Showing 39001 words to 42000 words out of 145203 words
ta yi.
"Ki shiga ki yi alwala ni inada alwalata" ya katse tunanin ta
Ai da sauri ta miƙe ta shige banɗakin. Duk yadda ta so ta daure ta yi alwala amma hakan bai yiwuba dole dai sai da ta je ta zauna a toilet. Ƙarshen kunya sai ga shi ƙaran gudawan na fitowa da ƙarfi wanda tabbas ta san AbdulWahab da ke ɗakin ya ji.
Ta gama amma kunya ya sa ta kasa tashi ta yi flushing, ta jima tana zaune daga baya ta yi ta maza ta tashi ta flushing na shi sannan ta yi alwala. Sai dai ka sa fitowa ta yi daga banɗakin dan ba ta san da wanni ido za ta kalli AbdulWahab ba.
Jin shiru kuma ta ƙi fitowa ya ce " gimbiya ko na zo na fitar da ke ne?"
Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito. Daga bakin ƙofa ta tsaya kanta a ƙasa ta ce a hankali " I'm sorry, cikina ne ya ruɗe Yaya"
Tasowa yai har wajen da ta ke tsaye ya kamo hannunta ya ce " There's nothing to be sorry about my dear, mun riga mun zama ɗaya ai"
Sai da ya zaunar da ita sannan ya ce "kinsha magani?" Ta ɗaga ma sa kai.
"Barin haɗo mi ki tea sai ki fara sha"
Fita yai daga ɗakin wanda cikin minti shabiyar da ya ɗauka sai da Maijiddah ta sake zagayawa banɗaki.
Lokacin da ya dawo ya sameta a ɗan kwance gefen gado. He know she's nervous shiyasa ta ke experiencing wannan abun. Ya tuna akwai wani abokinsa mai irin wannan, ko exam za su yi sai ya ɓarke da gudawa, a ranan da za su fara exam na Waec shekaru da dama da su ka wuce sai da Hussaini ya makara saboda ruɗewa da cikinsa yai.
A yadda ya ganta she's already weak, idan yai yunƙurin yi ma ta wani abu that will label him a cruel man.
Taimaka ta yai ta tashi ta sha tea ya haɗa ma ta da kaza.
"Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zan miki, ki ci ki samu ƙarfin jikin ki"
Shi da kan shi ya fara ba ta naman a baki har ta ƙoshi. Ya ce ta shiga ta yi wanka ta ce na yi.
"Kinga yanzu jikinki ya tsatstsafo da gumi saboda tea da ki ka sha. Ki je ki watsa ruwa"
Gaba ɗaya kunya sai ya sake rufeta. Ta tashi ta shiga ta sake wanka da ta fito ba ta same shi ba ya tattara wajen. Ta yi saurin buɗe closet ta nemo kayan bacci riga da wando ta sa, sannan ta ɗaura hijab akai.
Da ya dawo a zaune a bakin gado ya sameta.
"Hauwerh cire hijabin nan akwai zafi"
Ba mu su ta cire hijabin ta sunkuyar da kai tana wasa da bakin pyjamas ɗin ta.
"Ya cikin na ki?"
"Da sauƙi"
"Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru kin ji"
Ta gyaɗa kai.
"Now breath in and breath out"
Ba ta gane ba har sai da ya nuna ma ta yadda za ta yi da kan sa sannan ta yi yadda ya ce. Sai da ta yi kusan sau goma kafin ya ce ta kwanta.
Kafin ya shimfiɗa sallaya yai sallar nafila tuni bacci ya sace amaryar sa. Da ya idar sai ya gyara ma ta kwanciya sannan ya kwanta bayanta ya musu addu'a ya kashe wutan ɗakin...
Washe gari da kunyar sa ta tashi tunowa da tai da abinda ya faru jiya. Sai dai shi kam ko ajikinsa, nuna ma ta yai wannan shine amfanin auren domin sun riga sun zama ɗaya. Duk wani matsalarta na shi ne, haka nan duk matsalarsa na ta ne.
Da dare su ka je gidan su sallama, daga nan su ka wuce gidan su Maijiddan. A wannan lokacin Farida ta tambayeta ko gudawar ta tsaya kafin ango ya shigo. Maijiddah ta ce "inaa, Anty ni kam ai na sha kunya" a taƙaice ta gaya ma ta abinda ya faru Faridan ta yi ta ma ta dariya.
Ba su jima ba su ka wuce saboda da sassafe jirgin su zai tashi.
Daren ranan ya gaya ma ta basic abubuwan da ya kamata ta sani gameda airport da jirgi. Sannan ya jaddada ma ta ba abinda zai faru yana tareda ita.
Ko breakfast ba ta iya yi ba saboda kar ta ci wani abu ya dameta. Ƙarfe tara jirginsu ya wuce Lagos. Kuma Alhamdulillah Maijiddah ba ta yi gudawa ba, sai dai ta tsorata kam lokacin da jirgin zai tashi, ba dan AbdulWahab na riƙe da hannunta yana kwantar ma ta da hankali ba ƙila da ta yi kuka. Sai da jirgi ya lula sama sannan ta ɗan samu nitsuwa kaɗan...
Asha amarci lafiya Maijiddah (banda gudawa plz😁)
.........................
Safiyar Monday Farida ta fito aiki duk da kuwa gajiya bai saketa ba, sai dai kamar yadda ta yiwa Maijiddah dariya sai gashi itama tana tsaka da aiki cikinta ya hautsina. Da farko sharewa ta yi tana mita " mutum ya yi ta ciye-ciyen mai kwana biyu ba dole ciki yai ta kuka ba"
Sai dai fa lokaci guda ta kasa yin komai ta tashi ta nufi office ɗin Najeeb da gudu dan nan ne kusa da ita sannan ta ɗauka baya office ɗin dan ya fita ɗazu ya je meeting. Abinda Farida ta manta shine ya riga ya dawo tuntuni.
Da gudu ta zo ta wuceshi yana zaune yana aiki, kafin ta ƙarasa ma ta saki tusa a hanya.
Yana shirin buɗe baki yai magana kan shigo ma sa office da ta yi da gudu ya ji ƙaran tusan da ta yi...
Hankali kwance Farida ta zauna ta zazzage kayan cikinta, dama tun ran asabat rabon da ta yi, ga shi ba ƙaramin abinci ta ci ba a bikin nan. Ta jima a ciki kafin ta wanke ta yi flushing, kasancewa banɗakin yai gum sai ta ɗau air freshner ta feffesa ta ƙara buɗe windown banɗakin da kyau saboda iska ya ratsa.
Ta fito tana ɗan daddanna ciki tana faɗin "kai abubuwan da na ci a bikin nan ai sai barka. Kashi rahama ne Allah, ka ji yadda na ji wani saƙayau lokaci guda"
Cak ta tsaya da tafiya lokacin da muryan da ba ta taɓa tunanin ji ba a wannan lokacin ya doki kunnenta
"Miss Salihu"
Kaman ta nitse cikin office ɗin haka ta ji sai dai ita Aisha Farida ce dole ta nuna dakewarta. Tukunna ma dama yana office lokacin da ta shigo? ko dai bayan ta shiga banɗakin ne ya shigo office ɗin.
"Miss Salihu whats the meaning of this?"
Da ƙarfinta ta waiwayo bayan ta sauke ƙaramar ajiyar zuciya. Ita ɗin expert ce wajen waskewa, ta ce
"Daɗin abin ma kowa yana yi, abinda na yi ba farau ba ne akai na. Ni'ima ce da ubangiji ya baiwa bayinsa dan ya nuna ma na mu ɗin ba komai ba ne. Da Sarki da shugaban ƙasa da maikuɗi da talaka, malami da jahili, mai kyau da mummuna, mace ko namiji, fari ko baƙi. Dukkan mu muna da buƙatar wannan ni'ima. Abu ne ba babba ba yaro"
Ta ɗan haɗe rai ta ce " yanzu haka Sir Najeeb kai ma wannan ni'imar sai da ka yi ta kafin ka zo office yau, ko tun jiya rabon da ka yi?"
The girl is really crazy, taya za ta yi abin kunya and pretend kaman ba komai. Masifa ya ke so ya ma ta amma maganganunta sai su ka kusa sa shi dariya. Ya daure ya ce " Miss Salihu a wani dalilin ya sa ki ka yi min amfani da banɗaki?"
"Saboda ya fi kusa da ni mana"
"This should be the last time da za ki yi haka"
"Ok Sir"
Har za ta wuce sai ta juyo ta ɗan yi gyaran murya ta ce " Sir ina da magana"
Ido ya ɗaga ma ta alamar miye.
"Sir, tsakani da Allah tusar da na yi ɗazu ka ji ta?"
Kallon-kallo su ka tsaya yi. Har ga Allah tana son sani dan bayan ƙarar da tusar ta yi ba ƙaramin wari ne ya biyo bayan tusar ba.
"Get out of my offfice"...
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Last Free page*
0️⃣1️⃣5️⃣
"Mama har yanzu bai kirani ba, ina ga bai san ma na yi yaji ba fa" Aneesa ta faɗa cike da damuwa a ran ta.
"Ya ki ke so na miki? Na kira AbdulWahab na ce ka zo ka bada haƙuri matar ka ta yi yaji ko ya?"
"Mama do something please, ba zan iya sharing mijina ba"
"An riga an ɗaura auren Aneesa live with it. Ke ne za ki san yadda za ki riƙe gidan ki ta yadda yarinyar ba za ta samu kan shi ba"
Aneesa ta ɗan ɓata fuska ta ce "Mama ta ya zan yi hakan bayan bana zama a Lagos"
"Za ki ajiye aikin ki kenan?"
"Hell no. Ta ya zan bar career ɗi na when i'm at its peak. Ko kaɗan"
Mama ba ta ce komai ba, to mi za ta ce. Itama mace ce da mijinta ba ya gabanta. Ta taso da aƙidar 'yan cin kai, yau tana Dubai gobe tana China wajen saro kaya, kasuwancin ta shine a gaban ta. Auren fari ta haifi Aneesa da Nazir, da ta auri Alhaji Abdullahi ma ɗa ɗaya ta haifa ta rufe haihuwa. Kuɗi kuɗi su kawai ta sa a gaba ba ta da lokacin kula da iyalin ta balle tarbiyyan yaran ta, shi ya sa ko kishiyoyin ta ba sa gaban ta, dama kuma kowa gidan ta daban...
.....................
Farida na zaune wani saurayi ya shigo neman Najeeb.
"Wa za a ce?" Ta tambaya lokacin da ta ɗau wayar.
"Ki ce ƙanin shi"
"Sir wai ƙanin ka na neman ka"
Ajiye wayar ta yi ta ce " ya ce ka shiga"
Ba a jima da shigar wannan baƙon ba Anas ya zo shima ya shiga.
Dukkan su uku zama su ka yi ana taɗin bayan rabuwa.
"Big B tunda ka ƙi auruwa mu zamu shige gaban ka fa, dan na gaji da zama tuzuru"
"Shege yaushe ka dawo da za ka fara maganar aure. Anas see this small boy fa"
Anas dai murmushin ya ƙe yai dan ya san inda maganar za ta tsaya ba za ta ma sa daɗi ba.
Farida ta shigo ta samesu a haka, bayan Anas ba ta taɓa ganin Najeeb ya sake yana taɗi da wani ba. Sai dai kamar yadda wannan saurayin ya ce shi ƙanin sa ne ƙila su na da alaƙa tunda dai a yadda Anas ya gaya ma ta ƙanwar Najeeb ɗaya ce wato Najdah. Wata 'yar girman kan kaman yayan na ta.
Kai tsaye wajen Najeeb ta nufa a wajen kujerun da su ke zaune wanda anan ya ke saukan baƙin sa.
"Sir ga wannan ana buƙatar signature ɗin ka anan" ta faɗi lokacin da ta miƙa ma sa wasu takardu.
Ya amshi takardun ya fara dubawa.
"Kai Big B wannan hottie as a secretary ai za ta ɗauke hankalin ma su zuwa wajen ka"
Najeeb ya ɗago ido ya ma sa wani kallo wanda ya sa yai saurin chanja magana da cewa.
"Ba wanda ta kai sweety na kyau ai. Najdah is the epitome of beauty ba ƙarya"
Gyaran murya Anas yai sannan ya ce "Musty zan wuce office, sannu da zuwa"
Musty ya miƙa ma sa hannu su ka gaisa. Idon Farida na kan Anas wanda ta ga ya chanja lokacin da Musty yai maganar Najdah. Tun farko-farkon fara aikinta ta san Anas ya na son Najdah, duk da kuwa Anas ɗin bai iya buɗan baki ya faɗawa Najdan ba har yau.
"Ya Anas dan Allah ka ɗan jirani minti biyu" ta faɗa tana murmushi.
Sauke idon da za ta yi domin ƙarɓan takardun da Najeeb ya gama signing sai ta ga idon shi chul akan ta. Ba ta san ma'anan wannan kallon ba amma ta fassara shi da cewa kallo ne da ke nuni da zan gamu da ke.
Da ta amsa takardun ta ce "Allah na gani ni ban ci bashin kowa ba, kurwata kur"
Har ta fita daga office ɗin bai daina kallon ta ba.
Musty cikin fake American accent ɗin sa ya ce " Your secretary is funny and cute"
"Ba ka daina halin na ka ba ko?"
"Sorry Babban yaya"
Tana fita ta tadda Anas na tsaye yana jiran ta. Gaba ɗaya fiskar sa ta chanja bisa yadda ta san shi da, shi ba kaman Najeeb bane kullum fiskar sa a sake ta ke gashi da son barkwanci.
"Yaya na ban gane wannan ɗan adawar ba fa, shi waye?"
Murmushin ya ƙe yai ya ce "ɗan ma su gida ne. Mustafah Sulayman Jibo kenan"
Kalmar da ya faɗa ta 'ɗan ma su gida' ya sa ta tuna da audion da aka ce ta yi kwanakin baya inda ake cewa shi ɗin ɗan Maigadin gidan su Najeeb ne, kenan da gaske ne.
"Ya Anas kar ka damu mu akai za mu dangwalawa. Idan da so ai ya share komai"
"Ki na ga Najdah za ta tsallake ɗan uwanta ta zaɓe ni ko kuma Daddy ne zai watsar da zumunci ya zaɓe ni?"
"Ya Anas da wannan ma amma tun farko kai ka yi sake. Da ka gina soyayyar ka a zuciyar ta da tuni an wuce wajen"
Girgiza kai yai ya ce " Farida ba za ki gane ba"
Wucewa yai ya bar office ɗin ran sa ba daɗi...
Najeeb na zaune da Musty ne amma hankalin sa na kan tunanin mai Farida za ta faɗawa Anas. The girl is mischievous, yanzu haka wani gulma ta ke yi.
A wajen cin abinci Farida ta samu Anas shi kaɗai, bai ordering abinci ba, ruwa ne kawai a gaban sa, yana zauna amma hankalin sa yai nisa cikin tunani.
"Ya Anas yau da garau-garau na zo, za ka ci" Farida ta ajiye kular tana ƙoƙarin buɗewa.
" 'yar uwa yau ba na jin yunwa" ya faɗi ba tareda ya kalli abincin ba.
"Allah sai ka ci, nan nan na hana Yakubu abincin nan na ce a yaya na zan kaiwa amma ka gwaleni ba ka isa ba"
Ta fara zuba abincin a plate tana faɗin "Ya Anas yajin ya ji maggi fa, ga man ma sai ƙanshin albasa ya ke"
Sai da ta gama haɗawa ta tura gefen sa ta ce " dan Allah ka ci"
Ba yadda zai yi dole ya ɗau spoon ya fara ci. Ita ma ta haɗa na ta ta fara ci. So ta ke ta ma sa maganar Najdah shi ya sa ta zo.
"And what is the meaning of this?" Muryan Najeeb ya gauraye ilahirin wajen.
"Anas miye haka?, babu respect tsakanin Oga da mere secretary. Ta ya za ka bari ta zauna a inda na ke zama na ci abinci. Are you trying to disrespect me kamar yadda ta ke disrespecting ɗi na"
"Najeeb is not..."
"Shut up" Najeeb ya katse Anas da tsawa. Wannan ya ja hankalin kowa ya koma kan su.
Ta shi Anas yai zai bar wajen. Farida ta ce "Yaya dan Allah ka tsaya ka ci abincin ka, ni barin bar ma sa wajen"
"Bar shi na gode Farida" ya faɗi sannan ya bar wajen.
"Girma ya faɗi, kuma wallahi an ji kunya"
Hannu Najeeb ya kai zai ma ta mari sai kuma ya tsaya yana huci hannun na reto a sama " I'm warning you Miss Salihu, ki kama matsayin ki ko kuma na nuna mi ki"
Haɗiye miyaun da ya tokare ma ta maƙoshi ta yi lokacin da Najeeb shi ma ya juya ya bar wajen. Ta gama sadakarwa Najeeb marin ta zai yi. Har ta hango yadda fiskarta zai koma idan da marin ya sauka a fiskarta.
Ranan dai ita ɗin ma ka sa cin abincin ta yi. Mi ya ke damun Najeeb da har zai yiwa Anas haka, hakan ma agaban jama'a wanda duk a ƙasan Anas ɗin su ke...
Kai tsaye office ɗin Anas ta wuce da ga canteen. Yana zaune yana ta kan zane a takarda wanda da ka gani ka san yana zanen ne saboda huce haushi.
"Yaya na kar ka ce na cika gulma amma anya Sir Najeeb yana da lafiya kuwa. Gaskiya a binciki ƙwaƙwalwar sa"
"Lafiyar sa ƙalau Farida, kawai dai he has a rough life ne. Mahaifiyar sa then Sabreen, su suka maida shi haka"
"Sabreen?" Farida ta faɗa da alamar tambaya.
"Macen da Najeeb ya fara so ba"
"Dama duk girman kan Sir Najeeb ya taɓa soyayya? Abun mamaki"
"Kar ki damu da abinda ki ka ga ya yi ɗazu, anjima kaɗan za ki ga ya zo ba da haƙuri"
"Duk da haka Ya Anas, abinda yai bai ma ka adalci ba wallahi"
"Kar ki damu, abinda yai bai kai zuciyar sa ba"
"Wannan sirikin na ka Allah kaɗai ya san yanayin sa. Yau ka gan shi shiru anjima ya fara faɗa gobe idan ya fara banbamin bala'i har wani spark bakin sa ya ke yi"
Ai Anas bai san sanda ya fara dariya ba "kai Farida kinada abin dariya ba kaɗan ba"
"Allah Ya Anas wani lokacin kaman majnuni ya ke, ka san lokacin da aka kidnapping ɗin mu haka mu ka kwana mu ka wuni bai min magana ba daga baya kuma bini-bini sai ya ɗaukeni"
"To waya sani ko ke ce ke sa shi haukan"
"Ni Aisha Farida! Rufa min asiri kafin yanzu na ga query letter"
Ta ɗan gyara zama ta ce " yawwa, da ma maganar Najdah zan ma ka"
Ya ɗago ya kalleta
"Mi zai hana ka faɗa ma ta kana son ta, you never know, sai ka ga an dace. Balle ni ina ganin tana son ka ma"
"Baba na gadi yai a gidan su har ya rasu, karamci na Daddy ne ya sa ya sponsoring karatuna tun daga primary har masters da na yi shi ya sa na zama abinda na zama a yau. Daddy is like my father amma kuma na san indai akan maganar Mustafah ne to zai zaɓeshi ya bar ni, domin Mustafah jinin sa ne"
" tsoro shi zai sa ka rasa masoyiyar ka wallahi. Ba ka taɓa ce ma ta kana son ta ba, ba ka gayawa Najeeb ba balle kuma Daddy, to dan Allah ta ya za su san kana yi balle har a dubi wanne ya fi dacewa da ita tsakanin kai da Mustafah"
"Ki bari kawai Farida. Gara na zauna a matsayina"
"Dan Allah kar ka bani kunya ma na"...
...........
Lokacin da aka dawo daga break ta koma office ɗin ta. Ko da aka zo neman Najeeb ta kira office ɗin sa amma bai ansa ba, ta shiga office ɗin amma baya nan. Har banɗaki sai ta leƙa amma shiru. Numbar sa ta fara kira amma ba ta shiga.
Daga ƙarshe dai ranan har aka