Showing 51001 words to 54000 words out of 145203 words

Chapter 18 - SAKATARIYA TA COMPLETE

Azizat   

13 Jul 2024

25687

da ita wa Lukman da zimmar tana ƙarewa za su yi aure.

Kowa ya san Alhaji Ilyas Magaji dattijon arziƙi ne, haka nan ɗan sa Lukman shima saurayi ne da aka ma sa shaida mai kyau a ko ina.

Rana ba ta ƙarya Farida ta gama diploma, aka fara shirye-shiryen bikin ta da Lukman.

A Wase za'ayi auren dan haka sati ɗaya kafin ɗaurin aure Farida ta koma chan. Mutanen Kano da Dukku duk sun hallara a wannan biki. Ba wanda ya fi jin daɗi ma kamar Baffa Musa saboda shi bai so har ta kai harka ba tareda an aurar da ita ba. Shi Mutum ne da bai yarda da karatun mace a gidan su ba.

Anyi kamu, anyi walima komai ya tafi lafiya. Ranan Asabat aka ɗaura auren Lukman Ilyas Magaji da Aisha Farida Salihu. Bayan an ɗaura aure ana ɗan gaggaisawa cikin 'yan uwan Alhaji Magaji da su ka zo daga Kebbi, wani ya fara magana da Alhaji Magaji bayan ya tabbatar a kusa da Baffa Musa su ke kuma maganar ta su ba a hankali su ke ba.
"Allah ya jiƙan Khairat, yau da kun ma ta tarbiya kaman yadda ku ka yiwa Lukman da Lukman bai zama ɗan shege ba"

Alhaji Magaji ya haɗe rai yana hararan ɗan uwan na sa wanda su ke 'yan uba.

Cikin rashin fahimta Baffa Musa ya ce " ban gane ba Alhaji Magaji. Wani irin ɗan shege?"

"au ba ku san Lukman ɗan shege ba ne? Lallai! Ai Lukman jikan Alhaji Ilyas ne, wadda 'yar sa ta haifa ma sa shi shege. Ance ma saurayin na ta ma wani bayahuden bature ne" Alhaji Kamalu yai wa Baffa Musa bayani.

Lokaci guda Baffa Musa ya hau faɗa yana masifa, kafin ka ce me wajen ɗaurin aure ya hautsine. Alhaji Magaji ba abin da ya ke sai hawaye.

Lukman na wajen masallaci su na hotuna da abokan sa aka zo ma sa da wannan mummunan labarin. Da farko bai yarda ba sai da ya shiga masallacin ya ga Alhaji Magaji yana hawaye. Shi kuma Alhaji Kamalu yana ƙara zuba bayani kan yadda Alhaji Magaji ya sakalta 'yar sa Khairat har ya kaita ga karuwanci a ƙasar waje.
Lukman dai a take a wajen ya suma.


Amarya Farida tana cikin ƙawayen ta ana hira ana ma ta kwalliya. Sai tsokanarta su ke wai yanzu kam an ɗaura aure ta zama Mrs Lukman Ilyas Magaji.

Wajen ƙarfe sha biyu ta gota kaɗan labarin abinda ke faruwa ya iso mu su gida.

Wassu cikin 'yan uwan su mata su ka fashe da kuka ana ta kururuwa ciki har da Inna Tabawa.
Wannan hayaniya ya sa Farida da ƙawayen ta su ka fito daga ɗaki su na tambayar abin da ke faruwa.

"Wai ashe Lukman ɗan shege ne" wata ta faɗa da ƙarfi.

"Ɗan shege kuma?" Farida ta faɗa cikin rashin fahimta.

"Wallahi, ance uban sa ma kafiri ne. Yanzu haka su Baffa Musa sun ce sai ya sake ki dan ba za ki auri ɗan sheg..." ta tsaya da maganan lokacin da Farida ta yafuto ta tana dukan ta ta ko'ina.
Da ƙyar aka raba Farida da matar nan. Farida sai zage-zage ta ke tana faɗin ita ko Lukman ɗan Alade ne za ta aure shi.

Gidan biki fa sai ya zama tamkar gidan makoki. Zuwa ƙarfe tara na dare kafin su Baffa Musa su ka dawo kowa so ya ke ya ji mi ake ciki amma Bai yi magana ba cewa yai kawai a fara haɗa kayan lefen da aka kawo da duk wani abu da aka san daga gidan su Lukman aka kawo.

Farida ta yi kuka kamar idon ta zai zazzago. Zuwa tsakar dare zazzaɓi ya rufeta a inda ta ke zaune ta fara kakkarwa, ƙarshe ta faɗi ta suma...


A ɓangaren Lukman ma ko da ya farfaɗo sai da ya sake suma sau uku. Zuwa yamma da jikin sa ya ɗan warware su Baffa Musa su ka zo gadon sa da buƙatar ya rubutawa Farida takardar saki, tareda cewa sun mayar ma sa da sadakin sa yana wajen Alhaji Kamalu tunda Alhaji Magaji ya ƙi ƙarɓa.
Lukman bai ce mu su ƙala ba sai hawaye kawai da ya ke ta yi.

Washe garin da wannan al'amari ya faru Baffa ya karɓo takardar sakin Farida wanda har lokacin tana kwance a asibiti.

Duk da 'yan uwan Lukman ba su buƙaci kayan da aka kaiwa Farida ba amma Baffa Musa sai da ya sa aka mayar mu su.

Wasa-wasa sai da Farida ta yi sati biyu a kwance a asibiti kafin aka sallamota. Tun daga nan ta koma kamar ba ita ba, ba ta surutu balle hayaniya. Kano Baffa Musa ya so ta bishi a lokacin amma ta ƙi, ta koma wajen Ummin ta a Jos.

Bayan wata ɗaya da dawowanta Jos, Lukman ya zo ya ma ta sallama akan zai tafi Egypt ƙaro karatu. Ya ma ta fatan alkhairi tareda cewa har abada ba zai dena son ta ba. Duk yawan surutun Farida ranan ka sa cewa komai ta yi sai kuka.

"Aisha ina miki fatan alkhairi, ina kuma mi ki kwaɗayin ki cigaba da karatu, and above all" ya goge hawayen da ke shirin zubo ma sa.
"I want you to open your heart for someone else. I want you to always be happy no matter what"

Ta fi jin tausayin shi fiye da kan ta. Shekaru talatin da ɗaya ace rana tsaka kawai a sanar da kai kai ɗin ba ka da asali, kai ɗin ɗan shege ne.

"Greeneyes, yanzu duk alƙawurran mu, duk burikan mu sun tafi a banza kenan?. Yanzu duk yadda mu ke son junan mu ba za mu kasance tare ba?"

Ajiyar zuciya yai ya ce " za ki samu wanda ya fini Aisha. Kyau, ilimi, dukiya da wayewa za ki samu wanda ya fini su. Za ki samu wanda zai so ki fiye da yadda na ke son ki Aisha. You never know, sai ki ga idon sa ma yafi nawa kyau"

Farida ta ɗan yi dariya ta ce " green eyes babu mai irin wannan siffan fa"

(Ni kam na ce ba ki je Kano ba ne😁)

Wannan ne ƙarshen Farida da Lukman. Tun daga ranan ba ta sake ganin sa ba har yau.
(Amma ta ga mai siffofin da Lukman ya bayyana😁)

Lokacin da aka fara saida form ɗin HND ta siya ta koma makaranta.

Wannan kenan.

........................


Satin su ɗaya da dawowa daga Lagos aka aiko cewa sun winning bidding ɗin da su ka je, kuma an ba su dama su yi samfurin (modelling) wannan gine-gine da za a yi.

Wannan karon kam ta ga seriousness sosai a kamfanin, domin ko yaushe ana kan meeting yadda komai zai tafi dai-dai domin aiki ne da za su yi wa federal government kuma ba ƙaramin miliyoyi za su samu ba idan su ka yi aikin.

Wani lokacin Sir Najeeb a office ya ke kwana. Cikin kwana biyar har ramewa Farida ta ga Sir Najeeb ya yi. Yadda ta ga kowa na kaffa-kaffa da shi haka ya sa itama ta ke taka tsan-tsan da shi.


Yau monday aka shirya meeting a conference room na su, duk wani babban Engineer ko Architect da ke aiki a Najeeb constructions sai da ya hallara.

Bayan an playing mu su power point da ke ƙunshe da zannen da aka yi. Sannan Najeeb ya zo gaban wani table mai faɗi ya ce "Ladies and Gentlemen. Ga biggest project na mu na wannan shekara, project Alpha"

Lokacin da ya buɗe mayafin da aka rufe teburin da shi sai ga modelling ɗin ginin da za su yi. Har ta Farida da ba ta san komai akan aikin zane-zane da ƙere-ƙere ba sai da wannan modelling ya matuƙar burgeta.

Maganar Farida ta ranan ya tuno lokacin da ya ga Farida ta buɗe ido da baki tana ganin model ɗin.

Jawabin godiya ya fara bayan an gama kallo.

"Ina godiya wa team Alpha da su ka taimaka da bani ideas, wanda da su na yi amfani na fito da wannan zanen. Special thanks to Architect Anas, Architect Ifeanyi, Engineer Ɗayyabu, Engineer Mathew..." haka ya kira mutane goma da su ka yi aiki tare ya mu su godiya.

"Sir Najeeb ni ma a gode min, na yi ta aikin zirga-zirgan kai saƙo da ƙarɓo saƙo ai" muryan Farida ya ƙaraɗe hall ɗin. Nan aka fara dariya. Najeeb kam kallon " are you for real" yai wa Farida...


........

Tana shirin fita daga gida ta ji shigowar alert a wayan ta. Ta ɗauko wayan ta duba dan ta san ba ƙarshen wata ba ne. Dubawan da za ta yi sai ga alert ɗin miliyan biyu da ga VESTAC.Inc......



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0️⃣2️⃣0️⃣



Tana zuwa office ta samu ana ta shirye-shiryen baƙin da za su zo. Ba ta yi maganar kuɗi da kowa ba dan dama Yakubu ta ke son tambaya ko ya san kamfanin VESTAC. Kafin ta tafi Bank ta bi bahasin wannan uban kuɗi da ba ta san ko ɓatan kai yai ya shigo account ɗin ta ba.

Ba ta ga Sir Najeeb ba, ta san shima yana chan yana ta shirye-shirye.

Sai ƙarfe tara da rabi Najeeb ya zo office. Wankan yau ma daban ta ke, ta san yana da kyau kuma ya iya wanka ba ƙarya sai dai yau wani extraordinary kyau ya ma ta na daban.

Minti goma da shigan sa office Anas ya zo ya wuce a bircike, ko amsa gaisuwan Farida bai yi ba.

Maganar da yaiwa Najeeb ne ya sa Najeeb ya tashi a hargitse yana faɗin What!

"Najeeb takardun zanen ba sa nan and the model is..."

Najeeb bai saurari ƙarshen ba ya fita da gudu.
Farida na zaune tana cin aya ɗanya da ta siya jiya ta ga Najeeb ya fito da gudu. Kasancewar ance Aya na sa ƙarin ni'ima ya sa ta lazimci cinsa ko kuma ta yi kunun aya ta sha tunda ta kusa shiga daga ciki.

Shima Anas bin bayan sa yai da gudun.

Yana tsaye gaban table ɗin yana kallon yadda aka faffasa model ɗin da ya sha wahala wajen haɗawa, and box ɗin da aka ajiye takardun zanen, shi ma empty ba komai a ciki.

Yana tsaye yana huci idon sa ya kaɗa yai ja hannun sa ya fara kakkarwa. Leɓensa na ƙasa ya ciza da ƙarfi amma still bakinsa bai bar rawa ba.

"Na sa an duba camera footage ɗin amma kuma tun jiya da rana baya aiki. It seems kamar an tampering na shi ne"

"Who is the last person to enter this place?" Ya faɗa cikin muryarsa mai fidda amo.

Anas yai shiru dan bai san ta yadda zai fara ma sa bayani ba.

"Who?" Ya sake faɗa da ƙarfi.

"Ba na tunanin za ta yi haka, CCTV footage ya nuna ta shiga ta duba model ɗin har ta ɗau hoton su sai ta fita daga nan kuma bai sake aiki ba"

"Who?" Ya faɗa wannan karan a hankali.

"Farida, your secretary"

Juyowa yai a hankali yana huci, yadda Anas ya ganshi sai da ya tsorata.

"Najeeb i'm sure ba ita ta faffasa abun nan ba, there's explanation to this"


"Sir Najeeb baƙin sun iso" wani staff ya shigo ya faɗa.

Kawai sai Najeeb ya fashe da dariya, dariya sosai har da ƙyaƙyatawa.

"Najeeb fa za mu yi?"

Cikin dariya ya ce " ya za mu yi? Hhhhhhhh. Dude she won, she succeeded. Abinda ta ke so kenan dama, to make me look stupid. Ka san mi ta yi ranan? Na san ta gaya ma ka ma, but let me tell you again. This crazy bitch puts superglue on my seat, and ...and do you know what she said?"
Ya sake fashewa da dariya " she said *Tsuliyar CEO Najeeb Constructions a waje* the bitch dare say that to my face. Yanzu na san mi ta ke nufi, she wants me to be humiliated, to look stupid"

"Najeeb plz calm down" Anas ya faɗa yana ƙoƙarin dafa abokin na sa.

"Calm down?"

"Za mu nuna mu su 3-D powerpoint ɗin sannan mu ba su haƙuri akan modelling ɗin sai gobe, then kafin goben...."

"If you are stupid i'm not Anas, we've lost this contract"

Ya mangaje Anas ya fita a wajen. Wajen baƙin ya je aka gaggaisa sama-sama. Anas na wajen yana tunanin mi Najeeb zai yi.
Kawai sai ya ce baƙin su biyoshi. Su na zuwa ya nuna mu su modelling ɗin da aka ɓata.

"I'm sorry but a bitch secretary i hired did this"

Nan su ka fara masifa " this is unprofessional, Mr Jibo taya za ka bari mu zo tundaga Abuja only to see a destroyed work"

Anas ya shiga ba su haƙuri yana ƙoƙarin nuna mu su hoton zanen a Tab ɗin sa amma ba su saurare shi ba. "We are highly dissappointed in you Mr Jibo" babban cikin su ya faɗa sannan ya juya su ka tafi. Najeeb bai ce komai ba shi kuwa Anas bin bayan su yai yana ƙara ba su haƙuri amma ba su saurare shi ba...

Najeeb ya jima a ɗakin kafin ya fito, yadda ya ke tafiya kaɗai ka san yana cikin tsananin ɓacin rai.
Yana shiga office ɗin ta ya tadda Farida tana waya sai dariya ta ke.

Kallon tsana ya fara ma ta kafin daga baya ya nuna ta da ɗan yatsa " i will revenge Miss Salihu, bit by bit"
Tunda ta ga yadda ya shigo fiskarsa ba alamun wasa ko kaɗan ta yi saurin kashe waya tana sauraron mi zai ce dan ta ɗan tsorata da yanayin sa.

"Ni kuma mi na yi" ta faɗa lokacin da faɗi kalmar ɗaukan fan sa.

Ba a jima ba Anas ya shigo.

"Najeeb mutanen nan sun tafi, we lost the project"

Najeeb bai kulashi ba ya ma rigingina kansa jikin kujera yana kallon sama ya ɗan juyawa a jikin kujera a hankali.

"Najeeb lets investigate this issue. Ina da yaƙiƙin ba Farida ba ne ta yi wannan aiki"

"She did it" Najeeb ya faɗa a hankali.

Kafin Anas ya fito Yakubu ya zo office ɗin Farida yana ba ta labarin abinda ya faru. Farida ta dafe ƙirji tana faɗin " wayyo Allah, yanzu wahalan Sir Najeeb duk a banza"

"Farida mi ya sa ki ka shiga wajen nan?"

Ta ɗan rage murya ta ce " ba dai kana tunanin ni na yi wannan aika-aikan ba"

"Farida camera ya nuna ke ce ki ka shiga wajen nan na ƙarshe and ke yanzu ake zargi"

"Na shiga uku wata sabuwar sharrin da za a min kenan. Ni fa abin ne ya min kyaun na je na ɗau hoton sa. Ga ma hotunan a wayana" ta ƙarisa maganar tana ƙoƙarin buɗo hotunan a wayarta.

Anas ya fito ya same su, the same tambaya ya ma ta akan miya sa za ta shiga ɗakin nan, amsar da ta bawa Yakubu shi ta bawa Anas.
Anas ya girgiza kai ya ce " Farida akwai matsala fa, Najeeb yana zargin ki, kuma idan ba'a gano wanda yai wannan abin ba i'm sorry but abinda Najeeb zai iya mi ki ba zai tsaya a kora kaɗai ba"

"Wayyo ni Aisha, yanzu ba za a barni na rabu da Sir Najeeb lafiya ba"

Bayan sun bar office ɗin ta ta shiga office ɗin Najeeb, har lokacin yana zaune yana kallon sama.

"Sir Najeeb wallahi wallahi ban ruguza ma ka aikin ka ba, hoton abin kawai na ɗauka saboda ya birgeni" haka ta dinga zancen ta ita ɗaya ba tareda ya tanka ma ta ba, da ta gaji da kan ta ta fita daga office ɗin.

Wannan abu ya sa ta manta da batun miliyan biyu da ta gani a account ɗin ta da safe.

Zuwa rana duk Farida ta shiga damuwa, wannan ya shigo ya ma ta Allah wadai da halin ta wannan ya shigo yana son yi tsaigumi da gulma. Tun tana mu su masifa har ta gaji ta haƙura, idan mutum ya zo har ya tafi ba ta tanka ma sa. Ranan fa gaba ɗaya kamfanin ya rikice. Rashin samun wannan contract zai jawo mu su asara sannan sunan Kamfanin su zai samu mummunan shaida a gari da ƙasar ma gaba ɗaya.

Lokacin da aka tashi Farida da ƙyar ta tashi ta tafi bayan ta leƙa Sir Najeeb wanda har lokacin ke zaune a kujera.

"Sir na san inada rigima amma wallahi ba zan yi abinda na san zai janyo wa kamfanin ka asara ba, tunda na san dukkan mu nan muna ci a ƙarƙashin ka" abin da ta faɗa kenan lokacin da za ta fita.

Ko da ta je gida ka sa taɓuka abin kirki ta yi. Jira kawai ta ke Yakubu ya dawo ta ji mi ke faruwa. Sai dai Yakubu bai dawo ba har chan dare lokacin ita kuma ta yi bacci.

Washe gari da sanyin jiki ta shirya ta tafi wajen aiki.
Ta fara zuwa office ɗin Yakubu amma ba ya nan. Haka ta wuce office ɗin ta tana fargaban mi za ta tarar.

Tana zuwa ta leƙa office ɗin Sir Najeeb amma ba ya ciki. Ta koma na ta office ɗin ta yi jugum. Ƙarfe tara saura Anas ya shigo, fiskar sa ba yabo ba fallasa.

"Yaya na ya aka yi?"

"Akwai babban matsala Farida. Kina cikin matsala, za'ayi board meeting a kan ki anjima. A ina ki ka san kamfanin VESTAC Farida?"

"VESTAC kuma?"

"Account details ɗin ki ya nuna kamfanin sun turo mi ki kuɗi miliyan biyu jiya"

Sai lokacin ta tuno da maganar kuɗi.
"Yaya ni ban san su ba, jiya nima na ga alert, abinda ya faru jiya ne ma ya sa ban yi maganar ba"

"Farida.." shigowar Najeeb ya sa ya katse maganar ya tashi ya bi bayan Najeeb ɗin.


"Allah ga ni gareka ni 'yar marainiyar nan. Wanda ya nufeni da sharri ka mayar ma sa ya Allah. Ya Rabbil Alaamin ka ceceni" ta faɗa a fili

Ba a jima ba Najeeb da Anas su ka fito, daga baya kuma Yakubu ya zo ya kirata.
"Farida ki yi ta addu'a kawai" abinda ya iya faɗa ma ta kenan lokacin da su ka baro office ɗin na ta.

Da Bismillah ta shiga hall ɗin.

Su kusan tara ne ko goma a wajen kowa yana zaune Najeeb na tsakiyar su.
Nu na ma ta kujeran da ke tsakiyar wajen aka yi ta je ta zauna. Kowa ya zuba ma ta ido. Ba ma kaman Najeeb da ke ma ta kallon tsana.

"Miss Aisha Farida Salihu, bincike ya nuna ma na ke ki ka lalata modelling da aka yi, ki ka sa aka sace takardun zanen. Mi za ki ce gameda wannan?"

"Ni ba abinda na yi, kawai dan na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login