Showing 108001 words to 111000 words out of 145203 words
rana ɗaya za a ɗaura mana aure da su Anas. You see Aysherh ki na da kyau kuma kin min abinda ba zan taɓa mantawa da ke a rayuwata ba. You'll always be my first wife amma kuma Sabreen will always be my first love"
Dariya Farida ta fara dan maganar Najeeb bai kama hankali ba kwata-kwata.
"Wasa ka ke yi Najeeb, kuma ba na son irin wasan nan, zuciyata za ta iya bugawa"
"I'm serious Aysherh. Na san Sabreen ta yi ba dai-dai ba a baya amma yanzu ta chanja. She loves me"
"Da Sabreen da soyayyar ta sun ci kutumar uban su. Wai Najeeb me ka ɗauke ni ne. Shashasha ko? Wallahi ba zan yadda ba. Yau ko mata uku za ka auro ka auro amma banda Sabreen. Wai tukunna kan ka ɗaya kuwa. Sabreen fa, Sabreen da ta gudu ana saura kwanaki a ɗaura mu ku aure, Sabreen da ta shiga harkan film tana sheƙa ayarta yadda ta ke so, Sabreen da kana kwance baka da lafiya ta shure ƙafa ta tafi ta barka wai za ta je ta yi film da Kwano Reeves ne ko Keanu Reeves ne ma..."
"I know, na san komai Aysherh but kin san soyayyar farko ba ta taɓa gushewa"
Hawaye fal a idon ta ta ce "ni tawa soyayyar fa? Duk son da na ke nuna ma ka a banza kenan, ba ka ɗauke shi a bakin komai ba ko?"
"Aysherh i have feelings for you amma kin san Sabreen..."
"Ya isa haka!" Ta daka ma sa tsawa.
"Ni ba zan zauna da kai ba matuƙar za ka auri Sabreen. Idan ma ba za ka iya zama dani ni ɗaya ba, ka nemi wata mana. Ko acikin cousins ɗinka ka aura amma banda Sabreen. Wallahi ba zan zauna da Sabreen ba"
"Aysherh please, na yafewa Sabreen ke ma ki yafe mata" ya faɗa yana kamo hannunta. Tureshi ta yi ta tashi ta je wajen closet ta fara haɗa kayan ta. Zan bar ma gidan ka, zan bar rayuwan ka, ka zauna da Sabreen ita kaɗai tunda matacciyar zuciya gareka"
"Kin san ina buƙatar ki, Kamfanina tana buƙatar ki. Please Aysher"
"Kai wanni irin mutum ne Najeeb. Ba ka sona, ba ka tausayina, ni dai kawai na zauna da kai saboda amfanin kamfani"
"Ba haka ba ne Aysherh please ki fahimceni"
Tsugunnawa ta yi a wajen tana kuka. Zuwa yai zai rarrasheta ta buge hannun sa ta ce ya bar wajen ta. Yana tsaye a gefe har ta gama kukan ta ta tashi ta shiga banɗaki ta jima a banɗakin dan aƙalla ta kai kusan minti talatin kafin ta fito. Direct gado ta je ta hau ta kwanta ta rufe dukkan jikin ta...
Yana jin kukan ta a ransa, he wants to tell her it was all a trick amma ya san halin ta, idan ya gaya ma ta komai za ta nuna rashin damuwa, hakanan kuma abinda ya shirya ba zai tafi dai-dai ba dan Sabreen za ta iya ganewa.
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0️⃣4️⃣4️⃣
Ba baccin daɗi Farida ta yi ba, bacci ne ta yi na wahala. Da huturun sanyi aka tashi da asubahin ranan. Da ƙyar ta tashi ta shiga banɗaki ta yi alwala. Sanda ta farka Najeeb ya fito kenan yana shirin fita masallaci.
Tana idar da sallah ta nemi wata ƙatuwar rigan sanyinta wanda aƙalla ya yi shekara shida da ta ke amfani da shi. Rigan sanyin doguwa ce mai hula, dan idan ta sa yana wuce gwiwanta. Ko lokacin tana Jos idan ana tsananin sanyi idan ta sa shi ta sa dogon wando da socks shikenan ta yi maganin sanyi. Tana son rigan saboda Ummi ce ta siya ma ta...
Daga sallaya gado ta koma, kan ta ke wani mugun sara ma ta, ga cikinta da ke ta kukan yunwa.
Ba bacci ne a idon ta ba, asali ma jiyan ba ta kwanta da wuri ba. Yadda cikinta ke juyawa ya sa ta tashi dan ta sha gestid ko za ta ji sauƙi duk da kuwa ta san ciwon cikin ba na magani ba ne na yunwa ne. Tana tsaye a wajen dressing mirror tana shan maganin Najeeb ya shigo.
Ta yi kaman ba ta ganshi ba, maimakon 10ml da za ta sha sai ta ƙara wani 10ml ya zamo 20ml, tana tsayen ma wani jiri-jiri ta ke ji.
Yana tsaye yana kallon ta. Har ta ajiye maganin ta je ta hau gado. Bai ce ma ta ƙala ba, zuwa yai ya buɗe fridge ya ɗauko apple guda biyu da su ka saura a ciki. Dama shi kam bayan ruwa to fruits kawai ya ke sawa a ciki.
Sai da ya zauna gefen ta sannan ya ce "Aysherh tashi ki ci apple, bai da ce ki sha magani ba tareda kin ci wani abu ba"
Shiru ta yi ba ta ce komai ba.
"Aysherh"
A harzuƙe ta tashi ta na masifa "ina ruwan ka da ni, na ce ina ruwan ka dani. Na ci abinci, ban ci ba, wannan ba matsalar ka ba ce"
Juyawa za ta yi ta kwanta ya ce "Aysherh amma rigan sanyin kin nan gwanjo ce ko? As in Okrika, fairly used cloth..."
"Eeh shi ne, gwanjo ne, amma ka san me? ta fi designer cardigans ɗin da ka ke sawa. Tunda shekara da shekaru tana min maganin sanyi"
"Oh really, kinga banbancin ki da Sabreen kenan. Sabreen ba za ta taɓa saka irin wannan kaya ba"
"Mugu, butulu, ka bi ka damu mutane da Sabreen Sabreen, daɗin abin ma karuwa ce. Karuwa mai lasisi ma. Idan ita ba ta sa gwanjo ni a ina sa gwanjon ka ganni ka ɓata min aure saboda ka aure ni. Ka ga gwanjo kuwa sun min rana"
Sake miƙa ma ta apples ɗin yai wannan karan ta wafce a hannun sa.
Sai da ya ga ta fara ci sannan ya ce " Sabreen ta tuba Aysherh. Kuma Allah Gafurun Rahimun ne zai gafarta ma ta"
"Allahu Akbar, Ashsheikh Najeeb Adam Jibo Rahimahullah. Aje dai a ƙarata da ragowar kafirai" fa faɗa tana hararar sa
"Yawwa Uwargida na, Aysherh mai gwanjo"
Dundu ta fara kai ma sa da apple ɗin a hannunta tanayi tana kuka, dayaga abin na yi ne ya tashi a gadon da sauri yana dariya...
...............................
Ƙarfe shaɗaya ta fito dan ta maida plates ɗin abinci kitchen. Sabreen ta gani da tawagarta a falo su na duba wassu jewelries.
"Aishah" Sabreen ta kira sunan ta.
Farida ba ta juya ba, ta dai tsaya.
Sabreen ta taso ta zo gaban ta riƙe da sarƙa. Ta kai hannu za ta gwada sarƙan a wuyan ta Farida ta buge hannun.
"Kar ki taɓa ni!" Ta faɗa da tsawa.
"I wanted to give it to you Ayshah, i mean no harm"
"I dont want anything from you, you whore" ta faɗa tana barin wajen.
Sabreen ta yi murmushi dan ta san kishi ke cin Faridah...
Daga kitchen ɗakin Mom ta wuce. Mom ɗin ma jewelry box ta buɗe tana ware jewelries da za ta bawa Najdah da wanda za ta bawa Farida.
Da sallama Farida ta shigo, ko gaisuwa babu ta tsugunna a gaban Mom ta ɗaura kan ta a cinyarta tana kuka.
"Miya faru?, Aishah talk to me, miya same ki?" Dan ta tsorata da yanayin ta.
"Mom dan Allah ki ce Najeeb kar ya auri Sabreen, Mom mutuwa zan yi idan ya aureta. Mom dan Allah"
Tana maganan tana kuka.
"Farida, Najeeb yana son ki. He loves you so much"
"Mom ƙarya ne baya sona, idan yana sona ba zai ce zai auri Sabreen ba. Mom yaushe ma ya samu lafiya da har zai yi zancen aure. Wallahi idan har ya aureta ba zan zauna da shi ba" ta sake fashewa da kuka
"Farida sai ki barwa wata mace mijin ki, mijin da ki ke tsananin so"
"Mom ba zan iyaba, mutuwa zan yi, Mom please ki ma sa magana"
Tausayin Faridan ne ya kamata. Tsoron ta kar garin neman gira a rasa ido. Ya sa ta yanke shawaran gaya ma ta gaskiya.
"Barin gaya mi ki abinda ke faruwa, amma ba na so ki nuna kin sani"
Farida ta girgiza kai tana share hawayen da ke shimfiɗe a fiskarta...
...........................
Bisa shawaran Mom ta fara attending class ɗin da Miss Jean ke yiwa Najdah. Ranan da ta zo kunya ne ta cika ta, da ƙyar ta iya ƙarasa class ɗin. Baturiyar matar nan ba kunya ba komai ta ke bubbuɗe mu su abubuwa, tun daga sizes na girman abun zuwa yadda su ke idan suna cikin aiki. Bayan an gama bayani aka koma kan su mata. Da Faridan da Najdan dukkan su ashe shatara su ke cikon ishirin. Sun Jahilci abubuwa dayawa gameda jikin su da kuma yadda za su sarrafa mazajen su saboda kar a samu matsala...
A ranan lecture na biyu Jean ta fara nuna mu su different sex positions. Farida ganin abun na wuce gona da iri ya sa ta tashi za ta fita, sai ga Sabreen ta shigo.
Ɗan dariya ta yi ta ce "you're still a virgin? You mean Noory never ..." sai ta sake kwashewa da dariya.
Haushi ya cikata har wuya, ba dan ta san gaskiya ba, da yanzu ba abinda zai hanata marin Sabreen.
"Dont be shy Ayshah. Na san kin fi Najdah buƙatar lectures ɗin nan. Domin sai kin yi da gaske kafin ki samu kan Noory idan mu ka yi aure"
Farida ta cize leɓen ƙasa tana huci. Sabreen zuwa ta yi ta gayawa Jean saƙo sannan ta fita. Sai da ta fita Farida ta koma ta zauna, duk da dai tana jin kunya haka ta daure tana ƙaruwa da bayanan Miss Jean...
Najeeb kan bai fahimci komai ba saboda Farida ba ta nuna ma sa ta san plan ɗin shi ba. Har yanzu ba ta sake mishi fiska, maganan kirki ba ta shiga tsakanin su...
Wasa-wasa ranaku su ka dinga tafiya har ya saura kwana huɗu ayi aure. Gidan na su ya fara cika da mutane. Da ke Najeeb ya cewa Sabreen baya son hayaniya shiyasa ba ta nuna zaƙewa kan wassu lamuran ba. Dama itama ta ce tanason auren ne a sirrance dan kasancewarta celebrity idan maganar auren ya fito fili za ayita cecekuce, tafiso ko da za ayi gulma to ya zama bayan auren ne...
Ba wassu 'yan uwa ba ne su ka zo daga ɓangaren Sabreen mahaifinta ma tun zuwan sa Walimar Najeeb da ya koma ciwon sa ya tashi, yana chan London ana kulawa da shi. Sabreen independent woman ne. Da 'yan uwa, ba 'yan uwa za ta yi aure ba abinda ya shafeta. Ƙanin Mahaifinta ne ya zo sai kuma yayan Mom da yayar Mahaifiyar Sabreen...
Daddy ya ce baya son hayaniya saboda albarkar aure ake so ba komai ba. Najdah ta so ayi dinner amma Daddy ya hana. Shi Daddy tun ciwon Najeeb yai wa kan sa karatun ta nitsu wajen almabazzaranci da kuɗi. Da da ne ba ƙaramin bidiri za ayi a bikin ba, dan ko lokacin auren Najma ansha shagali sosai...
Daddy bai san mi Najeeb ke shiryawa ba sai da ƙanin Baban Sabreen ya ma sa maganar sadakin Sabreen. Abun ya ɗaure ma sa kai, a take a wajen ya kira Najeeb.
Da Najeeb ya zo haƙuri ya bayar tareda nuna mu su cewa ya yi hakan ne saboda ya kowa wa Sabreen hankali.
Daddy ya rufe shi da faɗa yayinda Hajj Khalid Abu Nasir ya fahimci Najeeb ɗin. Tunda shi kan sa ya san lokacin da aka kashe maƙudan kuɗi wajen shirya bikin su amma Sabreen ta gudu ta bar su da abun kunya. Hakanan bai taɓa goyon bayan shiga film da Sabreen ta yi ba...
Ranan Jumu'ah bayan an yi sallar Jummu'a aka ɗaura auren *Architect Anas Ali Almustafah da Najdah Adam Jibo* biki ya samu halartar manya-manyan mutane...
Sabreen wani farin wedding dress ta saka wanda ta aje maƙudan kuɗi aka designing purposely saboda ita. Ta sha ado na dimond da gwalagwalai. Hakanan make-up artist da ta zo da ita Arfa ta rangwaɗa ma ta kwalliya, ba ƙarya ta yi kyau sosai.
Wanda su ka dawo daga wajen ɗaurin aure ne su ka fara labarin yadda taro yai taro. A wajen Mouna yayar mahaifiyar Sabreen ta ji aure ɗaya aka ɗaura, auren Najdah da Anas. Mamaki ya sa ta wuce ɗakin Sabreen wanda ke ta ɗaukan selfie cikin kayanta na aure kafin su zo su yi hoto da angonta...
Maganar da Mouna ta gaya ma ta ne ya sa jikinta ya fara rawa. Waya ta ɗauko da sauri ta kira uncle ɗin ta wanda ya ƙara jaddada ma ta auren Najdah kawai aka ɗaura ban da na ta. Wayar hannun ta ya suɓuce ta yi durƙushe a ƙasa kanta na ma ta wani nauyi, zuciyarta na cigaba da bugawa da ƙarfi-ƙarfi kaman wanda zai bulluƙo...
* ku wanke idon ku da kyau gobe za'ayi abubuwa*
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0️⃣4️⃣5️⃣
Duk yadda ta daure ma zuciyarta ta ka sa saboda wani ƙunci da ya cika ma ta zuciyar.
"Ahhhhhhhh" ta fashe da kuka
"Noory dont do this, dont do this to me plz" sunbatun da ta farayi kenan tanayi tana kuka.
"Mahlan yaa Sabreen, Mahlan binti" Mouna ta faɗa tana ɗan bubbuga bayan ta.
Lokaci guda ta yi wuff ta miƙe tsaye tareda tattare rigarta da ya baza waje ta fita da gudu, su Mouna su ka bi bayan ta...
Ɗakin Mom ta shiga ba ta nan dan haka ta sauko ƙasa da gudu tana kiran Noory.
A falon ƙasa ta yi kiciɓus da Najma. Najma cikin rashin sanin miya faru ta fara tambayan lafiya, Noory kawai ta iya furtawa.
Najma ta ce bayanan. Sabreen ta fita da gudu tana kiran Noory...
Yana wajen reception Najma ta kira shi akan ga Sabreen tana ta kuka tana neman sa. Ya san za ayi haka, hankalin sa kwance ya ce a bashi 30mins yana zuwa. Shi yadda ya tsara ma baya so ta gano shi har sai dare idan ya zo da niyyar zai ɗauki amarya. A yadda ya sharara ma ta ƙarya cewa yai shi zai zo ya ɗauketa su je gidan sa inda anan za su ci amarcin su. Ai raka amarya ƙauyenci ne, ita kuma Sabreen ba 'yar ƙauye ba ce...
Zuwa yanzu kusan kowa agidan ya san abinda ke faruwa. Sabreen tana zaune tana kuka, fiskar nan duk ya chaɓe, kwalliyar da aka wa idon duk ya zazzago sai idonta ya zama kaman wani horror.
Sai lallashinta ake, wanda ba su san mi Sabreen ta yiwa Najeeb ba su ka fara zagin Najeeb, wassu har cewa su ke ƙila ƙwaƙwalwarsa ce ta motsa tunda ance tun rashin lafiyan da yai ƙwaƙwalwarsa ba ta dawo dai-dai ba. Ka ji mutane fa...
Farida tun da sassafiya da su ka tashi ta fara wani tsumewa ita a dole yau za a mata kishiya. Da Najeeb ya ɗau wanka ya sha manyan kaya zai tafi ta ce ma sa "Allah ya taimaki angon Sabreen"
Yai dariya kawai ya fita. Kwanciyar ta ta yi, sai ƙarfe goma sha ɗaya ta tashi. Bayan ta yi wanka ta shirya sannan ta fito. Ƙasa ta sauka dan ta nemi abinci dan tsayawa sai Adama ko Tasallah sun kawo ma ta har ɗaki ba adalci ba ne dan ta san aiki ya sha mu su kai..
Bayan ta karya Mom ta kirata, da ta je kaya ne ta bata wanda za ta sa a yau ɗin, ta karɓa tana godiya...
Tana ɗaki ta idda sallar azahar kenan ta ji ihun Sabreen. Jin hayaniya ya fara yawa ya sa ta sauko dan kar ayi show ɗin ban da ita...
Ba ƙaramin cika aka yi a falon ba. Kowa da abinda ya ke cewa zuwa yanzu Sabreen ta dena ihun kuka. Hawaye ne kawai ke zuba a idon ta...
Har lokacin kayan da ya sa ya je ɗaurin auren ne a jikin sa amma babu malun-malun ɗin. Bai yi mamakin ganin yadda mutane su ka cika falon ba dan yasan mata da gulma. Najma da Mouna ne ke gefen Sabreen su na ƙara lallashinta.
"Ga Najeeb ɗin" Najma ta faɗa lokacin da ya shigo.
Zumɓur ta miƙe ta nufe shi.
"Noory why? Why?" Ta faɗa tana dafe ƙirjinta da ke ma ta zafi.
Ɗan murmushi yai sannan ya ce "Why? Sabreen ki na tambaya na Why?. The same why da ki ke tambaya shi na yi ta tambayan kai na 9yrs ago. We were inlove remember, we made so many promises. Sabreen why? Abinda na yi ta tambayar kai na kenan. It took years kafin na amince wa kai na cewa ni ko soyayyata ba komai ba ne a wajen ki. That being an actress ya fi ni muhimmanci a wajen ki. That having a role in a movie ya fi aure na a wajen ki, That the love we shared was fake, that everything about you is fake"
Sabreen ta tsugunna a ƙasa tana ƙara danne ƙirjinta saboda gani ta ke idan ta cire hannunta ƙirjin ne zai fito saboda yadda ya ke bugawa da ƙarfi.
"Kina ji kaman zuciyar ki za ta fashe ko? Thats exactly how i felt and even more, na tsani kowa na tsani komai, na zamo tamkar mahaukaci. Sai da na yi watanni bana cikin hayyacina Sabreen. Ba na iya bacci sai na sha magani ba na iya cin abincin kirki. Years went by and i couldnt love again, kyawawan mata, mata ma su matsayi da ƙasaita fiye da ke sun nemeni amma idona ya rufe, ba na kallon kowa sai ke. In those 8years da na yi ta yawo da dakon soyayyar ki not once ki ka waiwaiye ni, not even once Sabreen. You're busy creating your fake life, kin manta da ni gaba ɗaya. In 8yrs kin je an mi ki butt enlargement, kin je an miki plastic surgery an gyara miki wide lips ɗin ki, in 8yrs kin dating manya-manyan mutane guda uku, in 8yrs kin zubar da ciki that almost killed you because you nearly bled to death. In 8yrs kin renouncing addinin ki saboda kina son auren wani ƙaton kafiri. In 8yrs..."
"Noory stop, plz stop" Sabreen ta faɗa tana kuka tana riƙe ƙafar sa.
"Sabreen ban miki haka dan na punishing ɗin ki ba sai dan na nuna mi ki cewa rayuwar ki tana tafiya ne base on movie scripts and you need to wake up. A year ago da ki ka dawo kin ce kin ajiye film saboda ni, kin ce kina so ki zauna kusa da ni ki samu soyayyata a