Showing 78001 words to 81000 words out of 145203 words

Chapter 27 - SAKATARIYA TA COMPLETE

Azizat   

13 Jul 2024

25699

saboda kuka ne dan ya san ba ta wasa da abinci.

"Ashe za ka zo, shi ne ko ka faɗa min. Mu shiga ciki"

Sai da ya ɗau minti ɗaya ya na kallon ta kafin ya bi bayanta su ka shiga gidan...


Da ke kwana na tara kenan da rasuwan duk an watse sai iyalin sa kawai. A daddafe ya gaisa da su. Kusan awa ɗaya yai a gidan saboda yadda 'yan uwa da maƙota ke zuwa gaida mijin Farida wanda yawanci gulma su ke zuwa saboda su ga mutumin da ya sa aka fasa aurenta da Rayyan, su ga ya ya ke. Sai dai kowa ya zo da Masha Allah ya ke tafiya baki buɗe. Sun ga kyau, sun ga kuɗi, sun ga aji, sun ga ƙasaita...


Lokacin da zai tafi bayan ta raka shi wajen motar sa ya ce " za'a koma aiki monday yaushe za ki dawo?"

"O'o ni Aisha Farida, dan aiki kawai za a neme ni. Ni kam dole idan na koma a chanja min matsayi ya kamata a upgrading ɗi na, na bar matsayin sakatariya"

" ki na son ƙarin matsayi ne?"

"Haba Sir Najeeb wa ya ƙi cigaba a duniya"

Bai san ya ake zuwa gai da sarakai ba shi ya sa bai zo da komai ba. Ya dai bar musu dubu ɗari a gefen ɗrinks ɗin da su ka kawo ma sa wanda ko taɓawa bai yi ba...

Har motar sa ta ƙule Farida ba ta bar wajen ba. Tana ƙissima abubuwa dayawa a ranta. Zuwan Najeeb ya sa Najeeb ya ƙara samun wani matsayi na daban a zuciyar ta...





*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0️⃣3️⃣1️⃣




*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*




Yana hanya ta kirashi lokacin koma fita daga Jos bai yi ba. Ya saƙala bluetooth ya amsa kiran.

"Sir Najeeb shi ne har da ɗawaiyina haka. Mun gode Allah ya ƙara buɗi. Allah ya kai ka lafiya"
Amin kawai ya ce ya kashe kiran.


Da ya isa Kano yana so ya kira ta amma ya ka sa. Sai ya ɗauko wayar zai danna numbar ta sai ya fasa ya ajiye, ana huɗu da yai haka sai ga text ɗin ta ya shigo tana ma sa ya hanna da fatan ya isa lafiya.
"Na isa" kawai ya daure ya rubuta ya ma ta reply da shi. Maimakon ta haƙura a haka sai ta kuma turo da wanni text ɗin.
"Sir N mi zan taho ma ka da shi? ina son zuwa Wase gobe"

Bai san ina ne Wase ba, dan haka ya minimizing wayar ya browsing sunan nan ya gane wata ƙaramar hukuma ne a Jos.

Ya ma ta reply da "ok"

Ta sake turo wani saƙon " Sir N ba ka faɗi abinda zan kawo ma ka ba"

Ya na so ya ajiye wayar ya shareta amma zuciyar sa ta hanashi

"Kan ki" ya tura ma ta ba tareda ya gama tantance ma'anar faɗin hakan ba.

"Kan kifi? Sir N kan wani irin kifi?"

Ganin reply ɗin ta ya sa shi murmushi. Ya ɗan jima kafin ya tura ma ta "Mrs Jibo sleep"

Good night kawai ta sake turowa daga nan ba ta kuma turo da wani saƙon ba. Shi ma ya ajiye wayar sa gefe ya kwanta.

.......................

Safiyar Sunday ya aika ma ta da Iliya driver akan ya je ya ɗauko ta. Ita kam tana chan tana kan haɗa kayan tsaraba da za ta zo da shi. Sai da Iliya ya kusa isa cikin Jos sannan ya kira ta ya ce ya kusa isowa.
Wani matsayi ta ke kuma hangowa kan ta idan ta koma Kano. Ya sa an kawota da mota ya kuma turo ma ta driver ya dawo da ita. Wannan karramawar sai Mrs Jibo ai...

Lokacin da su ka isa gida ana kiran sallar maghrib. Iliya ya je ya kira Friday su ka shiga da buhun dankalin turawa da ta zo da shi da kuma wata ƙatuwar jakan ghana-must-go.

Ɗakin Mom ta je dan ta gaidata ta samu ba ta nan, ta wuce ɗaki ta shirya ta yi sallar la'asar da magariba...

Ƙarfe tara ta sauko ƙasa dan ta nemi abinda za ta ci, ba komai a dining ɗin hakan ya sa ta shiga kitchen shi ma wayam. Yunwa ta ke ji dan haka ta tsaya ta girka noodles da soyayyan ƙwai, ta fito ɗauke da plate ɗin shi kuma Najeeb ya shigo.

"Sir Najeeb" ta kira sunan sa. Juyowa yai ya ganta tsaye riƙe da plate da cup

Sai da ya gama kallon ta daga sama har ƙasa sannan ya juya ya tafi. Ta bi bayan sa da baki buɗe.

A dining ta zauna ta ci abincin ta dan idan ta haura sama za ta ji ƙiwuyar saukowa, sai da ta gama ci sannan ta wuce ɗaki.

"Sir Najeeb irin ba ka ji daɗin ganina ɗin nan ba, ko sannu da zuwa babu"
Bai kulata ba hakan ya sa ta gane akwai abinda ke damun sa dan bayan bai kulatan ba fiskar sa ya nuna yana cikin damuwa.

"Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?"

"Please stop talking" abinda ya iya faɗa kenan ya gyara kwanciya a kan gado.
Tabbas akwai abinda ke damun shi dan Najeeb ba ya bacci da wuri, sannan duk rintsi sai ya yi wanka ya sa kayan bacci kafin ya kwanta.

Kaman yadda ya buƙata ɗin, shirun ta yi tana tunanin ko me ke damun shi.
Har ta kwanta Najeeb bai tashi ba, ba kuma baccin ya ke ba dan idon sa a buɗe lokacin da ta leƙa shi...



Washegari da ta shirya ta fito ne ta haɗu da Tasallah a kitchen wanda ke shaida ma ta Mom ba lafiya an ba t gado.
"Ayya ashe shiya sa jiya da na dawo na ji gidan shiru. Ya jikin ta?"
Tasallah ta ce da sauƙi. Maimakon office da ta yi niyyar zuwa sai ta wuce asibitin lokacin Iliya ya kawo Adama za ta ɗauki wassu kayan buƙatu sai su ka tafi tare.

Ta yi mamakin yadda Mom ta faɗa haka. A wajen Najdah ke cewa " tunda yanzu ke ki ke juya Big B sai ki sa ya zo ya ga Mom. Kin wani yanko ƙafa kin zo irin son a sani ɗin nan"

Farida ta kalli Najdan sannan ta kalli Mom da ke kwance tana bacci.

"Na san da cewa ba kya son ganina tareda yayan ki, amma ki sani shi ya kawo ni gidan ku ba ni na kawo kai na ba. Tun farko-farkon zuwa na ki ke ta ƙananun magana akai na, ban tanka mi ki ba. Kar ki sa na kalle ki da idon Aisha Farida dan ba za ki ji daɗi ba. Ki bini a hankali mu tafi a yadda mu ke yanzu"

Najdah ta yi tsaki, ta ɗau waya ta fara latsawa.

Farida ta fice daga ɗakin gudun kar ta fara masifa ta tada Mom daga bacci. Amma tabbas za ta ware lokacin Najdah nan ba da daɗewa ba...

Kai tsaye Najeeb constructions ta wuce sai dai da ta je office ɗinta kama baki ta yi saboda chanji da ta gani, office ɗin ta da na Najeeb ya koma kusan guda ɗaya, maimakon gini da ke tsakanin su yanzu wani tinted glass ne ya raba su wanda daga office ɗin sa yana iya hango komai a na ta office ɗin amma ita kuma ba za ta ga na sa ba.

" ba dai wannan Sir Najeeb ya ke nufi da matsayi ba"

Ba ta gama zama ba Najeeb ya shigo ran sa a ɓace. Yanzu ya fito daga board meeting.

"Sir Najeeb ashe Mom ba lafiya shi ne ba ka gaya mun ba"

"Get back to work Mrs Jibo"
Gwiwanta yai sanyi ba dai duk wani zumuɗi da zaƙalewan da ta ke yi a kan sa duk na banza ba ne.

"Noory" muryan Sabreen ya dawo da ita daga tunanin da ta ke.

Murmushi Sabreen ta yi ganin Farida a wajen. Da alama itama daga wajen da Najeeb ɗin ya fito ta fito.

Ganin Sabreen ya sa ta ma tuna da zancen ta, ita harga Allah ta manta da wata Sabreen.

"Noory, you are just taking it personal, i'm here to work"

"Kar ki sake kirana da wannan sunan. Here and anywhere else i am Najeeb to you"

Ta ɗan ji haushi saboda a gaban Farida ya faɗa. Amma ta dake ta ce "fine"

Farida ta fice daga office ɗin ta koma na ta duk da ta san daga inda ta ke su na kallon ta.

Wani yanayi ta tsinci kan ta ciki. Sabreen ta fara aiki anan, mi hakan ya ke nufi? Kenan watarana Sir Najeeb zai aiketa wajen Sabreen ko Sabreen ɗin ta ba ta saƙo dan ta kaiwa Sir Naheeb. Ba zai yiwu ba, dole ta ajiye aikin nan. Ba za ta yi aiki tana ƙarƙashin Sabreen ba, wannan cin fuska ne.

"Congratulations 'yar uwa. Finally gaskiya ta fito" muryan Anas ya doki kunnen ta.

"Wani gaskiyar?" Ta tambaya tana ƙoƙarin ɓoye damuwar ta.

Zama yai zai ma ta bayani sai ga Sabreen ta fito.

Tana ganin su ta yi wani murmushi sannan ta juya tana catwalking ta fita.

Anas ya juyo ya kalli Farida wanda itama bin bayan Sabreen ɗin ta yi da kallo.
Ya ce "asirin wanda su ka kitsa mi ki sharri ya tonu. Gaskiyar zance ta fito"

"Haba! Yaya na wani ɗan Alatsinen ne ya ke son ganin baya na"

"Wallahi Khalidah ce"

"Ban yi mamaki ba dan za ta rina"

Nan ga shiga labarta ma ta yadda aka yi gaskiya ta fito.
Da kotu za su shiga amma an settling case ɗin tsakanin Kamfani da su saboda Alhaji Matawalle ba ya so a je kotu domin ya na siyasa kuma ya na son fitowa takaran senator. Na biyu kuma Alhaji Tukur mahaifin Khalidah ba ya son wargaza alaƙar sa da Najeeb, 8% shares na shi a kamfanin shi ya san kuɗin da ya ke samu, shi ya sa shima ya zaɓi teburin sulhu.

Alhaji Matawalle zai biya kamfani taran miliyan ishirin ita kuma Khalidah za ta biya Farida miliyan biyu.

" 'yar uwa mun yi kuɗi fa. Dan Allah ayi kason da mu"

Farida murmushi kawai ta yi dan ba wannan ba ne damuwar ta.

Ranan duk wani ɗokin dawowa Kano da ta yi ta ji Kanon ya fita ma ta a kai. Da yamma bayan ta dawo Baba Sabuwa ke kiran ta akan 'yan uwan Najeeb sun kawo lefen ta yau da safe. Su kan su ba su san da zuwan ba ko karramawar kirki ba a mu su ba.
Farida kin ga kaya ki godewa Allah gaskiya domin an zuba dukiya a lefen ki. Yanzu ya za ayi? Za a kawo mi ki shi chan gidan kun ne ko ya?

"Baaba Sabuwa duk yadda ku ka yi" ta faɗi hakan ne saboda ko kaɗan maganar lefen bai sa ta ji raɗaɗin da ta ke ji ya ragu a zuciyar ta ba...

........................

Yana shigowa Daddy ya kirashi tambayar sa yai ko ya je ya duba Mom ya ce bai je ba.

"Yanzu Najeeb ka kyautawa kan ka, da girman ka da ilimin ka amma ba za ka kyautatawa mahaifiyar ka ba. Duk abinda ta yi ma ka bai kai ace tana kwance a asibiti yau kwana uku ka kasa zuwa ka dubata ba. Najeeb tsinuwa ka ke nemawa kan ka?"

Maganganun Daddy su na shiga su na fita ta ɗaya kunnen ne, saboda ba jin su ya ke ba hankalin sa ya tafi wani wajen. Jini kawai ya ke gani malale a ƙasa ga kuma gawar Aisha...

Daddy ya gama ma sa wa'azi sai Najeeb ya tashi ya fita ba tareda ya ce komai ba...


Tuƙi ya ke amma zuciyar sa na tuno ma sa abun da ya faru shekaru da su ka wuce. Duk da yanzu ya girma kuma ya san ƙaddarar Aisha ne ta zo da haka amma wannan trauma ɗin da ya dasu a ransa tun yana yaro ya ƙi sake shi...

***

Cikin Aisha na wata takwas abin ya faru. Immediately Adam ya saki Nabilah ta tattare yaranta ta bar ma sa gida. Sai dai hakan bai sa Najeeb ya dena zuwa wajen Aisha ba. Idan ya taso daga makaranta chan zai wuce sai dare ya dawo. Mom ta ma sa faɗan amma baya ji.
Ana haka sai ɗaya daga cikin ma su kula da Aisha ta yi tafiya saboda Maman ta da ta mutu. Ganin haka ya sa Najeeb ya dawo wajen Aisha da zama duk da kuwa akwai Mrs Beverly tareda ita. A kwana na uku da ya koma wajen Aisha, Mom ta zo da ƙarfin tsiya ta tafi da shi gida ta hana shi zuwa wajen Aisha. Abu da renon turawa sai ya fara maida ma ta magana akan ba ta isa ta hana shi fita ba, Ya fita da gudu.
Mom ta nemi restraining order daga kotu akan ba ta yadda ɗan ta ya je gidan Aisha ba saboda tana tunanin Aisha za ta ma sa lahani. Da ke Najeeb under 18 ne sai ya zama dole yana ƙarƙashin kulawar iyayen shi. Ranan da letter ɗin ta fito haka Mom da jami'an kotu su ka je su ka ɗauko Najeeb tareda faɗawa security ɗin gidan ko da wasa kar ya bari Najeeb ya shiga gidan.

Daren ranan yai wani mummunan mafarki akan Aisha ta mutu hakan ya sa da safe ya kira Daddy da ke Belgium a kan ya sa baki yana son zuwa wajen Aisha.
Mom ta ce indai ya na America yara za su zo wajen sa amma Yaran ta ba za su je wajen Aisha ba. Da Najeeb ya fita school bai je ba sai da ya fara biyawa wajen Aisha ya ga tana lafiya kafin ya tafi.
Yammacin ranan da ya dawo ya samu Mom tana masifa akan Aisha ta dameta da kira. Najeeb bai kulata ba sai da Najma ta dawo ta ke ce ma sa yau ta ji tausayin Aisha domin ta kira kusan so biyar amma saboda ba ta magana ba ta iya ba da saƙon da ta ke son faɗa ba. Ƙila tana son ganin ka ne.

Hankalin Najeeb ya tashi, tunda su ka raba gida Aisha ba ta taɓa kira ba. Ta kira sau biyar kam yana nufin tana cikin matsala ne. Haka ya fita da gudu ya je ya ɗau keken sa ya tafi gidan Aisha duk da kuwa Mom tana ƙwala ma sa kira akan ya dawo.
Da ya je gidan tun daga falo ya fara kiran Aisha amma ba ta fito ba ya duba Mrs Beverly a kitchen ba ta nan sai ya haura sama da gudu. Kai tsaye ɗakin Aisha ya shiga. Amma mi sai ya ji kukan jinjira, yana duba gefen sa ya ga Aisha kwance ga jini duk ya ɓata wajen. Irin jinin da ya gani sai da wani jiri ya kusa kada shi ya dafe gini na wasu mintuna kafin ya ƙarasa wajen ta yana jijjigata amma ba ta tashi ba. Cikin kuka ya je ƙasa da gudu ya kira emergency line na police...

Yana tsaye aka zo aka ɗauke gawan Aisha, duk abinda idon sa ke sa ma sa shine Mom ce ta kashe Aisha. Ranan shima asibiti ya kwana dan yana tsaye a wajen bayan ansa gawar Aisha a mota ya faɗi ya suma...

Ko da bayan autopsy na Aisha ya fito kan ba kashe ta aka yi ba, haihuwa ta yi ita kaɗai jini ya tsinke ma ta kuma rashin Mutum a kusa da ita ya sa ba a kawota asibiti da wuri ba har ta mutu.
Najeeb bai daina ganin Mom a matsayin wanda ta kashe Aisha ba. He was very traumatized a lokacin da har ta kasance baya iya bacci sai da magani. Ya jima yana visiting therapist kafin daga baya aka ce ya dawo normal amma still a hakan bai koma dai-dai da Mom ba.
Rasuwan Aisha ya sa Mom ta saduda da rayuwa, ta nemi Adam ya maidata dan ta kula da Najdah...

"She wanted her dead all along, she's evil" abin da ya faɗa kenan ya buga steering ɗin motar. Idon sa na buɗe amma duhu ya ke gani, yana ƙoƙarin saita motar ta shi wata babbar mota ta zo ta buge motar sa, motar Najeeb ta yi sama sannan ta dawo ta faɗi ƙasa...



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0️⃣3️⃣2️⃣





*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*


*wannan page ɗin na ki ne ke kaɗai Anty nah Surayyah. Wishing you health, wealth, peace, grace, mercy and joy amin. Allah ya ƙarawa rayuwarki ta Oga da ta yaran ki albarka amin. Happy birthday🍾🥂🎂*



Tana zaune sai cika ta ke tana batsewa, abu ɗaya ta sani shi ne ta ajiye aiki da Najeeb sannan kuma dole ta rama abinda Sabreen ta ma ta. Ba za ta bar karuwan nan ta sha banza ba.
Tun tana duba agogo tana jiran Najeeb har bacci ya ɗauketa akan Sofa...


Daddy kam bayan fitan Najeeb kiran matar sa yai su ka yi hira, da ke jikin tan da sauƙi, dan likitan ya ce za'a iya sallamarta gobe.

Ƙarfe shaɗaya na dare wayar sa ta fara ringing, daga kan gado ya sa hannu ya lalubota ya ɗara a kunne dan ko gama gane numban da ya kira bai yi ba.
Abin da aka ce ma sa ne ya sa ya tashi zaune yana maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju'oun jikin sa na ɓari.
Ɗaukan key yai ya fita daga ɗakin da sauri duk da kuwa pyjamas ne a jikin sa...


Tunda aka shigo da shi ake ƙoƙarin tsaida jini, yadda jini ke zuba a jikin sa da ma gefen kansa ka ce duka jikin sa zai tsiyaya zuwa ɗan ƙanƙanin lokaci.

Wani na ganin Najeeb Adam Jibo a jikin ID card ɗinsa ya gane ko ɗan waye, shi ya sa aka kira numban Daddy...

Yadda Daddy ke jinsa gani ya ke ba zai iya jira har Iliya ya taso daga BQ ya zo ya kai shi ba duk da an hana shi tuƙi da dare saboda idon sa.
Yana fitowa yana ƙwala sunan Malam Aminu maigadi akan ya buɗe gate, yadda ya ke kiran, shi kan sa Maigadi sai da ya tsorata... Ikon Allah ne kawai ya kai shi asibitin lafiya amma ƙila da shi ma hatsarin zai yi.

Yana zuwa aka ce har lokacin likitoci na kan sa. Jikin sa rawa ya ke bai iya zama ba yana safa da marwa zuciyar sa cike da addu'o'i. Tsabar rikicewa ko fitowa da wayar sa bai yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login