Showing 9001 words to 12000 words out of 145203 words
tsaya yaiwa mahaifiyar sa proper burial kaman yadda al'adar su ta tanada. I hope you understand that"
"Oh please Anas! Not this talk again"
"Ka na so, ba ka so, gaskiya ce dole na faɗa ma ka duk min ɗacin ta kuwa"
"Find another secretary for me Arch Anas Ali Almustafah"
Kallon-kallo su ka yiwa junan su kafin Anas ya fice daga office ɗin.
*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Free page*
0️⃣0️⃣4️⃣
Ranan Tuesday sai ga Joseph ya zo office, ya sani sarai Najeeb zai yi fushi da shi amma bai ɗauka abin zai kai ga kora ba. Infact, irin koran walaƙancin da Najeeb ya ma sa sai da yai dana sanin fara aiki da Najeeb. Tun farkon zuwan sa kamfanin ya samu labarin halin maigidan na sa a wajen sauran ma'aikata, sai dai bai ɗauka abin na sa ya kai yadda ake faɗi ba sai da ya gani muraratan.
Anas dai ba yadda ya iya ne amma ran sa ya sosu da abinda Najeeb yai wa Joseph.
"Sir, he gave me 3 days, only 3days. I left Kano on tuesday morning, i reached my village on wednesday. My mother was buried on saturday and i make sure i squeezed myself and came back to Kano on Monday night. But he wont listen"
Joseph ya faɗi yana goge hawaye. Shi takaicin sa ma bai wuci yadda Najeeb ya nuna halin ko in kula da mutuwar mahaifiyar sa ba.
Anas ya kalle shi ya ce "please dont take it personal, Najeeb doesnt even respect his own mother. I'm sorry about your loss Joseph, i lost my mother when i was only 7yrs so i know how you feel"
Kalaman Anas su suka kwantarwa Joseph hankali har ya ƙarɓi check ɗin da Anas ya bashi sannan ya tafi...
.....................
Ido Yakubu ya zaro lokacin da Anas ya gaya ma sa akwai vacancy na ɓangaren secretary ɗin Najeeb.
Indai kana aiki da Najeeb Constructions to dole ne ka san halin Najeeb balle kuma jiya-jiya Najeeb ya gama koran Joseph wanda harda kira ma sa security su fita da shi, ba dan Anas ya sa baki ba Allah kaɗai ya san halin da Joseph zai shiga.
"Kana tsoron kar a walaƙanta ƙanwarka ko?" Anas ya jefa ma sa tambaya
"Na ma ka alkawari zan yi ƙoƙari na ga ƙanwarka ba ta walaƙanta ba, za tai aiki da Najeeb na lokaci kaɗan ne ana samun wani vacancy ɗin zan chanja ma ta aiki"
Yakubu ya sauke ajiyar zuciya ya ce " Aikin Farida da Sir Najeeb ba mai yiwuwa bane, idan Farida ba ta ƙona shi ba to shi zai murɗe ma ta wuya ya kasheta. Ka san Farida kuwa? Ai Najeeb da Farida su ka haɗu anan kamfanin inaga ƙonewa kawai zai yi dan wuta da wuta ne"
Dariya Anas yai ya ce " har akwai yarinyar da za ta iya karawa da Najeeb? Gaskiya zan so ganin wannan Faridan"
"Hmm, na san halin Sir Najeeb na kuma san 'yar uwata Farida, amma wallahi duk inda Sir Najeeb ya kai da jin kai da miskilanci to Farida ta taka shi. Maganar ta zama Sakatariyar sa ma bai taso ba. Farida Farida Hmm..."
"Wallahi ni kuma da ka yi bayanin nan sai na ga sun dace gara a samu wacce za ta iya taka ma sa birki ko zamu huta da halin san nan"
"Allah akwai matsala idan Farida ta yi aiki da Sir Najeeb, yaƙi za'ayi fa a kamfanin nan"
"Kar ka damu mutumina, ka turo ta kawai na ma ta interview"
...........................
Ɓangaren turaruka ya nufa a Mall ɗin saboda favourite perfume na shi ya kusa ƙarewa. Kamar daga sama ya fara jin muryan ta, kamar ranan da ya fara ji yau ma masifa ta ke yi. Zuciyar sa ce ta raya ma sa ba ita bace amma kunnensa ya ƙaryata hakan, domin kuwa muryar sak da wadda ya ji ranan a restaurant. Yana so ya maida hankalinsa kan abinda ya ke dubawa amma kuma idanuwan sa na ƙwaɗayin gaskata abinda ya ke ji, shin yarinyar ranan ce? ko kuwa wata ce mai irin muryarta.
Kasa daurewa yai sai daya juya ya maida dubansa ga inda ya ke jiyo muryan. Ita ɗince dai, 'yar mitsilar yarinya mai shegen surutun nan. Ya kai duban sa ga wanda ta ke wa masifan ya ga ba saurayin ranan bane wani ne daban, haka kawai ya ji tsanar yarinyar dama ma su irin halinta kam ina za su iya kama kai.
He couldn't believe it, garin kallonta sai ga shi har turaren da ya ɗauka yana shirin faɗuwa daga hannunsa. Yai saurin taro turaren tareda sake murmushi saboda wautar da yai, garin gulma. Abin haushin ma ba wai ya san yarinyar bane amma kuma gashi halayyarta ya dameshi. Ya saurin kauda kan sa lokacin da su ka zo za su wuce shi, tana tafiya tana surutu, kafaɗarta ya ɗan gogi bayansa kaɗan, yai saurin juyowa ya bi bayanta da kallo amma she's too busy talking to even notice what happened.
"Lousy girl" ya faɗi a fili sannan ya ɗau turaren ya bar wajen...
"Ni wallahi da na san ɗan abinda za mu saya kenan da ban biyoka ba Yaya Faruƙ. Duk abinda mu ka ɗauka ka ce yai tsada. Dama ai abu mai kyau shi ake siya da tsada"
"Wallahi mijin ki ya shiga uku Farida, ke fa ki ka ce mu zo nan ba ni ba. In ba dan ke ba mi zai sa na zo siyayya a nan"
"Amma Yaya ai ba ka cemin ba ka da kuɗi ba ko!"
"Allah ya shiryeki dai"
Har su ka bar Mall ɗin ba ta dena complain ba, dama wasu kaya ne Yaya Faruƙ zai siya na bikin ƙannen sa. Ƙarshe dai daga Mall ɗin kasuwa su ka wuce...
......................
Ana zaune ana duba kayan da su Faridan su ka siyo Maijiddah ta shigo tsakar gidan da sallama, dawowarta kenan daga yiwa Hajiya Yelwa kitso. Kai tsaye ɗaki ta nufa bayan ta gaishe su.
"Ke Jiddah zo nan" Farida ta kirata.
Ba mu su ta dawo ta tsugunna gefen Faridan ta ce "gani Anty"
"Kina gani kowa yana duba kaya yana sa albarka ke za ki tsallake ki shige ciki"
"Lah Anty zan cire hijabi ne na wanke hannuna sai na fito"
Zainab ta ce " ba wani, baƙin ciki ta ke ba nata kayan bane"
Farida ta wurga mata wani awarwaro wanda ya doki hancinta maimakon bakinta da Faridan ta yi niyya.
"Zan ci Ubanki agidan nan, sa'arki ce da zaki dinga yaɓa ma ta magana son ran ki. Na ce sa'arki ce!" Ta daka ma ta tsawa.
Anty Hanne wanda ita ce ta biyu a matan Baffa Musa kuma Umman Zainab ta ce " Yo ba gaskiya ta faɗa ba. Anyi auren ƙannenta biyu yanzu za a sake wasu biyun. Ai abin kunya ne ace ko mashinshini ba ta da shi"
"Da kyau, dama Zainab ai daga nono ta sha. To barin gaya mu ku, tafi ƙarfin tayi baƙin ciki da bikin ƙannenta saboda duk cikin su ba wanda yake auren mijinta. Na ta mijin na nan zuwa, za ku ganshi handsome gentleman da shi"
Hajara ta ce " waya ga handsome mijin shortie" gaba ɗaya sai aka sa dariya banda 'yan ɗakin su Maijiddan wanda su ke tausayinta. Maijiddah ta fashe da kuka ta tashi za ta bar wajen Farida ta riƙe hannunta ta ce " ba inda za ki je. Ki tsaya ki kalli kowacce ido cikin ido ki maida mata martani daidai da ita"
"Anty Farida gaskiya su ka faɗa, na yi kwantai"
"Ji mim shirme, inba dan ke da su ɗin duk 'yan ƙauye bane dan kina 20yrs ba ki yi aure ba shine kin yi kwantai. Tukunnama ke za ki aurar da kan ki ne? Ko mijin ya zo kin ce bakya so"
Ta kalli Hajara da ke dariya ta ce " ke kuma fantsararriya, za ai aurenki at 16yrs ba abinda ki ke hangowa sai kwanciyar aure saboda abinda ki ka sani kenan. Gaya min me ki ka iya? Wacce sana'ar ki ka iya? Jakar banza kawai, yanzu haka wankar tsarki mai kyau ba ki iyaba, tun tasowar ki ke daƙiƙiya ce, shiyasa ko jarrabawar WAEC ma ki ka ce ba za ki rubuta ba. Har mijin da za ki aura abin alfahari ne, ina shi ma wani tunkuzan ne kamar ki, ba ilimin Arabi bare boko"
"A hakan dai auren za ta yi, ta fi wasu da maneman ma ba ta da su" Anty Hanne ta faɗi tana hararan Farida
"Wallahi Jiddah ta fi ƙarfin ta auri miji kaman Haladu, mi za tai da irin su Haladu ai shi kam sai jaka irin Hajara. Mijin Jiddah ɗan gayu kuma mai ilimi ne Insha Allah"
Tuni wajen ya kaure da hayaniya, Baaba Sabuwa dama tuni ta shige ɗaki saboda takaici, ita ɗin kanta ba daɗin ganin Maijiddah ta ke agidan ba. Anyi auren ƙanwarta Murja duk da kuwa tsakaninta da Murjan shekara ɗaya ne to yanzu ga Salima ma za ayi na ta amma ita shiru. Tana jin hayaniyar su amma ko leƙowa ba ta yi ba.
Farida kam duk ta inda aka ɓullo kare Maijiddah ta ke ta hanata tafiya kuma ta hanata kuka. Ƙarshe dai sai gajiya su ka yi su ka barta dan indai wajen ɗasa magana ne to Farida ta kere su...
Da dare da za su kwanta Farida ta sa Maijiddah a gaba da masifa.
"Ke sai ana magana ki fara kuka, ba dole su raina ki ba. Ai su na magana ki na magana, wanda ya gaji ya bari. Tukunna ma ke idan za ki fita sai ki dinga saka dogin hijabai kamar matan Malam, a haka kam ai ko mutum zai tsaida ke a hanya ma zai ɗauka ke matar aure ce ya fasa"
" Lah na saba ne ai"
"A wannan zafin, to kul, kisa ɗan dai-dai amma banda dogin nan, idan ba haka ba zan sa almakashi na rage mi ki tsayin su"
"Kai Anty"
"I'm serious"
Maijiddah ta sa dariya...
Washe gari da sassafe Farida ta shirya za ta bi Yakubu wajen aiki saboda interview da ya ce za a ma ta yau. Sai da za ta fito daga ɗaki taga Maijiddah na shiryawa itama da alama fitan za tai,
" 'Yan mata ina zuwa da sassafe haka"
" Hajiya Yelwa ce ta kirani wai dan Allah na zo na yiwa jikokinta kitso yau za su tafi"
"Ba za dai ki gyara ba ko"
"Mi na yi Anty?"
"Jiya mi na gaya mi ki?"
"Kayya Anty"
Farida ta je ta binciko ma ta wani hijabi cikin kayanta wanda bai da tsayi ta miƙa ma ta. "Sa ka wannan"
"Anty da kin barshi, skirt ɗin da na sa fa ya ɗan kama ni"
"Saka!"
Ba mu su ta amsa hijabin ta saka, da ke ita ɗin guntuwa ce ya kusa kai ma ta gwiwa.
Haka su ka jero su ka fito, ɗakin Baaba Sabuwa kawai su ka shiga su ka gaisheta sannan su ka fita...
..............................
A office ɗin su Yakubu ta zauna wanda shi da colleage ɗin sa Engr Mathew su ke sharing. Tun a office ɗin ta dinga sa Mathew dariya da surutunta. Ƙarfe tara da rabi Yakubu ya dawo office ɗin ya ce Farida ta biyoshi. Kai tsaye office ɗin Anas su ka je. Da sallama su ka shiga office ɗin lokacin Anas na duba wasu takardu. Ɗagowar da zai yi ya ga yarinyar ranan, ta ke murmushi ya suɓuce ma sa cikin ransa yana ayyana abubuwa dayawa.
"Bismillah zauna" ya faɗi yana nuna ma ta kujera.
Yakubu ya ce " sir ni zan wuce office"
" Ok Yaks"
Sai da Yakubu ya fita sannan ya kalli Farida ya ce " Aisha Farida Salihu right?"
"No" ta faɗi tana kallon cikin idon sa.
"No kuma, ba sunan ki kenan ba" ya faɗi da mamaki
"To yallaɓai ka ga takarduna ka ga sunan da ke jiki kuma sai ka sake tambaya"
"Hmmm. Well na ga takardun ki kuma ba laifi i'm impressed. Sai dai aikin da za ki yi babban aiki ne kuma aiki ne da sai kin yi haƙuri sosai"
"Rayuwar duniya kanta sai da hakuri, balle aiki a ƙarƙashin wani" ta amsa tana kallon laptop ɗin da ke gaban Anas
"Da alama dai Yaks bai yi ƙarya ba gameda yarinyar nan, tabbas za a sha kallo tsakaninta da Najeeb" abinda Anas ya faɗi a zuciyarsa kenan. A fili kuma ya ce
"Malama Aisha, kasancewa muna buƙatan Secretary da sauri so gobe za ki fara aiki. Kafin nan zamuje ki ga office ɗin ki sannan zan nuna mi ki yadda za ki dinga gudanar da ayyukan ki"
"Abin da sauri-sauri haka?" Ta tambaya
"Ko ba za ki iya ba ne?"
"Kana ganin Ogan ka zai iya korana ne? Dan ance mini abu ƙiris mutum zai yi ya koreshi"
" I see, ashe kinada labarin wanda za ki yi aiki a ƙarƙashinsa. Kin san ba ya ɗaukan raini, Malama Aisha"
Farida ta ɗan yi murmushi ta ce "ni kuma banda mutunci ba, ga rashin haƙuri kamar zawo"
Anas yai murmushi sannan ya miƙe ya ce " welcome to Najeeb constructions miss Aisha Farida"
"Thank you" ta faɗi tareda miƙewa itama...
Ta yi mamakin ganin girman wajen da aka nuna ma ta a matsayin office ɗinta, cikin ranta tana ayyana irin shagalin da za ta yi a wannan waje, ga ƙaramar fridge ga AC, kai aiki cikin jin daɗi haka.
"Ehmm, Ogan ki bai ƙaraso ba tukunna so zuwa gobe idan kin fito za ki ganshi. Ba sai an nuna mi ki shi ba kina ganin sa za ki ganeshi" maganar Anas ya dawo da ita daga tunanin da takeyi.
"Ba matsala Sir Anas"
Anas ya ce " Kira ni da Anas ɗin kawai ai ke ƙanwar mu ce"
"Rufa min asiri, rashin kunyata ba ta kai nan ba. Kai fa sa'an Yaya Faruƙ ɗin mu ne"
"To kirani da Yaya kawai kinga dama ba ni da ƙanwa mace"
"Na gode Ya Anas"...
Ba su shiga office ɗin Najeeb ba haka su ka fito. Ya ƙara ma ta wasu bayanai gameda aikin, sannan ya ba ta takardar shaidar ɗaukanta aiki. Sai da ta biya office ɗin Yakubu sannan ta wuce gida.
Anas kuwa Farida na fita daga office ɗin sa ya ɗau waya ya kira Najeeb. A take ya sanar ma sa an samu sakatariya kuma gobe za ta fara aiki.
"she better be good" abinda Najeeb ya faɗa kenan.
Anas ya ce " ai mutumina sai ka ganta kawai. Wannan karan kai da chanja Secretary sai dai in ita ce ta ajiye aikin"...
Sai da Najeeb ya tsaya har Hajiya Mama ta gama ganin likita sannan ya maida ta gida. Da zai tafi kamar kullum sai da ta tsokale shi
"A dawo lafiya tuzuru"
"Ke fa tsohuwar nan kinada matsala" ya faɗi yana ɗan hararanta
"Matsala ta ɗaya ce, kai aure ka ajiye iyali kamar kowa. Ko sai ka gama tsohewa kafin kai auren"
"Ke zan aura ai, zan ɗau ragowar Alhaji Mustafah"
"Allah ya jiƙan rai, ai shi bai fi rabin shekarunka ba ya ajiyeni a gidan sa"
"Tsohuwa na tafi, kar ki riƙeni da surutu"
"Allah ya bada sa'a tuzuru"
Girgiza kai kawai yai sannan ya fice daga falon. Idan da sabo ya saba da tsokalar kakar ta sa, wanda da ita ya ke sakewa yai walwala kamar mahaifiyar sa. Kulawar da bai nunawa mahaifiyar sa ba a Hajiya Mama ya ke ba wa...
*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Free page*
0️⃣0️⃣5️⃣
Daga Najeeb constructions kai tsaye gida Farida ta wuce, ba ta samu Maijiddah a gida ba dan haka kaya ta chanja su ka wuce kasuwa da ƙanwar Maijiddan, amarya Salima. Da ke ita ɗin tafi Hajara mutunci shiyasa ta su ta ɗan zo ɗaya da Farida, duk da ba ta kai Maijiddah kirki ba inji Faridan.
Ɓangaren Maijiddah kuwa da ta je ta samu jikokin Hajiya Yelwa suna karyawa dan haka sai da ta jira su ka gama sannan ta mu su kitson, da ke ba wannan ne karan farko da ta ke mu su kitso ba, su na yi su na hira. Yawanci in sun zo hutu wajen Hajiya Yelwa to ita ke mu su kitso.
Ta tsantsara mu su kitso mai kyau harda adon beads. Dama ga yaran 'yan gayu da su. A Lagos su ke da zama ko hausan kirki ba sa ji. Maryam da su ke kira da Baby saboda sunan Hajiya Yelwa da ta ci 'yar shekara bakwai ce, sai ƙaramar Alizah 'yar shekara huɗu.
Maijiddah ta na zaune a ɗakin Hajiya Yelwa tana jiran ta, ta riga ta gama yiwa yaran kitso tun ɗazu amma Hajiyar ba ta nan, ta ce kuma ta jira ta har ta dawo.
Tana zaune kan carpet tana danna ƙaramar wayarta ƙirar Tecno wanda ya ji jiki ya tsufa. Tun wanda Yaya Faruƙ ya siya ma ta ne lokacin da ta yi sauka shekara huɗu da su ka wuce.
Ba ta ankara ba ta ji shigowar Alizah ɗakin da gudu. Ɗago idon da za ta yi ta ga ƙatuwar kyanwa ta yo kanta, ƙwalla ƙara ta yi ta hau gadon Hajiya Yelwa da sauri, ai kuwa kyanwar ma kawai sai ta hau gadon da alama kyanwar gudun Alizah ta ke. Maijiddah ba shiri ta dira a gadon ta nufi ƙofa da gudu. Ɗaga labulen da zai yi yai karo da ita, da ke guntuwa ce kanta ya tsaya ma sa iya ƙirjinsa. Ƙoƙarin tureshi ta ke ta wuce dai dai nan kyanwar ta shuri ƙafarta ta fice daga ɗakin. Laushin jikin kyanwar da ya taɓa ƙafarta ya sa Maijiddah ta yi suman tsaye a wajen.
Alizah ta fara cewa " Daddy, please catch the cat for me"
Bai saurari yarinyar ba, ya ɗauki Maijiddah cak yai kan gadon Hajiya Yelwa da ita. Miƙar da ita yai sosai sannan ya cire ma ta hijabi dan ta samu iska ya shigeta sosai, Ƙaramin fridge da ke ɗakin ya buɗe ya ɗau goran ruwa mai sanyi. Ya zuba ruwan a hannunsa ya shafa ma ta a goshinta da wuyanta amma still ba ta farfaɗoba. Ya sake yin haka a karo na biyu wanda yana shafa wuyanta da ruwan sanyin ta jaa dogon numfashi ta buɗe ido, ta fara ƙoƙarin tashi dan ta zauna, ya sa hannu ya tallafa ma ta tareda faɗin "relax"
Sai alokacin ta fara wuri-wuri da ido saboda ganin ba hijabi ajikinta ɗankwalin kanta ma ya zame.
"Duk a dalilin kyanwa ki ke son hallaka kan ki. Miye abin gudu a jikin kyanwa?"
Ba