, Allah"

Tana maganan tana hawaye. Mom ta kamo hannun ta ta ce " Farida it's ok, addu'ar mu kullum shi ne ya tashi ɗin. You're just hallucinating ki kwantar da hankalin ki, Bi izni kun fa ya kun zai tashi nan ba da daɗewa ba" jin haka Farida ta tubure akan wallahi Najeeb ya motsa yatsar sa. Ƙarshe dole aka kira likita wanda ya zo ya sa aka kunna mu su video footage ɗin wajen. Dama babban amfani na sa cctv cam ɗin kenan saboda a dinga bibiyar shi ko da zai iya motsawa ko ya farfaɗo ba tareda wani na wajen ba.

Lokacin da su Daddy su ka gani su ka gan hakan ne ta faru Najeeb ya motsa yatsun sa, farin ciki su ka ji marar misaltuwa tareda ƙara samun hope akan Najeeb zai tashi.

"Daddy zai tashi, yana so ya tashi Daddy zan ajiye aikin nan kar ya tashi ba na kusa da shi" ta faɗa tana goge hawayen da ke zubo ma ta.

Daddy zaunar da ita yai yana ƙara ma ta nasiha akan tashin Najee. Ko ta na kusa da shi ko ba ta kusa zai tashi Insha Allah, kuma zai fi jin daɗi idan har ya tashi ya ga ta kula ma sa da Kamfanin sa.
Ranan su Daddy ba su bar asibitin ba sai wajen ƙarfe sha biyu na dare.
Farida kam bayan sallah da ta tashi ta yi ba abinda ya sa ta ɗauke idon ta akan Najeeb gaba ɗaya daren ranan ji ta yi kamar zai buɗe ido ya ma ta magana. Ka sa bacci ta yi saboda kar ya buɗe ido tana bacci...



..........................


Su uku ne su ka zo domin yin wannan yarjejeniya. A ɓangaren team ɗin Najeeb constructions kuwa su biyar ne Madam CEO tana tsakiyar su.

Dogon bayani Mr Smith yai wanda du ka bayanan sa kan yadda su za su fi samun riba ne ba komai ba. Da ya gama Mr Nokovic ya karɓa ya fara magana amma shi maganar da yai akan wai ba su yadda da shugabancin Farida ba ne.

Da su ka gama ta su bayanin Farida ta karɓa ta fara bayani.

" a duk bayanan ku abu biyu na fahimta. Na farko ba ku yadda na zama CEO ba na biyu kuma ku na son cire hannun jarin ku"

Mr Nokovic ya ce " mu na son ƙara siyan hannun jari ba wai cire hannun jari ba"

"Oh really, ashe har kun tsorata kenan. Ni abinda na gani a rubuce shi ne kuna son ƙara siyan hannun jari ko kuma ku cire hannun jarin ku. So ni na riga na yadda maganan siyan hannun jari yanzu batun hannun jari da za ku cire za mu yi magana akai. So nawa za ku siyar ma na"

Kallon-kallon su ka farayi suna mamakin yadda lokaci guda ta juya abun kan su.

"Ba ni da lokaci da yawa, kaman yadda ku ka sani ina da majinyaci a asibiti wanda ke buƙatar kulawata"

"Mrs Jibo (ya faɗi jibon kaman wani *Jaebo*) mun san halin da kamfanin nan ke ciki ba za ta iya siyan shares ɗin mu ba."

Farida ta yi murmushin yaƙe ta ce " waya gaya mu ku Kamfani ba ta da halin siya. Ni nan ni zan siya kunga abu ya dawo gida kenan. So mu fara cinikin $200,000,000 mi ku ka ce?"

"Mrs Jibo" Mr Smith ya kira kafin ya ƙara da wani abu Farida ta ce " $205,000,000 wannan fa?"

Shiru su ka yi dan ba su zo don su siyar da shares ɗin su ba dama burga da barazana ne kawai.

"Ku na cewa ba ku yadda na shugabanci wannan kamfani ba a wani dalilin? Saboda ina mace?"

Mr Vladimir wanda bai yi magana ba tun ɗazu ya ce "mun yarda ki shugabanci wannan kamfani a bisa sharaɗi ɗaya"

Farida ta ɗan gyara zama ta ce " wanni sharaɗi"

Mr Vladimir ya ci gaba da bayani " akwai bidding da za ayi a Abuja nan da sati huɗu. Manya-manyan kamfanoni za su shiga wannan bidding su submitting picth ɗin su saboda duk wanda ya ci contract ɗin, its worth billions. Sau ɗaya wannan kamfani ta taɓa winning contract mai tsada kamar haka, but wannan ya ma fi wanchan da aka yi a Lagos.
Mu na so ki yiwa wannan kamfani register ki kuma jagoranci wannan kamfani har ta winning wannan contract ɗin. Idan Najeeb constructions ta samu wannan project, mu mun amince za mu sayar mi ki 5% na shares na mu amma idan wannan kamfani ta shiga gasan nan ta faɗi to za ki sayar ma na da 10% na shares ɗin ki"


"Idan kuma na ƙi shiga gasar fa?"

"Za mu cire duka 11% shares na mu wanda ka iya kassara wannan kamfani saboda halin da ta ke ciki"

Tsawon minti biyu ba wanda ya sake magana. Sai murmushi turawan su ke ganin sun sa ka Farida a wani hali.

" Najeeb constructions za ta shiga wannan gasa kuma za ta ci Insha Allah"

Anas ya kalleta yana faɗin "Farida akwai matsala, ba za mu iya..."

" Ni Aisha Farida Mrs Najeeb Jibo, na amince za mu shiga wannan gasa kuma za mu ci da yardar Allah"

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0️⃣3️⃣4️⃣




***
Tana shiga office yana biyota.
"Farida kin san abinda ki ke faɗa kuwa, a halin da wannan kamfani ta ke ciki shine za ki samu cikin gasa. Do you have any idea irin manya-manyan kamfanin da za su shiga wannan gasa, ko da Najeeb yana nan chance ɗin winning is very low balle kuma baya nan"

"Ya Anas so ka ke na ƙasƙantar da mu a gaban yahudawan turawan nan?"

"A'a so na ke ki cire girman kai, ki ce ba za mu yi gasan ba. Idan sun cire shares na su ko Daddy za mu iya neman taimako a wajen sa"

"Ya Anas kenan, mutanen nan sun san mi su ke fa, ɗaurin goro su ka ma na. By all means so su ke mu faɗi, mu ji kunya. Ni ban shirya turmusa wannan kamfani a ƙasa ba"

Wannan karan a hankali yai maganar ya ce " kin zaɓi a shiga gasan nan mu faɗi, Najeeb ya rasa 10% na shares na shi?"

" wanda su ke zama wani abu a rayuwa mutane ne that are willing to take risk. Ya Anas i'm a risk taker, ba na kallon 10% da za mu iya loosing, abin da na ke kallo shi ne 5% ɗin nan, kuma sai mun samu Insha Allah"

"Farida please, ka da ki yi haka. Ka da ki jefa mu cikin wani hali da zai kawo mu ga dana sani. Idan Najeeb ya tashi ya tarar ya loosing 10% na shi saboda ke he will never forgive you"

"Tun lokacin da ka hango nasara wa kan ka, to nasara tana tareda kai. Ya Anas za mu shiga gasan nan"

"Ba zan amince ba Farida, ba zan bari 7yrs of hard work ya crumbling a sati huɗu ba. Zan yi magana da Daddy za mu samu wata mafutar"
Har ya juya zai fita ta kira sunan sa " Ya Anas"
Daga bakin ƙofan ya tsaya bai juyo ba.

"Daddy kullum cikin kashe kuɗi ya ke, ta ya zamu tuntuɓe shi da maganan maƙudan kuɗi haka. Ka san ko nawa ya ke kashewa a kowanni rana yanzu saboda Najeeb? Ka san ko nawa ya ke biya wa kowani kwana ɗaya da Najeeb ya ke yi a gadon asibiti. Da ceto rayuwan ɗan sa zai ji ko da ceto kamfanin ɗan sa?"

Anas bai yi magana ba ya fita daga office ɗin.
Ta jima a tsaye kafin daga baya ta je ta zauna, ba ta jima da zama ba Mrs Confort Masoyi sabuwar sakatariyar ta ta kawo ma ta wassu reports da za ta duba. (yeeeh mu ma muna da sakatariya😂)...

Ranan gaba ɗaya Anas avoiding ɗin ta yai. Ita kan ta ta san cinye gasan nan abu ne mai matuƙar wahala amma kuma ba za ta janye ba, ai ance sai an gwada akan san na ƙwarai.




............................


Tun kafin ta tashi Daddy ya kirata akan idan ta tashi daga kamfani ta zo ta sameshi a gida. Tunda su ka yi wayan ta san Anas ya mishi maganar gasa ne. Ta ƙudira a ranta idan Daddy ya ce ta haƙura da gasan za ta haƙura tareda kuma ajiye matsayin da ta ke yanzu.

Daga office maimakon ta wuce asibiti kaman yadda ta saba sai ta wuce gida. Tasallah ta samu a falo tana goge-goge ta tambayeta ko Daddy na gida ta ce ma ta yana nan. Kai tsaye sama ta haura ta wuce falon sa. Da sallama ta shiga falon ya amsa ma ta yana kora ruwa, da alama magani ya sha dan ga tulin magani a gaban sa.

Sai da ta gaishe shi sannan ta ma sa ya jiki. Ba ƙaramin zabgewa yai ba, to ba dole ba shalelen ɗan sa yana kwance a asibiti shi da mai mutuwa banbancin su kaɗan ne.

"Aisha ya aikin?" Ya katse shirun na su

"Alhamdulillah Daddy"

"Allah ya taya ki riƙo" ta amsa da amin.
"Ki na cin abinci kuwa? na ga kin rame"

"Ina ci tareda Sir Najeeb mu ke ci"

Daddy yai shiru bayan yai addu'an Allah ya bawa Najeeb lafiya.

"Aisha, Anas ya zo wajena ɗazu da rana kuma ya min wassu bayanai, na saurare shi kuma na fahimce shi. A wani ɓangaren kuma ke ma na fahimci inda ki ka dosa. Alhamdulillah dukkan ku manufar ku ɗaya ne, sai dai ra'ayin ku ne ya banbanta kan yadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login