Showing 102001 words to 105000 words out of 145203 words

Chapter 35 - SAKATARIYA TA COMPLETE

Azizat   

13 Jul 2024

25725

ya sa hannu yana tare gaban sa.

Farida ta fashe da dariya tana faɗin "to na nawa kuma. Bayan angama ganin komai"

Har lokacin bai ɗaga hannun sa ba ya ce " you're lying"

Tana cikin dariya Anas ya shigo.

"Wannan dariya haka, Farida ko dai ya tuno komai ne?"

Farida ta girgiza kai. As usual ya kawo ma ta wasu documents ne ta duba.

Anas ya gaida Najeeb wanda har lokacin yana kare gaban sa da hannu.

"Abokina ya dai? ko wani abu ya samu wajen ne?"

Pillow ya jawo ya sa a wajen kafin yai wa Anas wani mugun kallo.

"Mutumina ka godewa Allah da ya ba ka jarumar mace. Ba dan ita ba da kamfanin ka ta samu matsala"


"Ko a wanni duniyan ne secretary ta ke zama Oga oho?"

Ya kalli Farida da ido ya ce "what did you know Miss Salihu?"

Farida ta zaro ido, shi kuwa murmushin yaƙe ya mata ya maida hankalin sa kan Anas.

Abubuwa dayawa ne ke yawo a cikin ƙwaƙwalwarta. Kenan Najeeb ya tunata, komai ya tuna? ko kuma dai ba komai ba.

"Alhamdulillah mutumina. Ka tuna Miss Salihun ka, the stubborn Miss Salihu"

"Ko ba Miss Salihu ba ne ta sa min superglue a seat?"

Anas ya kwashe da dariya. Ita kuwa Farida jikinta ne yai sanyi.
Najeeb ba wai ya tuna abin ba ne da kan sa. Ranan ne Najdah ta nuna ma sa video ɗin da Anas ya nuna mu su ranan birthday ɗin sa, yana gani kuma wassu abubuwa su ka dinga dawo ma sa gameda Farida, musamman lokacin su na office...

Bayan Anas ya tafi, Farida ta ce " My Champ ka tuna komai ne?"

"The last time i remember ba da wannan suna ki ke kirana ba. What changed?"

Da gayya ya gaya ma ta haka, shima rama abinda ta ma sa ɗazu yai.

"Saboda..." sai kuma ta kasa magana.

Ranan gaba ɗaya gwiwarta yai sanyi. Duk yadda ta yi dan ta fahimci ko ya tuno komai na rayuwar su amma ta ka sa. Sai ya dinga gwaleta idan ta tambayeshi...

Washe gari da safe ƙarfe goma sai ga Lukman. Bayan ya yiwa Najeeb ya jiki sai ya ke faɗa ma sa cewa gaskiya ya riƙe Farida da kyau domin ta ma sa abinda ba ko wacce macce ne za ta iya yi ba.

"Oh! and how do you know?"

Lukman ya ƙaƙaro murmushin dole ya ce "saboda na gani da ido na"

"Nagode da gaisuwa, Dr Lukman right?"

Lukman ya gyaɗa ma sa kai tareda barin ɗakin, chan ƙasan zuciyarsa kishi na cin sa...


"Shi kuma wannan daga ina ya ke?" Ya tambaya yana tsare Farida da ido

Ba tareda ta kalli idon sa ba ta ce "he's my ex husband"

"Ashe ma bazawara na aura ban sani ba"

Ɗago rinannun idanunta ta yi tana ma sa wani kallo. Abinda ma zai ce ma ta kenan wai bazawara. Anya za ta taɓa samun matsayi a wajen Najeeb musamman yanzu da bai gama gane kan sa ba...

...............................

Bayan anyi sunan ɗan Maijiddah da kwana uku AbdulWahab ya koma Lagos. Bai samu Aneesa a gida ba, dama ta ce ma sa Abuja za ta je. A washe garin ranan da ya dawo ta dawo. Ita ba ta ma san ya dawo ba...

Tana zaune a falo tana kallo tana cin pringles sai ga kiran wata ƙawar ta.

Bayan sun gaisa ƙawar ke tambayarta ya kishiyar ta.

" shegiyar fa haihuwa ta yi, namiji kuma"

Ɓangaren ƙawar ta ke ma ta faɗa akan ta yi sake da har ta bari Maijiddah ta haihu a gidanta.

"To ya zan yi Binta, kwanan baya har cikin ƙarya na ce ina da shi dan na samu attention ɗin AbdulWahab kuma na samu a lokacin. Daga baya na mata sharri akan ta tureni cikin ya zube. Da farko ya yarda daga baya ya ƙaryata zancen. I really dont know what to do again..."

Ko mi ƙawar ta ce oho. Aneesa dai cewa ta yi "ni kin san ba na son shige-shigen nan. Ka je ma duk su ci kuɗin ka a banza ba biyan buƙata"

Jayayya su ka fara yi da ƙawar akan zuwa wajen Boka, daga ƙarshe Aneesa ta kashe wayan tareda cewa za ta yi tunani akai.

"Nonye....Nonye"
Ta fara kiran mai aikin ta. Jin shiru ya sa ta miƙe tsaye, ai kuwa da sauri takoma ta zauna daɓas tana riƙe baki.

"Sweetheart" ta faɗa baki na rawa.

Yana tsaye ya harɗe hannuwan sa a ƙirji yana kallon ta, idon sa yai wani irin ja.

"Aneesa why? Why? Ki rasa abinda za ki yi sai ƙarya"


"I can explain AbdulWahab, please" ta faɗa tana haɗa hannuwan ta biyu.

"Wajen Boka ko, ki je Allah ya bada sa'a" yana faɗin haka ya haura sama.

Jikin ta na rawa ta tashi ta bishi da sauri...

Buga ƙofar sa ta ke yi amma bai kulata ba balle ya buɗe, ta zauna a bakin ƙofar tana ba shi haƙuri tana hawaye...

Kwanaki uku su ka gifta amma kalma ɗaya ba ta ji daga bakin AbdulWahab ba. Ta yi kukan ta bada haƙurin amma bai ma kulata ba balle ta san ko ya yafe ko bai yafe ba.
A rana ta biyar ya ce ma ta idan har ta zaɓi zama da shi to za ta ajiye aikin ta ta zauna ta kula da shi da kuma yaranta, amma idan ta zaɓi aikin ta to zai sawwaƙe ma ta.

It was a very tough decision for her. Tana son AbdulWahab tana kuma son aurenta. Duk da dai ta san ba ƙaramin asara za ta yi ba idan ta ajiye aiki amma kuma ba za taɓa zama bazawara saboda aiki ba. Ta kira Mama neman shawara, inda Maman ta ce ma ta ta zaɓi abinda ta ga ya fi ma ta, amma ta sani ba za ta taɓa samun wani miji kamar AbdulWahab ba musamman ma a shekarun da ta ke yanzu.
Ƙarshe dai shawaran da ta yankewa kanta shine ta ajiye aiki...

Duk da ta ajiye aiki hakan bai sa AbdulWahab ya koma ma ta kamar da ba. Cewa ma yai ta je ta bawa Maijiddah haƙuri. Girman kai ba zai bar ta ba, ta girmi Maijiddah sosai, kusan shekara shashida ta bata. Da ta ga uwar bari dole dai sai da ta kira Maijiddan a waya ta ba ta haƙuri. Maijiddah kam ta yafe tuntuni tunda mijinta ya gane gaskiya kuma ya yarda da ita ai an wuce wajen... kafin Aneesa ta samo kan mijinta sai da ta kai wajen wata ɗaya...



.................................


Yau aka sallami Najeeb daga asibiti bayan kwanaki hamsin da huɗu da yai da farfaɗowa. A report ɗin da su ka bayar sun nuna cewa ba shida matsala, a hankali zai dawo da dukkan ƙarfin sa, haka kuma bisaga tambayoyi da kuma shaidar 'yan uwansa sun tabbatar da cewa ya tuno kaso tamanin na rayuwar sa ta baya kuma a hankali zai ƙarasa tuna komai...

Gefen sa na dama Farida ɗayan kuma Najdah a haka su ka fito daga asibitin Daddy da Mom kuma na gaba farinciki yana nan tattare da fiskokin su. Motar Farida su ka shiga, yadda Najdah ke maƙalewa Najeeb ba dan su Daddy na wajen ba da ta gaya ma ta maganar banza.

Maimakon Najdah ta bi motar su Daddy sai ta shiga tasu motar.
Su uku ne a baya sun sa shi a tsakiya.
"Dan Allah ki fita ki bamu waje, mata da miji suna son ganawa da junan su"

"Wayaga mata. Ba inda zan je. Yaya na son kasancewa da ƙanwar sa"

"Tunda sirrin miji da mata ki ke son gani, Bismillah" ta faɗa tana hawa kan cinyar Najeeb, kafin ya ce wani abu ta haɗe bakin su, yana so ya tureta daga jikin sa saboda Najdah da ke motar amma gangan jikin sa ya betraying ɗin sa. Maimakon ya tureta sai ma ƙara matseta yai a jikin sa, yayinda kuma hannunsa duka biyu su ka fara yawo tsakanin bayan ta zuwa hips ɗin ta.

"Dreba tsaya zan fita" Najdah ta faɗa tana jan tsaki.
Sun fito daga gate ɗin asibitin kenan ko nisa ba su yi ba.
Ya samu waje yai parking

"Karuwa kawai" ta faɗa tareda banko mu su ƙofar motar.
Abdullahi dreba ya fara dariya ƙasa-ƙasa yana faɗin "to kema miji ya kwanta a asibiti tsawon watanni ba lafiya, yanzu ya samu lafiya ki zo ki liƙe ma sa, ai duk abinda ki ka gani ke ki ka jawo"


Lokacin da ta ji Najdah ta fita ta fara ƙoƙarin janye bakinta.
"My Champ" ta faɗa cikin sarƙewan numfashi tana nuna ma sa ƙeyar dreba wanda bawan Allah kam kiɗa ma ya sa a motar ya ƙure volume sosai, dan kar kunnen sa ya jiyo ma sa ba dai-dai ba.

Kallon-kallo su ka fara yiwa junan su, idon Najeeb yai wani ja guguwar sha'awa ta bugeshi.
Ya san a mota su ke amma kuma duk wani ƙoƙarin hana jikin sa aikata wannan abu ya ka sa, jikin sa har rawa ya ke yi. Ƙoƙarin tashi ta ke yi daga jikin sa gaba ɗaya. Ya maidata da sauri, "My Ch..." Najeeb bai bari ta ƙarasa ba ya jagoranci wannan kiss ɗin, wannan karan da zafi zafin sa ya ke yi, ya cire ɗankwalin ta ya sa hannun sa cikin gashin ta yana shafawa. Kafin ta ankara yai wani juyawa da ita sai gashi tana ƙasa yana samanta still bakin su haɗe da na juna. Ta san glass ɗin motar tinted ne amma kuma ko da Abdullahi dreba bai juyo ya leƙa su ba, ya san dole su na aikata wani abu a bayan motar.

Ƙoƙarin zuge zip ɗin doguwar rigarta ya ke ta yi saurin riƙe hannun sa. "A mota mu ke My Champ" ta faɗa lokacin da bakin su ya rabu. Ya jima yana kallon idon ta kafin ya tashi daga kan ta. Itama ɗin tashi ta yi ta ɗau ɗankwalin ta tana ɗaurawa. Tunda ya juyar da kam sa gefe bai sake juyowa ya kalleta ba, numfashi kawai ya ke saukewa da sauri sauri. Ita kan kwantar da kanta ta yi a kafaɗar sa tana ayyana abubuwa dayawa a ranta...

Najdah kiran Mom ta yi akan su dawo su ɗauketa, da ke motar su ta riga ta yi nisa.
Cikin Daddy da Mom ba wanda ya tambayi dalilin da ya sa ta sauka a motar su Farida. Tunda dama tun farko bai kamata a ce ta shiga ba. Ta zauna a gaban mota sai tsaki ta ke yi tana ƙara jin tsanar Farida. Ita fa tun day one da ta ga Farida yarinyar ba ta mata ba, balle yanzu da ta ke jin ina ma tanada yadda za ta yi ta raba Najeeb da Farida saboda tsanar da ta ma ta...






*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣4️⃣2️⃣






Motoci ne cike maƙil a compound ɗin gidan lokacin da su ka shigo.
"Ya na ga gidan ya cika haka?"

Juyowa ya yi ya kalleta kallon irin kin fini sani ai.

Wayarta ta ɗauko ta kira numbar Mom.

"Mom gidan a cike sosai kaman wanda ake biki?"

"Dear, Walima ce za'ayi"

"Oh"

"Gamunan ma mun iso"

Katse wayan ta yi tana jira motar su Daddy ta shigo.

"My Champ" ta kira shi a hankali

Ɗaga ma ta gira yai.

"Wai an shirya ma ka Walima. Yadda aka cikan nan na san za ayi hayaniya, ko mu wuce kawai ka je ka yi wanka ka kwanta?"

Girgiza ma ta kai kawai yai.
Sai da Mom ta zo ta ƙwanƙwasa mu su window kafin su ka buɗe ƙofa su ka fito. Yana fitowa daga motan ya fara kallon gidan na su. Tabbas ya tuna gidan, hakanan kuma ya tuna cewa shi ya zana gidan, lokacin ma yana degree ɗin sa na farko ne.

Wannan karon Daddy ne ya kama hannun sa su ka nufi hanyar garden inda aka shirya Waliman.
Farida kam cikin gida ta wuce bayan sun yi musayar harara ita da Najdah.

Tana shiga ta tadda baƙi sun cika falon ƙasa, kusan ba zai fi mutum biyu ta gane a ciki ba sauran duk baƙin fiska ne a wajen ta. A tsanake su ka gaisa kafin ta haura sama.

Wanka ta yi da ruwan zafi saboda jikinta da ke ma ta ciwo. Bayan ta fito ta shafa mai ta ɗau wata atamfar ta riga da skirt ta sa. Dariya ta farayi lokacin da ta kalli kan ta a madubi ta ga yadda kayan ya ma ta ruwa. Gaskiya yanzu kam ta yarda ta rame sosai. Cire kayan ta yi ta je ta ɗauko wani Anarkali gown kalar abin cikin ƙwai, zanen adon flowers da ke jikin kayan kuma ja. Ba wani kwalliya ta yi ba powder ce kawai da kwalli, sai ta ɗan goga jan lipstick kaɗan a lips ɗin ta. Tana yafa gyalen tana murmushi. Ta ya ba za ta yi farin ciki ba, taya fiskarta ba zai zamo ma'abocin murmushi ba akoda yaushe. Kaman yau fa ta ke cikin nishaɗi saboda first kiss ɗin su, gashi duk da matsaloli da su ka fiskan ta, duk da ƙaddara da ta afka mu su. Allah ya sake dawo da wani ranan da su ka sake sharing kiss. Akwai lokutan da ta ke jin kaman ba zai tashi ba amma sai ta dake ta dinga maimaitawa kanta cewa ita da Najeeb akwai rayuwa mai tsawo a gaban su, rayuwa mai tarin farinciki da annashuwa, rayuwa da za su ga 'ya'ya da jikokin su.
Wani abu ta tuno da ya sa ta rufe fiskan ta tana murmushi. Tana kuma fatan Allah ya sa wannan rana ta iya jurewa ta daure ta faranta ma sa rai sosai...
Kiran Ummi ne ya katse ma ta dogon tunanin da ta tafi.

"Mun iso gidan na ku ki fito ki shigo da mu"

"Ummi na yaushe a gari? Shi ne ba ki ce za ki zo ba"

"Ba na son surutu ki fito yanzu, ba ni ɗaya ba ne harda su Baaba Sabuwa"

"Yeeeeh, ganinan zuwa"...


Taro ne da ya haɗa manya-manyan mutane, 'yan uwa da abokan arziƙi. Wanda aka gayyata da wanda su ka zo gayyar soɗi duk an cika garden ɗin maƙil. Manya manyan tents huɗu aka kafa amma sun cika maƙil har ma wassu ba su samu wajen zama ba.
Abinci kam Masha Allah domin anyi varieties kala-kala, caterers aka ɗauko su ke serving mutane abincin.

Malami aka kira ya fara buɗe taro da addu'a kafin Daddy ya yi jawabin godiya da kuma farinciki da ya ke ciki a yau. Daddy yai hawaye lokacin da ya ke bayyana halin da su ka shiga da Najeeb ya shiga coma, tun ana irga kwanaki da satuttuka aka koma irga watanni, daga ƙarshe ma da Allah ya tada shi sai da aka yi kusan wata biyu cur kafin ta kai har yau yana tafiya normal, yana magana yana kuma gane mutane, gaskiya abin godiya ne. Bayan ya gama jawabi aka kira Najeeb. Najeeb ya karɓi mic yai taƙaitacciyar jawabi wanda godiya ce ga dukkan wanda su ka taya shi da addu'a da kuma wanda su ka dinga ware lokutan su mai muhimmanci su na zuwa dubashi a asibiti bayan sun san ba ganin su zai yi ba balle ya ji su. Har ya miƙawa MC mic ɗin sai kuma ya ƙarɓa ya ce "Aysherh Farida Salihu should please come here"

Farida na zaune kusa da su Ummi ta ji abinda ya ce. Dama tunda ya fara magana hankalin ta ke kan shi.

"Mrs Jibo" ya sake kira.

Duƙar da kan ta ta yi tana ƙoƙarin danne hawayen da ke shirin zubo ma ta.

"Farida ba za ki je bane?" Muryan Ummi ya doki kunnen ta.

"Mrs Jibo please come out" ya sake maimaitawa.

A hankali ta ke tafiya kan ta a ƙasa, ba wai kunyan mutanen wajen ta ke ji ba. Abubuwan da su ka faru ne su ke mata zirya a ƙwaƙwalwar ta.

Tana isowa wajen da ya ke ta ɗaga ido ta kalleshi, shi ma ɗin ita ya ke kallo. Hannunta ɗaya ya kama ya jawota kusa da jikin sa sosai.

"Ga wanda ba su san wacece wannan ba, ko su ke tunanin minene alaƙata da ita. To dai Aysherh Farida Salihu sakatariya ta ce"

Wurin ne ya ɗau hayaniya, domin dayawa sun san Farida matar sa ce.

Ɗan murmushi Najeeb yai wanda ya ƙara bayyana kyaunsa.
Ƙirjin Farida ya fara bugawa da sauri-sauri.

"Then she became my wife. Auren mu bai cikata wata biyu ba na yi hatsari na shiga coma, i was unconcious for months. Kun san mi ta yi?"

Aka haɗa ba ki aka ce a'a

"Ta jira ni, ta kula min da gida da dukiya, ta aiwatar da duk wani responsibility da mata za ta yiwa mijin ta. Ba ta gujeni ba, ba ta ƙyamace ni ba, ba ta kuma nemi rabuwa da ni ba in my vulnerable state. Ba ko wace mace ba ce za ta iya abinda Aysherh ta yi. Ina so ku sani cewa Aysherh jaruma ce, she always fight and she always win"

Ya kalli Farida da ke kallon ƙasa idon ta na hawaye, ya sa hannu ɗaya ya goge ma ta hawayen da ke fiskar ta.

"Thank you Aysherh, Thank you for everything"

Fashewa ta yi da kuka me haɗe da dariya, Ya jata jikin sa ya rungumeta. Gaba ɗaya wajen aka sa tafi...

Anyi ruwan hotuna kam kamar ba gobe har sai da Najeeb ya gaji da tsayuwa. Ƙarshe da ya ji hajijiya na kama shi ya excusing kan sa ya bar wajen.

Yana ƙoƙarin shiga gida sai ga Sabreen ta biyoshi.

"Noory"

Juyowa yai ya kalleta yana jin haushinta na taso ma sa tun daga ƙasan zuciyar sa.
Lokacin da ta iso ya yi ƙoƙarin sake fiskar sa ya ce "Sabreen"

"Noory na san na yi laifi a baya kuma kana fushi da ni amma ka sani har yanzu ina son ka. Ba zan taɓa son wani kamar yadda na so ka ba. I love you Noory, Please give me another chance"

Kamar ya shaƙota ya haɗata da gini ya ke ji amma ya dake ya ce "i still have feelings for you Sabreen, but you know i have a wife now"

Marairaice murya ta yi ta ce ba ta damuba ta ƙara da cewa "I want to be your wife too, ko da ta biyu ce ba matsala"

Najeeb yai murmushi ya ce ta bari idan komai ya lafa zai wa su Daddy magana.

Murmushi ta yi ta zo za ta rungumeshi ya ce "we'll talk later"

Har ya shige ba ta bar murmushi ba. Ba ta ɗauka Najeeb zai ƙarɓi bukatan ta da wuri haka ba...

Yana shiga ɗakin su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login