Showing 3001 words to 6000 words out of 145203 words

Chapter 2 - SAKATARIYA TA COMPLETE

Azizat   

13 Jul 2024

25712

wani cikin ya sa ta ajiye batun karatu a gefe tukunna. Ta cigaba da renon cikin ta.
Zaman Amina da Alhaji KB zamane na amana yana son Farida tamkar shi ya haifeta har lokacin da ta haifi Hamza bai taɓa nuna wa Farida banbanci ba. Alhaji KB ɗan asalin Jahar zamfara ne yanada 'yan uba amma a wajen mahaifiyar sa su biyu ne shi da ƙanwar sa Hannatu. Mahaifiyarsa ta rasu tun yana shekara shida. Uƙuba na matan uba ya sa ya koma wajen ƙanwar Mamansa da ke aure a Jos lokacin yana shekara sha ɗaya. Anan yai karatu ya zauna har ya kai matsayin da ya ke yanzu. Hannatu ta jima da rasuwa. Ta rasu jim kaɗan da barinsa Zamfara. Raliya ɗiyar Hajiya Aina'u mariƙiyar sa ya aura. Sai dai har Allah ya ma ta rasuwa ba su taɓa haihuwa ba. Haka nan bai ƙara aureba sai akan Amina. Sau biyu tak ya kai Amina Zamfara inda anan ta gane 'yan uwan Alhaji KB ba sa ƙaunar ta, shi ɗin ma abin hannunsa ya sa su ke ɗan girmamashi.

Abdul na da shekara biyu Alhaji KB ya rasu. Mutuwar da ta gigita Amina da Hajiya Aina'u. Lafiya-lafiya ya tafi Zamfara kawai sai yayan sa Ubaidu ya kira wai Kabiru ya rasu zazzaɓi ya sashi a gaba da dare kafin safiya ya cika.
Amina ba ta shiga tashin hankali ba sai da kwana ishirin kacal da rasuwan Alhaji KB 'yan uwan sa su ka zo su ka koreta a gidan sa. Ƙarshe a gidan su ta ƙare takaba. Kafin wata uku da rasuwar sa su ka saida makarantar sa da gidan sa da mafi yawancin kadarorin sa. Hajiya Aina'u da Amina sun yi ƙoƙarin shigar da ƙara Kotu sai dai tun farko da su ka yi yunkurin hakan aka rufe bakin su. Haka nan Amina wadda 'ya'yanta ke kira da Ummi ta koma gidan jiya sai dai wannan karan tana da ilimi daidai gwargwado da kuma wayewa. Wata makarantar ta nema aiki kuma ta samu da wannan ta ke yin hidimar yaranta da shi. Tsohon mijinta Ibrahim ya nemi ta yi kome saboda yanzu ya rabu da Kubura kuma Alhamdullillah matar sa Hafsatu tanada kirki. Ummi ta ƙi tace ita da aure har abada. Ba yadda Babanta bai yi ba amma ta ƙi ta ce aure huɗu da tayi a baya sun isheta. Yaranta uku na gabanta Farida, Hamza da AbdulMalik. Shi ma Faruƙ ya kan zo hutu wajen Ummin sa lokaci zuwa lokaci har lokacin a Kaduna ya ke. Hajiya Aina'u na ƙoƙarin taimakawa Amina da ɗawainiyar yara daidai gwargwado sai dai fa har yau 'yan uwan KB ba su waiwayeta ba balle su nemi taimakawa yaran marigayi. Gado da ya bari kuma babu batunsa dan tuni sunyi wasan kura da dukiyar sa.

Aisha Farida Salihu yarinya da ta taso da ƙiriniya ga surutu. Ba dai ka faɗa ta yi shiru ba. Kwata-kwata ba ta da tsoro, tana son umminta sosai gashi ba ƙaramin shaƙuwa su ka yi ba, idan ka ga suna hira tamkar wa su ƙawaye. Sau tari ma akan ɗauka ya da ƙanwa ne su. Tunda su ka koma gidan su Ummi, Farida ta dena zaman banza ganin dai yanzu ba da bane. Ta koyi kitso da lalle tana yi, ga saida kayan ƙwalama da ta ke yi a school. A haka har ta ƙare secondary school ɗin ta. Jamb ɗin ta na farko ba ta ci ba dan haka ta fara zuwa koyon computer a shagon ƙanin Umminta Ahmad. Ta koyi abubuwa da dama dan Alhamdulillah Allah ya bata ƙwaƙwalwa. Da ta sake Jamb ta tafi Federal polytechnic da ke Bauchi saboda UJ da ba ta samu ba. Business Administration ta karanta a ND da ta zo HND ta koma Marketing. Aisha Farida 'yar kasuwa ce tuƙuru. Dan tana makaranta ba ta zauna haka ba ita ce saida turare, takalma da jakukkuna. Ga shi duk hutu idan ta je Jos za ta saro gwanjuna ma su kyau ta zo tana sayarwa students. Wannan ya sa 'yan ajin su ke kiranta Aisha mai gwanjo.
Yanzu shekarar ta ashirin da uku, tana service a Yola. Tun a camp su ka haɗu da Yasir Sa'ad ɗa ga senator Sa'ad Babagana. A UK Yasir yai karatu. Da farko su na fita daga camp zai relocating zuwa Abuja Inda iyayen sa su ke sai dai soyayyar Farida da ya shigeshi farat ɗaya ya sa ya fasa. Hakan ya sa a Inda aka turata primary assignment ɗin ta shi ma ya je. Duk iya watannin da su ka yi tare Farida ba ta bashi dama ba. Tausayin sa ta ke ji ta girme shi da shekara ɗaya ita kuma tana ganin tsayawa soyayya da shi ɓata lokaci ne. Ga uwa uba kiran da Hajiyar sa ta mata akan ko da wasa kar ta amince da soyayyar Yasir saboda karatu zai yi hakanan akwai alƙawarin aure tsakanin sa da wata. Ita dai Farida ba dan tsoro ta ke baya-baya da shi ba ko kuma ta ƙi son sa ba sai dai bazata bawa kanta ciwon kai a kan Yasir ba. "Yaushe ma ka girma?" Abinda ta ke yawan gaya ma sa kenan.


*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0️⃣0️⃣2️⃣


Da dare baƙuwar number ya kirata, da ta ɗauka sai ga muryan Rayyan.
"Ɗankwassi! a ina ka samu number ta?"
"My Farida kenan, abinda ka ke so ai duk wuya duk rintsi sai ka samu"
"Chan ta matse ma ka" ta faɗi tareda kashe wayar.
Ya sake kira ba ta ɗauka ba. A hankali a hankali Rayyan ya cigaba da kiran Farida, tun tana ƙin ɗauka har ta koma idan ta ɗauka za ta surfa ma sa masifa, shi kam da gaske ya ke dan haka bai damuba duk abinda za ta ce ma sa shanyewa ya ke. Cikin sati uku sai da ya san yadda ya ja hankalin Farida har tana ɗan kulashi ta dena ma sa faɗa idan ya kira.
Ranan da su ka yi passing out ɗin su sai ga shi a Yola. Ta ji mamaki hakanan kuma ya ɗan samu matsayi a zuciyarta. Saboda Yasir ya haƙura da ita ya sa ta introducing Rayyan a matsayin saurayin ta. Yasir kamar ya haɗiyi ran sa saboda baƙin ciki haka su ka rabu da shi baran- baran. Ko sallama babu.

Rayyan Abdullahi ɗan Kano ne kuma ma'aikaci a Zenith bank. Ya je Bauchi ta'aziyar 'yar yayarsa da ta rasu su ka haɗu da Farida. Sosai ya ke jin Farida a ransa, tsiwarta da masifarta yana burgeshi matuƙa. Ya ɗau ɗamaran koyawa Farida son sa musamman da ya gane ba ta da wani tsayayyen saurayi. To ina za ta yi saurayi bayan masifarta kaɗai ya isa ya sa samarin su dinga gudun ta.


..................................

Isowar sa kenan cikin gidan a gajiye. Kai tsaye ɗakin sa ya wuce dan ya san Daddy ba ya nan balle ya je ya gaida shi. Ya na shiga ya danna SHS zuwa Main kitchen "lemon tea in 10minutes" ya faɗi tareda zama ya fara cire socks na shi daga nan ya cire gaba ɗaya kayan jikin sa sannan ya shiga toilet.

Adama ta zo haurawa ɗauke da tea ɗin Najeeb ta haɗu da Afrah da ke shirin haurawa saman. Ta duƙar da kai ta gaisheta, Afrah ta amsa a gatsine.
"A Ya Najeeb za ki kai wa?"
Adama ta amsa da "eh"
"Kawo zan kai masa" ta ƙarɓi tray ɗin daga hannun Adaman.
Ta cigaba da hawa stairs ɗin tana tafiya ƙarar takalminta na ba da sautin ƙas- ƙas- ƙas...

Tana jin ƙaran ruwa a banɗaki lokacin da ta ajiye ma sa tea ɗin a ɗakin, kamar za ta fita sai kuma ta samu kujera ta zauna tana jiran sa. Kusan minti biyar sai ga shi ya fito ɗaure da towel. Ya na faman goge gashin sa da ɗan ƙaramin towel ya ganta ta ƙura ma sa ido.
"What the fuck! Mi ki ke yi a ɗaki na" Ya daka ma ta tsawa

Daburcewa ta yi ta fara kame-kame.
"Get out" ya daka ma ta tsawa ba shiri ta fita da gudu dan ta san halin sa sarai.

Sai da ya shirya cikin farar riga da wando baƙi three quater sannan ya buɗe laptop ɗin sa ya na duba wani aiki da Joseph sabon sakatarin sa ya turo ma sa. Yana dubawa yana sipping tea ɗin sa a hankali. Ba laifi Joseph yai ƙoƙari, da alama ya san aikin sa dan tunda ya fara ma sa aiki bai samu kuskure ɗaya cikin ayyukan da ya ke sa shi ba, sai dai da saura tunda dududu sati biyu da Joseph ɗin ya fara ma sa aiki kenan.


..........................

A hankali soyayyar Rayyan da Aisha Farida ta fara nisa, domin har ya je Jos ya gaida Ummi...

"Farida ba magana na ke mi ki ba"

"Ummi dan Allah ki haƙura da wannan zancen, zan dai dinga zuwa mu su akai-akai yanzu tunda na gama bautar ƙasa"

"Kin sani sarai har yau Alhaji Musa ni yake ɗaurawa laifi akan na raba ki da dangin Baban ki. Sun fi ni iko da ke Farida"

"Ni kan Ummi ki yi haƙuri, ba zan je ba, albarkacin Inna na ke zuwa mu su dama, kuma ta rasu shikenan"

"Ki yi yadda ki ke so Farida" Ummi ta faɗi tareda barin ɗakin.

Ita ta rasa dalilin da zai sa sai yanzu Baffa Musa zai takura wai ta koma wajen sa da zama. Ita yaushe ma za ta juri zafin Kano balle uwa uba rashin kunyar yaran sa. Dama dalilin Inna ke kaita Kano kuma tunda ba ta nan kowa ya riƙe kan sa. Da wannan tunani ta janyo purse ɗin ta tana irga kuɗin da ke ciki a karo na biyar kenan tun safiyar yau.

Sosai Ummi ta nuna ɓacin ranta akan ƙin zuwa Kano da ta yi, ko gaisuwarta yau da safe ba ta amsa ba.

"Nanna dan Allah ki cewa Ummi ta bar ni na yi zamana anan. Wallahi ba jin daɗin zaman Kano na ke yi ba"

Nanna da ke shan kunu da ƙosai ta ce " kin dai san da daɗewa Ummin ki tai alƙawarin za ki koma Kano da zaran kin gama makarantar ki. Alhaji Musa da kan shi ya kirata jiya ya ke cewa ya ji shiru. Ke idan ba ke bama ba saurayin ki ɗan Kano bane, idan ki ka je chan sai ku saita kan ku, kinga ba sai an sha wahala ba daga nan sai dai mu je bikin ki chan Kanon"


Ta turo baki tana faɗin "Allah dama kun gaji dani. Ni dai ba zan je Kano ba"

"Ah to, sai ki kira Baffan na ki ki gaya ma sa ai"

Farida ta zumbura ba ki ta fice a ɗakin....


Cikin kwana biyar ta gama shirin ta tsaf, ba wai tana son zuwa Kano bane, sai dai tunda abinda Ummi ke so kenan dole ta yi shi. Ranan asabat ta wuce Kanon tsabar haushi ko kiran Baffa Musan ba ta yi ba balle ta sanar ma sa da zuwan ta.
A ƙofar gida ta haɗu da su Kamal yaran Baffan su na wasa, da gudu su ka zo su ka tareta sannan su ka tayata ɗaukan kayan ta.

Da sallama ta shigo tana ƙarewa cikin gidan kallo wanda ya sha sabon fenti da alama dai saboda bikin Hajara da Salima da za a yi ne.
Baaba Sabuwa ta fara gani wanda ihun yara ya sa ta fito daga kitchen. Duk cikin matan Baffa Musa ita Farida ke ɗan gani da mutunci saboda itace uwargida kuma ba laifi tana da kirki.

"Oyoyo mutanen Jos. Sannu da zuwa"

Gyalenta ta saƙala ajikin igiyar shanya tana faɗin "fatan mun sameku lafiya"
"Lafiya lau, ya su Ummin na ku?"
Daga kitchen ta ke amsa ma ta da lafiya. Sai faman buɗe tukwane ta ke yi tana neman abin da za ta sa a baka.

"Baaba Sabuwa ni kam har yanzu ba ku bar baƙar al'adar ku ba, ace abincin rana sai ƙarfe uku"

"Lah yanzu na ke son ɗaurawa ai"

Farida ta dubi wayar ta tana faɗin " a ƙarfe ɗayan!"...



Sai da dare Baffa ya sa aka kirata. A falon shi ta sameshi yana cin abincin dare. Bayan ya ma ta ya hanya sannan ya fara bayani " Aminah ta ce ba ki fara aiki ba dan haka zan sa Yakubu ya nema mi ki aiki a kamfanin da ya ke aiki ko za a dace kema ki samu. Kafin nan kuma ki cewa yaron da ke neman ki ya turo saboda mu san da gaske ya ke yi. Kin dai ga yanzu shirin auren ƙannen ki a ke yi, zuwa ƙarshen shekara ke ma ayi na ki"

"Ni dama na san dalilin cewa in dawo Kano kenan, ni Baffa ban san mi na tare ma ka ba. Kanata wani ƙannena-ƙannena, na ga su suka ƙi karatu su ka ce aure za su yi. Ni dana zaɓi karatu na yi kuma na gama ai sai a bar ni na ɗan sha iska kafin a fara maganar aure na"

Ya ma ta daƙuwa ya ce "Uban ki Farida, na ce kin ci ƙaniyar ki. Wato har yanzu ba ki bar rashin kunyar ki ba ko" .

"To Baffa ina zaman zamana a Jos, ka takura Ummi wai ta turoni Kano. Duk abinda na yi ai kai ka ji za ka iya..."

Marfin kwanon silver ya wurga ma ta ta kauce ba shiri. " ki kiyaye ni Farida wallahi zan mummunan saɓa mi ki. Tashi ki bani ware! Ja'ira kawai"

Sum-sum ta tashi ta fice a falon dan ta san ƙarshe zai iya marin ta ko ma ya daketa. Dan Baffa Musa akwai saurin hannu.


..........................

Ba ƙaramin kyau yai ba cikin shirin sa na riga da wando baƙi sai kuma blazer kalar navy blue. Ɗauke da briefcase ɗin sa ya sauko daga stairs ɗin cikin takunsa na girma da ƙasaita.
Ƙai tsaye wajen dining ya je inda iyalen gidan ke cin abinci. Ya sunkuya yaiwa wata budurwa peck a kumatu yana faɗin " good morning baby"

"Morning Big B" ta amsa tana ma sa murmushi

Itama Afrah da ke gefe ta ce " Good morning Yaya"
"Morning" ya faɗa a taƙaice.

Tea ɗin da ke gaban Baby ya ɗan ƙurɓa ya ce " sai na dawo ko"

Wata haɗaɗɗiyar mata da ke zaune opposite da Baby wanda tun saukowar shi idon ta ke kan sa ta ce "have breakfast with us, please"
A dararance ya kalleta ya ce "na gode Justice Nabilah"
Har ya bar falon ba ta dena kallon sa ba, zuciyar ta na ƙuna. Sai yaushe ne ɗan ta zai kira ta da sunan uwa? Sai yaushe alaƙar su zai dawo dai-dai kamar kowace uwa da ɗan ta? Shekaru sun ja amma har yau babu wata chanji tsakanin su.

Baby ta ce"Sorry Mom"
Justice Nabilah ta girgiza kai ta ce " kar ki damu Najdah" ta ƙaƙaro murmushin dole dan jaddada maganar da ta yi.
Ita dai Najdah jikin ta ne yai sanyi, har yau ta kasa gano dalilin ƙiyayyar Yaya Najeeb da Mom, wanda tun tasowar ta haka ta same su.
Tambayar duniyar nan ta yiwa Big B da Mom amma duka babu wanda ya bata gamsashshiyar amsa. Harta Daddy bai san dalilin wannan gabar ba. Tun yana faɗa akan wannan ƙiyayyar ta su har ya haƙura ya zuba mu su ido...

Tunda ya fita daga gidan kai tsaye wajen motar sa ya wuce. Wanda tuni aka fito ma sa da ita daga parking lot. Sau ɗari zai ɗau driver sau ɗari zai koresu. Shi ya sa yanzu kusan wata uku kenan rabon da ya sake ɗaukan driver. Shi ya ke tuƙa kan sa, ran da yake son yin aiki a cikin mota kafin ya ƙarasa office to zai sa drivern Daddy ya kai shi office.



*Najeeb Adam Jibo*

matashin da ya ke ji da kyau,kuɗi,ilimi da kuma gata. Ɗa namiji guda ga tsohon Ambassador kuma Professor Adam Jibo da Justice Nabilah Al-Jabir.

Adam Usman Jibo ɗan asalin ƙaramar hukumar Kumo ne da ke jahar Gombe, sai dai kasancewar tun rasuwan mahaifinshi ya dawo wajen ƙanin Baban sa da ke Kano da zama ya saka zamansa ya koma Kano. Alhaji Mustafah Jibo babban ɗan kasuwa ne da ya ke da arziƙo tun a wancan lokacin.

lokacin da Adam ke da shekara bakwai a duniya mahaifin sa ya rasu, dan haka zaman sa da shi da ƙannen sa mata biyu su ka dawo hannun Alhaji Mustafah , lokacin Mustafah da matar sa shekarar su takwas da aure amma basu taɓa haihuwa ba. Sun riƙe Adam da ƙannen sa Ruƙayya da Fatima tamkar 'ya'yan da su ka haifa. Sai da su ka shekara goma sha biyar da aure ba haihuwa sannan Hajiya Mama wanda haka su Adam ke kiranta ta dage akan lallai Alhaji Mustafah ya ƙara aure ko za a dace.

Wata ƙanwar maƙocinsa kuma amininsa ya aura. Budurwace dan a lokacin da aka yi auren su shekararta shashida. Cikin ikon Allah watan Halima goma ta haifi ɗan ta namiji ya ci suna Sulaiman. Murna wajen Alhaji Mustafah ba a magana. Bayan Sulaiman ta haifi Abubakar sai da ta shekara huɗu kafin ta haifi Aisha wanda lokacin haihuwanta ta wahala sosai, tun lokacin haihuwar kuma ta ke jinya bayan sati uku ta rasu. Mutuwar da ta girgiza iyalen Alhaji Mustafah gaba ɗaya.

Hajiya Mama ba ta haifa ba amma ta ɗauki duka yaran tamkar ita ta haifesu, wanda ko kaɗan ba za ka taɓa ganin abu ɗaya da zai nuna ma ka ba ita ɗin ta haife su ba. Ba ma kamar Aisha wanda ita ta shayar da ita. Haka yaran su ka taso ba su da wata uwa da ta wuce Hajiya Mama. Kuma har lokacin da Alhaji da Hajiya Maman ba wanda ya banbanta tsakanin yaran marigayi Usman Jibo da kuma ainihin yaran Alhajin. Sai dai a hankali su ka fahimci Aisha ba ta magana, kurmiya ce. Anyita magani amma shiru, tana ji amma ba ta iya magana. Wannan lalura ta sa da Alhaji da Hajiya Mama su ka maida hankalin su wajen kula da Aisha sosai.


Da Adam ya gama primary school na shi Alhaji Mustafah ya kaishi Lagos karatu. Bayan kammala secondary school na shi a kings college da ke Lagos ya wuce Harvard yai degree ɗin sa a fannin International relation,daga nan ya wuce London Business

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login