Showing 93001 words to 96000 words out of 145203 words

Chapter 32 - SAKATARIYA TA COMPLETE

Azizat   

13 Jul 2024

25695

ce zai je yai magana da likita.

"Ya hanya" Anas ya katse shirun na su.

"Alhamdulillah mun je lafiya mun dawo lafiya. Sauro bai cize mu ba haka Cinnaka ba ta cize mu ba balle ayi tunanin mun wahala. Kuma dai girma ya faɗi"

"Farida dan Allah ki yi haƙuri. Na san ba ni da hujja akan abin da na aikata amma ki yi haƙuri ki yafe mun"

"Ya Anas a nan ka zo ka roƙe ni Allah Annabi akan na zama CEO amma mi ka yi bayan na zama CEO. Ka bauɗe min, ka ƙi goya min baya har ka na ganin gara ka bar aikin da zama na CEO ko?"

"Ba haka ba ne Farida, kawai dai ba na so kamfani ta shiga matsala ne"

"Da kyau, saboda ga Aisha Farida mai farar ƙafa ko?"

"Duk abinda ki ka ce i deserve it. Ban riƙe amanar abokina ba, i'm truly sorry"

"Ka san mi ake cewa namiji matsoraci? To Ya Anas kai matsoracin namiji ne kuma ragon namiji. Idan ba ka dena sa tsoro a lamurran ka ba to ba inda za ka je a rayuwa. Kuma ko a gidan ka za ka samu matsala. Kana ganin da ina da tsoro zan kai yadda na kai da Najeeb, ka san da ni matsoraciya ce da tun ranan da Najeeb ya koreni da na bar aiki a kamfani kenan. But i fight back, na nuna ma sa ni ba ƙwallo ba ne da zai dinga bugawa duk lokacin da ya ke so. Ka san miyasa Najeeb ya ka sa korata? Because he needs me. Najeeb na son mutum mai zafi, mutum da ba ya da tsoro ko kaɗan"

Ya ji haushin kiran sa rago da ta yi amma kuma gaskiya ta faɗa, sau tari ta inda su ke samun matsala da Najeeb kenan.

"Ki yi haƙuri dan Allah"

" na ji haushi kuma har yanzu ina jin haushin ka. Ka bani lokaci na huce tukunna"

"Ba komai, amma dan Allah ki yafe min"

"Na yafe"

Ba su sake wani maganan ba har Daddy ya dawo su ka tafi.


"My champ ka ga abokin ka ko, ka ganshi ko" ...

......................
Washe gari tana shigowa kamfani aka fara tafi, ana ma ta congratulations.
Duk wanɗanda su ke ma ta wani gani-gani to yanzu sun sha jinin jikin su. Madam Farida kamar yadda yanzu aka fi kiran ta ta zama Boss lady. Tundaga lokacin da ta ƙarɓi matsayin CEO kowa ya shiga taitayin sa saboda ita ma zafi gareta kamar Najeeb. Wani zubin ma gara Najeeb ɗin dan shi idan ya ma ka tsawa shi kenan amma wannan sai ta bika da baƙar magana wani lokacin idan ta yanko ma ka magana sai ka ji kamar ka kama kai ka rusa kuka.
Ga wanda ya bita sannu kuma tana da sauƙin kai...

Su Mr Vladimir bayan ya tabbata Farida ta leading team kuma anci gasa ba ƙaramin baƙin ciki su ka yi ba. Neman sulhu su ka fara yi dan kar su rasa 5% da au ka yi alƙawari amma kuma Farida ta ce bata san zance ba. Su su ka faɗi sharaɗi kuma dole su bi shi yadda ya ke. Haka dai ba tareda sun so ba su ma sa hannu a takardar da ke shaidar sun ba da 5% shares ɗin su a Najeeb. Ranan Farida sai da ta yi hawaye saboda hango farin cikin da ta yi a idon Najeeb idan ya farfaɗo ya ji abinda ta yi...


......................

Gidan AbdulWahab kam yanzu zaman lafiyan ba kamar da ba. Tunda Aneesa ta dawo Lagos da aiki sai komai ya chanja. Kullum cikin taƙalar Maijiddah ta ke yi, duk da ma yanzu Maijiddan ta dena tsoron ta kuma ta na ɗan maida ma ta magana amma still wassu lokutan shiru ta ke ma ta. Aksarin lokaci Maijiddah tana burin inama ace itama ta iya magana kaman Farida da za su dai-dai ta tsakanin ta da Aneesa.

Haka kawai ta hana yaran shiga harkan ta, duk da yaran na so amma abinka da uwa da ɗa sai ya zamana ta yi musu tsawa shikenan. Ɗan gara ma Alizah wani lokacin tana ƙin bin umurnin Maman na su.

AbdulWahab na iya ƙoƙarin yin adalci tsakanin su duk da ma yanzu Maijiddah ta fara ganin chanji a tattare da shi lokacin da Aneesa ta dawo. Tana renon cikin ta lafiya amma wani lokacin gani ta ke tunda Aneesa ta dawo kaman yanzu AbdulWahab ya rage ba ta kulawa da kuma ɗokin cikin da ta ke ɗauke da shi.
Cikin ta na wata bakwai Aneesa ta fara laulayin ciki. Ta gano hakan ne ranan su na zaune suna cin abinci ta fita da gudu tana amai a banɗakin da ke guest room.
Daga baya kuma Aneesan ta fara tsirface-tsirfacen abubuwa irin na ma su ciki.

Lokaci guda hankalin AbdulWahab ya koma kan Aneesa. Ranan su na cin abinci da ke Maijiddan ne ta yi girki, Aneesa ta fara kushe abincin akan an hana ta yawan cin mai a asibiti kuma ga shi abincin Maijiddan ya cika mai.

"Sweetheart ba ka gaya ma ta abinda likita ya ce ba ne?" Ta faɗa tana kallon Maijiddah.


"Anny zan gaya ma ta ba yanzu ba akwai yara a nan"

"Na san ba za ka iya gaya ma ta ba. To Malama Maijiddah ciki ne da ni kamar yadda ki ka sani, kuma likita ya ce saboda mahaifata tana da rauni na guji aikin wahala da yawan stress na kuma rage cin wassu abubuwa saboda kar cikin ya zube. Sai ki kiyaye nan gaba"


Maijiddah ta buɗe baki da hanci tana ganin wannan cin fuskan. Ƙarin haushin ma AbdulWahab bai yi magana ba.
Ajiye cokali ta yi ta bar wajen. Da ya ke kwanan ta ne AbdulWahab da ya zo sai ya ke ƙara gaya ma ta report ɗin da likita ya ce gameda cikin Aneesa.

Haushi ya kawo ma ta har wuya, ka sa shiru ta yi ta ce "amma Abban Alizah ni ma fa ciki gare ni kuma ko da babu likitan da ya gindayamin sharaɗi, dai a matsayin da na ke yanzu ina buƙatar kulawa ta musamman"

"Hauwerh dont get me wrong please, ba wai ina nufin ke baki buƙatar kulawa ba ne..."

"Sai yanzu na gane gaskiya. Dama saboda matar ka ba ta nan ka auro ni, to yanzu ta dawo ban da matsayi ko?"

"Shhhhh, kar ki sake faɗin haka Hauwerh ki na da matsayi babba a rayuwata"

" a rayuwar ka haka ne amma a zuciyar ka Anny ce kaɗai"

Kamo hannun ta yai ta wafce hannun.

"Plz Gimbiyata, ki yi haƙuri. Ki na da matsayi a zuciyata da rayuwata gaba ɗaya"

Ranan dai AbdulWahab da ƙyar ya shawo kan amaryar sa...

.....................


Ko mi zai ma ta ba za ta koma Lagos ba. Gara ya dinga zuwa yana dubata duk ƙarshen wata. Ta bar mu su waje su sakata su wala yadda su ke so. Sai da motar su ta ɗau hanya sannan ta jingina kanta da seat tana hawaye. Babbar motar Macapolo ta shiga da zai je Kano daga Lagos. Duk da kasancewa dare ne hakan bai sa ta ji wani fargaba ba. Su na tafiya tana tuno maganganun AbdulWahab...


Sai da su ka dawo daga asibiti sannan ya je ɗakin Maijiddah dan ya bata haƙuri tsawan da ya ma ta ɗazu. Ya sani sarai bai kyauta ma ta ba. Duk abinda ya faru bai kamata ya gaya ma ta magana haka ba.
Wayam ɗakin ba kowa. Ya duba ko ina ba ta nan. Mai aikin su dama ba ta nan ta yi tafiya. Fita yai ya je ya samu mai gadi inda ya sanar ma sa Maijiddah ta fita. Faɗa ya fara ma sa akan miyasa zai barta ta fita ita ɗaya da tsohon ciki. Maigadi ya ce shi ya je ya samo ma ta taxi ma domin kuka ta ke yi ta ce an musu rasuwa ne za ta je gida kuma kai ka ce ta tafi saboda kun fita da Madam Babba.
Tsaki yai ya koma ciki. Ya kira numbarta sau ba adadi amma a kashe. Ba dai Maijiddah gida ta tafi ba.
Aneesa na kwance sai nishi ta ke ita a dole ta yi ɓarin ciki kuma kishiyar ta ce sanadi. AbdulWahab ya shiga tashin hankali sosai ina ya san zai nemi Maijiddah da daren nan...

Washe gari da safe ya samu labarin ta shiga mota ta tafi Kano. Kiran Hajiyar sa yai dan ya ji ko ta iso sai ya ga Hajiya ba ta ma sa maganar ba sai ma tambayar sa da ta ke ina Maijiddah. Sai alokacin ya waske da cewa ai tana hanyan Kano ma yanzu.

"Ko kai fa amma ka ce wai ta zauna a chan ta haihu"

Dama Hajiya Yelwa ta nemi ya bar Maijiddah ta haihu a kano ya ƙi shiyasa ba ta kawo komai aran ta ba.

Ƙarfe goma na safe su ka isa Kano inda direct gidan su mijinta ta wuce. Yanayin yadda Hajiya Yelwa ta ganta ya sa ta gane ba tafiyar jirgi ta yi ba.

"Lafiya Hauwa na ga kin kumbura, duba ƙafafuwan ki"

"Ba komai Hajiya zama ne kawai ya sa yai haka"

Hajiya Yelwa ta kira AbdulWahab tana ma sa faɗa akan barin Maijiddah da yai ta zo ita ɗaya sannan a mota ba a jirgi ba.

Hamdala yai lokacin da ya ji Maijiddah ta isa gida lafiya. Ya bawa Hajiya haƙuri akan ayyuka su ka ma sa yawa.

"Hajiyata ki ɗan bawa Hauwa wayar na kira numbar ta baya shiga ina ga wayan ya mutu ne"

Hajiya ta miƙawa Maijiddah wayar wanda ganin idon Hajia ya sa ta karɓa.

"Haba Hauwerh kin min adalci kenan, idan wani abu ya same ki fa."

"Na isa gida lafiya a gaida marar lafiya" ta kashe wayan saboda Hajia ta fita a ɗakin...


Kwanan ta na uku sai ga AbdulWahab. Tana zaune tana cin abinci a ɗakin Hajia sai ga shi ya shigo.
Ganin sa da ta yi sai da ta ɗan yi jim amma ta dake.
Zuwa yai ya zauna gefen ta ya kamo hannunta ɗaya ya ce "Gimbiya ta haka kike da zuciya dama. Haba dan Allah, kin san ina son ki kuma ba zan taɓa yin abinda zai ɓata miki dai ba"

"Amma ai ka yadda ai lokacin da matarka ta ce na tureta ta faɗi. Na yi sanadiyar rasa cikin ɗan Lele ko"

"Na san na yi kuskure Gimbiyata a min haƙuri"

Namiji dai da daɗin baki haka ya gama kwantar ma ta da hankali da kalamai ma su daɗi. Dole dai ta miƙa wuya ta haƙura ƙarshe ma ita ta koma tana bashi haƙurin kan tahowa da ta yi cikin dare ba tareda ya sani ba...
Washegari ya tafi dan ya san tunda ta riga ta zo sai ta haihu tunda dama tun farko Hajiya Yelwa ta nemi hakan...



.......................

Sati biyu da zuwan Maijiddah kano ta haifo santalelen ɗan ta mai kaman uban sa. Haihuwan nan ya sa Aneesa ta tada daru akan AbdulWahab dole ya bi ma ta hakki tunda Maijiddah ce ta yi sanadiyar zubewar cikin ta. Shi kam bai biye ma ta ba dan sai a lokacin yake ganin wautarsa ranan. Domin ya san Maijiddah ba ta da faɗa kuma yadda ta ke ɗan jin tsoron Aneesa haka kawai ba za ta tureta ba dan dai maganar fatar baki. Balle Maijiddah na da tsohon ciki ita kuma Aneesa cikin ma wata biyu ne.
Ana saura kwana biyu suna ya tattaro yaran sa su ka zo Kano. Aneesa kam Abuja ta wuce ta ce ba za ta je sunan ba...


Daga gidan suna ta wuce asibiti.

"My Champ ka ga babyn Maijiddah kuwa? Wallahi kyakykyawa da shi. Ka tashi muma mu yi abubuwa na samu ciki na haifi Baby mai kaman ka. Ka ji miji na"
Ta ƙara kissing hannun sa tana faɗin "sunan Babyn na su Muhammad Al'amin, nima My Champ ina son suna Muhammad. Sunan ɗan mu na farko kenan Insha Allah"...


Ƙarƙashin jagorancin Madam Farida Najeeb Constructions ta samu cigaba sosai kuma an samu gyararraki kan abubuwa dayawa.
Yau ma wassu baƙi ta ke meeting da su da su ka zo daga Kaduna.

Tana shiga office ɗin ta Anas ya shigo.
"Farida ba ki sa hannu a wannan takardan ba"
Ya miƙo ma ta wani takarda. Ta ƙarɓa ta yi signing sannan ta miƙa ma sa.

Tana zama sai ga kiran sakatariyar ta.

"Hello Madam, Mr Rayyan Abdullahi is here to see you should i send him in?"

"Rayyan Abdullahi?"...

Mi Rayyan zai zo yi wajen ta. Rabon ta dashi tun ranan da ya zo office ɗin ta Najeeb ya ma sa kora da hali...






*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣3️⃣8️⃣



"Faridah" muryan Rayyan ya doki kunnen ta. Ta ɗan ɗago ta kalleshi, kallonta ya ke yi mai cike da ma'anoni.
Da yatsar ta ta ma sa nuni da ya zauna ba tareda ta kalle shi ba. Har ya zauna bai ɗauke idon sa a kan ta ba. Ita kuwa tunda ta ɗago sau ɗaya ta maida kan ta ga takardun da ta ke dubawa.

"Farida" ya sake kira

Ta ɗago kai tana juya biron da ke tsakanin yatsunta biyu.
"Mr Rayyan what can i do for you?"

"Farida ni ɗin, ni ɗin ne Mr Rayyan" ya faɗa yana nuna kan sa.

" ok to Malam Rayyan mi zan iya ma ka"

"Lallai duniya!"

"As you can see aiki na ke yi. Idan ba ka da abin faɗi dan Allah ka ƙara gaba"

Jijjiga kai yai sannan ya ce "ya jikin Mijin ki?"

"Alhamdulillah da sauƙi"

"Stop pretending Farida, waye bai san halin da Najeeb ya ke ba a garin nan. He's being in coma for months now, ba alaman zai farfaɗo balle..."

"Balle me? Balle me?" Farida ta daka masa tsawa.

"Kwantar da hankalin ki Farida ba faɗa na zo ba. Ina so ki sani cewa har yanzu ina son ki kuma ina son auren ki. An sa aure na da mai sunan ki nan da 2 months. Amma na roƙi Umma ta bar ni na aure ki bayan na auri 'yar uwata Aishatu kuma ta amince. Kin ga by the time kin gama iddah sai mu maida auren mu"

"Ban san ka da shan giya ba Rayyan, ko dai ka fara ne bayan rabuwar mu?"

"Farida ke kan ki kin san har yanzu ina son ki..."

"Rayyan idan ba giyan wake ka sha ba ya kamata ƙwaƙwalwar ka ta gaya ma ka ni matar aure ce, ni matar Najeeb ce"

"Wanni Najeeb ɗin, Najeeb da ke chan kwance kamar gawa. How long has it being, kusan 8 months fa"

"Yes Rayyan. Yana chan kwance for 7months 9 days, kuma zan jira shi ko da zai ɗau shekaru kafin ya farfaɗo. I love him and i will wait for him till the end of my life. Get that into your thick skull Rayyan" ta faɗa tana miƙewa tsaye.

"Far..."


"Leave!" Ta daka ma sa tsawa

"Farida ki..."

"Get out! Ka fita na ce!" Yadda ta yi tsawan wannan karan sai da ya ɗan tsorata.

Ba tareda ya sake yunƙurin magana ba ya tashi ya fita.

Zama ta yi ta fashe da kuka. Miyasa kowa ke ganin Najeeb ba zai tashi ba, miyasa su ke ganin a haka zai ƙarasa rayuwar sa. Haka jiya da su ka yi waya da Ummi ta ke ce ma ta ance ba lalle Najeeb ya farfaɗo ba, ko za a raba auren su. Miyasa ita ba ta gaji da jiran sa ba amma su sun gaji. Akwai wanda ta farfaɗo daga coma bayan shekara ishirin, ko da Najeeb zai shekara ishirin a haka za ta jira shi. Balle ta san ya na chan ya missing ɗin ta yana ƙoƙarin dawowa gareta...

.....................

A gajiye ta shigo ɗakin na su saboda aikin abincin sadaka da su ka yi. Duk Jummu'a ita ke zama da su Adama su girka jollof rice da naman rago su sa a take away guda dubu a kai wa almajirai da mabuƙata. Kullum sun sa ana mu su sadakan kunu da ƙosai da Masa.
Mom ma ba a barta a baya ba wajen sadaka. Ranan su Adama su ka tayata fitar da kusan duka kayayyakin ta da ke closet, wassu kayan ma ba ta taɓa sakawa ba, ga su kaya ne ma su matuƙar tsada, ta sa aka rabar sadaka. Mutum goma ta biyawa Umurah da lokacin azumi. Shi Daddy kam ba irin sadakan da yai Allah ne kaɗai ya san adadin sa. Ba wai dama ba ya taimako ba ne, amma abinda ya faru ya sa ya ƙara buɗe hanyoyin taimakon al'umma...

A Desk ɗin sa da ya ke zama yai aiki idan yana ɗaki ta zauna. Wani brown envelope ta gani, ta jawo shi. Wayoyin Najeeb ne guda biyu a ciki. Sai yanzu ta tuna cewa ita ɗin ce ta saka a wajen ranan da Anas ya kawo ma ta. Anas ya sa an buɗe wayan domin a duba wassu saƙonni. Ko lokacin da za aje Bank da Court wajen authorizing signature ɗin ta ya zama bayan Najeeb da Anas har da na ta signature ɗin wajen sarrafa abubuwan Kamfani har da wayan nan aka je. Ta tuna sai da ta yi rantsuwa a kotu sannan aka gama haɗa komai, abin tausayin ma maimakon signature ɗin Najeeb dole thumb print na sa aka sa.
Ranan da Anas ya kawo wayan tunda ta ajiye su a kan table ɗin ba ta sake bin kan su ba.

Ta ɗauki babban wayan ta kunna. Hoton sa ne a screen ɗin duk da ma screen ɗin ya ɗan tsatstsage. Ta ƙurawa hoton sa ido, ta sa hannu tana shafa kyakykyawan fiskar sa. Ta shiga gallery tana kallon hotuna wanda yawanci hotunan zane-zane ne, sai wani folder wanda hotunan Najdah ne da hotunan sa wanda su ka ɗauka da Anas wassu kuma da Daddy. Allah sarki ya yi hoto da yawancin 'yan uwan sa amma ba hoton Mom ko guda ɗaya a wayan da ta gama ta koma kan text messages ta ga duk yawanci alerts ne sai saƙonni na ma'aikata ko clients.
Ɗaya wayan ta kunna, wannan kam da ta shiga gallery ɗin hotuna biyar kacal ta gani aciki. Hoton farko na Mom ne tana budurwa kaman ma ranan aure ne dan ta sha ado na gwalagwalai da dimond ga shi kayan da ta sa wani kaman bridal dress ne kalar pink. Sai ɗaya hoton kuma Mom ne da wani ɗan yaro a gaban cake. Ta zooming hoton sosai sai ta ga a jikin cake ɗin an rubuta *Najeeb is one*. Dariya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login