Showing 57001 words to 60000 words out of 145203 words

Chapter 20 - SAKATARIYA TA COMPLETE

Azizat   

13 Jul 2024

25706

goma sha ɗaya na dare lokacin ba ta fi 'yan mituna kaɗan da kwantawa ba kiran Rayyan ya tashe ta. Tana ɗauka ya ce ta fito waje yana ƙofan gidan su.

"My Ray lafiya ka zo da daddaren nan?"

"Ki fito Farida akwai saƙon da zan ba ki ne"

Maganar saƙo da ya ce sai ta ji zuciyar ta ya buga. Ta tashi ta sa hijabi ta fito.
Akwai wa su baƙi da ke kwance a barandar tsakar gidan su na hira, da ke ba su jima da tattara tsakar gidan ba.

"Amarya ina zuwa haka?"

"Ƙofar gida zan je an kawo min saƙo"

"Samarin zamani dai, angon ne ya ka sa hakuri haka"

Ita dai ba ta sauraresu ba ta fita.

Wajen motar sa ta je ya buɗe ta shiga.

"My Ray minene, hankalina ya mugun tashi fa"

Da ke dare ne ba iya kallon fiskarsa ta yi sosai ba balle ta ga yanayin sa.

"Farida ashe za ki iya cin amana ta"

Dum ta ji ƙirjin ta ya yi.

"Wallahi ban ɗauka za ki min haka ba"

"Na shiga uku ni Farida ba dai za a kuma ba. Rayyan mi na yi?"

"Ashe soyayya ku ke da Ogan ki. Ashe duk yadda ki ke zagin sa a gabana iya fatar baki ta tsaya"

"Rayyan dan Allah kar ka sa zuciyata ta buga yanzu. Idan ma wasa ka ke ka dena please "

"Da kan sa ya je gida ya ce wa Baba ke karuwarsa ce"

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun, Lahaula wala ƙuwwata illa billah. Sir Najeeb ne ya faɗi hakan?"


Miƙa ma ta wayarsa yai ya ce ga hotunan da ya kawo. Ina tunanin ma waɗannan lokacin da ku ka je Lagos tarene ku ka yi holewarku achan.
Ta amshi wayar ta fara kallon hotunan. Hoton farko tana zaune kan cinyar Najeeb ta sa hannayen ta a kafaɗun sa tana murmushi, ɗaya kuma suna tsaye ya rungumeta ta baya, lips ɗin sa a daidai wuyan ta. Ta swipping na gaba wanda tana kallo hawaye na ɗiga a jikin wayar. Suna rungume da juna bakinsu a haɗe kamar suna kissing.

"Ba ni bane, wallahi ba ni bane. Wannan sharri ne. Rayyan ka yarda da ni"

"Dama na zo na faɗa miki ne da kaina kafin gobe a zo gida a faɗa. Na fasa auren ki Farida, ina son ki amma ba zan iya auren ki ba. Najeeb yana da kyau yana da kuɗi, ko bayan mun yi aure idan ya neme ki za ki amince da shi. Ba zan iya aure da zargi a ciki ba"

Bakin ta ne ya fara rawa, tana so ta yi magana amma ko me ya taho zai fito sai ya maƙale a wuyan ta. *"Na fasa auren ki Farida"* shine maganar da ke ta maimaituwa a ƙwaƙwalwarta.

"Gobe za su zo su karɓi sadaki da lefe, sauran abubuwan na yafe. Na gode da Allah ya tona asirin ki kafin ma ayi auren, dama Umma ta sha faɗamin ba ta yarda da ke ba dan 'yan Jos ɗin nan yawancin ku 'yan iska ne"...

Ba ta san ya akayi ta buɗe ƙofa ba, ba ta san kuma ya akayi ta shiga gida ba. Zuwa ta yi ta zauna a bakin gado hawayen da ta ke yi ma ya tsaya. So take ta gane mafarki ta ke yi ko gaske ne. Bacci kam ranan ba bu shi a idon Farida.

Washe gari da safe aka tashi da shirye-shiryen walima. Farida ta kasa magana ta kasa faɗan abinda ya faru jiya, ita har lokacin gani ta ke mummunan mafarki ta yi jiya da dare.

Zuwa ƙarfe goma sai ga Baffa ya shigo yana faɗace-faɗace. Kiran Ummi da Nanna da Baaba Sabuwa yai zuwa falon sa. The next thing da akaji sai kukan Ummi. 'Yan gulma su ka yi falon da sauri Baffa musa ya fatattake su.

"Amina ki dena kuka, ni ban yarda da abin da su ka ce ba, kuma koma hakanne dole sai na aurar da 'ya ta gobe. Ba zai yiwu a fasa aurenta har sau biyu ba, sai duniya ta zageni. Ni nawa 'ya'yan ina aurar da su lafiya ita kuma da ta ke amana gareni ake samun matsala duk lokacin bikin ta"

Nanna da ita kaɗai ce ba ta fara kuka ba ta ce "yanzu wa za ta aura?"

"Yakubu, Yakubu zai aureta, ku cigaba da shirye-shirye Allah ya kaimu goben"...

Farida na ɗaki har lokacin tana zaune jugum, Maijiddah ta yi tambayar duniyar nan amma ba ta kulata ba.

Ummi ta shigo ɗakin tana hawaye. Zuwa ta yi ta tsugunna gaban Farida ta ce "faɗa min gaskiya Farida, akwai abinda ke tsakanin ki da Ogan ki?"

Farida ta kalli Ummi da rinannun idanuwan ta ta ce "da gaske ne ko? Da gaske Rayyan ya fasa aurena?. Ummi banida sa'a a rayuwa kenan? Ummi ina son na yi aure, ina son na samu gidan kai na, ina so na haihu na tara 'ya'ya, ina so na samu ladan biyayyar aure, ina so na cika miki burin ki Ummi. Ummi ko dai aure ba ya cikin ƙaddara ta ne?"

Ummi ka sa magana ta yi sai kuka.....

Zuwa ƙarfe shabiyu 'yan gidan su Rayyan su ka zo karɓan kaya. Daga wajen ma su ke cewa aje a kwashe tarkacen da aka jera a gidan ɗan su. Abubuwa dai su ka rinchaɓe a wajen.

Kowa a gidan da abinda ke ran sa, wassu baƙin na shirin komawa amma da su ka ji Baaba Sabuwa ta ce aure ba fashi za ayi, sai su ka tsaya dan su ga ƙarshen Farida.

Farida tun safe ko sau ɗaya ba ta fito a ɗaki ba, ko wanka ba ta iya yi ba balle abinci kam ba a zancen sa.
Da yamma Yakubu ya dawo daga wajen aiki sai a lokacin ya ke jin labarin abinda ke faruwa. Baaba Sabuwa ce ta ma sa maganar auren Farida da ya koma kan sa. Duk da bai shirya aure yanzu ba sannan bai taɓa kawo auren Farida a ransa ba amma indai dan ya cececi mutuncin 'yar uwar sa ne to zai aureta da gudu ma. Abinda ya ƙara ɗaure ma sa kai baifi yadda aka ce wai 'yan gidan su Rayyan sun ce wai FARIDA karuwar Ogan ta ba ne. Ya san Farida kuma ya san Sir Najeeb, ko da dai chan ƙasar zuciyar sa yana zargin Sir Najeeb na son Farida amma bai kai har ace wai suna neman junan su ba.

Yana cikin wannan tunanin ya ji wayar sa na ringing. Yana dubawa ya ga Farida ai da sauri ga ɗauki kiran.

"Dan Allah Yakubu ka sameni a ƙofar gida"

Da sauri ya tashi ya fita.
Lokacin da ya ganta wani tausayinta ne ya kuma shigan sa. Lokaci guda Farida ta chanja ta zama wata iri, fiskanta ya kumbura ga idon ta da su ka ƙanƙance saboda kuka. Tunowa yai da shekara uku da su ka wuce exactly haka ta lalace lokacin da aka raba aurenta da Lukman. Gara lokacin da sauƙi tunda matsalar daga Lukman ne to yanzu fa.

Ya ƙarasa wajenta yana faɗin "Farida dan Allah ki yi haƙuri, ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce"

"Ka kaini gidan su Sir Najeeb" abinda ta faɗa kenan cikin muryarta da baya fitowa sosai saboda dashewa da yai...


Adama ce ta buɗe ƙofa lokacin da ta danna doorbell ɗin.
"Daddy na nan?"

"Eh ki shigo"

A tsaye ƙiƙam ta tsaya idon ta na kallon ƙasa, kan ta ke sarawa, duk yadda ta ɗaga kan sai ta ji wani raɗaɗi.

Mom ce ta fara saukowa ganin yadda Farida ta ke ya sa tasan yarinyar na cikin damuwa.

" 'yan mata ki zauna mana" ta faɗa da Hausanta da bai gama nuna ba.

Farida ba ta ce komai ba sannan ba ta zauna ɗin ba. Kitchen Mom ta wuce ganin Farida ba ta cikin hayyacinta.

Minti huɗu sai ga Daddy ya sauko.

"Ina wuni Daddy" ta faɗa da disashshiyar muryarta.

"A'a Aisha Amarya?"

"Na'am Daddy"

"Lafiya dai ko?, shekaranjiya Baban ki ya kawo min katin biki, ina ce ba wata matsala ba ne ta taso ?"


"Daddy kai uba ne na gari amma ɗan ka bai ɗauko hali na gari ba. Najeeb ya min sharri, ya raba ni da farin ciki na. Ya sa min tabo a rayuwata wanda ban san ranan da wannan tabo zai gogu ba. Ni marainiya ce, ba ni da gatan da ya wuce Allah, kuma na haɗa Najeeb da Allah. A kamfanin sa ban tsira ba, na bar aiki da shi ma ban tsira ba. Allah zai saka min" ta fashe da kuka ta fice daga gidan da gudu. Daddy yana kiran ta amma ba ta tsaya ba. Daddy kan shi ya ɗaure dan bai gane ina maganganun Farida su ka dosa ba.

Tana fitowa ta tsaya ta goge hawaye sannan ta fara tafiya duk da kuwa ba ta da ƙwari a jikinta. Ta kusa isowa wajen Yakubu da ke jiran ta jiri ya ɗebeta ta faɗi ta suma. Yakubu ya yiwo kan ta da gudu...





*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0️⃣2️⃣3️⃣








Maigadi da dreba da su ke zaune a benchi su ka taso da gudu.
Ce ma sa su ka yi ya kai ta mota yayinda Iliya dreba yai sauri ya shiga gidan don ya faɗawa Daddy.
Daddy na falo har lokacin yana waya da Anas.

Ya na ma sa bayani Daddy ya ce muje-muje.

Daddy na gaba Yakubu na baya ɗauke da Farida wanda har lokacin ba ta farfaɗo ba duk da kuwa sun yayyafa ma ta ruwa. Kafin su isa asibitin ta farfaɗo amma ba ta san inda ta ke ba....

Chan gida kuma Baffa ne ya ke ta faɗa kan miyasa za'a bar Farida ta fita a wannan halin. Maijiddah ne ta ce tare su ka fita da Yakubu. Sai a sannan yai shiru ya zaro wayar sa a aljihu ya fara kiran numbar Yakubun amma bai ɗauka ba.

"Shima ɗan gatan'wa, ko ina ya shiga oho"...



Ruwa aka ɗaura ma ta aka ma ta alluran bacci dan sun ce jinin ta ne ya hau. Sai da ta fara bacci tukunna Yakubu ya samu damar kiran gida ya faɗa mu su.

Daddy ya dubi Yakubu ya ce " mi ya ke faruwa ne? mi Najeeb ya ma ta?"

Da kaman ba zai faɗa ma sa ba,sai dai girman Daddy da kwarjininsa ya fi gaban ya ƙi ma sa magana. Duk abinda ake ciki ya tsirge mi shi tundaga farko har ƙarshe.

Da ya gama bashi labarin Daddy ya ɗauko waya ya kira wata number.

"Anas ka na ina ne?"

Yakubu bai ji mi ake ciki ba ya dai ji ya ce "muna room 18 a sama"

Ba'a jima ba sai ga Anas ya shigo. Ganin Farida a kwance ya sa shi mamakin mi ya faru.

"Yakubu ya jikinta?, mi ya sameta?"

Da sauƙi kawai Yakubu ya iya ce masa.

"Ina ɗan banzan nan ya ke?"

Daddy ya tambayi Anas.

Ya gane Najeeb ya ke nema dan haka yai saurin cewa yana office nima daga office ɗin na ke.

"Har da kai ake rusa rayuwar mutane ko?"

Anas ya zaro ido ya ce "A'a Daddy"

Daddy ya miƙe ya ce "Yakubu Allah ya bata lafiya, ina nan dawowa anjima"

Yana Fita daga ɗakin Anas ga bi bayanshi da sauri.
A motan Anas ɗin su ka wuce Najeeb constructions.

Ya jima yana tunanin ko wani hali ta ke ciki. Wani ɓangare na zuciyar sa na faɗa ma sa bai kyauta ba wani ɓangaren na nuna ma sa ya yi dai-dai.
"She deserve it" ya furta a fili.
Yana ƙoƙarin duba wasu takardu da aka submitting ma sa tun da safe amma ya kasa fahimtar komai. Haka kawai zuciyar sa ke ma sa ƙunci....

A hanya Daddy ke sanar da Anas abinda Najeeb yai, Anas ya kaman salati yana salallami.

"Daddy ban san Najeeb zai iya yin haka ba especially saboda zargin da na ke masa akan yana son Faridan"

"Dan uban sa dan yana son ta sai ya mata sharri"

Anas dai shiru yai yayinda Daddy ke ta surfa ma sa masifa kaman wanda shi yai laifin.

Da ke an riga an tashi wajen shiru ka ke ji. Daddy da Anas su ka haura third floor.

Ya kifa kan sa akan kujera saboda wani zazzaɓi da ya rufeshi lokaci guda, ya rasa mi ya sa shi shiga wannan yanayi. He supposed to be happy ya rama kaɗan daga cikin asaran da Miss Salihu ta sa ya yi. But instead his sad.

Buɗe ƙofar office na shi da aka yi ya sa ya ɗago kan sa da sauri.
Ganin Daddy da Anas sai ya miƙe. "Dad " kaɗai ya iya faɗa kafin saukan mari ya sa ya haɗiye koma mi ya ke shirin faɗa.
A karo na biyu Daddy ya kuma marin sa, ji ka ke taas. Anas na gefe ya sha jinin jikin sa dan faɗan uba da ɗa sai Allah.

"I'm ashamed to call you my son"

"Dad" Najeeb ya faɗa a hankali

"Ashe tarin shekarun ne kawai akan ka ba hankali. Mahaukacin banza Mahaumacin wofi. Sai ka samu me idan ka hanata auren? Tukunna ma, miye dalilin yi ma ta sharri? Miye dalili? "

"she deserve it Dad, she wanted to ruin me. Na rasa big contract saboda ita saboda haka 2 project da mu ka fara su ka soke contract da mu. She tarnished my image and the repeatition of my company"

Wani marin Daddy ya kai ma sa. " i didnt know i have a monster son. Asaran kamfaninka yana dai-dai da ruguza mutuncin mutum kenan?. Shin ka yi tunanin halin da yarinyar nan za ta shiga? What if she died of shock, sai ka haɗa party kana murna ko"

Ya nuna shi da ɗan yatsa yace " Anas, kalli banzan yaron nan fa,8yrs ago da Sabreena ta gudu ta barshi kafin auren su he almost died, he was depressed for months. Ya je theraphy section na watanni huɗu kafin daga baya ya warke ya dawo Nigeria. Do you know that this fool here yana shan antidepressant drugs har yau saboda baƙin cikin yarinyar nan. Amma shi ne ya ke da guts da zai je ya hana auren 'yar mutane"

"Najeeb" ya ka sa magana ma saboda baƙinciki da ya tokare ma sa wuya.
Daddy juyawa yai ya fita, Anas ya kalli Najeeb, kallon ka bani mamaki sannan ya bi bayan Daddy da sauri.


Gidan su Rayyan Daddy ya ce Anas ya kai shi. Da su ka je su ka sa a yi sallama da Baban Rayyan ɗin, aka ce mu su yana kasuwa. Numbar sa su ka karɓa su ka kirashi jin sunan Alhaji Adam Jibo ne ya sa mahaifin Rayyan ya ce yana nan zuwa. Haka su ka zauna zaman jiran sa, kafin ya dawo ma an fara kiran sallan maghrib su ka yi sallah a masallacin anguwar.
A ƙofar gidan aka shimfiɗa mu su tabarma lokacin da Baban Rayyan ya zo.

Daddy bai ɓata lokaci ba ya ma sa bayanin ko shi waye da kuma abinda ya ke tafe da su.

"Malam Abdullahi, wannan hoto da aka kawo muku ba tare su ka ɗauka ba, editting na shi aka yi, kasan yanzu fasahar zamani ba abinda ba ayi. Wannan yarinya ta na da tarbiya kuma kowa ya shaideta da haka. Duk abinda Najeeb ya zo ya faɗa muku to wallahi ƙarya ne, ya yi hakan ne dan ya cimma wani banzan burinsa. Ku yi haƙuri a maida maganar auren yaron ku da Aisha"

Yadda Daddy ya ke magana cikin kwantar da murya ya sa Malam Abdullahi yarda da maganar sa domin Daddy babban mutum ne a gari kai a ma ƙasar gaba ɗaya ba zai yiwu ya zo wajen sa dan kawai ya ma sa ƙarya ba.

"Alhaji na fahimceka, sai dai gaskiya al'amarin nan ya riga ya ɓaci. Ni da Alhaji Musa mun samu saɓanin harshe a yau ɗin nan saboda wannan magana. Yanzu haka maganar da na ke maka an riga an dawo mana da sadaki da kuma kayan lefe da aka kai. Harta kayan yarinyar da aka kai gidan yarona sun je sun kwashe. Al'amarin ya ɓaci sosai gaskiya"

"Malam Abdullahi a duba dan Allah. Auren nan idan aka fasashi alhakin yarinyar nan zai bi Najeeb 'ya'ya da jikokin sa"

"Gaskiya zan faɗa ma ka Alhaji ko da za a dawo da bikin nan to ba gobe ba"

Shiru Daddy yai na tsawon lokaci kafin ya ce wa Anas su tafi.

...........................


Su Baffa da su Ummi sun zo asibitin da aka kwantar da Farida. Baffa kam a lokacin ma ya ƙara tabbatarwa kan sa ko mi zai faru to gobe sai ya aurar da Farida, domin idan gobe ta wuce bai san halin da Farida za ta shiga ba, balle ya san halinta yanzu sai ta ce ta haƙura da aure gaba ɗaya ta ce karatu za ta cigaba da yi.

Bayan ya tabbatar da ankawo duk abubuwan da za su buƙata sannan ya musu sai da safe saboda ance sai gobe za a sallameta. Ya zo zai fita daga asibitin da shi da Yakubu su kuma su Daddy su ka shigo.

"Alhaji Musa dan Allah ka tsaya" Anas ya faɗa lokacin da ya ga Baffa Musa ya gan su amma sai ya kau da kai yai kamar bai gan su ba.

Baffa Musa ya juyo ya kalli Daddy yana ƙarasowa wajen su, girman sa ya sa ya fasa masifar da ya ke shirin yiwa Anas.

"Alhaji Musa dan Allah ko za mu iya magana da kai"

"Ni yanzu gida zan wuce Alhaji, ina sauri"

"Ba komai Alhaji Musa za mu bika gidan"

Baffa Musa dai bai so ba amma ba yadda ya iya. Haka su ka wuce gaba, su ma su Daddyn su ka bi bayan su.

Daddy da Baffa Musa ne a falon. Yayinda Anas da Yakubu ke ƙofar gida suna tattauna wannan abin al'ajabi mai kama da almara.

Duk girman Daddy da matsayin sa haka ya fara yiwa Baffa Musa magana cikin sanyi da harshe mai taushi.

"Alhaji Musa dan Allah ka duba wannan al'amari. Na yiwa Malam Abdullahi magana kuma ya ce za su duba, kar a fasa auren nan gobe dan Allah"

"Aure ai ba za a fasa shi ba, kamar yadda na gayyace ka da farko ba chanji. Gobe ƙarfe shaɗaya na safe za a ɗaura auren Farida da ɗa na Yakubu. Tunda sun shaƙu da juna idan anyi auren za su fahimci junan su sosai"

"Alhaji idan ka yi haka ba ka yafe ba kenan"


"Alhaji ko ka san ni ɗin nan ni na shiga na fita har na ga na amso takardar Farida saboda ɗan shege mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login